Author : M Shakur Category : Romantic Hausa Novels
ganin girman ka lokacin, amma ina! see Alhaji kobaka sakeni ba nisai nakaika kara alkali ya raba auren namu am fed up am so done with you like..." Tai shiru kafin tawani irin komar mai da hanunshi cikin karfi da zafi yay baya zai fadi yarike karfen gadon gam gam yana wani irin kallon ta cike da mamaki dakuma fushi, yace "bama saikin kaini kotuba ni na sake ki hajara! nace na sakeki saki daya! Nasake ki saki bi.." da sauri Muhsin dayakeji kaman zai mutu dan yana gane maganganun su yafara kokarin daga hanunshi yace "Abb..." hannu Abba yadaga mai cikin fushi sosai yace "barni Muhsin, karka sake kasa baki cikin wanan matsalan na nida uwarku" yajuya ya kalli Mum dakemai wani irin kallo yace "nasake ki saki biyu! Na sakeki saki Uku Hajara!" wani irin kwalla Mum ta share daya zubo mata da sauri tanajin bakin ciki da tsananin kunci aranta, Abba ya nunata da yatsa daga sama zuwa kasa yana mata wani matsiyacin kallo yace "me akeyi da mace irinki dama amatsayin mata? Kome nadawo yau, kowani hali na shiga ayau ke kika sakani, kekika jefani hajara, ko zunubin ma mu biyu za'a rabama wa dankece wacce takaini ga halaka harna fara sha'awan Princess, me akeyi da mata irinki kinada lokacina? Kina bani hakkina? Kin kare mutunci auren ki kullum saidai yawo zuwa kasashe aci gayu, yau asa en en yama sunan atampan ku? Yauwa Supa, yau asa Supa, gobe holadis, gata voyal, citta diamond da engilish, azubu zinarai ajiki kina yanga akan titi kina shaking hannu da mazan daba maharraman kiba da sunan business, ke gaki wayayya me kike dashi tell me Hajara? Me kika tsinana min? Princess tafimin ke sau dubun dubara malala gashin tinkiya, I will say it and say it again tafimin ke Hajara, ko damuwa taganni ciki zatazo da wanan cool, calm, innocent, melodious and babyish voice dinan nata tace " _Abbana menene are you sick?"_ ke kinamin haka? Ina fushi kina kan waya business call, tayaya za'ayi bazan so princess ba, kullum nida ita kike bari agida, namata tsifa namata taza, nakaita saloon mudawo gida namata wanka tun kafin tai hankali tell me ni gunki ne, little by little I began to grow found of her, after all ba yar dana haifa bace, akwai aure tsakanina da ita, Hajara ina kikasa aka kaimin y'a ina princess?" cikin fushi Mum ta kalleshi dan maganganun shi sun mugun soya mata rai, sun tabata sun kuma girgizata tace "har abada bazaka kara ganinta ba Alhaji, haka zaka kare maye kawai tsohon Najad..." da sauri Ahmad dake tafarfasa ya kirata yace "Mum!" hannu ta dagama Ahmad tace "Ahmad leave the room if you don't wanna watch, nagaji! Nagaji! babanka nata zagina yana cimin mutunci yana zagina for wat now? What have I done? Tafiyana doesn't justify him trying to rape princess, tamanta alkhairina, yamata the bond we once shared, yamata alkhairaina agareshi da mahaifiyar shi kafin ta rasu, yamata komi sai zagina kawai yake, da mutunci na da daraja ta, da yarana, zai tsaya yana zagi, nafada nakara fada bazaka kara ganinta ba har abada sabida princess na hanun wayanda suka fika iko da ita bazaka kara ganinta ba, Alhaji bazaka kara ganinta ba" wani irin dariya Abba yayi mai ciwo, kaman wani zararre yace "nikika cema tsohon najadu? Look me, kalleni da kyau Hajara, yimin kallo daga sama har kasa wlh nafi karfin kicemin tsoho duka duka da shekara nawa na girmeki iye? Cha nayi inada ashirin da hudu kinada ashirin mukai aure iyye? Yanzu inada 56 kinada 52 kajimin mata nitake cema tsoho, waya cemiki namiji na tsufa? nida ke waye tsoho dan ma mayukan ku na mata na rufa miki asiri, ina kyautata zatoma tiri kike sama gashin ki saisa yay bakin kirin haka dan sa'oninki kansu hurhura yagama cikashi, wlh kema kinsan waye mijinki kinsan ni nafi karfi ki kirani da tsoho kinsan yanda nake baki kashi adaki Hajara cha nayi ihu kike na barki wani zub... " da sauri Ahmad yajuya yafita daga dakin cikin fushi bazai iya tsayawa yana sauraran yanda iyayen shi ke tonan tsilili hakaba, duk hankulan su sun gushe yawani irin bugomusu kofan bam, da harara Abba yabi kofan yace "ka karata chan dan uwatata mai hali irin na uwatata" yajuyo ya kalli Mum da idanunta sunyi jajir yace "Bakin ciki kike da princess ko saisa kika hada baki kikasa yamin duka ya dauketa, bari kiji saina bar numfashi ne zan dena son princess aduniyan nan Hajara, bakin ciki kike yarinya tafiki kyau, tafiki hankali, tafiki natsuwa, tafiki diri, tafiki shape, tafiki gashi, tafiki mamma, wlh Mamma manya a tsaye, yarinya gata jinsin larabawa, ga ilimi gata uwa uba kyau, ga karatu book da islama tafiki komi Hajara, dan haka kiyi sallama da bakin ciki dan inhar bakiga aurena da princess dinaba ba sunana Naseeru ba, I will make princess mine, I will spoil her, zaki gani all my property zan maidashi sunanta, I will be 3 in 1 ma princess, i will be her Abba, her momma, and her lover her baby kina jina hajara" wani irin kallon tsana Mum ta watsa mai tana share hawayen daya zubo mata tace "wlh Alhaji ka shiga uku, ka bani, kai ka shiga uku, kaji kunya, tirr da hali irin naka, tsohon bunsuru kawai" "ni kika kira bunsuru? Kincemin tsohon najadu namiki shiru bance komiba, shine kuma yanzu nikike cema bunsuru?" Abba ya fada cikin wani irin dacin rai yanaji kaman ya kashe Mummy, cikin ihu Mum tace "eh anfada Alhaji kaidin kai bunsuru ne" wani irin bazatan mari ya watsama Mum da sauri Muhsin dake numfashi da kyar yafara kokarin motsi yatashi yakasa, wani irin ihu Mum tayi ta chakumo Abba tace "eh ka kasheni, ance bazaka ga princess dinba har abada, kuma kotu zan saka I will accuse you of rape, sanan da dukana, bazaka kara ganin princess ba tsohon bunsuru kawai, zuwa masallacin ka kana sahib farko baima amfani ba, mai gemun banza kawai" tsabagen yanda zuciya kecin Abba dan yanda yakeji sabida kin gayamai gaskiyan inda princess take dataki yasa yawani irin rufe Mum da duka tana ramawa, sukahau dambe sosai, da kyar ya tadiye ta ta fadi akasa itama ta fizgo riganshi yafado kanta ta shake mai wuya tace "wlh saika kasheni yau, saika kasheni nace Alhaji, kan princess kakemin haka ko toka kasheni nasan yes kana sonta, son yakai so" cikin fushi Abba dake kifa mata naushi a ko'ina yace "ina kika kaimin baby girl eyeh, makirar mata yar bakin ciki, annamimiya bai farar kafa" ance karfin mace danamiji ba dayaba duk yanda Mum taso ta rama kasawa tayi karfin ba dayaba, Abba sai kibarta yake baji bagani, bude kofan akayi wani Dr da nurse dake ward round suka shigo, salati likitan yayi yace "subhannallah me haka?" yana kallon yanda tsoho da tsohuwa ke dambe, da sauri nurse din dake bayanshi tace "look d patient Dr" tanuna mai Muhsin dake kan gado, dawani irin gudu sukai kan Muhsin dake wani irin nishi yana bankarewa yana dafe kirjinshi idanunshi na juyawa batare da sunbi takan Abba da Mum dakecin dambe baji bagani ba, machines din dakin dake jone da gadon Muhsin sai kara suke din din din dinnnnn, wani irin ihu Dr yayi ya kalli nurse din yace "get defibrillator, we are loosing him" da hannunshi yasa yafara daddanne kirjin Muhsin yana ihu yana counting numbers. "one! Two! Three" cikin ihu Dr yace "he's not responding to hands, be fast nurse get defibrillator" dawani irin mugun sauri Abba ya saki Mum dake neman suma bakinta da fuskanta ya kumbura bakinta najini, ya tsaya yana zaro ido yana kallon Muhsin da ake faman cetowa, Mum ma ta tashi da kyar ta tsaya gefen Abba tana kallon Muhsin, wani irin nishi Muhsin yayi kafin yay kalman shahada ararrabe.
_Oh no m Shakur ba Abban ba ba Mum dinba dukansu mahaukata ne rubabbu._
[9/23, 10:15 AM] +91 88002 49616: *Karki karanta in baki biyaba*
*Maman Abd Shakur*
Adaidai lokacin nurse din ta shigo da gudu tana gunguro defibrillator din ta tsaya chak agaban gadon tana karanta machine din dake hade da gadon Muhsin tana kuma kallon patient din da idanunshi suka koma sama, daga kai tayi ta kalli Dr din da ahankali ya zame hanunshi daga kan kirjin Muhsin ya dagokai ya kalli nurse din tareda girgiza mata kai yakai alamun bashi kuma, hannunshi ya daura kan fuskarshi Ya Muhsin ya rufe idanunshi ahankali tareda jan farin bargon gadon yarufe shi ya juyo ya kalli Abba da Mum dake wani irin numfashi da sauri da sauri sunyi suman tsaye ko kyafta ido basayi kallon Muhsin da aka rufe suke ba kakkautawa, cikin tsananin fushi Dr ya kalli Nurse din yace "get his folder from my office time of death 4:30PM" ya kalli Abba da Mum da babu wanda ya iya wani kwawkwaran motsi cikin su yace "I hope you guys are happy now kun kashe danku" yay pointing Mum da yatsa yace "I made it clear to you ranan dakika zo office dina cewa yaron nan bayason any type of hayaniya, bayason damuwa karku, bayason tashin hankali, karku daga mai hankali kark..." bude kofar dakin akayi hakan yasa Dr yadaga kai ya kalli kofan Ahmad ne ya shigo kaman wani abu ya wurgo shi idanunshi sunyi jajir yabi su Mum da yaga fuskarta akumbure da jini da kallo kafin ahankali ya juyo da kanshi ya kalli gadon dayaga an lullube Ya Muhsin da bargo harkai.
Tsaki Dr yayi cikin bacin rai yace "da girman ku, da girman ku, manya daku xakuzo kuna dambe agaban danku mara lafiya, a hospital for dat matter, ku yarane? You guys are very very selfish my God, anyways the damage has been done already, kuzo kuyi clearing komi kokuma nan da 10min zan aiko awuce dashi mutuary" yajuya yabi ta gefen Ahmad dako motsi yakasa yana kallon Muhsin dake alullube, fita Dr yayi hakan yasa Ahmad yadaga kafa ahankali kaman mai matsala a kafa yakarasa jikin gadon ya tsaya chak kafin ya mika hannunshi dake rawa sosai ya daura akan bargon yaja kasa nan yaga fuskar Muhsin da zufa kekan goshinshi idanunshi a lumshe, wani irin faduwa yayi akan guiwowinshi kaman mara lafiya ya fashe dawani irin kuka ya daura kanshi akan gadon yace "innalillahi wa inna ilahi raji'un, Ya Muhsin! Ya Muhsin! dan Allah karka tafi ka barni ni kadai dawayanan mutanen we called our parents, Ya Muhsin you are my strength, my support system, my guardian please wake up, am sorry is my fault, is all my fault, na fita nikadai na barka tareda mutanen nan, Ya Muhsin dina!" yawani irin tashi yana jijjigashi amma ko gezau, fashewa yay dawani irin kuka yama kasa magana da kyar ya iya dago dakai ahankali hawayen dayake suna diga ajikin Ya Muhsin yaja bargon yarufe shi back yana tofamai addu'a kafin yawani irin juyowa cikin fushi yatako har zuwa gaban Abba dake kallonshi jiki asake yace "Alhaji Naseer Aluminum!" saida zuciyar Abba tawani irin girgiza sabida yanda dan cikin shi ya kira sunanshi kai tsaye haka, wani irin kuka kecin Ahmad da kyar cikin kuka ya iya yay magana. "karka, never in your life call me your son, kaiba mahaifina bane, I regret ranan danazo duniyan nan amatsayin danka, na tsanake na tsaneka sosai, I hate you, and kaje sai Allah yamana hisabi dakai kashemin dan uwana dakayi bazan taba yafema ba!" zaro ido Abba yayi yana kallonshi idanunshi sunyi jajir yarasa ta cewa, yajuya ya kalli Mum dake wani irin kuka kanta akasa yace "and you Mum, am so so disappointed in you, kome Mutumin nan zai miki saiki biye mai? I tried talking to you but kince namiki shiru nabarki kiyi magana and vent out your anger, that you are tired, so yanzu you've vented your anger kinyi son ranki danki kuma yarasu kun kasheshi da bakin cikin ku are you happy now? Are you happy Mum? Are you satisfy? Kozaki cigaba ne?" yay maganan yana kuka sosai, girgiza mai kai Mum tayi cikin kuka sosai kaman zata mutu, hannu Ahmad ya daga yana musu clapping yana hawaye yace "wow, wow, wow you guys deserve an award na kashe danku" yajuya dawani irin sauri cikin fushi yafita daga dakin dan zuwa clearing everything ya tafi da wanshi gida, da kyar cikin kuka Mum tadago kanta ta kalli Abba da shima ita yake kallo da idanunshi dasukayi kaman an jijjiga bera a buta tsabagen fitowa, atare sukai wurin gadon suka tsaya, cikin kuka sosai Mum ta kalli Abba tace "Alhaji danmu, Alhaji Muhsin, my son da gaske ya mutu Alhaji?" tai maganan kaman zararra tana janye blanket din daga fuskarshi tana wani irin kallon shi tana kuka, kallon Muhsin din Abba yayi gabaki daya kanshi ya kwance yakasa furta komi sai zaro ido dayake yi gabanshi na faduwa, bude kofan dakin akayi Ahmad da idanunshi sukai jajir ya shigo dawani abokinshi Bello dauke da makara dakuma babban tabarma, wani irin nishi Abba yafara yi yana kallon Ahmad din dako kallon inda Abban yake baiyiba suka ajiye komi akasa yazo ta gaban gadon shida abokinshi zasu dagashi da sauri Abba ya mika hannu zai dagashi Ahmad yamai wani irin kallon da idanunshi dasukai mugun jajir saida gaban Abba yafadi ahankali ya janye hanunshi ya maida kirji kaman mai shirin yin salla yana kallon Ahmad din, Ahmad da abokin nashi sukadau Ya Muhsin suka sakashi a tabarman suka sakashi a makara suka dauka suka fita daga dakin Mum nawani irin kuka tabisu da gudu Abba ma yabisu da sauri ko kallon su Ahmad baiyiba suka sakashi cikin motan ambulance din asibitin dasukai haya suka shiga kafin Mum dake kuka sosai da Abba su iso yawani irin rufe motan yacema direban su tafi suka fita daga asibitin, Mum ta tsugunna a wurin tana wani irin kuka kaman zata mutu bama tasan meke mata dadiba, Abba ya tsaya akanta yana kallonta ahankali yace "H...Ha..Hajara, tashi mutafi, kinji tashi muje" ahankali Mum tamike kaman tababba tace "a'a ina zani dakai wajen Muhsin zani shi kadai muka bari adaki" da sauri ta juya zata koma cikin hospital din Abba yarike hanunta da sauri yace "Hajara dubi, kalleni" cikin kuka sosai ta kalli Abba, Abba yace "Allah yafi nida ke son danmu, dama kuma shiya bamu shiko?" yatambayi Mum ahankali, da sauri ta girgiza mai kai hawaye na bulbulowa Abba yace "to Allah yama Muhsin rasuwa, addu'a zamumai ba kukaba kinji, yanzu zomu tafi gida naga banga motar ki a parking space ba, bakizo dashi bane" gyadamai kai Mum tayi tana wani irin kuka, juyawa yayi ahankali rike da hanunta ganin bata hayyacinta yay bakin gate da ita, yatare musu taxi suka shiga suka zauna yaciro wayarshi yafara kiraye kirayen abokan arziki da abokan business.
***
Dan shiru tayi tai dan murmushi kadan ta dauke kai batare datace komiba tadan matsa gefe sabida yanda suke kusa kusa da Marwan daketa daddanna system abinshi kamshin shi na fizganta, dan dago kai tayi karaf suka hada ido da Abdallah daketa kallonta hoping zatace wani abu again, dan hararan shi tayi tana wasa da yatsun ta tana turo baki tana kukkuni kasa kasa tace "ni banason ana kallona fa" "lalalala" Abdallah yafada yana saukar da kafanshi kasa, da sauri ta kallai murmushi yay escaping bakinta, ta wutsiyar ido Marwan keta kallonta, Abdallah ya kalli Ya
Marwan yace "Ya Marwan wlh kama amaryan ka magana ba kaga tanamin kukkuni ba" murmushi sosai tayi, hakanan batasan mesa she always find the guy funny ba, kamanYa Ahmad haka yake mata, ahankali Marwan ya janye system din yana wani irin kallon ta kaman yahadiyeta yakasa magana, turo baki Abdallah yayi kaman zaiyi kuka yace "Ya Marwan bakace komiba kagama dariya takemini" murmushi tayi sosai harda daura hanunta akan fuskarta, daidai lokacin aka bude kofa Omari ya shigo dakin dauke da sallama shima idanunshi akan kanwar tasu da sauri Abdallah ya kalleshi kaman zaiyi kuka yace "Ya Omari kaga amaryan Ya Marwan na tsokanana ko, wlh this nurse ko she's so tsokanacious" fashewa tai da dariya hartana bige kafan ya Marwan, dukansu tsayawa sukayi suna kallonta barin ma Ya Marwan dake gefenta dayakeji kaman ya tsaga jinin shi ya sata ciki, Ahankali Omari daya kasa dena kallonta ya shigo dakin ya zauna gefen Abdallah gani yayi dariyanta kaman na Momma su, da kyar tai shiru tana murmushin data dade batai irinshi ba dimples dinta nawani irin lotsawa, dukan cinyan Omari Abdallah yayi yace "ehen nurse zokiga Ya Omari yaji ciwo a hannu dama dazu yabige da table ko Ya Omari?" kallon Abdallah Omari yayi, Abdallah ya kannemai ido hakan yasa Omari ya kalleta suka hada ido yace "y..y..uhm" da sauri Abdallah ya fizge hanunshi yaja hanun riganshi sama yace "zoki gani nurse" make kafada tayi ahankali tana leken hanun nashi daga inda take zaune tace "aini banga ciwo a hanunba, in bigewa ne jamai kawai za'ayi zai dena zafi, kajamai" da sauri Abdallah ya kwalalo ido yace "ni? Wai bakiga katon hanun Ya Omari bane kaman na Ya Marwan" murmushi yayi ya kalli hanun ya Marwan din dayay kaman baya jinsu nanko kunenshi nakan duk abinda suke cewa, juyowa yayi ya kalli Nadeera itama shitake kallo ya nuna mata hanun Ya Marwan yana cemata look yana nuna mata manyan muscles dinshi Yana nuna mata ta kalla, makemai kafada tayi taki kallo, turo mata baki Abdallah yayi hakan yasa kaman daga sama tace "wlh kacika shagwaba" hararanta yayi shima harsaida tai murmushi yace "nakai ki?" da sauri tace "ni? Ni ai banda shagwaba" tabe baki yayi yace "wai talle kema audi gori" kama baki tayi tace "wai a ina kaji hausa? You don't look like a hausa man" murmushi yayi yace "kema u don't look like a hausa girl shagwababbiya kawai" makemai kafada tayi ta kalli Omari daketa kallon su kaman yasami film yanajin son kanin nashi aranshi tace "dan Allah waini shagwababbiya ce?" girgiza mata kai yayi ya tallabe keyan Abdallah yace "don't mind him lil sis keba shagwababbiya bace" dan murmushi tayi tana komawa jikin