Author : Zahra Surbajo Category : Romantic Hausa Novels
shine halin da mijinta yake ciki wanda batasan A Wanne hali yakeba.
Wasu ƙartine sukazo da wasu manyan bulalai tana ji tana gani aka fara dukanta dasu wanda ko goma ba ay mata ba ta saki futsari dan azaba,taba kururuwa.
Seda suka ga ta galabaita sannan suka barta kwance jinajina.
******
"Kamar yadda sarauniya ta kawo Shawara ranka ya daɗe hakan zaa daure ayi,aje ga uwar masarauta,dan samu acire wazeer daga wannan hali da yake ciki"cewar ɗaya daga cikin ƴan majalisar sarkin,bayan ya sanar dasu shawarar sarauniya.
Haka ya dinga sauraran raayin kowa inda kowa ya gamsu cewa aje ga uwar masarauta.
"to tunda kowa ya gamsu,da aje gareta,to masarauta ta gamsu zaaje ɗin dan haka aje asanar da boka muna nan tafe."Cewar sarki.
Koda akaje gurin boka da saƙon sarki,amsawa yayi sannan ya shiga cikin bukka, ya fara kimtsawa dan tafiya gurin uwar masarauta.
Saida akayi sallar laasar sannan aka kawo motoci na alfarma sarki da muƙarrabansa suka shiga boka ma yazo yashiga aka ɗunguma zuwa gidan uwar masarauta dake can bayan gari.
Wata ƙatuwar Bishiya ce me girman gaske,wacce kallonta kaɗai nasa mutum ya ji tsoro.
Bayan sun firfitone boka yayi gaba yana wasu surkulle wanda take bakin kogon jikin bishiyar ya fara hayaƙi.
Ya jima yana yi kamin ya dena,wata iskace ta fara kaɗa ganyen bishiyar da ƙarfi gamida ƙara kamar na guguwa,a daidai nan ne boka ya fara magana.
"Ya ke uwar masarautar roman,sarkin romanne gabanki yazone da buƙatat ki gafarci ɗan uwansa wazeer salman bisa laifin ƙin kwanan turaka da matatsa kamin ya aureta,ya saɓawa umarninki"
Wata iskace me girman gaske ta ƙara kaɗawa,inda wani ƙaton ganye ya faɗo daga kan bishiyar ɗauke da rubutu,bokane ya ɗauka sannan ya fara karantawa da ƙarfi.
"Uwar masarauta ta amshi kokenku,sede kamin ta yafe masa dole ne akwai Sharruɗan da zata gindaya muku,in kun amince dasu kan kuje gida wazeer ze samu lafiya ."Shuru ya ɗanyi sannan yaci gaba da karantowa.
"Sharaɗin farko shine sarauniyar jazbeer nada ciki"
Da sauri sarki umar ya miƙe tsaye dan vasu san tana dashi ɗinba se yanzu,murna da tsorone suka bayyana a fuskarshi lokaci guda.
Bokane yaci gaba da karantowa",abu na biyu wannan ɗa da zata haifa ko so ɗaya kada yasha nononta,sede akaiwa hadima hindou shi,ta shayar dashi a magarƙama ya rayu acan tare da ita na tsawon shekaru goma,bayan wannan wa'adi ya cika zaa sallami hindou daga wannan magarƙama tare da wannan ɗa ba tare da wani yayi yunƙurin ƙwacewa ba,da zaran anyi hakan wazeer ze samu lafiya"
Tun kan boka ya gama karantowa sarki ke fifita,taya tsawon shekara ashirin da auransa be samu haihuwaba se yanzu Allah ze basa ace ya salwantar da ɗan nasa.
To kuma haka ze bar ɗan uwansa a haukace har ƙarshen rayuwarshi.
Mude je zuwa
[8/14, 06:43] Ummu Fadila: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*KWANAN TURAKA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra Surbajo*
*Bissmillahirrahmanirrahim,wannan littafi me suna asama na kuɗine,kabiya kanka karanta dan gujewa cin gumin da banaka ba*
*paid book 500 for normal class*
*1k for Vip,banbancin shine a vip zaki samu damar karanta paid book ɗina na baya,wanda baki siya ba,sannan zaki sami damar karanta sabon littafin tantaɓara ba tare da kin biya*;
*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*
*07044600044 Aturo shaidar biya tanan*
*3*
......Hankalin sarki umar in yayi dubu ya tashi,dan in banda gumi ba abinda yakeyi.
Bakinshi na kakkarwa,yacewa boka"to kuma babu wani zaɓi sede wannan ɗin kawai?"
"Uwar masarauta bata vada zaɓi sede eh ko aa dan haka zaɓi na gareka me ƙasar roman,sannan ku sani duk tsayin lokaci in aka karya wannan yarjejeniya to duk abinda ya biyo baya ku kukaja sannan wazeer salman baa amince ya ƙara muamalar aure da hindou va har se bayan shekaru goman da aka faɗa muku,in aka ƙi bin wannan doka matsalace babba ga wannan ƙasa baki ɗaya"cewar boka.
Sarki bashi da sauran magana haka ya koma gida gurin sarauniya jazbeer jikinsa a mace.
Bayan ƴan rakiyar sarki sun fitane,jazbeer ta tako taxo gaban mijin nata cike da kwarkwasa ta zauna a ƙasa ta kwantar da kanta akan cinyarshi tace a tausashe"Sarki me cikakken iko da ƙasar roman,inaso ka natsu ka kwantar da hankalinka kaimin bayanin damuwar datasa kazo gareni acikin wannan yanayi da banji daɗinsa ba".
Tausayin matar tashine ya kamashi dan haka da ƙyar yace"sarauniya jazbeer,uwar masarauta ta shaidamin cewa kina ɗauke da juna biyu, kuma ɗa namiji zaki haifa,"
Wata irin faraace ta bayyana a fuskarta ga wasu hawaye sirara dake biyo kyakkyawar fuskarta,tace murya na rawa"in na fahimceka kana nufin na kusa haifa maka magaji kenan?"
"Hakane sarauniyata,sede ba tabbacin ze gajenin dan na yarda ɗan uwana ya samu lafiya acan gurin uwar masarauta."
"Inaso kaimin bayanin me aka sanar dakai,wacce hadaya ce zakayi dan samuwar lafiyar wazeer salman?"
"Ɗan dake cikinki zaa ba hadima hindou matar wazeer salman ta shayar dashi daga lokacin da kika haifeshi, har tsawon shekaru goma,kuma zaa sallameta daga yari in ba itace ta ajiye ɗanba da kanta kar wanda ya ƙwace mata,"
Kuka sarauniya tasa ta kife ajikin mijin nata,dan tasan dolene a aykata abinda uwar masarautar tace,
Ta jima tana kuka kamun daga bisani ta share hawayenta ta ɗago ta dubi sarki umar tace"na amince ranka ya daɗe Allah kuma ze bamu ikon cinye jarabawarmu,karka damu insha Allahu zata bar mana ɗanmu tare damu."
Sum jima sina ƙwararawa junansu guiwa sannan kowansu ya gamsu,sarki ya tura aka sanar da boka ya faɗawa uwar masarauta sun amince ta yafewa wazeer salman.
A daren ranar wazeer salman ya dawo hankalinsa, koda ya dawo ba abinda ya fara tambaya se inda matarsa hindou take.
Lokacin da yay arba da hindou a magarƙama ba ƙaramin takaici yayi ba,itako taji daɗin ganinsa cikin hayyacinsa.
******
Tun kan sarki ya fito faɗa wazeer ya iskeshi acikin gida a falonsa zaune da sarauniya jazbeer.
Da sallamarsa ya shiga falon da sauri sarki ya taso yazo ya rungumeshi yana faɗin "nayi farinciki da samuwar lafiyarka ɗan uwana salman"
"Nagode ranka ya daɗe sosai"cewar wazeer sannan kowa ya zauna.
Gaisawa sukayi da sarauniya jazbeer,sannan ya dubi sarki yace"ranka ya daɗe me ƙasar roman nazo gareka ne kasa a sallami me ɗakina daga gidan kason da kasa asata tunda na warke"ya faɗi cikin ladabi.
Miƙewa sarki umar yayi ya taka daga inda yake zuwa gaban wani ƙaton hotonsu shida salman ɗin riƙe da takubba,ya goya hannunsa a bayansa ya ɗaga kansa sama yace.
"Salman matarka bazata fito daga gidan kaso ba har se nan da shekaru goma masu zuwa"
A zafafe salman ya miƙe tsaye jikinshi na rawa, bakinshi na kakkarwa yace"laifin me tayi me munin data cancanci hakan?"
"Uwar masarautace ta gindaya hakan,kamun ta amunc ta yafe maka laifin kin kwanan turaka da kayi,bayan muna mun sallama ɗan cikin dake jikin sarauniya amatsayin hadayar warkewarka."
Kuka ya fashe dashi hawaye na biyo idonshi kamar mace yace "lalle ka nuna soyayya gareni ɗan uwana,kuma nagode maka na jinjina maka bisa wannan namijin ƙoƙari da kayi,sede bazan iya zama tsawon shekaru goma ina kallon hindou a yariba bazan iyaba ranka ya daɗe,zamana a haukace ze fimin sauƙi akan hakan"ya faɗi yana kuka.
Rungumeshi sarki umar yayi yana faɗin"salman dama ance maka abune me sauƙi sarki kamarni barin ɗansa ɗaya tak a duniya ya rayu a yari tun daga haihuwarsa,ay se dole,don Allah salman ina sonka da ƙaunarka kar ka ƙi biyayya ga wannan umarni "cewar sarki shima hawaye na biyo idonsa.
Sun jima sarki na roƙon wazeer kamin ya gamsu zeyi biyayya ga dokar.
*******
Wazeer seda ya kwashi watanni tara besa hindou a idonsa ba sakamakon sauya mata gurin zama da sarki yasa akayi a ɓoye b tare da sanin wazeer ɗin ba.
Yau sarauniya jazbeer ta tashi da ciwon naƙuda wanda sosai tasha wiya,kamin Allah ya sauketa lafiya ta haifi ɗanta me tsananin kama da ita, namiji.
Rungume ɗan tayi ajikinta tana kuka me tsuma zuciya,na rabuwa da zatayi dashi yanzu,shi kanshi sarki seda yayi kukan rabuwa da ɗa nasa.
Huɗuba ya masa inda ya raɗa masa suna Hameed
Tana ji tana gani ya amshi ɗan ya fice dashi,ko wazeer be bari ya ga ɗanba,dan kar ya maƙale masa yace se yaga inda aka boye hindou.
Sarki da kanshi yakaiwa hindou jinjirin,tayi mamakin jin vayanin da sarkin ke mata,bakinta na rawa tace.
"wannan zalincine ranka ya daɗe,aljanu suna wasa da hankalinku azuwan al'ada,taya zaka raba uwa da ɗanta azuwan al'ada wallahi ƙaryane ba abinda ze faru inkun ki biyayyar,"
Tsawa sarki umar ya daka mata sannan yace,"kin fi mu hankali kenan,koba biyewa zantukanki bane ya jefa salman halin hauka wanda duk kece silar faruwar komai,to ni bana faɗi ayi jayayya"yana kaiwa nan ya ajiye mata jinjirin dake ta faman tsala kuka ya juya ya fice,
Da gudu sarauniya jazbeer ta ɓoye a lungu gudun kar ya ganta dan tun fitowarshi ta biyoshi abaya.
Koda taga inda yakai mata ɗa,da sauri takoma inda ya barota gudun kar ya zargi wani abu.
Koda ya koma rarrashinta yaci gaba dayi,sannan ya shirya ya tafi fada dan rana tayi.
Bayan fitarsa sarauniya shigar badda kama tayi ta koma gun hindou,inda ta samu se jijjiga yaron take yana tsala kuka itama tana tayashi.
Masu gadin gurin ganin sarauniya sosai sukai mamaki sede kalamunta ya firgitasu"wallahi matukar wani ya faɗi labarin zuwa na nan sena sa an kasheshi,"
Ayko jiki na ɓari suka buɗe mata ƙofa ta shigo lokacin da hindou ta ganta da gudu tayo kanta tana faɗin"ranki ya daɗe ki riƙe ɗanki karki vari arabaku zalincine"ta faɗi tana kuka.
Ɗaukar ɗan jazbeer tayi tana share hawaye tace "hakane hindou nasani sede ban isa in karya dokar sarki bane shiyasa nai biyayya."
Ɗan na jin ɗumin mahaifiyarshi yayi shuru yana tsotsan hannu,wasu hawayen tausayinsune ya zubowa hindou tace"ranki ya daɗe ki bashi nono yunwa yake ji"
Ayko sarauniya batai ƙasa a guiwa ba,ta ciro nono ta fara bashi nono,auko carab ya karɓa yq fara sha.
Seda yasha ya ƙoshi sannan bacci yayi gaba dashi.
Shuru sukayi su duka sannan hindou tace"ki daure ki shayar da ɗanki,kar Allah ya tambayeki,kinga ni bani da nonon bashi"
Haka suka tsara tsakaninsu kan zata dinga zuwa shayar dashi a sirrance.
*******
Injinan matsar nono sarauniya tasiyo masu yawa asirrance,ta matsi ruwan nononta,tasa acooler da vaze barshi yay sanyi ba da feeder masu yawa ta tafi a sirrance takaiwa hindou,
.Cikin dare hindou take bashi har wayewar gari ta yadda baya kukan yunwa,
Sarki duk abinda Hameed ze buƙata na sutura ba abinda be kaiwa hindou va,inda aka ƙara ƙawata inda take tsare da kayan alatu,dan ɗan sarki Hameed.
Sarauniya kullum seta zo ta shayar da ɗanta tai masa wasa sannan take tafiya.
BAYAN SHEKARA BIYAR
Prince Hameed ne ke tafiya a tsakar gurin da aka tanadar musu shida hindou yana wasansa tana tayashi,sosai take ƙaunar yaron bada wasa ba,dan ta shaƙu dashi,gashi albarkacinshi tasamu walaha a inda take.
Kullum da tunanin mijinta take kwana take tashi sede ta rasa wa zata tambaya ko yananan ba.
Shiko wazeer kaɗaicin matarsa ne yasa ko shiga mutane bayayi shima ya zauna a ɗaki zaman jiran dawowarta,dan yana son hindou da duk zuciyarsa.
Yau sarauniya ta shigo gurin su hindou,tunda tun bayan yaye prince tana jimawa bata zoba dan har sati tana kaiwa.
Bayan sun gaisane ta kalli hindou tace"wai ke hindou bakya kewar mijinki ne,?"
Da sauri hindou ta ɗago tana kallonta hawaye na biyo idonta,tace"inayi ranki ya daɗe amma shi ay ya manta dani"
Kwashe duk yadda akayi jazbeer tayi ta faɗawa hindou sannan ta ƙara da cewa"in har kinason ganinsa ni zan sa hakan"
Da sauri hindou tace "inaso ranki ya daɗe"
Saida dare yayi sosai sannan hadimin da jazbeer ta wakilta yazo ya ɗauki hindou yazo,ya mata jagoranci.
Ƙofar abuɗe take wacce wazeer ke ciki,hindou a sanyaye ta tura ƙofar ta shiga,rungume da hameed a hannunta.
Muje zuwa.
[8/14, 06:43] Ummu Fadila: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*KWANAN TURAKA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra Surbajo*
*paid book 500 kasayi wannan ka karanta tantabara free,*
*Zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*
*07044600044 Shaidar biya*
*7*
........Wazeer ya shiga damuwa ba kaɗan ba,kullum cikin kallon wayarsa yake yaga ko zega kira daga nigeria amma shuru,
Can ɗakin hindou na magarƙama yaje kewaye dan yaji daɗi,dan kewarta yi take kamar ta kasheshi.
Kayanta na ɗakin har yanzu dan haka kayan ya fara ɗauka yana shinshinawa,kwatsam idanunsa suka sauka kan agogo da numbar wayarshi daya ba hindoun.
A zabure ya miƙe tsaye riƙe dasu a hannunsa,wata irin mahaukaciyar zuface ta shiga keto masa ta koina.
Me hakan ke nufi,hindou mantawa dasu tayi? koko hakan na nufin ta gujeni kenan,?"kai haba ina hindou bazata gujeni ba,tabbas akwai abinda ke faruwa ba daidai ba"sune zantikan dake fita bakin wazeer ba tare da yasan yana yinsu ba.
A hargitse ya fice daga ɗakin,ya nufi sashin shi,kallo ɗaya zaka masa ka san baya cikin kwanciyar hankali, ko fadawan dake gaisheshi da masu take masa baya baya tatasu.
Koda ya shiga ɗakinsa kulle kansa yayi,ya zube bakin ƙofar kawai seya fashe da kuka kamar ƙaramin yaro.
Yajima yana kukan kamin ya rarrashi kanshi yayi shuru,ta ina zema fara ne,wannan itace tambayar da yakewa kansa.
Haka wazeer ya koma kamar mahaukaci sabida hindoun sa,ba inda yake zuwa yana ɗaki yana tunanin a inda ze samo hindou.
*********
Yau sarauniya jazbeer ta shirya fita yawan rangadi da prince hamid,dan ta nunawa masarautar magajinta.
Cike take da farinciki sabida sarki umar ya sahale mata yin hakan.
Masu shirya shi ne suka shigo dashi fess dashi se ƙamshi yake,gwanin burgewa.
Da sauri jazbeer ta miƙe ta isa gabanshi tana masa waƙoƙi irin na ƙauna da harshen su na romanawa.
Miƙa hannun da zatayi ta ɗaukeshi se gani tayi an sureshi anyi sama dashi ana jujjuyashi asaman kamar wata takarda,se ƙwala ihu yake yana kiran ta ta taimakeshi.
A gigice jazbeer tasa ihu tana faɗi cikin ƙaraji"aa uwar masarauta,karki cutar dashi nice ,nai miki laifi ki ƙyalemin ɗana, don girman Allah"ta faɗi tana ihu.
Ya jima ana juyashi asama kamin a faɗo dashi ƙasa,tim.
Da gudu tayi kanshi ta ɗagoshi,tana kiran sunansa,hannunsa da ƙafarsa sa bakinsa ta samu duk sun shanye,se zubar da miyau yake.
Wata uwar ƙara ta saki ta faɗi gurin sumammiya.
Sarki ihunta ya jiyo yana ɗakinsa da gudu ya fito zuwa gareta,sede abinda ya gani ba ƙaramin razanashi yayiba.ɗanshi acikin halin nakasa wanda ko tantama bayayi uwar masarautace tayi hakan.
Taimakon maaikatan ɓangarenta ya nema aka kwashesu a mota se asibiti,dan gaba ɗaya ya rasa me zeyi.
Wazeer jin hayaniya tayi yawane ba kamar yadda ya saba jiba yasa ya miƙe ya taso ya fito dan yaji hayaniyar harda ta me martaba,
Sako ƙafarsa waje keda wiya,se ganin duhu yayi a idonsa,murje idon yashiga yi da duk ƙarfinsa sede duhun na nan be yayeba.
Wasa wasa wazeer na ɗaukar lamarin wasa se gani yayi idon ya rufe ruff ko yaso buɗewa be buɗuwa.
Nanfa ya shiga lalube yana karanto duk adduar datazo bakinsa,jikinsa na karkarwa,masu tsaron lafiyarsa ne suka farga da halin dayake ciki,nan sukai kansa kai masa agaji.
Su sarki umar zuwansu asibiti ba jimawa jazbeer ta farko,se kuka take tana riƙe sarkin wanda shima hawayne ke biyo idonsa.
Shiko prince duk wani abu da zaay masa an masa inda aƙarshe de likitan ya shaidawa sarki sede suyi haƙuri ya riga da ya nakasa.
Tashin hankalin da suke ciki baze faɗuba.haka suka tattara suka dawo gida,shigarsu gidan ne kuma suka iske labarin makancewar wazeer.
Sarki umar kuka ya fashe dashi lokacin da yay arba da halin da ɗan uwansa ya shiga,cikin kukan yake faɗin"in na faɗi magana ko na zartar da hukunci seka ƙi yard salman yanzu ka duba kaga abinda kuka jawo mana,prince nacan ta shanye shi kai kuma gaka ta makantaka duk meye wannan?"ya faɗi cikin kuka"
"Yaya komai da sanin Allah,nide na faɗi maka nadena yin biyayya gareta koda kuwa kasheni zatayi,kawai kaimin addua,in zan warke zan warke in kuma shikenan to ina godiya ga Allah,dama idanun da ba hoton hindou cikinsu ay basu da amfani a gurina"cewar wazeer cikin dauriyar murya.
Haka ranar sarki gurin wazeer ya kwana in banda kuka na tausayin ɗan uwan nasa ba abinda yake yi.
*******
Hindou da kanta ta taci gaba da wankan jego kamar yadda taga iya jummai na mata.
Hankalin hindou be tashi va seda taga abincin da zataci babu shi agidan.
Ga mahaifinta dake kwanca yana fama da cutar shanyewar ɓarin jiki komai se an masa gashi abincin da zata bashi ma babu.
Wai wacece hindou ne?
Haifaffiyar garin yako a ƙaramar hukumar kiru can jihar kano.
ƴace ga malam kabeeru headmaster,mahaifiyarta ta rasu tun hindou na yarinya,shine riƙonta ya koma hannun iya jummai matar mahaifinta daya aura bayan mutuwar mahaifiyarta.
Iya jummai ta shanye malam beda kataɓus agidansa se abinda jummai tace,shiyasa tsoronta ma yakeji vada wasaba.
Hindou ba irin azabar da bata sha a hannun iya jummai amma mahaifinta betaɓa kalla ba bare ya tanka.
Ana wannan tsukunne taba umma me kai yara aykatau ƙasashen waje,ita,dan itama akaita ta samo mata abun duniya sabida ita bata taɓa haihuwa ba.
Bayan tafiyar hindou ƙasar romania ne mahaifinta baƙinciki yasashi ya yanke jiki ya faɗi yasamu wannan ciwo.
Tunda iya jummai taga ya nakasa ta fara neman maraba dashi amma ta rasa,burinta ta fice tabar ƙasar ta tafi saudiyya,ta yadda baze ma ƙara ganinta ba sabida bazata iya bautar ƙazantarshi va.
Ana hak tsawon shekaru,shine hindou ta dawo wanda hakan ne yaba iya jummai damar guduwa saudiyya tabar hindou da jigilar kulawa da uban nata itade ta kama kanta.
Muje Zuwa.
[8/14, 06:43] Ummu Fadila: https://chat.whatsapp.com/DQsgTQR1BnJJlytCN4E670
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*KWANAN TURAKA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra surbajo*
*500 ne vip 1k kisiya kisamu damar karanta littafin tantabara kyauta*
*Zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*
*07044600044*
*8*
......Yau Hindou tunda suka tashi taje ta gyarawa mahaifinta shimfiɗarsa tai masa wanka,ne kuma ta dawo tsakar gida ta zauna tunanin me zasu ci kawai takeyi.
Hawaye ta share masu zafi lokacin data tuno mijinta wazeer,ko awanne hali yake oho,miƙewa tayi tasa hijabi ta fice neman abinda zasu ci.
Gurin Abashe me kanti taje,bayan sun gaisane tai ƙasa da idonta tace"dama bashin abinda zamu karya nazo ka bani zan kawo ma kuɗin"
Murmushi abashe yayi yace"hindatu tun kan kibar ƙasar nan nake sonki to amma kika
nuna ke ba haka ba,yanzu tunda kin zama sauran fararen fatar kawai mu ƙulla harƙalla koda yaushe zan dinga baku abincin ni kuma kidinga bani kanki"
Runtse ido hindu tayi hawaye na biyo idonta,da ace tana da yadda zatayi da ba makawa seta kwasa masa mari amma haka ta daure ta saita kanta sannan tace.
"yanzu de kabani zan kawo kuɗin inyaso daga baya mayi maganar dakazo da itan"ta faɗi tana kauda kanta.
Ayko jiki na ɓari yaje ya ɗeɓo mata kayan tea da biredi masu yawa harda shinkafa da wake,kaya shirgi guda,ya bata,kallonshi tayi tace"ba me yawa nake so ba dan bani da halin biya"
"Karki damu kawai kyauta na baki wannan ma kaɗanne in har zaki dinga biyamin buƙatata"ya faɗi yana murmushi.
Ko godiya batai masa ba ta ɗauki