Author : M Shakur Category : Romantic Hausa Novels
natsuwa abinda ke damunshi, tsaya mai tayi aka tana goge kwalla tace "where is Princess Alhaji?" dagokai Abba yayi ya kalleta yace "kaman ya where is princess ta bace and case din na hanun police ko and u know that very well" ihu Mum tamai tace "Alhaji ina kakai min Nadeera?" wani irin kallo Abba yamata yace "are you okay ko bakijina ne, ance tabata, ba saida nahadaki awaya da commissioner dazu ba" cikin tsawa Mum tace "am tired of your silly lies, Alhaji where is my daughter wlh koka fitomin da yata ko i will use all the money i have in this world na kulleka saika fitomin da Nadeera, Alhaji, Alhaji yanzu yarmu kake nema? How could you, yaushe kadawo haka, wani irin shameless man ne kazama haka? Yarmu kake nema Alhaji?" zaiyi magana Mum ta nunamai yatsa cikin kunan rai tace "wlh karka sake like karka fara ka shararamin karya, I've seen everything a CCTV footage, Alhaji yarmu yarmu, OMG am hurt, how could you? How could you? Wlh bazan taba yafema ba" share kwallan datakeyi tayi tana kallonshi yanda jikinshi ya saki yakuma kasa musawa, tace "tell me inda kakai ta naje na daukota? Alhaji princess zaka nema? wlh bazan taba yafema ba duniya wa lahira, inhar kama yarinyar nan wani abu wlh kotuce zata rabani dakai, like how could you, yaushe ma princess ta girma mema takeda shi ajiki dahar zakayi sha'awan ta eh? She's just 22, our poor little girl, wlh banyafe ma ba, Kai wani irin bunsur...." wani irin saukan mari dataji akan fuskarta yasa takasa karasa maganan datake shirin yi tai karan azaba tana kallon Abba dake wani irin huci yana nunata da yatsa yace "tunda kin riga kinsan komi good and fine, ubanwa yasani a matsalan danake ciki bake bace? Dakika tashi kikai tafiyan ki kin tambayen? Kafin nadawo daga Kadunan danaje ai dawowa nayi natarar kinyi tafiya, kina kula dani? When was d last time danaci abincin this your two hands acikina?" yakamo hannayenta yanuna mata yace "when was the last time da nida ke muka hada shimfida? when was d last time dana kiraki kika amsani, everyday kina meeting meeting, meeting, ni dan iska ne? Kin taba ganin nai iskanci? Tun kafin muyi aure kin sanni banda ra'ayin aure auren? What do you want me to do? Kina bani kulawa?" yawani irin daga mata murya cikin tsananin fushi yace "listen and listen very well, kin riga kinga komi so am going to tell you this Hajara, banyi regretting act dinaba kinsan mesa? Because I love her, tafiki komi, tafiki iya girki, ke saurara kiji idan inacin abincin princess jinake kaman na sume dan dadi, tafiki hankali inta ganni wani iri she always ask Abbana menene are you okay mekakeso? dawanan melodious calm babyish voice dinta dinan, tafiki taushin jiki, tafiki diri, ke tafiki komi dakika sani na ya mace, koda nai wani abu da princess i have good intention because i want to marry her and make her mine, auren ta zanyi ban yarda mun daukota tun tana yar 3month mun raineta just to give wani kato ya aure kiwon danayi ba kinajina Hajara? so am going to the court after an ganta zama araba shegen aurenta da wanan dan iskan gangster dinan ne, but get this straight to your business head i love princess and auren princess zanyi, kije chan continue with your business business tycooner, princess tafimin ke sau miliyan akan miliyan, I love her, love ma batun nayauba, kina jina? Take me to the end of the world ba court kadai ba, inhar kan princess ne nima am ready to burn down my cash sai inda karfina ya kare useless woman".
[9/13, 11:52 PM] Lady: *inkin karanta baki biyaba keda Allah*
*Maman Abd Shakur*
*22 Years Ago*!!
_Egypt Cairo_
Wata matace data dan manyanta fara haka tana sanye da doguwan riga baka har kasa tana gudu sosai kana ganinta kaga balarabiya da tsohon ciki agabanta haihuwa yau ko gobe, tana gudu agalabaice dan batada ragowan karfi gefenta kuma wani farin yarone balarabe dabazai wuce 12 years ba yana goye da wani namiji abayanshi da bazai wuce 6 years ba, yarike hanun wanda bazai wuce 8years ba duk suna gudu suna waigen baya, baya mai cikin tayi zata fadi agalabaice hakan yasa babban cikin yaran yay ihu yace "Umm" ya saki wanda ya rike yataro ta da sauri amma harta sume hakan yasa ya saukar dana bayanshi daya fashe da kuka kasa cikin harshen larabci ya kalli dan kimanin shekara takwas dake gefenshi yace "yi wasa da Abdallah" cikin kuka ya daga Abdallah dake kallon maman nasu yana jijjigashi yana wasa da hanunshi shikuma babban ya shimfidar da maman tasu da kyar akasa dajin wajen idanunshi sunyi jajir ya janye dan handbag din hanun maman tasu ya bude dan goran ruwa yaciro yabude da sauri ya yayyafa mata a fuska hakan yasa ta farfado dawani irin azababben ciwon mara da ciwon baya sosai, wani irin nishin azaba tayi tana cije baki ta kama hanun yaron tarike gam tana numfashi, arude cikin harshen larabci yaron yace "Umm menene, meke miki ciwo?" kasa magana tayi saima juyawa idanunta suka fara tanaso takara suma, da sauri wanda ke rike da Abdallah ya zo wajen ya tsugunna shima yana share hawaye ya dafa babban yana kallon maman tasu data rufe idanu cikin kuka sosai yace "meke damun Momma Ya Marwan?" rungumeshi yayi tareda karban Abdallah dake kuka sosai yana sharemai hawaye ya kwantar da Abdallah a jikinshi yana sharema Omari hawaye shima, girgiza mai kai yayi cikin murya datai rauni sosai yace "don't cry" gyadamai kai Omari yayi sanan ya sakeshi, sake yayyafa ma Maman nasu ruwa yay a fuska hakan yasa ta bude ido wani irin nishi tayi tai juyi cikin azaba sukaga jini nabin kafanta takara yin kara takara sumewa, kiran sunanta sukayi amma shiru hakan yasa ya mike tsaye, goya Abdallah yayi abaya ya kalli Omari yace "stay with Umm lemme call help" da gudu yajuya yafara bin dajin nan yana gudu da Abdallah dake kuka abayanshi yay kusan gudun 8min sanan yakai bakin titi duk wacce yagani saiya tsayar da ita yace dan Allah ataimaka musu maman su zata haihu amma ba'a kulashi ba, da kyar yasamu wata yar tsohuwa dattijuwar balarabiya ta tsaya itama dan yanda taga Abdallah na kukane ga wannashi yay zuru zuru saisa suka bata tausayi tambayarshi tayi menene yace mata maman su nada ciki jini nabin kafarta kuma sai suma take, shiru tsohuwan tayi saikuma tace nakuda ce su kaita asibiti, cikin tsananin tashin hankali yace tayakuri basu da kudin kaita asibitin ne da kyar tsohuwan ta yarda ta biyoshi masifa ma tadinga mai ahanyar dajin wai wajen yay nisa kodai yan cinkai ne, rantse rantsr ya dinga mata kafin da kyar ta yarda tabisu koda suka kai sun tarar Omari na kuka sosai Maman tasu asume jini yay mala mala akasan wajen, daga Omari yayi yana sharemai hawaye ya rungume shi yana kallon maman tasu dake nan kaman mara rai, Tsugunnawa tsohuwar tayi akanta tace "subhannallah metayi ta galabaita haka jini ya tsinke mata?" ahankali yace "gudu mukayi" girgiza kai tayi tace "assha ku matsa daga tachan inga mezan iya mata Allah bani sa'a" jan hanun Omari yayi yana rike da Abdallah suka koma chan daga dan nesa basa ganin su, rungume Abdallah yayi yana bubbuga bayanshi danyay bacci shikuma Omari ya daura kanshi akan kafadarshi ya rikeshi duk sunyi zuru zuru gawata uwar yunwa dake cinsu tun asuba suke gudu gashi har yamma tayi da kyar Abdallah yay bacci dan yunwa yakeji, sunkai kusan awa uku zaune sanan matan tazo inda suke rike da dan kwalin Maman su tana share hanunta dake da jini sosai idanunta sunyi wani iri tace "kuzo Maman ku na kiran ku" da sauri Omari ya mike tsaye shima tashi yayi rike da Abdallah dayay bacci gabanshi na faduwa sosai yarike kanin nashi sukai wajen, akwance sukaga Maman nasu inda suka barta ga jaririyan data haifa acikin wani mayafin ta baki an nannadeta, dago kai maman nasu tayi da kyar ta kallesu da gudu Omari na kuka ya tsugunna agabanta ya daura kanshi akan hanunta yana kuka, murmushi tayi ta shafa kanshi kafin ta daga hanunta ahankali ta mikama Marwan dake tsaye goye da Abdallah dake bacci abaya, ahankali yataka kafa yawani irin tsugunna agabanta idanunshi sunyi ja yana kallon fuskar Maman tasu yanda tai fari sosai tai wani irin haske kaman mara jini, dago jaririyan tayi ta mikamai hakan yasa ya sauko da Abdallah ya mikama Omari shi ya karbi yarinyan yana kallon fuskanta very cute baby girl ga gashi kanta bakin kirin har goshi tana bacci, dayan hanunshi ta kama hakan yasa ya kalleta ahankali ta mikama Omari hannu hakan yasa ya riketa shima yana kallonta cikin kuka murmushi tamusu da kyar cikin harshen larabci tace "Marwan" dago kai yayi ya kalleta yama kasa magana tsabagen yanda yakeji ahankali tace "ga sister kunan nasa mata suna Rahma da babban ku kafin ya rasu yace inhar nahaifi mace sunan dazamu samata kenan, Marwan ka kula da kaninka kaji, duk runtsi duk wahala karka sake ka rabu dasu ko ka nisan cesu, Omari" takira sunanshi tana kallon fuskarshi asanyaye, daga mata kai yayi cikin kuka yakasa magana, ahankali tace "kubi yayan ku kaji, kome yace shizakuyi, karku saba mai ko sau daya, kuhada kanku kuso junanku, farin cikin dayan ku ya zamto na dukan ku, bakin cikin dayan ku ya zamto na dukan ku, karku sake ku koma gida dan zasu kashe ku kaman yanda suka kashe mahaifin ku, Marwan" takira shi ahankali tanadan nishi, cikin wani irin raunanniyar murya yace "Umm" ahankali ta daga hanunta dake rawa ta mika zata daura akan kan jaririyan dake hanunshi takasa sabida yanda hanunta ke rawa hakan yasa ya kamo hanunta ya daura akan yarinya murmushi tayi wasu hawaye suka gangaro ta gefen idanunta da kyar ta iya magana tace "ina so bayan na rasu kutafi motherless home achan za'a kula daku zasu tayaku rainon Rahma kanajina" gyada mata kai yayi daidai lokacin Abdallah yatashi da kuka sauka yayi daga jikin Omari yafada jikin maman tasu yace "Momma are you sick?" cikin kuka, rungumeshi tayi sosai tafashe da kuka sosai danya karya mata zuciya, hannu tamikama Omari dake kuka shima harda majina yafada jikinta ta rungume su biyu tana lallashin su tana kallon Marwan da idanunshi sukai jajir yana kallonsu, dagasu tayi ta kalli Marwan tana murmushi takamo hanunshi da kyar hawaye nafita ta gefen idanunta tace "my strong brave boy, the only Man damuke dashi, haka nakeson ka da jarumta, karkai kuka okay dan aduniyan nan kaikadai ne gatan kaninka, inaso ka rage zuciyan nan naka, wanan hot temper dinan ka rageshi kaji Marwan, ga kanwarku nan ka kulanmin da ita, mace ce ka tsaremin ita ka kare mutuncin ta, katuna abinda Abban ku yafada akan idan har mace na haifa? Gyada mata kai yayi ahankali, tai murmushi tace "Masha Allah, karka manta da hakan, Omari karku manta kota girma bata yardaba ku fada mata abinda iyayenta sukace ce kuma suke so, inaso ku kula da junanku kuso junan ku, ku hada kanku ku dawo daya, karku sake ku raba kanku, ku tuna kuku dinan kune ku, kuna gatan kanku, Allah ya muku albarka ya tsaremin ku, ya karemin ku, ya kulanmin da ku, i love you so much yarana" sosai Abdallah da Omari ke kuka ahankali ta zare hanunta daga kan macen idanunta na kukkulewa ta mika hanunta tanaso ta shafa kan Abdallah wani irin jini ya balle mata paaa da sauri tsohuwar da matsar dasu Abdallah tana salati ta tsugunna tana cema Marwan ya matsa tashi tsaye yayi yana kallon maman nasu rike da jaririyan su Omari da Abdallah suka wani irin rungumeshi suna kuka sosai suna kallon maman nasu da jikinta ke rawa, kafe maman nasu yayi da ido ko kyaftawa bayayi tun yana ganin alamun numfashi ajikinta har yadena gani ya lumshe ido zuciyarshi na wani irin rawa ya tsugunna ahankali ya kankame kaninshi yana sauke ajiyan zuciya da sauri da sauri, mayafinta tsohuwar ta cire ta lullube ta tajuyo ta kalli yaran dataji sun bata tausayi sosai tace "bari naje nakira jama'a amata sutura" fita tayi tabarsu awajen daidai lokacin jaririyan ta tsala ihu tashi yayi ya shiga jijjigata yana kallon fuskarta sai ihu takeyi gasu Omari na kuka suma hakan yasa ya sakamata yatsarshi abaki ta dinga tsotsa tana bacci hawaye yacika idanunshi ahaka bacci yasake dauke ta gaba daya ya zare yatsar yasake rungumeta yana kallon gawan Umm dake lullube.
Ba'a wani jimaba tsohuwar tadawo da mutane kusan 20 mata da maza da jarkokin ruwa a hannun su nan dai aka kebance wajen mata suka mata wanka ana gamawa aka shiryata suka sallaceta aka kaita makwancinta Abdallah Omari sai kuka suke yana lallashin su, tsohuwar da mutanen ne suka tasasu agaba suna tambaya basu da yan uwa da kyar ya iya girgiza kai yace "basu dashi kuma baban su yarasu" hakan yasa tsohuwan tace to azo aje akaisu motherless home kaman yanda mahaifiyar su tafada kodan wanan jaririyan nan akula da ita achan, cikin mutanen wani dayazo da machine ya kwashe su aka kaisu motherless home din dake garin nan fa aka karbesu ga yara da dama agidan, aka karbi jaririyan da ya yarda ya bayar da kyar aka mata wanka aka bata madara aka saka mata kaya za'a kwantar da ita akan gadon jarirai ya karbeta ya rungumeta tsam hakan yasa suka barshi da ita, Abdallah dake zazzabi sosai aka bashi magani aka basu abinci sukaci banda shi daketa kallon yarinyar su Omari na gamawa sukai bacci akan gadajen su shiko yana zaune da jaririyan yana kallonta yanda take bacci abinta.
Ahaka rayuwan tacigaba ana kula dasu sosai a motherless home din, ma'aikatan wajen nada kirki har an sansu dan kullun tare zaka gansu su uku wuri daya babbban yadau jaririyan da ayanzu har yama iya mata wanka yaro dan 12 years yanama jaririya wanka yabata abinci ya shiryata yariketa, basa wasa da sauran yaran koda yaushe suna tare a manne suna jikin wansu.
Jaririyan na kimanin wata biyu wata rana suna zaune a compound din motherless home din suna zaune a simenti a karkashin bishiya yana rike da Rahma da idanunshi biyu tana rike da yatsarshi gam tana kallon sama, Abdallah yay bacci ya daura kanshi akafarshi shikuma Omari ya jingina da bayanshi yana wasa da duwatsu yaga an bude gate din gidan wasu manyan motoci hudu sun shigo an rufe gate din, wacce ake kira da Ameera dake in charge of the motherless home tafito tana murmushi aka bude kofa wani babban Alhaji dayasa kayan yan Nigeria malum malum dawani balarabe dayasa farin jallabiya da rawani ne suka fito, tunda yafito yake kallon su Marwan har hada ido sukayi da Marwan daya kafesu da ido shima yakasa dena kallon yaran, Ameera ce ta nunasu ganin yanda yake kallonsu tace "wayan chan marayu ne maman su tamutu tabar kanwar su mace jaririya watan ta biyu yanzu, muje office Alhaji wanan karan adopting kazoyi ko siya kazoyi? Dan gaskiya kudi yakaru" wucewa sukayi sukai ciki office dinta Alhajin na kallon yaran.
Motherless home din abinda gwamnatin garin basu saniba shine suna sayar da yara kuma wanan Alhajin suke saida mawa duk bayan wata biyar yake zuwa saya, nan Alhaji ya nuna yana sonsu mazan yabiya miliyoyi akansu ya shiga mota shida abokin shi balarabe yacema Ameera da daddare insunyi bacci zai turo adauke su gyadamai kai tayi tana murmushi dan tunda yake siya bai taba biyanta irin kudin wanan karan ba, aranan da daddare duk suna bacci shidai Marwan sama sama yake bacci dan tun ranan dasuka fara dira gidan marayun yaji hankalin shi bai natsu ba baya iya bacci saisa bini bini yake tashi ya kalli kaninshi sanan yakara kwanciya yana rungume Rahma da kyau, lekowa Ameera tayi dakin tawani irin huro wani hoda, strange wari dayaji yasa yabude ido yana kokarin laluban touch light yaduba Rahma dasu Abdallah amma kafin ya farga kawai yay passing out, shigowa wasu kattai sukayi suka kama Marwan, Abdallah da Omari suka fita dasu aka sakasu awani bus a sussume akabar motherless home din dasu. Wani irin ihu Rahma dake kan gado ta sandara da sauri Ameera data taushe hanci ta shigo ta dauketa tana jinjigata tafito sanan ta saki hanci tace "sorry baby anbiyani da kyaune saisa na saida brothers dinki kema karki damu in kinada luck wani zaizo yasiyeki in baki dashi haka zaki girma ahannuna yarinya".
[9/13, 11:52 PM] Lady: *don't read in baka biyaba*
*Maman Abd Shakur*
Gyada mata kai yayi yace "okay" zare safan yayi daga hanunshi tawani irin kafe hanun da kallo ganin hannu fari fat kaman na bature kafin ahankali yana kallonta ya zare na dayan hannun ya ijiye safan akan table din wurin, ahankali ya sauko da jakan dayake goye a bayanshi ya ijiye kan table yana kallonta, hanunshi ya daga sama ahankali ya kwantar da hulan hoodie dake kanshi baya, hanunshi yakai kan fuskar nashi slowly yana kallonta, sosai kirjinta ke wani irin bugawa da kana ganinta ma zaka gane hakan, saukar da hanun yayi zuwa wuyanshi kafin ahankali ya juya mata baya, cire black mask din yayi gabaki daya ya ijiye kan table batare daya juyoba, tundaga keyanshi har molon kanshi take kallo da babu gashi ko daya kan saiko dashi, ahankali yace "are you ready" gyadamai kai tayi kaman yana ganinta ta kasa magana tsabagen yanda kirjinta ke bugawa, wani irin juyowa yayi ya fuskance ta, ihu tayi sosai ta diro daga kan kujeran tai hanyar fita daga kitchen din da sauri sakamakon wani irin fuska data gani mai kama dana dodo, fuskan babu gashin gira gashi wasu irin kuraje kuraje da wani irin dabbare dabbare baki baki kaman fuskan aljani a fuskan, bakinshi baki kirin, wani irin gudu tayi amugun tsorace zata fita daga kitchen din kamota yayi hakan yasa ta saki ihu ta kankame jikinta ta kulle idanunta gam, ahankali ya jawota jinkinshi yajuyo da ita yahada jikinshi da nata yadanyi dariya dashi kanshi yamanta rabonshi