Author : Hadiza D. Auta Category : Aysha Cool Novels
Baba!
Ya fad'a a rikice ainun.
Nan da nan kuwa baba ya sassauta ya dinga yi masa nasiha tare da nuna masa illar gooyin gatan da yake yiwa ya'yansa da sunan tausayi.
"Ka bari sun sangarce su an kai su d'akinsu su kasa zama lafiya da mazajensu saboda ba'a masu tarbiyar da ta dace da su ba".
Kan Asad na k'asa ya ce "Duk na d'auki matakin gyarawa, in sha Allah Baba za'a ga sauyi, a mini hakuri".
"To batun yarinyar nan k'anwar matarka lallai ta koma gaban gyatumarka duk abin da zaka yi mata na alheri ka aika mata zaman ya isa haka".
Cikin nutsuwa ya ce "Yanzu ma daga Kaduna na ke da kaina na mayar da ita gida. Dan Allah Baba ka yi hak'uri".
Baban ya numfasa ya ce "Ai yanzu tunda Bilki ta kwnaa biyu baka nemeta ba na gasgata Lallai Sulaiman ba ni kad'ai zai iya yiwa wulakanci ba Har Baba k'arami don kullum sai na yi kukan da mahaifinsa na da rai AI ba zai yi mini abin da ya yj ba, amma kai ma da gwada mini Sai na gane ashe fahimta ne ban yi daidai zai yi mini ko baban naku na da rai".
Faruk6ya kamu da tausayin Babansu don kuwa babu yadda za'a yi rana ta fito ta fadi Baba Bai yi maganar Sulaiman ba, kullum bakinsa da zuciyarsa na ambatonsa amma Shi dan tsabar iskanci ya yi tafiyarsa ya bar kowa da kowa babu waiwaiye. Ya k'udire a ransa duk ranar da ya dawo gida tabbas sai ya saka saka dorina ya zane shi ciki da Bai yasan ba zai cukume Shi da fad'a ba, amma bak'incikn da ya kunsa musu ya kunsawa baba Babba ba zai tafi a banza ba. Sai ya tabbatar masa dan babu baba Karami ba shine zai yiwa Baba Babba wannan dibar albarkar kuma ya share kalau ba.
Hankalin Asad ya kai k'ololuwar tashi ta ya ya baba zai kwatanta laifinsa da na Sulaiman din da ya shafe shekaru uku yana cikin ta hud'u da fantsama duniya? Kwanaki biyu kacal da bai zo ba, alhalin shima ta ci mutuncinsa, bayan haka ba cewa ya yi ta taho ba ai, inda wanine mijinta ya tabbatar a take za'a mayar da ita tunda zaman Abida a gabansu ba k'aramin dukansu yake yi ba gabad'ayansu.
Murya babu amo saboda tashin hankali ya ce "Ka yafe ni Baba, na ci darajar manzon Allah! Gabad'aya suka ce "S.A.W..
Baba ya nisa ya ce "Na hak'ura amma lallai ka yi gyara a gidanka, ka san me kake ci, sannan lallai ba Aysha kad'ai za'a aurar ba har da Hafsatu , itama Khadijah da take London tunda bana zata gama duk a had'asu a kawar da su. Idan babu maneman sai a nemo musu".
"To" Baba ya amsa a ladabce.
Sannan ba zan ce Bilki ta koma ba, Faruku ma ba zai saka baki ba, ka yi mata magana da kanka idan ta yarda zata bika ku koma haka nake so, idan ba ta yarda ba to lallai zata cigaba da zama har zuwa sanda zata sami nutsuwa. Save Restricted Contents Bot, [Sep 23, 2025 at 15:39]
Asad a zuciyarsa ya ce "Ai kuwa Wallahi ba zan yarda da wannan hukuncin ba tunda tauye ni aka yi da nuna son kai".
A fili muma ya ce "Na gode Baba Allah ya k'ara lafiya."
Daga haka ya mike ya nufi d'akin Momi . Jikinsa ya sake mutuwa a dalilin a shake ta amsa gaisuwarsa har da yi masa shaguben ba zai hucewa Baba Babba takaici ba, tunda tun yanzu murnarsa ta fara komawa ciki na kyakkwan zaton al'amura zasu daidaita a dalilin aurensa da Maigado.
Ya dinga bata hak'uri. Ta ce ita ba ruwanta amma tabbas ba zata saka baki Maigado ta koma gidansa ba tunda ba tsarin musulunci yake bi wajen yiwa yara tarbiya ba.
Idan ya shawo kanta ta huce ta ce zata koma shikenan.
A sanyaye ya bar dakin ya nufi na Abida. Ya ga bata nan. Ya tuna Ashe bata dawo daga asibiti ba. Ya fito ya shiga na Maigado ya tarar tana kwance. Ya Kira sunanta yafi sau biyar ta yi bakam ita ala dole barci take yi.
Murya a dakushe ya ce "Duk wulakancin da kika yi mini na zargina da yarinyar da nake yi mata kallon d'iya hakan bai isa ba sai kika saka k'afafuwanki kika bar gidana babu iznina, kika dauko diyarki, kika watsar mini da yara. Sannan kika mini sanadin fishin Baba da Momi ko?"
Ta yi shiru tana sauararensa zuciyarta ta fara karyewa don yadda yake magana babu kuzari tasan a rikice yake ainun.
*Dan Allah ku dinga dannawa labarin nan likes a YouTube.*
*Episode 1_10 Kawai ake buk'atar likes din.*
*Na gode muku gabad'aya Allah ya saka da alheri*.
*Surayya Dee*
✍
[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Ta cuno baki cikin fishi na sosai ta kawar da fuskarta daga kallon gabas ta mayar zuwa arewa.
Ya sassauta ya sake matsowa kusa da ita sosai ya ce "Zo mu tafi gidanmu kin ji Maigadona. So nake yau mu jijjiga gadon zinaren nan na ki da kyau. Ta so mana ai na ce ba zan sake ba, ki huce dan Allah kin sa duk ahalin gidan sun dau fishi da ni ba kuma wanda ya yi nufin taimakona a cikinsu."
Ko uffan bata ce ba. Ya gurfana a gabanta ya ce "Zo ki d'are na goyo ki, mu tafi gidanmu".
Dariya ta subuce mata, dattijo da shi zai wani ce ta ta zo ta d'are alhalin Baba babba ko momi zasu iya ganinsu. Wato dai shi namiji babu ruwansa da kunya.
Ta kawar da fuskarta tare da ce wa "Ba fa zan koma ba, ka yi tafiyarka, na riga da na gane ba zan iya wannan zaman ba. Ban iya yaudara ba, idan ma na iya ai ba zan yaudare ka ba Baban Bilkisu! Ka yi hakuri kada maganar nan ta sake cakalcakala mana al'amarinmu".
Ya mike tsaye cak. Ya zuba mini idonsa na saci kallonsa na ga har wani tsumuwa yake yi watakila da wani k'aramin d'an sanda ne ya bata masa rai da ya d'and'ana kudarsa domin ya fusata ainun.
Da kakkausan harshe ya ce "Kawai dama dai ki ce auren manufa kika shirya yi da ni?"
Ya yi mata kwarjini k'warai da gaske, tsoronsa da ta rayu da tashi ya taso mata.
Ta kasa ce wa komai.
Jin bata ce komai ba ya sanya ya sake maimaita tambayar da ya yi tabbacin amsatra yake dako.
Murya na rawa ta ce "Ba Hakan bane ko kadan. Ban same ka a yadda na zace ka bane. Na dauka ka aure ni dan kana sona kana kuma burin ka rayu da ni cikin adalci da jink'ai tare da wanke mini dukkan bak'inciki da na kwankwada. Sai dai tun tafiya bata yi nisa ba na gane manufar aurena bata wuce ace kana da iyali a idon jama'a ba, sai kuma dan ka sauke buk'atarka a duk sadda ka so. In ka cire hakan babu wani dalilin so, ko tausayina a tare da kai da na ga ni a aikace idan kuma akwai to tuna mini dan ni ban gansu ba."
Ya numfasa ya ce "Amma ai na ba ki hakuri, na ce zan gyara dukkan laifukuna, indai ba wani abu bane a ranki ai sai ki bani wata damar, idan ba ki ga sauyi ba, na amince da kaina zan dawo da ke gaban Baba babba cikin mutunci za'a yi komai tamkar yadda ya ba ni ke cikin mutunci. Da hankalinki Maigado ba za ki taimake ni ba, gabadaya fa daga Momi har Baban fishi suke yi mini. Ba akan komai sai a kan ki"
Hawaye ya b'alle mata ta ce "Saboda hakan ai na ce zan tafi na kama haya, ba zai yiwu na ce ba zan zauna da kai ba, sannan na zauna a gabansu indai ina da kunya da mutunci "
Kuka sosai ya k'wace mata, yinsa take yi tunda ga k'asan zuciyarta. Tare da ayyana dama dai ta yi hakuri ta rayu da y'ay'anta, da ta yi hakuri bata tirsasa mijinta ya sake ta ba, da yi zamanta a gidanta ta rayu da ƴay'nta. Idan mijin ya zo fine Idan bai zo bama fine. Don ta riga da ta saba da rik'e gida, dan haka ba zata gaza ba. To ko bai kawo komai ba. Tana da rufin asirin da zata rik'esu ba tare da ta ji komai ba. Amma yanzu ta bar yaranta suna ragaita a hannun yarinya k'ank'anuwa, ta zo tana hidima da yaran da suke ganinsu daidai da ita sannan babu godiya ko yabo a wajen mahaifinsu.
Kukan da take yi, ya yi matukar tayar masa da hankali domin dai ba yaro bane ya fahimci kukane na tsantsanin damuwa. Kukane mai nuna kololuwar gajiya da kunsar bak'inciki.
Jikinsa ya yi sanyi sosai ya ce "Dan Allah ki yi hak'uri! Gaggawa fa kika yi, dama zan d'auki mataki kuma yanzu haka fa na mayar da Laura gida tunda kin ce ba zata zauna miki a gida ba. Ki yi hak'uri ki yi mini uzziri."
Ita dai bata iya bude baki ta ce masa uffan ba. Ba kuma ta ji a jikinta zata motsa bare ta ba shi amsa ba. Don kuwa ita dai ta riga ta gaji da yadda take rayuwa cikin gidansa.
Ya yi rarrashi, iya rarrashi amma bata tanka ba.
Ya gaji ya zauna yana fad'in "Innalilahi wa inna ilaihir rajiun! Ya dafa kansa da alamu suka nuna juya masa yake yi ko kuma ciwo mai tsananin gaske.
[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: "Murya babu amo, kuma cikin bacin rai ya ce "Da kina sona Bilki na tabbatar za ki yi hakuri da dukkan laifukana, za ki jure, bare na ce ki yi hakuri zan gyara. Amma kin kafe na tabbatar da ace Faruk kika aura za ki yi hakuri da matsalar da tafi wannan tsanani a tare shi, na kuma yi imani kin ci karo da matsalolin da suka fi wannan nauyi da tozarci a cikin aurenki da yaron can, amma ba wanda ya taba ji ko ganin kin yi yaji kin bar gidan duk da k'arancin shekarun da kike da shi a lokacin.!
Duk da a cikin kuka take sai da maganganunsa suka yi mata dabaibayi, suka nemi d'arsa mata tausayinsa tare da haifar mata da sanyi jiki magashiyan.
Bai jira jin ta bakinta ba, ya sake tsananta rukon hannunta ya ce "ki ji tausayina Maigado. Kin sani tun kina budurwa nake son ki, dan haka zancen ki ce ba dan ina sonki na aure ki ba ai tatsuniya ce kawai irin ta shifcin gizo. Don a lokacin haihuwar Bilkisu da kin ba ni dama da tuni na aure ki. Amma kika bijire mini, kika yi tamkar ba ki gane inda na dosa ba. Na tabbatar zuwa yanzu an kwashe shekaru kusan sha takwas, idan kuwa hakane ai bai kamata ki ce bana sonki ba, ko da wasa ba kuwa, domin Wallahi tunda ga lokacin har zuwa yanzu ban huta da bugawar zuciya a dalilin soyayyarki ba. Na tabbatar Ubangiji ne ya musanya mini da ke a daidai lokacin da ya yi mini jarrabawar mutuwar uwar ya'yana, tunda ya sani ya jefa mini soyayyarki mai yawa a zuciyata, idona da gangar jikina gabadaya."
Na sassauta kukan da nake yi domin yadda yake magana kasan yana yi ne cikin tsantsar k'arfin zuciya. Domin tamkar ya rushe da kuka.
Tsawon lokaci ina shesshekar kuka yayin da ya yi bakam yana saurarona. Can ya numfasa ya ce "Tashi mu tafi".
Ko kwakkaran motsi ban yi ba a karo na biyu.
Ya saki hannuna daya ya dago hab'arta ya zuba mata ido sosai, itama ta zuba masa nata idanuwan da suka yi luhu luhu, suka yi jawur tsabagen kuka.
Ya yi kasa da murya ya ce "ki yi hakuri, daure mana, ki ji tausayina, idan har ke da kike jinina kin gaza akan lamarina da yarana wa kike tunanin zata rungumemu? Ba ni dama guda daya tak idan har ban sauya ba na amince da duk hukuncin da zaki dauka. Ina son ki, ina son rayuwa da ke, dan Allah ki daina tayar da hankalinki, me yasa kike son mayar mini da abin da yake cikinki sabon maraya, zuciyata zata iya bugawa idan ke ma na rasa ki tamkar yadda na rasa Rukayya.
Hawaye ya sake balle mata domin tabbas ya bata tausayi ta yadda ya raunana kwarai da gaske. Ta kuma gasgata shi mutum ne mai k'arfin zuciya na gaske.
Ya zaro tissue a aljihunsa ya hau goge mata hawaye yana ce wa "sorry Maigadona, very sorry!
Murya babu amo ta ce"Zan kwanta sai da safe"
Ya ce "Na dauka fa zamu tafine Sarauniyar shaiba! Ta girgiza kai ta ce "ka yi hakuri kaina ciwo yake yi, kasan kuma likita ya ce na dinga yin barci a wadace."
Nan da nan ya hau gyara mata gadon da shimfidarsa take a hargitse. Ta bishi da ido tana kallon yadda yake gyara mata gado mutumin da zai iya ajiye zaratan yan sanda dubu su yi masa.
Amma da kansa yake yi cikin rawar jiki da son ta ga gwanintarsa.
Ya dawo kusa da ita ya ce "za ki shiga bayi ne?"
Kai ta girgiza tunda fitowarta daga bayin ke nan ya shigo.
Ta mik'e ta d'ingisa ta hau gadon domin ji ta yi ƙafar ta yi mata tsami.
Ya tofe ta da addu'o'i tare da shafe mata jikinta. Tana jinsa yana ta faman laluben k'irjinta dan ya gane sune weak points ɗinta. Ilai kuwa nan da nan jikinta ya amsa ta nemi birkicewa. Sai kuma ta yi jarumtar saka hannu ta make masa tare da ce wa "Bana so, da iyayenmu a tare da mu kake yi mini haka?"
Ya mike daga durk'ushen da ya yi, murya babu amo ya ce "Na tafi Maigadona ki yi hakuri ki huce so nake gobe na zo mu tafi gidanmu. Kin san ba ni da juriya akan ki Balqees ki taimaki yayanki kin ji".
Ta gyara bargon sannan ta ce "Ni fa ba zan koma ina kallon yadda ka zuba ido yara na mini yadda suke so ba, ba zan koma kana daukan alamuran da suke hakkinane kana basu ba. Wannan shine gaskiyar magana ".
[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Ya fesar da iskar damuwa ya ce "Amma na ce "Zan gyara ko? Akan me ba za ki ba ni dama ba? Na gamsu na yi kurakurai, na kuma yarda zan canja menene kuma ya yi saura indai ba tada zaune tsaye kike so ba!
Ya fada cikin fishin da yake ta danne shi kar ya k'wace masa.
"Hmm" kawai ta furta dan kuwa ba yarda zata yi ta koma ba, sai an baje maganar nan a gaban manya. Ta riga da ta fahimci kawaicinta ba zai yi tasiri akan lamarin yaran nan ba. Ba wacce take mamakinta irin Hafcy. Yarinyar da shekarar da aka yi aurenta yar yayace, tare da tuna irin soyayya da take a tsakaninta da Hafcyn har su Aysha amma wai yau sun yi girman da suke ganin bata kai ta zame musu uwa ba.
Sun washi su bude ido su ga babansu ya shiga al'amarinta ko dakinta. Tunda dangin uwarsu sun zugesu, tare dafad'a musu rabon aurenta ya kashe musu uwarsu.
Ya juya ya tafi bai sake cewa komai ba.
Ta idar da azahar ke nan ta koma gado k'arfe shida na asuba.
Wayarta ta dinga gumza(vibration).
Ta saka hannu ta duba ganin Baban Bilkisu ne ya sanya ta ajiye wayar ba tare da ta amsa ba.
Amma tana katsewa k'iran ya sake shigowa.
Ta dauka ta yi masa sallama murya babu amo.
Cikin taushin harshe tamkar ba shine ya tafi da fishi ba jiya. Ya ce "Maigadona tafiya ce ta kama ni kwatsam zuwa Calabar dan Allah, dan Allah na roke ki, ki raka ni domin kowa da matarsa za shi. Ki mini wannan rufin asirin sarauniyar shaiba. Na gamsu na amince idan mun dawo nan zan dawo da ke ba gidana ba" .
Ta yi shiru tana tunani tare da nazarin yadda zata ce wa su Baba zata yi masa rakiya alhali ta ce musu ta gaji da zama da shi.
Ya tausasa harshe ya ce "Pls sarauniyar shaiba ki kubutar da ni kunyata a idon magauta. Taron karramaq manyan jaruman tsaro za'a yi ki taimake ni, alk'awari na yi zan dawo da ke inda na d'auke ki."
Ta numfasa ta ce "To me zan ce wa su Baba?".
Da sauri ya ce "Kawai ki fad'a musu na roke ki za ki raka ni Calabar za'a yi bikin karrama mu".
To yaushe za'a dawo?
Yini ne kawai, ya yi tsananin gaske ne a tsallaka gobe".
Ta saki ajiyar zuciya ta ce "To".
Dad'i ya ratsa shi yana ganin nasara a k'udurinsa.
Ya ce "Ki shirya jirgin k'arfe goma na safiyar nan zamu shiga. Zan sanarwa da su Baba. Me da me zan dauko miki?"
A sanyaye ta ce "To".
Dan gaskiya ta yi missing d'insa da kalolin jagwalgwalonsa masu tsuma zuciyarta da gangar jikinta gabad'aya.
Ta zarce da fadin "Sabbin abayas din nan da ka siya mini a wajen Umm Aslan mai Egyptian abayas har da rigar barcin nan da ka ce ta yi maka kyau".
"Na gane su, rigunan barcin ma ai kamar a wajenta ne ko?"
Ya tanbaye ta a hankali.
"Eh duka a wajenta ne lokacin da muka je Eggypt, ka tuna har da su jewelleries da su jakunan mata na k'asaita".
Ya amsa da fadin"Ai zan sake siya miki wasu don ina matuƙar son products din da take siyarwa dukkan kayanta da wahalar gaske ka ga irinsu a wani waje."
+2349162662750
+201121544627
A hankali ta furta na gode.
Tare da fad'in zan yi barci ko na 1 hour ne ".
Ya ce "Amma ki tashi kafin takwas don ki shirya, zan zo kafin tara kin ga kafin mu isa iyafot ma tafiya ce mikakkiya."
Murya babu amo ta ce"To"
Alarm ta saita ya tashe ta k'arfe 7:45, ta ajiye wayar a gefe sannan ta gyara ta yi kwanciyarta.
Bata fita ba sai da ta yi wanka ta shirya tsab , cikin jikinta ya bayyana alamun ta fara nauyi ke nan. Sosai ta yo kyau, filazal bata rabuwa da materials din Umm Nihla. Don sosai take jin dad'insu bare yanzu da ta yi nauyi ba abin da take sanyawa sama da su, shafal suke babu zafi babu takura. Gasu farashinsu daidai da aljihun kowa ne.
Yanzu haka ma tattaunawa take yi da ita akan ta dinga turo