Author : Hadiza D. Auta Category : Aysha Cool Novels
2384876855*
*Surayya Ibrahim*
*Zenith Bank*.
08032773332.
*Don samun damar karantawa cikin aminci a telegram*
*Teemah data service mtn monthly*
*1gb @550*
*2gb @950*
*3gb @1450*
*5gb @1700*
*8037026306 Fatima Musa Ibrahim opay*
Wadannan kalaman da ta amayarwa Anisa ya sanya Anisar jin itama ba zata iya zuwa gidan oga Asad ba. Don haka Saddiqa ce kawai ta zo, matar Ansari ma ba ta zo ba, bisa hujjar tana da tsohon ciki itama.
Amma shi ya zo ya duba Bilki tun tana asibiti ya ga twins sai dai bai zo wannan bikin ba.
Rashin zuwan y'anuwan Bilki wannan gagarumin taron da oga Asad ya shirya ya sake tunzura shi akansu tare da tayar masa da hankali, ya kuma fahimci gyaruwar zumuntarsu zai yi wahalar gaske tunda Bilki ta yi jinya, ta haihu amma basu zo ba saboda kasancewar shine mijinta. Da ya yi nazari sai ya gane gidansa ne ba zasu zo ba, tunda ko Ansar da ya saukaka gabar iya asibiti ya je, yanzu da a gidansa ko gidan Baba zai yi masauki sai bai zo ba".
Wannan rashin zuwan nasu ya tabashi fiye da zatonsa. Hakan kuma ya sake ragewa Bilki kuzarinta matuk'a da gaske.
Idan ta kalli yadda Basma da Alawiyya suke shiga suke fita a cikin hidimar sai ta ji hawaye yana k'wace mata, tare da fad'in ina ma Yaya Hamida da Anisa ne. Don sun fi Saddiqa kazar kazar. Duk da ba'a hutun makaranta ake ba, tare da Amrah da Faruk suka taho mata.
Ganin yaranta cikin nutsuwa da rashin takura ne ya rage mata damuwar rashin ganin y'anuwanta.
*Katsina*
Hawwah gabad'aya ta susuce a dalilin cikin ya yi mata shigar sauri d'iyarta Ifrah bata kai watannin yaye ba aka cire ta. Don haka kukan yarinyar da karatunn makaranta hadi da rashin cikakkiyar lafiya sai suka yi mata rubdugu.
Gabad'aya ta yi yaushi ita da Ifrah. Sannan tun makwanni biyu da suka shud'e da Sahal ya ji labarin haihuwar Bilki. Ya zama wani iri, ya rikice komai nasa ya sauya, ko kad'an bata gane masa. Yayin da shi kuma haihuwar tagwayen da ta yi a wani gida yake nukurkusarsa tare da saddakarwa ya rasa ta forever.
Ya tabbatar a yanzu Allah ya yi sakayya tsakaninsu duk da kuwa ta furta mass ta yafe masa.
Ita Allah ya bata wanda ya fishi komai, shima Allah ya bashi wacce ta dace da shi daidai da irin matsayinsa.
Nauyin da suka yi masa k'awanya babu kuma mataimaki ya sanya babu ta bayyana masa.
Amma dai cikin ikon Ubangiji nai rasa abinci irin wanda zai iya affording ba. Sannan yana biyan kudin karatun yaransa booko da islamiya. Hidimar Hajiya da ta Hawwah ma yana iya kokarinsa sai dai da yake bai iya harkar kasuwa ba sai iya aikin Slsai ya zama a takure yake ainun. Rashin samun nutsuwa daga wajen Hawwa ya sanya ya fara tsufa ba tare da ya kai shekarun da zai zama haka ba. Tsakaninta da shi ana zaune ne kawai. Amma ita kallon mayaudari azzalimi take yi masa. Duk abin da zai mata bata godewa bare ta yaba kokarinsa tunda ita fiye da hakan ya nuna mata zata samu. Daga lokacin da ta fahimci duk wani k'yallin da ta ga ni a tare da shi ba nasa ba ne, na matarsa ne tun lokacin ya fita a ranta tamkar kibau, tana zaune saboda bata da wani cikakken gata, sannan tausayin d'iyarta Ifrah na yi mata dabaibayi, tare kuma da son ta kammala karatunta da take yi a Katsina.
Tunda Bilki ta haihu ta ga ya rikice itama ta sake murde masa tana ta zungure zunguren maganar da take sake k'ona masa rai. Har zuciyarta ta daina kishin Bilki ko na y'ay'anta don ta gane ba kowacce mace ce zata yi kawaici kan bak'in cikin da Sahal ya shayar da ita ba. Ita da kanta idan ta tuna da kudaden Bilkin ya rudeta ta amince masa sai ta ji ta fashe da kuka tare da taya Bilki jin wani irin kuttu mai yunkurin fasa zuciya da mak'oshi. Kai maza na sharafinsu k'warai da gaske. Allah ya yafe musu don kuwa iyayenmu ne, garkuwarmune. Ya zamu yi to?😅
Na ce ba kina sallah akan lokaci kuwa?
Dan Allah kina yin walaha don yiwa kanki guzuri? Save Restricted Content Bot, [Oct 13, 2025 at 11:45]
Kina kiyaye hak'kin mijinki tare yi masa biyayya kan jiki kan k'arfi tare da yin imanin Allah ne ya kallafa mana yi musu wannan biyayyr?
Kina sane da cewar aljannar mace tafi samuwa ne da yadda mace ta yi hak'uri da biayyyar aure?
Amma ina fatan kin yarda su din a halittarsu polygamist ne?
Na ce kin gamsu ba abin da zai hana su so mace sama da guda?
Wai kuwa kin fahimci zurfafa soyayya hana sukunin zuciya take yi tare da haifar da wani irin zazzafan kishi mai saka azabben ciwo a k'irjinki a kullum?
Kin san idan kina da sana'a ba ki da lokacin kanki balle ki yi lokacin sakawa miji ido akan hurumin da ba na ki ba?
Yauwa na ce ba kina mayar da hankalinki wajen yiwa yara tarbiyar da zasu amfani kansu kema ki moresu a gobe, ko kuwa kina nan kina ta kushe ubansu a gabansu tare da fad'a musu ba ya yi miki adalci, yana cin mutuncinki?.
Kina mayar da hankali wajen yiwa yaranki addu'ar a tsare musu zuciya daga hassada da kyashin junansu?
Kina musu addu'ar a jefa musu tausayi da soyayyar junasu kuwa?
Abubuwan k'alubale masu tayar da hankali sun mana k'awanya amma basu dame mu ba sai lamarin kishi, akan me zamu fitini kanmu ne irin haka fisabidillahi, tunda har a aljanna ma mataye birjik za'a halatta musu🥲
Y'ar uwa kin yarda ke mai kyau ce a duk yadda kike?
Doguwa, gajeriya, siririya, lutiya, dirarriya ko ramammiya fara ko bak'a dukkanmu muna da kyau a yadda muke. Kada fa ki yi gangancin sauya halittarki don kawai ki burge Rijalu. Duk yadda kike ba zai hana su so wata ba, sai dai idan k'addararsu ce zama da mace d'aya.
Ni kuwa an fahimci wanda ma ya k'ara auro wata macen ya kawo ta gidansa yafi mutunci da kiyaye ka'idojojin shari'a akan mai zuwa yana yi miki tsome tsomen jijiyar nan da ake so da wasu matan banzan bila adadin?
Mu yi ibada, mu yi biayyyar aure, mu kula da tarbiyar yara, sai kuma mu k'ulla soyayya mai yawa da neman kud'i na halali.
Idan kuma kin bijire, kin kafe kin fi k'ulla soyayyar rijalu a ranki to fa ki sani at your own risk.
I come in peace my fans. 😅😅
Sati guda kenan da hidimar suna da murnar k'arin girma da ƙarin shekarun Oga Asad. Wanda ya yi daidai da wata guda da isowar tagwaye wannan duniyar mai cike da hargitsi.
Zuwa lokacin sun yi girma kammaninsu da juna sun sake bayyana.
Bilki kanta ta girgije ta yi kyau, tamkar ba mai shayar da yara biyu ba.
Alti na nan tana kula da ita da cima iri iri.
Komai suke bukata ga shi nan birjik tamkar banza.
Amma wata k'addara kuma zuciyarta ta kasa nutsuwa. Rashin zuwan y'anuwanta gidanta tare da korar Farha da oga Asad ya yi ya kasa barin zuciyarta. Ga shi ya dawo da ita amma abin na mintsininta tana ganin yarinyar bata da security a kowanne lokaci zai iya cewa ta bar masa gidansa tunda dai d'iyar Sulaiman ce. Ta kasa faÉ—awa Abida, ta kasa faÉ—awa Basma. Ta kasa faÉ—awa Yaya Hamida. Shiyasa abin yake cinta matuk'a da gaske.
Ta kuma kasa sakewa da shi duk k'ok'arin da yake yi mata kan jiki kan k'arfi.
Yayin da shi kuma yake zargin y'anuwanta ne suke zugata tunda a bayyane sun fahimtar da shi basa sonsa da gaske.
Don haka shima ya fara zuba mata ido tare da rungumar shariyar da take yi masa.
Gabad'aya ya zama desperate. Idan ya fita ayyuka ne a birjik a sabon office d'insa, idan ya dawo gida babu walwala.
Ga batun tafiyarsu Baba umrah, don ma ya barwa Faruk shige da ficen neman visa da sauransu.
Shirye shiryen tafiya umrah ya kankama.
Ranar ake jira kawai.
Ranar lahadi da yamma Abida ta isa gidan Bilki. Sun gaisa da Alti ta fice ta basu guri bayan ta turo Saudatu da abin motsa baki da kayan ruwa. Tana cikin sabbin maiakataj da aka kawo. Yarinya ce da bata wuce shekaru sha biyar ba.
Bayan yarinyar ta fita suka gaisa. Abida na kare mata kallo ta ce "Kin yi kyau kin sake fari amma kin rame fa uwar Farha".
Bilki ta ce "Wataƙila shayar da yaran nan ne amma lafiyata k'alau".
Ta numfasa ta ce "Nasan zuwa yanzu kin fara sallah zuwa na yi mu fara wuridin nan akan wanccan mutumin Bilki". Save Restricted Content Bot, [Oct 13, 2025 at 11:47]
Bilki ta yi murmushi ta ce "To Abida ai bamu samu sharadin da k'aidar ta cika ba. Iya kakanmu na uku muka san sunansa. Ko kin tambayi Baban ne?"
Ta girgiza kai ta ce na dai gano yanzu zuwa na hud'u mu fara a hakan zuwa gaba idan Baba ya samu lafiya ko da a Saudi ne sai na tambaye shi. Idan ya fad'a mini sai na fad'a miki ke ma".
Bilki ta ce "Hakan ya yi Dr bari na doro alwallah mu fara".
Abida ta ce "To don ni da alwallahta".
Bata jima ba, ta fito da alwallarta. Ta ce "Tuna mini ma abin da zamu karanta. Ta fad'a mata sannan ta bude jaka ta fito da jotter É—inta tana nunawa Bilki ta ce duba ki karanta dan ki rike".
Bilki ta ga an rubuta Sulaiman bin Isa, bin Garba, bin Bello bin Uzairu".
Dariya ta k'wace mata ta gaske ta ce "Abida a ina kika samo mana Uzairu ne?"
Ba wasa a fuskarta ta ce "Wallahi ba wasa Uzairu ne ya haifi Bello. Yanzu sunan uban Uzairu da kakansa ne ya rage sharadin ya cika. Da mu larabawa ne sunan ubanka na dari ma ba zai zama abin wahalar samuwa ba bare ubanka na bakwai kai Hausawa basa rik'e nasabarsu da kyau".
Bilki ta guntse baki.
Har ta yi shiru sai kuma ta ce "Ko dan irin haka kuwa ai ya kamata a dinga kiyayewa."
Daga haka Abida ta bude ledar da ta shigo da ita ta fito da wani irin rafkeken carbi ta fara ja.
Dariya kara kubucewa Bilki tana ayyana tsananin ya kai tsananin a wajen Abidan Baba don kuwa ba dan da idonta ta ganta da wannan carbin da ya kai guda dubu goma ba, zata yi musun idan ance Abida zata kalle shi.
Wato daukarsu ma kad'ai jidali ne. Amma Abida ta kinkimo ta zo da shi. Asalifa Abida na cikin jerin mutanen da suke bin mazahabar da basu yarda da jan carbi ba kwata kwata.
Dariyar da take yi bai saka Abida ajiye carbinta ba, illa iyaka ta tsume ta shiga jansa da dukkan zuciyarta.
Ganin hakan da Bilki ta yi ya sanya ta yi maza ta had'iye dariyar ta mike ta saka hijab sannan ta dauko counter dinta da fara wuridin kiranyen mijin Abida.
Sai daf da magharib suka kammala. Abida ta ce "Gobe a gida zan yi. Idan zan fara zan k'ira ki ke ma ki fara. Da ni yake zancen. Duk inda yake a duniya sai wannan addu'ar ta susuta shi ya dawo da kansa".
Bilki ta ce "Allah ya amsa Abida, Allah ya kawo mana shi lafiya".
Daga haka ta rakata zuwa kasa ta tafi da ledar carbinta ta shiga tsaleliyar motarta irin ta Bilkin da bata jima da isowa ba.
Ranar tafiya da safe Abida ta kawowa Bilki junior. Idanuwanta kozai kozai tabbacin kukan rabuwa da shi ta yi. Bilki ta daure bata ce komai ba ta karba. Sai dai tun tana gidan ta rik'e hannunsa suka hau saman Dady. Yana fad'in "Mahmah Ammi ta ce "Zan dinga kwana a nan tare da su Farha da Noor".
Da murmushi ta ce "Haka kuwa junior amma fa idan ka yi kuka to ba zasu yarda su yi wasa da kai ba bare su barka ka je d'akinsu."
"Idan na yi kuka twins ne friends dina?"
Bilki ta ce "Sune kuwa tunda sune masu kukan banza".
Ya make kafaÉ—arsa tare da fad'in "Ba zan yi kuka ba Mahmah ".
Daidai lokacin suka isa falonsa. Yana zaune daga shi sai singileti fara kal da boxer. Yana ganin junior ya mik'a masa hannu Yana fad'in young police come closer".
Junior ya saki hannun Bilki ya isa gunsa. Ya yi saluting d'insa. Oga Asad ya murmusa ya shafa kansa ya ce "Magajin Dady how far, ina momi ina Ammi?"
Momi na gida, Ammi kuma na d'akin Mahmah".
Bilki ta ce "kawo shi aka yi ya zauna kafin su dawo daga umrah". To bana son sai ta tafi ka ce ba zai zauna maka a gida ba".
Ya hassala ya kalli junior ya ce "Je wajen Ammi muna zuwa."
Yaro ya juya ya tafi bayan ya sake saluting oga Asad.
Ya mike tsaye ya nunata da yatsa ya ce "Billahillazi a wannan yanayin da nake ciki idan kika nemi tayar mini da hankali sai na miki cin mutunci. To idan na ce ba zai zauna din ba sai ya ya?Wacce bata barin abu ya wuce cikin dad'in rai. Sai anyi tsiya tsiya. Yaune last time da zaki mini irin wannan rainin ki fita a idona. Haba a yi mace da taurin zuciya ba ki iya komai ba sai rik'o da kullaci ba wani alherin da zan samu daga gare ki sai da b'acin rai, ni ba haka na saba ba, komai matata da girmamawa take yi mini sannan bata iya fishi da ni ya zarce na kwana da yini, amma ke zuciyarki bata da kyau saboda kina da wata Save Restricted Content Bot, [Oct 13, 2025 at 11:51]
manufar da kika boye a ranki. Bilki! Bilki! Bilki! Billahillazi ki kiyaye ni." Hawaye ya k'wace mata mussaman da ta ga tafkeken frame irin window size din nan mai d'auke da hotonsa da maimurabus dukkansu sanye cikin k'ananun kaya ya rungumota ta baya fuskarsu da murmushi. Ba a k'asar nan suka yi hoton ba tabbas. Ita sun yi hotuna kala kala a America da London amma kusan shekara bai sa an yi frame don ya saka a wajensa ba tabbacin ba sonta yake yi ba tunda gashinan ya girke na wacce yake so.
Da muryar kuka ta ce "Ni ce ba ni da alheri ko Baban Bilkisu?"
Ido cikin ido ya ce "Fad'a mini alherin da kika yi mini don ni ban san shi ba".
Ta jijjiga kai ta ce "Shikenan! Ta juya ta fice.
2ga watan 9 jirgin suka shiga Saudi Airlines ya tashi da su.
Kaitsaye a Madina suka yada zango. Dukkansu sun sauka da farinciki da walwala. Da yake shigar dare suka yi kaitsaye masauki suka isa wanda yake makwabtaka da babban masallacin Arrasool(S.W.A).
Da asuba suka tafi masallaci. Bayan an idar da sallah sun yi addu'o'i sannan suka isa wajen ziyarar Annabi da sahabbansa. Suka shiga rauda. Baba Babba duk da yana cikin yanayi na rashin sukuni sai da nutsuwar zuciya ta same shi. Haka ma momi haske da farinciki ya cikasu. Ba inda ya kai Madina sauakr da walwala da annushuwa a zuciyar musulmai mussaman ace ka shiga babban masallaci sai ka ji ka manta komai da kowa saboda tsananin farinciki da k'aruwar imani.
Basu bar masallacin ba sai da aka fara kokarin za'a rufe sannan suka koma masaukinsu suka fara barcin gajiya.
Kwanaki biyar suka yi a madina sannan suka shiga mota zuwa Makka. Kullum Sai ta yi wuridin kiranyen Sulaiman a wannan masallaci mai alfarma tana Kuma gasgata addu'ar zata karɓu tunda ba shirka take yi ba.
A daren da suka shiga Makka a daren suka sauke Umrah. A wannan lokacin ma sai da rafkawa Malam Sule kiranye. Kullum kuma ta what'sapp sai ta ce da Bilki kina yin wuridin nan kuwa?"
Ita dai Bilki dariya take yi tare da madaukakin mamaki don Har zuciyarta mamakin Abida take yi k'warai da gaske.
Tun washegari Abida da Yaya Farouk suka fara fita zuwa asibitin Saudi-Germany dan sanin tsare tsarensu na ganin likita.
Kwana biyu suka yi suna jele sannan aka basu ranar da zasu ga likita.
Kwanaki uku masu zuwa.
Washegari sun je Harami suna d'awafi kamar an ce wa Farouk juya sai kawai ya hango wani tamkar Sulaiman ya kammala dawafi ya fice da sauri. Nan da nan ya burzana ya bishi sai dai shige da ficen mutane a wannan wajen ya sanya ya bace masa b'at.
Ya rasa k'ofar da zai bi ya gan shi don kuwa zuciyarsa tana bugawa da k'arfin gaske tabbas da ba Sulaiman ba ne ba zai ji irin wannan bugun zuciyar ba.
Kan dole ya juyo ya dawo tare da adduar Ubangiji ya k'addara wahalarsu ta sanin yana raye ko a mace ne ta zo k'arshe.
Sai dai me? Abida ya tarar a gefe tana tsaye ta kasa cigaba da yin d'awafin. Da azama ya isa kusa da ita yana fad'in "Menene?"
Hawayen da ta goge ya sake k'wace mata. A sanyaye ta ce "Na rantse na ga Yaya Sulaiman yanzun nan".
Da hanzari ya ce "Wallahi nima na gan shi, shi na bi fitar nan da na yi, amma ya bace mini kamar kibau . Share hawayenki kada Baba ya ga kina kuka ya tambayi
ba'asi. Ko Momi kada ki faÉ—awa mun gan shi. Idan ba haka ba, Baba zai rikice ne sosai."
Yana rufe baki kukan ya k'wace mata tana fadin "Mun had'a ido da shi fa Yaya Farouk. Ganin na gan shi shine ya zabura ya fice. Ni ina nan ina ta yi masa addu'ar Rahma idan mutuwa ce ta sure shi, idan kuma a raye yake Allah ya tsare shi ya bayyana shi, ya yaye masa dukkan kuncin rayuwa. Ashe shi baya ko k'aunar ganina?"
Yaya Farouk ya ce "Na ce ki yi shiru ko. Tunda yana Makka idan Allah ya amince ba zamu bar garin ba sai mun sake had'uwa. Ai gamu a guri mai alfarma. Mu dage da addua. Na yi imanin tasirin addu'ar da muke yi ya sanya muka gan shi da idanuwanmu ai da bamu da tabbacin yana mace ko yana raye ma."
Da k'yar ya shawo kanta ta nutsu. A ransa sai mamakin yadda ta rikice sosai yake yi. Ko da yake mijinta ne uban d'anta. Save Restricted Content Bot, [Oct 13, 2025 at 11:54]
Har suka dawo gida Abida bata da kuzari duk wata jarumtarta ta nema ta rasa. Haka suka koma hotel dinsu momi na tambayar ta dalilin sauyin nata. Baba ya ce "Ah kya