BOYAYYEN MUTUM BOOK COMPLETE BY M SHAKUR.txt

Author :  M Shakur Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   23 / 50

66K to 69K   out of 148.6K words

duba kayan tace "Princess bari nai magana da mijinki kinji" tashi tayi tsaye tanabin handbag din data dauka da kallo tace "ina zaki Mum" tai maganan idanunta na ciccikowa da hawaye, dawowa kusa da ita Mum tayi ta zauna agefen ta ta rungumeta tareda mata kiss a forehead sanan ta dauko magungunan data kawo mata tace "ki dinga shan wanan everyday da yogurt morning and night maganin kine, make sure kinsha am coming zanje na duba jikin yayan ki ne, zan sake dawowa na dubaki kinji" girgiza ma Mum kai tayi ta rirriketa tafashe da kuka sosai tace "Mummy dan Allah kitafi dani zanbiku Canada din, Mum bansan kowa anan ba, dan Allah karki barni kinji Mummy na" tafashe da kuka sosai, hawayen datake yi Mum ta share cikin lallashi tace "Princess look kinriga kinyi aure, Abban ki yariga yamiki aure banda iko dake yanzu dole ki zauna ki rungumi mijinki kiyakuri kinji Princess" fashewa tayi sosai da kuka tace "Mummy mesa Abba yamin haka, mesa yakemin abinda yakemin menama Abba ne? Mummy am tired wlh ni nagaji da komi da kowa I hate myself I hate my life I just wanna di...." da sauri Mum ta taushe mata baki tace "ke bakida hankaline, komi daya faru kaddara ne kimanta da komi saisa nan yafi miki tayanda Abba bazaima kara ganin kiba, yanzu share hawayen ki zansa abaki waya zamu dinga waya kullum and zan dinga turomaki abubuwa kina amfani dasu" share mata hawayen tayi sanan ta tashi da sauri tai hanyar kofa da gudu Nadeera ta mike tabita tafada jikinta ta kankameta ta kurma uban ihu da saida yafito da Marwan dasu Abdallah, kara kankame Mum tayi tana kuka tace "saikin tafi dani Mummy, dan Allah kitafi dani Mum, nagaji da rayuwa baki, to naji naji kizo ki zauna dani anan karki sake tafiya ki barni I don't know them" ta nuna su Marwan da hannu dake kallonta, tafashe da kuka, sosai take neman karya zuciyar Mum da kyar ta dago jajayen idanunta ta kalli Marwan tace "please zoka kaita daki Marwan, I have to go yayan su ya farka a asibiti" wani irin kankame Mum tayi tana kuka sosai tace "inkinama Allah Mummy na kitafi dani zan biku chan Canadan, nima inaso naga Ya Muhsin din please Mummy na kitafi dani" cikin wani irin raunanniyar murya Mum tace "dan Allah kidena kuka haka Princess ke yarinya ce wai, nace zan dinga zuwa and zamu dinga waya okay, gayan uwanki nan zasu kula dake" makema Mum kafada tayi cikin kuka, ahankali Mum ta dagota daga jikinta tana share mata fuska tace "to shikenan, naji" daidai nan taji an wani irin rike mata hannu kafin ta ankara ya fizgota yasata ajikinshi ya rungumeta da karfi ta yanda ko motsin kirki bata iyayi, aiko tafashe dawani sabon kuka tana mikama Mum hannu, murmushi tamata tajuya da sauri ta sauka kasa, bin bayanta Omari dazai mayar da ita yayi zuwa kasa, wani irin fashewa tai da kuka tana kwalama Mum kira kaman zata tsaga gida. "Mummy Mummyna" jijjigata ya shiga yi kafin yabude kofan dakinsu ahankali ya shiga da ita yay kan gado da ita ya zaunar da ita yana kallon yanda take kuka ko ina na jikinta na rawa, wani irin kwantar da ita yay kan gadon yahau ya janyota kan jikinshi ya daure fuska tareda daura yatsanshi akan lips dinta ahankali yace "kimin shiru" gyadamai kai tayi kaman wata marainiya hawaye na fitowa daga idanunta, rungumeta yayi yace "kinajin yunwa?" girgiza mai kai tayi cikin kuka mara sauti da sauri yace "mekika ci?" bakinta na rawa tace "dognut and..and dambun nama" "Mum takawo miki?" yay maganan yana sharce hawayen dayake gangaro mata, gyadamai kai tayi ahankali yay murmushi yace "Nima zanyi tafiya zaki bini Oman naje dake?" girgiza mai kai tayi tana kwalla kuka nacinta sosai amma yaki bari tayi, lips dinta dake rawan kuka yama kiss mai kara ya saki yace "why? Mesa bazaki bini ba? Are you scared?" gyadamai kai tayi, shiru yayi yana kallonta son ta namai wani irin Kane Kane azuciya, ahankali yana shafa wuyanta yace "kinfison kibi Mum kihadu da dat goat, you want him to molest you again?" girgiza mai kai tayi tafashe da kuka sosai dan ya mugun tuna mata da Abba, hannu yasa akan lips dinshi idanunshi sundan chanza kala yace "kinason dat goat yay raping dinkine?" girgiza mai kai tayi hakan yasa ya taba inda ya kumbura a fuskanta yace "kin kalli Mirror yau have you seen abinda yamiki?" kasa magana tayi tana kuka hakan yasa yadan fuzar da iska yace "stop crying and sleep bakida lafiya" gyadamai kai tayi jikinta na rawa, hada goshinshi yayi da nata yana kallon fuskarta ahankali yace "is okay stop crying, maisa bakisan gidan nan?" bakinta na rawa sosai tace "s..sabida gidan daji ne" kafeta yayi da ido yana kallon yanda kirjinta kewani irin bugawa yadan fuzar da iska yace "in chanza miki gida?" gyadamai kai tayi da sauri, murya chan kasa yace "ina kikeso na maida ke?" ahankali tace "cikin gari" hanunta yakama yahada da nashi yace "okay done! Wat else kikeso?" bakinta narawa tace "and...and st.." tai shiru, lips dinta nakasa yakama yana shafa bayanta batare daya sakiba yace "and wat?" raurau tai da ido tace "stop wearing mask" shiru yayi yana kallonta saikuma yay murmushi yahau yimata wani irin kiss kaman zai cinyeta da kyar yasake ta ya kalleta yace "you've changed me Rahma" kallonshi tadanyi kafin ta lumshe ido tana breathing heavenly bakinshi ya daura a kunenta yace "am sleepy make me sleep my amarya"....



***
Ahankali Abba ke bude ido akan gadon asibiti acikin hadadden dakinshi, anamai karin ruwa ansaka plasta a kasan hancinshi inda yafashe, da kyar yakarasa bude ido yana kallon saman dakin yabude baki cikin sambatun ciwo yace "why are you stubborn mana Princess? Kimin shiru anan, oya kamamin, kinfi maman ki dadi wlh Princess, kinfi maman ki zaki da komi, wayyyooo Princess kamamin, you're bless princess" wani iri iri maganganun ke fita daga bakinshi sabida hakoran shi biyu nagaba dasuka fita, sake bude bakin yayi ahankali yace "Princ..." afirgice yawani irin yunkuro zai tashi ya ware idanun tangararas yana kallon ko ina yana dafe kirjinshi dake wani irin bugawa komi na dawo mai, daidai lokacin wani Dr ya shigo dakin da stethoscope a hanunshi, binshi Abba yay da kallo harya karaso gaban gadon, Dr yace "barka da tashi Alhaji yanzu meke maka ciwo?" cikin tsananin fushi Abba yanuna shi da yatsa da maganan shi dabata fita da kyau yace "waya kawoni nan? Wata farar mata mai suna Hajara ce takawo ni halan? Ashe dama tasan inda Princess take, ashe Hajara tamasan wanda ya dauke Princess dan ai tare na gansu, Hajara kin cuceni kin cuci kanki kuma kin tsokano tsuliyan dodo" ya dago kai ya kalli Dr cikin kunan rai yace "nawane hakorin roba? Koma nawane akawo asamin original one din wanda baya kama da hakorin roba shinake so, zo tugemin wanan karin ruwan zanje nemo yata, yauwa kiramin kwamissioner ina wayana wai?" yahau waige waige yana dube dube akan gadon, sake kallon Dr yayi ganin bai ciremai karin ruwan ba yace "nace kazo ka cire min, tafiya zanyi wani ya gudun mun da y'a, shiyamin ma wanan dukan yanaso ya kasheni yarabani da y'ata" ahankali Dr yace " calm down Alhaji bazaka iya tafiya ko inama ba, bakada karfi, an mugun dakanka a ciki, da kyar muka shawo kan matsalan amma dudda haka wall din stomach dinka are very weak, dole you need to relax and heal, am advising you not to go anyway for now, ka kwanta yanzu zan kira dietician Dr zaizo yay examining dinka saiya sa akawoma abincin daya kamata kaci, zai kuma bama kitchen time table din abinci daya kamata kaci, bazamu iya sallaman ka yanzu ba koma menene za'a kira kwamissiona saisuyi handling everything za'a ga yarka in sha Allah" yanda yake maganan calmly trying to calm the patient down ammq Abba baisan wanan ba, ihu Abba yayi yace "kace am not strong kana nufin ni tsoho ne kome?" ya nunashi da yatsa yace "kai likita, kai likita kasan wacece Princess a rayuwata kuwa, she's my baby girl, my innocent baby girl, my chubby baby girl, my one and only baby girl, I can die for that girl kai, kawomin discharge against medical advice form lemme sign bazan iyaba, bazan iya zamaba princess na hanun wani kato Allah kadai yasan meyake mata, bakaji zuciyata bane yanda take suya, rashin ganin princess da sanin inda take, da tunanin me shegen nan kemata shizai fara kasheni ba wanan ciwon ba, Dr ka sallameni and give me drugs I can manage" yay maganan yana sauke ajiyan zuciya saikuma ya nuna kanshi da hannu yace "ni, ni wani kato ya daka kan yata? Ni dinan, niya zubar ma da hakora kan yata, ai wlh idan na yarda shege nake yanzu zan nunama koma waye shegen nan wanene ni, zan nunama waye Naseeru, badai you want to bring the monster in me out ba, am out and babu abinda zai iya containing dina, zamusa kafar wando daya dakai, kamoka da ganinka kuwan saidai idan ba'a Abuja yakeba amma ko'a takashin Uwatata ya buya wlh saina nemoshi" ya buga gado da hannu yana kwafa, juyawa Dr yayi yafita daga dakin ahankali tunanin kodai harda kai ya bugu ne, dan Alhaji doesn't seems normal.
[9/21, 6:00 PM] Lady: *karki karanta in baki biyaba, in kinason novel dinan, zaki turo 300 kota card kota bank sai nai adding dinki a group din danake posting kullum*.

_Acc no: 3107021073 first bank aisha Muhammad_

*You can contact me a watsapp number na kaman haka 07012181461 dan son wani karin biyani ko tambaya*


🕳🕳🕳🕳🕳

*BOYAYYEN MUTUN* 🕳🕳🕳🕳

*Maman Abd Shakur*


Baiwani jimaba ya shigo dakin yamika ma Abba dake ta bambami shi kadai paper da byro da sauri Abba ya karba yay signing , Dr yabashi ledan magunguna ya karba, Dr yace "na rubuta yanda zaka dinga shan su aciki, jikin kwalayen, please Alhaji don't play with your health, nama dentist magana shi kawai zaka jira yanzu yazo ya makalama hakorin, shikuma dietician din gashinan zuwa ya duba ka, Allah kara lafiya, dazaran kaji jikin yamaka wani irin dan Allah Alhaji don't hesitate kadawo mudubaka, Allah kara sauki" Ameen Abba yana kokarin zira rigan shaddan shi daya gani agefen gado, shikuma Dr yajuya yafita yana murmushi aranshi yana cewa wanan inyakai 90's akwai rigima wlh.

Ba'a wani jimaba dietician ya shigo yabashi abinci yadan tsakura sanan yabashi time table na abincin dazai dingaci yatafi dashi, saiga dentist yazo ya sakamai hakorin roba nan bakinshi yafito tsaff, kwamisona dama yariga yafada ma asibitin Bill da komi na kanshi hakan yasa suka kirama Abba taxi base on his request ya sauka yafito waje da kyar ya shiga yace yakaishi asibitin da Muhsin yake dan yasan anan zaiga Mum.



***
Bude ido tayi ahankali ta daura akanshi taga idanunshi a lumshe kaman wanda yake bacci, kafeshi tayi da ido tana numfashi da sauri da sauri, ita kanta batasan metakeji ba ahankali kaman wacce ake shirin yankawa tace "kai bacci?" ita kanta batasan ta ina maganan yafito daga bakinta ba, girgiza mata kai yayi batare daya bude idoba, murya chan ciki yace "nay! Am listening to my wife's breath" da sauri ta rike numfashin tana kokarin hana kanta numfashin da sauri da sauri, bude ido yayi ahankali dasuka kankance sosai ya sauke akanta, wani irin ajiyan zuciya ta sauke hakan yasa ya mata murmushi mai taushin gaske, dan zaro ido tayi tana kallonshi, ahankali yace "how many days kike mp?" da sauri ta lumshe ido tana kokarin juyamai baya akan gadon cike da kunya, dan ya mugun bata kunya da tambayan, yawani irin juyo da ita yana murmushi yace "are you shy baby?" wani irin kunya ne ya lullubeta hakan yasa ta runtse ido da karfi tafara kokarin tashi ta zauna murya chan kasa yace "ina zaki?" rasa me zatace yasa tace "sitting room, kallo zanyi" tashi yayi yace "okay muje tunda bazaki fadamin ba" sauka yayi ya sauko da ita yadau dan kwalinta ya mika mata yana kallonta, ahankali kaman wata mara gaskiya ta karba ta daura akanta kanta akasa taki bari suhada ido sanan yarike hanunta suka bude kofa suka fito, Abdallah kadaine zaune a falon rike da remote yana kallon match na Argentina da France, tunda yaji alamun tafiya ya dago kanshi ya kalli sama, bakaramin kyau Marwan da Nadeera daya rikema hannu sukayi maiba, suna tafiya daidai sai kallonta Marwan yake kaman bai taba ganinta ba, kaman zai hadiyeta, kafe Nadeera yay da ido dan bama ta lura da mutum afalon ba kanta na kasa, murmushi yayi wani irin dadi ya rufeshi, karasowa falon sukayi suka zauna akan kujera ta kafe Abdallah dake kallonta shima da ido ganin kaman ta taba ganinshi, murmushi yamata yace "amaryan bros" dauke kai tayi ta maida kanta kan TV kafin ahankali tace "ina yini" murmushi sosai Abdallah yayi yace "to haka ake gaisuwan ni wlh saikin kalleni zaki gaisheni ehe this nurse" da sauri ta juyo ta ware ido tana kallonshi surprisingly tace "laaaaa" da sauri Abdallah ya karasa mata yace "laaaaa is you, haka zakice ko amaryan bros sai yanzu kika tunani" murmushi Marwan yayi ganin dan murmushi akan fuskanta yaja system dinshi dake edge din kujeran ya daura akan cinyarshi yabude...



***
Adaidai gaban asibiti Mum tasa Omari yay parking tafito daga motan tana murmushi tace "nagode sosai Omari agaishe min da Princess, please kuyi keeping dinta company sabida kartai missing dina sosai" murmushi yayi yace "to Mum shikenan, agaida mai jiki, Allah kiyaye hanya" murmushi tamai tace "Ameen nagode sosai, Allah muku albarka" ta dagamai hannu shima hanun yadaga mata ya kunna motar yatada yabar wajen, saida Mum tadena hango motarshi sanan ta juya ahankali ta shiga hospital din tana kokarin ciro wayarta dake ringing ajaka tafito dashi, mai mata aiki datasa booking mata jirgi ne da sauri tai Picking call din, sanar da ita yayi yay booking din jirgin gobe da safe, jirgin karfe biyar da rabi na safiya zai tashi, zai turo mata tickets din ta email dinta, godiya tamai sosai kafin ta kashe wayan takarasa ciki hospital din da sauri tai dakin da aka kwantar da Muhsin ta tura kofan da sallama ta shiga, Muhsin tagani shi kadai adakin babu Ahmad idanunshi biyu yawani irin ramewa yana sauke ajiyan zuciya ahankali ahankali, tunda yaga Mum ya kafe ta da ido yana kokarin motsa jikinshi amma yakasa, da sauri Mum ta karasa wajen taja kujera ta zauna ta rungume kanshi tsamtsam tace "Son kai kadaine? Ina dan uwanka? Ina Ahmad?" da ido ya nuna mata bayi hakan yasa tace "okk yana bayi, meke maka ciwo yanzu?" zuciyarshi ya nuna mata da ido, murmushi tayi kaman zatai kuka ta daura hanunta akan zuciyarshi tace "in sha Allah you will be fine okay, gobe zamu tafi Canada da safe kana so kaje?" lumshe mata ido yayi ya budesu ahankali yana kokarin yin magana aka wani irin bugo kofan dakin da sauri Mum ta daga kai ta kalli kofan, Abba ne ya shigo dakin aduke rike da cikin shi yana ma Mum wani irin kallon rashin mutunci da tsana, dauke kai Mum tayi dan ko kadan batason ganinshi ta shafa kan Muhsin dake kallon Abban nashi yana wani irin saukar da ajiyan zuciya kaman zai suma, kanshi Mum ta shafa takira sunanshi. "Muhsin look, look at me kadena numfashi haka zaiyi affecting health dinka, everything is fine kaji my boy bakason damuwa" karasowa tsakiyan dakin Abba yayi kaman ana ingizoshi ya tsaya akanta yawani irin kira sunanta yace "Ke Hajara!" ko dago kai Mum batayi ba balle ta kalleshi hakan yakara tunzura Abba yace "Hajara dakefa nake, bake nake kiraba, Hajara ina Princess? Kifadamin nace ina princess?" ko dago kai Mum batayi ba saima hannun Muhsin data rike datake ta murzawa, cikin tsananin fushi Abba ya kalli Muhsin dake wani irin kallonshi cikin tsananin zafin ciwo da Abba baimabi takaiba yace" Muhsin, Ahmad" ya waiga dakin yana neman Ahmad cikin masifa yace "ina Ahmad din yake, Ahmad" yasake kiranshi kafin ya kalli Muhsin yace "Muhsin kuma maman ku magana tun muna mu biyu tafadamin ina princess take, ina tasa aka kaimin princess, harda sa bakinta abatan princess, tasan inda princess take, tareda gang dinan na gansu tare har tanasa anamin wanan dukan dayakusa kasheni to ta Allah bataki ba, ban mutu ba, Hajara nace ina princess?" yay shiru yana numfashi kaman wanda yaje yaki yana wani irin kallon Mum dako dago kai batayi ba ballema tasan anyi hallita a wurin, fitowa Ahmad yay daga bayi ya tsaya abakin kofa yana kallon yanda Abban nasu ke tsaye akan Mum kaman zai rufeta da duka wani irin takaici yaji yanaji wanan wani irin uba Allah yabasu, juyowa Abba yayi sabida karan rufe kofa dayaji ya kalli Ahmad dake jingine da bango cikin fushi yace "Ahmad dama ka iya kare uwarka ko, to zonan yimata magana tafadamin ina Princess take dan dasa bakinta abatan y'ata, inba hakaba wlh, wlh, kaji na rantse maka ko, kome namata ita taja, wanan dukan datasa akamin zan rama akanta ne" ya kalli Mum yace "Hajara ina kika kaimin princess? Amsa kawai nakeso naji naje dakaina na dauko y'ata, ina kikasa dan ta'addan nan yakaimin princess eh?" wani irin juyowa Mum tayi ta kalleshi tace "Alhaji aren't you ashame of yourself? na rufa maka asiri ban tonama yayana abinda kayiba amma kabiyoni har nan danka tonama kanka asiri ko, Alhaji kamin shiru, respect yourself and get out of here, ni da yarana we don't need you in our lives, kaje chan kaita neman princess, but lemme assure you one thing bazaka taba ganin princess ba, Alhaji Nadeera tamaka nisa, Nadeera natare da wayanda suka fika iko da ita ayanzu, Nadeera natare da yan uwanta, kama dena kirarin kai ubanta ne dan aranda kafara nemanta aranan katashi daga ubanta ka koma bunsuru" mari yawani irin kawoma Mum Mum tarike hanunshi gam tana huci, tace "da daka dakeni nai shiru na barka sabida inama kallon kai mijina ne, ina

23 / 50