DINGISHIN KWADO 3 & 4 COMPLETE BY HADIZA DA AUTA.txt

Author :  Hadiza D. Auta Category :  Aysha Cool Novels

Chapter   41 / 50

120K to 123K   out of 149K words

akan Bilki ba zata je da twins ba. Ta bar su tare da Alti a gida.
Daga shi sai ita suka zasu je. Kuma fuskarsa a daure ko ita bata ga fuskar tambayar dalilin da za'a bar yara a gida ba. A k'asan ranta kuma tana zaton tunda basu zo sun gansu bane da aka haife su shiyasa ya ce a barsu a gida baya son su gansu a yanzu.
Zuciyarta na hirji take shiryawa. Don gabad'aya ya koma yaya Asad din nan da kowa yake ji tsoron yin iyashege a gabansa, ba na yanzu da ya koyi kawaici da sassauci ba.
Addu'a kawai take yi kada Allah yasa rikicin da Yaya Sulaiman ya yi hasashen zai sake barkewa ya afku. Itama kwana ta yi tana addu'ar Allah ya sulhunta kullin da suke zukata su warware.
Save Restricted Content Bot, [Nov 5, 2025 at 12:26]
*Bojuwa herbs*
*Oder your kayan mata for women of class*
*Our products are healthy and original*.
*Tested and trusted*.
*Sanyi flusher dinmu zai raba ki da dukkan nau'in infection, ya kuma sabunta ki*.
*Ki zo ki saka order din ciccibin garari ko kazar sababi ki gode mini domin saiwowin da nake amfani da su na yi imanin ba kowa zai iya zuba kudi ya sarosu ba*.
*Duk wadda ta ci ciccibi sai tasan ta ci abu gangariya haka ma kazar sababi*
*Sanyi flusher kuwa best seller ne*
*Just DM for your order @08033773332*.

Karfe goma da rabi Hamida ta iso kuma Sulaiman da kansa ya je ya dauko ta a inda suka sauka da mijinta. Kafin ta fito daga hotel sai da mijinta ya yi mata nasiha tare da gargadin lallai ta yi biyayya ta tausasa harshenta a gaban Baba".
Ta ce "Zata kiyaye.
Haka Sulaiman da suka taho a mota ya dinga jaddada mata tasan me zata ce idan an bata damar yin magana. Kuma idan zata yi magana ta yi da lafuzzan da ba za'a ga raini ta yi ba".
Har falon gidan Sulaiman ya yi mata jagora Baba na zaune suan karyawa da Ansari.
Ya mik'e ya ce "Maraba da Hamida, sannu da zuwa. Sulaiman ka kyauta da ka kawo mini ita".
Kunya ta kamata ta tsugunna gefe tana fad'in "Sannu Baba" Don gabad'aya zuciyarta ta karye da ta ganshi yana yi mata maraba.
Ya ce "Taso ki zo kusa da ni".
Ba kuzari ta mike ta isa jikin kujerar da yake ta durk'usa kanta a k'asa.
Ya zauna ya saka ya dafa kanta ya ce "Hamida ya ya iyali, ya kwana biyu, ya ya mijinki?"
Ta kasa amsawa.
Murya ba amo ta ce "Ina kwana Baba ya jiki jikin?"
"Alhamdulillahi ya bayan rabuwa, ya kuma hak'uri?"
A matuƙar sanyaye ta ce "Alhamdulillahi.".
Sulaiman yana tsaye yana kallonsu.
Ansari ma ido zuba musu ya kasa cigaba da cin abincin da bai jima da zubawa ba.
Baba ya ce "Matso ki k'ara mana abinci tare zamu ci".
Bata musa ba ta matsa ta k'ara zubawa akan nasa.
Ya sauko kasa ya ce to saka mana a tsakiyarmu".
Hakan kuwa aka yi.
Suna ci momi ta shigo.
Ta bude baki cikin mamaki ta ce "A a Alhaji yau lallai kana cikin alheri dumu dumu".
Ya ce "Ke dai bari yau ga ni ga Hamida bayan tsawon lokaci ina mararin ganinta".
Sulaiman ya ce "Baba nima na saka hannu?"
Ya girgiza kai ya ce "A a zuba naka".
Sulaiman ya ce "To shikenan Baba."
Ana cikin haka Usman ya iso cikin kakinsa na soji. Don dai da ya je ya nemo excuse sannan ya taho gida.
Suka gaisa yana tsokanar Hamida da lallai batan kai ta yi.
Suka gaisa da Ansari da Sulaiman a takaice.
Baba ya zuba ido yana nazarin yadda amincin Usman da Sulaiman ya yi rauni sosai.
A haka Saddiqa da Anisa suka shigo, suma Baba ya karɓe su da walwala mussaman Anisa da ya jata jikinsa ya rungume hawaye na zuba masa. Itace k'arama kuma ita da Hamida ne bai sake saka su a idanuwansa ba tun rasuwar gyatumarsu sai a wannan ranar da Sulaiman ya kawo masa su.
Gata nan haka take kamar Abida yanayinsu daya tamkar cikinsu daya.
Abida ta iso sanye da labcoat dinta don sassafe ta je asibiti.
Tana ganin Sulaiman da y'anuwansa gabad'aya gabanta ya yanke ya faɗi. Idan har ya faɗa musu abin da ta yi to la shakka tasan komai ya b'aci ba zasu karbe ta ba. Idan kuma ya had'iye bai fad'a ba to da sauk'i.
Da walwala da kuzari ta ce "Yaya Hamida oyoyo".
Ta isa kusa da ita tana gaishe ta. Cikin sa'a ta amsa gaisuwar bata daure fuska ba.
Saddiqa da Anisa suka gaisheta ta amsa da fara'arta tana tambayarsu yaransu.
Haka ma Ansari ya gaishe ta, ta amsa da fad'in "Jiya na dawo dare ya yi, amma junior ya fad'a mini uncle d'insa ya zo".
Ya dan murmusa kad'an.
Ta kalli Sulaiman da yake cin abinci ta ce "Yaya Sulaiman an dawo lafiya?"
A takaice ya ce "lafiya lau".
Don ba k'aramin tunzura ya yi da ita ba da ta bata yi mass waya ba tunda ya tafi.
Ta mike tana ayyana Yaya Faruku da Dady ne basu iso ba, tunda ta ga Yaya Usman a waje yana amsa waya.
Faruku ya shigo dukkansu kowa ya gaishe shi, ya amsa yana tambayarsu yara. Save Restricted Content Bot, [Nov 5, 2025 at 12:37]
Baba ya kallesu ya ga sun cika gabansa.
Daidai lokacin waya Hamida ta d'auki k'ara.
Ta bude jakarta ta dauka ganin d'iyarta ce Ummu ya sanya ta fita waje.
Tana cikin wayar aka budewa oga Asad gate da ya tuko motar da kansa, Bilki na gefensa.
Har ya yi parking tana wayar. Suka had'a ido da shi ta yi kamar bata ganshi ba.
Zuciyar Bilki ta harba ta fara yi mata yake.
Ita kuma ta d'agawa Bilki hannu.
Asad ya shaka amma ya maze suka shiga cikin don gaisawa da su Baba.
Can oga ya tuna kwalin apple din su Baba. Har zai bawa Usman ya dauko ya fasa ya mike da kansa ya tafi daukowa.
Yana fita ya ga ta gama wayar amma ta dauke kanta ta ci magani. Wani irin abu ya yunk'uro masa. Ya wuce zuwa motar.
Ya juyo ya ga tamkar harara ta galla masa. Hak'urinsa ya k'wace ya dufafe ta da sauri.
Tana ganin haka ta yi maza ta juya ta shige falon ta tsallake kowa ta isa kusa da Baba ta zauna har tana cin tuntube. Baba ya ce "Nutsu, yi a hankali Hamida".
Asad ya shigo da huci yana ayyana ashe k'aryar rashin kunya take ji da shi. Ai tasan karonsu da ta tsaya, da ya nuna mata bata wuce ya bubbige ta ba.
Abida ta taso Salaha da take barci.
Ta fito. Duk yadda take da hak'uri sai da ta hak'ura da Hamida, ba irin bin ta da bata yi ba akan kada su yi gaba da juna amma Hamida ta toshe k'ofofin da zasu hadu ko su gaisa.
Itama har ta gaji ta shareta gabad'aya.
Sun gaisa sai dai ba yabo ba fallasa.
..
Yaya Asad ya bude taro da addu'a.
Baba ya yi gyaran murya ya yi musu sallama. Suka amsa a hankali.
Ya ce "Dukkanku nan kunsan abin da ya faru wanda bai shafi kowa a cikinku ba. Ni Babanku da kuma Maminku shaidan ya yi wasa da zukatanmu. Na kuma fahimci Ubangiji ya ba shi nasara ne akanmu bisa hujjar taka dokar da ya yi da kansa da muka yi.
Allah da kansa ya raba gado. Mu kuma Hausawa sai muke ganin rabawar kuskurene. A barshi a a had'e ko idan an raba din ma Babu rubutu Babu shaidu.
Tsananin shak'uwa da soyayyar da kuma yarda ya sanya ni da dan'uwana bamu yi iyaka aakn dukiyarmu ba. Abin da nake son ku fahimta guda d'aya ne, al'amarin d ya afku aya Allah ya buga akanmu don ya Zama izna Ga waɗanda suka had'a dukiyarsu basa yin rubutu kamar yadda Allah ya umarcemu. Addininmu na musulunci ba abin da bai kawo mana ba. Hatta bashi idan zamu yi a tsakaninmu sai da ya ce mu yi rubutu don kaucewa rud'ani, ayar da ta fi kowacce tsayi a cikin alkur'ani akan bashi da ka'idojojinsa ne. Haka nan Annabi ya yi ta jan kunnenmu tare da gargadinmu akan dukiya da jinimu da mutunci abin kiyayewa ne. Duk alummar da take tozarta amana d, take danne maraya, da alummar da take tauye mudu, da alummar da suke girmama dokar d'anadam sama da dokar Ubangiji, da masu cinye dukiyar maraya, da masu juyawa zumunci baya Annabi ya ce talauci zai yad'u cikin waɗannan alummomin. Zalunci Shugabanni zai tsananta don kuwa za'a koma rayuwa ne irin ta kashin dankali.
Har ila yau Annabi ya ce 'Duk alummar da suka tausayawa mata da k'ananun yara to zasu rabauta.
Annabi ya ce idan mata suka tsare farjinsu daga zina, suka yi sallau cikakkiya, suka yi biyayyar aure, suka barranta daga yin shirka kowacce iri aljanna ta zama wajabat a garesu."
Ya numfasa ya zarce da ce wa "Annabi ya ce "Bai yi zaton wahayi zai kammala ba tare da an saukar da ayar da zata ce makoci ya gaji makocinsa ba, saboda yadda Allah ya girmama sha'anin makwabtaka.
Cikin nasihohin Annabi da ya yi masu tsanani sun had'a da barranta daga shedar zurr don kuwa ya yi ta gargadi da babbar murya har sai da gwadonsa ya faɗi, don haka a kiyayi shaidar zurr. Kada ka yi shaidar abin da baka da tabbas, kada ka jinginawa wani sharri ko ka yad'a ya yi wani mummuna al'amarin da baka da tabbas din ya yi.
Shawara mafi girma da ya bayar ita ce kada mu zama masu fishi, kada mu zama masu yawan maganar da bata da amfani.
Sannan ya umarcemu mu bi uwa, mu kyautata mata, mu yi mata biyayya, mu bi uba mu godewa kokarinsa sannan idan sun kai shekarun girma mu ninka yi musu biyyaya duk abin da zasu ce kada mu gajiya ko mu yi musu magana a zafafe, uffan kada muce musu matuƙar ba mai dad'i ba ce. Save Restricted Content Bot, [Nov 5, 2025 at 12:40]
Har ila yau Annabi dai ya ce "Wanda baya sallah ba zai shga aljanna ba, wanda ya yi sanadin mutuwar mumini ba zai shiga aljanna ba. Wanda ya yanke zumunta ko aure ba zai ji k'amshin aljanna ba.
Jikin kowa ya yi sanyi tub'us da matashiyar baba a garesu.
Ya ce "Bana son tone tone, ba don komai ba sai don Annabi ya tsinewa wanda ya tono masifa. Don haka kowa ya warware zuciyarsa kada ya tono tahsin hankali. Ni dai ubanku ne gabad'ayanku. Duk wanda ya bata mini a cikinku Allah ne shaidar na yafe masa, duk wanda ya zo kusa da ni lallai ina tare da shi. Duk wanda ya yi nesa da ni to ina yi mass addu'a don duk sallar duniya sai na yi muku addu'a gabad'ayanku da iyalinku. Don kuma mutum ba ya yi da ni ai ba zan ware na ce ban da shi a addu'ata ba.
Na yafewa kowa duniya da lahira nima wanda yake ganin ban masa daidai ba to a yafe ni dan Allah."
Oga Asad ya ce "Baba dan Allah ka bada damar a tattauna cikin nutsuwa idan ba a amayar da gillinka da suke boye a zukata ba, ba za'a warware daga jin haushin juna ba, tunda na ga shaidan din ba shi kad'ai bane ya shigo cikinmu har da rundunarsa gabad'aya ya tattaro".
Baba ya yi shiru cikin nazarin shawarar Asad.
Ya nisa ya ce "Za'a tattauna amma duk wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira kada ya yi magana sai an ba shi dama. Duk yadda ka kai da son yin magana ba zaka yi ba sai an baka damar yi."
Kowa ya ce "To cike da girmamawa.
Oga Asad ya ce "Dan Allah Baba ina neman alfarmar a tambayar mini su Sulaiman gabad'ayansu me na yi musu, don a bayyane yake kowa a cikinsu a zafafe yake da ni".
Baba ya kalli Sulaiman ya ce "Ka ji me ya ce Sulaiman?"
Kan Sulaiman na kasa ya ce "Ya mana ba daidai ba ne Baba. Mun rayu a gidan nan muna ganin yadda kuke shugabantar da shi akanmu. Amma da wnanan tashin hankalin ya zo sai ya koma gefe ya ki taka rawar da komai zai daidaita kafin tafiyar ta yi tsayi. Sai kawai ya d'auke ka kacokan da sauran kannensa da ya gamsu k'annensa ne, mu kuma ko oho".
Baba ya ce "Hakane Hamida kina da matsala da yayanku ne?"
Kaitsaye ta ce "Matsalolima kuwa Baba. Ka ga na farko ya zo ya d'auke ka ya barranta mu da kai. Sannan bai zo ta'aziyar MAMI ba, sai na tafi a fahimtar don ta yi maka laifine, na uku da Abida ta bar gidan mijinta bai yi irin yadda kuke yi mana ba. Idan a lokacin baka da lafiya ai shi kam gar yake akan ƙafafuwansa, na tabbatar da ba Yaya Sulaiman ne mijinta ba, da ta dawo gida da sunan yaji da an mayar da ita ko bata so. Wadannan dalilan ya sanya na gane baya sonmu bai d'auke mu tamkar su Salaha ba. Shiyasa na hak'ura da shi, don ba zai yi mana adalci ba".
Baba ya ce "Ansari fa?"
Ansari ya ce "D'auke ka da ya yi a farko na gamsu lafiyarka ake nema maka tare da samar maka da nutsuwar da ta yi maka tutsu. Amma da mami ta rasu ka ce ka yafe mata ai da sai ku tausaya mana ka dawo gida don musan bamu rasa kowa namu ba.
Baba har nan na zo na gaishe ka tare da sake baka hak'uri. Na roki arzikin ka karɓa mini aure, na yi hakan ne don ka yarda ba ni da uban da ya wuce ka. Amma Baba ba wani a cikinsu da ya bika daurin aurena sai Yaya Usman wanda ba dad'in zuwansa na yi ba don ya budr baki ya yi fatan alheri bai yi ba. Kai ma baka zauna a gida kowa ya ganka ba, sai ka barmu mu kad'ai. Mami ce ta yi maka laifi to shi kuma Baba k'arami mai ya yi da aka cire mana rigarsa aka barmu tsirara? Kuma ni datse mu'amalar da suka yi damu na d'ora alhakin hakan akan Yaya Faruku tunda kowa a cikinmu nan ya gamsu Yaya Faruku nasa ne. Me yasa bai yi amfani da kyakkwar mu'amalar da yake da ita a tsakaninmu gabad'aya ba ya kawo daidaito sai kawai suka ware mu suke rayuwa isu isu a gari daya tare da mahaifansu."
Kuka ya sarke masa.
Hankalin Baba ya tashi ainun ya gano akwai k'amshin gaskiya cikin hasashen Ansari tabbas suma da irin nasu laifin a cikin rugujewar gidansu da mu'amalarsu bakidaya. Save Restricted Content Bot, [Nov 5, 2025 at 12:45]
Baba ya ce "A a ban da kuka Ansari share hawayenka ka cigaba da bayaninka. Yi hak'uri".
Ansari ya jima yana goge hawayen idonsa kowa na kallonsa ana ganin hankali ya ratsa shi sosai. Dama kuma idan akwia wanda mutuwar MAMI ta yi masa mahangurba to Ansari ne. Don gabad'aya ta saita shi tun lokacin ya zubar da komai don mutuwar wa'azi ta zame masa mai saka nutsuwa da nadama.
Ya kasa magana. Baba ya ce "Iya ni da Faruku ne bamu yi daidai ba?"
Ya girgiza kai. Ya yi jarumtar had'iye kukan ya ce "Baba Yaya Asad yana nuna mana son kai da banbanci ba dan kad'an ba a tsakaninmu da su Anty Abida. Ta ya ya munsan shine babba kuma nan gaba uba zai zama a wajenmu amma ya kasa taimakon Yaya Sulaiman. Shin ya yi laifin da ya cancanci a kashe masa aure ne bamu sani ba ko kuwa laifin MAMI ne ya yi sanadin da za'a bar matarsa ta zauna a gida alhalin ba sakinta ya yi ba?"
Kowa ya yi shiru ana ta auna maganganun a zuci.
Baba ya nisa ya ce "Bilki na yi miki tsallake na fara bawa Ansari dama sai na yi ta ganin shine babba ashe kaninku ne.
A sanyaye ta ce "Ba komai Baba.
Ya ce "Fad'i na ki damuwowin.".
Murya ba amo ta ce "Ba ni da matsala da kowa Baba".
Ya ce "Ke yanzu kin gamsu da yadda yayanku yake tafiya, haka kin gamsu Faruku akan daidai yake?"
Kanta na k'asa ta ce " So nake Yaya Faruku ya bude baki ya fadi abin da yake cinsa a zuciyarsa yana fad'a kuwa to ya huce domin duk danbarwar nan da ake yi bai ce kanzil ba, da kuma ya yi magana to da zai yi abinda ya dace na tabbatar."
Baba ya ce "To yayanku fa?
"Ba ni da matsala da shi".
Hamida ta ce "Ki dai ji tsoron zatin Allah Bilki ki fad'i wariyar launin fatar da yake yi".
Baba ya yi mata dak'uwa tare da fad'in "Hamida zan sab'ar miki, ba na saka dokar kada wanda ya yi magana matuƙar ba damar yin magana aka ba shi ba?".
Ta yi k'asa da kanta tare da fad'in "Ka yi hak'uri Baba ".
Baba ya kalli Salaha da take rik'e da biro da littafi ya ce "Kina rubuta korafin kowa ko?"
A nutse ta ce "Eh Baba."
"Ina Saddiqa?"
Baba ya tambaya.
Cikin sanyinta ta ce "Ga ni ".
"To Bismillah".
Kanta na kasa ta ce "Baba kawai ni babban tashin hankalina idan na hango gida irin gidanmu amma ya dare ya zama kufai. Idan na ji sha'awar na je gida sai na rasa inda zan dosa. Sai na yi kamar na zo nan sai kuma na tuna Yaya Asad ya dauko kune don ya barrantaku da mu, sai na fasa don ba ni da wajen zuwa".
Kuka ya k'wace mata na gaske.
Hankalin oga Asad ya yi wani irin tashin gauron zabi. Zuciyarsa ta shiga harbawa da sauri da sauri fiye da kima.
Gabad'aya ya ji kansa ya yi masa dundurus.
Kawai a zaune yake amma babu nutsuwa a tare da shi ko kad'an.
A wannan karon sai da Baba ya d'auki tissue ya goge fuskarsa.
Cikin jarumta ya kalli Anisa da take zaune kusa da shi ya ce "Ke kuma fa Anisa?"
Ta girgiza kai ta ce "Dangin miji na mini gorin gidanmu ya rushe wan ubanmu ya tafi da y'ay'ansa ya barmu saboda bak'in cikin uwarmu".
Muryarta ta karye. Ta yi shiru ta kasa cigaba da magana.
Tsawon lokaci ba wanda ya yi tari kowa tsit.
Sai can Baba ya yi gyaran murya ya sake yin addu'a da neman tsarin Allah daga sharrin shaidan da hargitsin zuciya.
Don ya fahimci gabad'aya yaran suna da hujjar an juya musu baya alhalin bai cancanji a yiwa Baba k'arami irin haka ba.
Dukkansu kuma sun yarda an wulakanta Sulaiman akan Abida.
Baba ya numfasa

41 / 50