Chapter 4 Reading KWANAN TURAKA COMPLETE BY ZAHRA SURBAJO.txt Arewa Novels

KWANAN TURAKA COMPLETE BY ZAHRA SURBAJO.txt

Author :  Zahra Surbajo Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   4 / 11

9K to 12K   out of 30.2K words

hameed aƙasa ki duba kiga yadda taimasa rauni shine kike cewa bazaa hukuntata ba"

Ko ajikin bahijja tace"to seme dan ta tureshi,ubanshi fin ubanta yayi da har zaku kamata da duka"

Cikin de ƙanƙanin lokaci guri ya hautsine,hakanne ya janyo hankalin sarauniya jazbeer da sarki umar dan an kira waya an sanar dasu.

Basui ƙasa aguiwaba suka nufi gurin,sosai hankalin jazbeer ya tashi ganin yadda prince yaji ciwo.

Shima sarki umar da aka masa bayani fusata yayi ya dubi bahijja yace"ta kada ɗan nawa shine kije hana aymata hukunci."?

"Ɗanka ay befi ɗan ɗan uwanka ba,dan haka bazaa daketa ba dan itama jininku ce"cewar bahijja ba tare da tsoron komai ba,dan lokaci yayi da zata ɗauki fansar kaita yarin da wazeer salman yasa akayi a shekarun baya kan laifin da ba ita tayiba,shiyasa tunda ta samu nurayya tasha alwashin seta ce shi ya mata cikinta.

Cikin rashim fahimta sarki umar yacs"ƴar waye ita ɗin?"

"Ɗan uwanka wazeer salman shi yamin cikinta agidan yari na haifeta"ta faɗi ba tare dataji tsoron komai ba.

Wani jiri ne ya kwashi sarki umar da sauri fadawa suka riƙeshi.

Ganin batun babbane yasa yace "ku kawota ɓaungaren wazeer ita da ƴar tata yanzu"ya faɗi lokacin daya juya da sauro zuwa sashin na wazeet ɗin da besan wainar da ake toyawa ba.






07044600044
[8/14, 06:48] Ummu Fadila: https://chat.whatsapp.com/DQsgTQR1BnJJlytCN4E670

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*KWANAN TURAKA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra surbajo*


*500 ne vip 1k kisiya kisamu damar karanta littafin tantabara kyauta*

*Zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*07044600044*


*11*


......Wazeer jin hayaniya a falonshine ya tasheshi a bacci,miƙewa yayi yana laluben hanya ya fito,inda sukaci karo sa sarki umar dake ƙoƙarin zuwa ɗaukoshi.

Ruƙo masa hannu yayi yamasa jagaranci,shiko faɗi yake"yaya lafiya kuwa meke faruwane agidan?"cewar wazeer yana murmushi.

"muje falon zakaji koma menene salman"cewar sarki.

Koda suka shigo falon a ruɗe bahijja ta kama nurayya ta rungume,dan taji tsoron ganin wazeer ɗin dan mutum ne me kwarjini da haiba dake cika idon mutane.

Bayan sun zaunane sarki umar ya dakawa bahijja tsawa da cewa "saketa tazo nan"ya faɗi yana nuna nurayya.

Ba musu bahijja ta saketa jikinta na rawa,Nurayya takawa tayi ta isa gaban sarki umar tana turo vaki gaba.

Hannunta sarki Umar ya kama ya kamo na wazeer ya sarƙe hannayen nasu cikin na juna.ya buɗe vaki da nufin magana amma jijjigar da hannayen suka fara itace tasashi yin shuru sakamakon ƙarajin daya jiyo wazeer nayi

Bakin wazeer na kakkarwa yake faɗin "hindou hindou hindou kin dawo ne?"faɗuwar da yayi jagwabce tasashi yin shurun dole.

Sarki Umar firgita yayi da yanayin na wazeer, dan betaɓa ganinsa ahakanba se bigebige yake kamar me farfaɗiya.

A karo na farko da nurayya taji tausayin wata halitta a zuciyarta,duƙawa tayi ta ɗora hannayenta akan ƙirjin wazeer ɗin tana faɗin"me yasameka ka tashi"ta faɗi tana shafo idanunsa dake zubda ƙwallah.

wata irin guguwace ta tashi daga jikin wazeer ta fara yawo asama kamin ta fice ta window falon.

Kowa ya tsorata agurin amma banda nurayya,jijjiga wazeer kawai takeyi,ayko ga mamakinsu zumbur ya miƙe zaune,mamakinsu be ƙaruba saida suka ga idanunsa a buɗe tangaras ba tare da alamun makantaba yabu ɗesu yana kallon kowa na gurin.

Hamdala ya shiga yiwa Allah gamida kirari,dan ko kaɗan bejin ciwo a idanunsa kuma ganinsa ya dawo.

A hankali ya kalli nurayya kallo na tsanaki,ya jima ahakan sannan ya dubi sarki yace "ina hindou take?"

Sarki umar wanda tun ɗazu tsabar firgici da mamakin faruwar komai yasa ya kasa magana zumbur yayi yace"wacce hindou kuma salman,mufa nan munzone muji daga gareka,dan wancan matarce tace kaine kai mata cikin wannan matashiyar yarinya dake gabanka agidan yari,shine mukazo muji gaskiyar magana."

Murmushi wazeer yayi me ƙayatarwa yace"ko makawa babu wannan ƴa jininace da hindou,jikina ya bani hakan,amma wannan mata ni banma santa ba,dan haka dogarai ku kamata kuje da ita kuita dukanta har sai ta faɗi gaskiyar inda ta samo wannan ƴar,dan ko kama ta jini bata da ita tsakaninta da ita hakan na nufin ba ƴarta bace"cewar wazeer ba tare daya ɗauke idonsa akan nurayya va.

Bahijja ihy tasa tana faɗin"wallahi ƴatace ni na haifeta kuma kaine kamun cikin ta sake faɗi tana ihu lokacin fadawa suka ƙaraso kanta.

Wani kukan kura nurayya tayi ta faɗa kan bahijja tana kareta cikin dakewa nurya dake nuna rashin tsoro,tace"wallahi bame taɓata agurinnan,in kunce ita ba mahaifiyata bace to wacece ta haifeni?"ta faɗi cikin ƙaraji.

"Ganinan ƴata nice mahaifiyarki"cewar hindou dake tsaye bakin ƙofar shigowar riƙe da akwatin kayanta idanunta na zubar da ƙwalla.


FREE PAGE YA ƘARE MESON CIGABAN SEYA BIYA 500 KAMIN YACIGABA DA SAMU.

TAKU HAR KULLUM

ZAHRA SURBAJO.




07044600044
[8/14, 06:48] Ummu Fadila: https://chat.whatsapp.com/DQsgTQR1BnJJlytCN4E670

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*KWANAN TURAKA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra surbajo*


*500 ne vip 1k kisiya kisamu damar karanta littafin tantabara kyauta*

*Zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*07044600044*


*12*


A gigice wazeer ya miƙe ganin hindou agabansa,tana hawaye,da gudunta ta saki jakar kayanta ta nufeshi,da sauri shima ya nufota,suna haɗewa suka rungume juna, suka fashe da kuka atare.

Sosai wazeer ya ƙanƙameta ajikinshi yana hawaye yama rasa mezece dan tsananin farin ciki.

Sun jima ahaka kamin muryar nurayya ta katsesu da cewa,"taya kika zama uwata kimin bayani.?"ta faɗi agadarance.

Waigowa hindou tayi ta dubi nurayya hawaye na biyo idonta,tace"bani da tabbacin ko keɗin ƴatace,kawai de abinda nasani shine,ranar dazan bar ƙasarnan na haihu abakin katanga,saidai jin abinda na haifa beyi kukaba kuma be motsaba yasa na ɗauka matacce na haifa ban waiwayaba na tafi,yanzu nazo ana tuhumar mijina da laifin shiɗin mahaifinkine,kuma ya gamsu shi ya haifeki,a matsayina na matarsa dole inso ɗan daya haifa koma da waye"ta ƙarasa maganar tana kuka.

Rungumota wazeer yayi jikinshi yace ba tare da damuwar komai ba,"hindou,wannan ƴa takice,zuciyata tavani tabbacin hakan,amma idan waccan shaiɗaniyar tace ba taki vace zamuje ayi gwajin dna,kuma wallahi inhar ya tabbata takice hukuncin kisa zan ƙaddamar mata"ya ƙarasa maganar yana nuna bahijja.

Ayko agigice bahijja ta kife gaban hindou tana riƙe ƙafarta tace cikin kuka"wallahi takice,tsintarta nayi nima"daga haka ta kwashe komai daya faru ta faɗi aƙarshe ta ƙarashe da neman afuwar wazeer bisa yunƙurin ɓata masa suna da taso yi.

Da gudu nurayya ta ƙarasa jikinn iyayenta ta rungumesu tana kuka,suma rungumeta sukayi,suna sa mata albarka,hindou,kallonta takai gurin bahijja tace tana murmushi,"bahijja nagode bisa riƙemin ƴa da kikayi ba tare da kin cutar da ita ba,nagode sosai da hakan,sannan ina miki albishir da cewa munyafe miki baki mana laifin komai ba kuma bazaki mana ba,kamar yadda kike uwa ga nurayya ina roƙonki da kivi gaba da zama amazauninki na uwa sabida kun shaƙu sosai da ita."ta faɗi tana murmushi.

Bahijja inbanda godiya ba abinda takeyi,dan ta ɗauka waadun numfashinta ne yazo yasa taiwa wazeer sharri.

Sarki umar ajiyar zuciya ya sauke me girman gaske,yace"wannan lamari sede ayi godiya ga Allah daya warware komai cikin sauƙi,dan haka se mu gode masa,Allah ya kawo ƙarshen matsalolin wannan gida amin,hindou ina miki barka da zuwa amatsayin yayan mijinki ba wai a matsayin shugabankiba"ya faɗi yana murmushi.

Duk maganar da suke hankalin hindou nakan hameed ɗanta wanda duk tsayin zamani da sauyawar halitta bazata kasa shaidashiba.

takawa tayi a hankali ta isa inda take zaune dagalo dashi ga raunukan da nurayya taji mishi ɗaxu.

Hannunshi ta kama ta durƙusa agabansa,tana kallon fuskarshi,ayko idonshine ya sauka akanta,azabure ya faɗa jikinta yana wani gwaranci dake nuna yasanta.

Fashewa hindou tayi da kuka ta rungumeshi,tana son hameed har ranta,tana jinshi kusa da zuciyarta,amma jibi yadda ya koma,wanda ko tantama batayi, uwar masarautace tai masa hakan.

Jazbeer ce ta taso ta iso inda suke,tana share hawayenta tace"kinga yadda ɗanki ya koma ko,sanadin karya dokar uwar masarauta,wanda hatta wazeer saida ta makantashi yaune ya warke"ta faɗi a raunane.

Sallamar bahijja da sauran dogarai sarki yayi suka fice, sannan yace"dukade mu cigaba da addua kamar yadda waxeer ya warke shima zai warke."

"Wai wacce tsinanniyace uwar masarautar dake gwada muku rashin imani haka kuma kuke girmamata?"cewar nurayya afusace.

Da sauri jazbeer ta rufeta baki tana faɗin"kiyi saurin tuba ƴata ga uwar masarauta,kar fushinta ya sauka akanki"

"Ko ƴar uban wacece ita ni bana tsoronta,koma wacece ita"cewar nurayya batare da tsoron komaiba.

Ganin bazata daina janyo musu masifar bane,tasa sarki ya musu sallama ya fice zuwa fada,jazbeer ma gida ta wuce.

prince ko dama hindou ta hana a tafi dashi, dan haka ɗaki na musamman aka kaishi a ɓangaren nasu,inda itama nurayya aka bata nata wanda hakan sosai yay mata daɗi,duniya sabuwa.

Ranar wazeer da hindou ansha soyayya wacce innace zan zanyanota littafin cikewa zeyi.

Wazeer sosai yasamu natsuwa,haka itama hindou to anjima baa haɗuba.

********

Tuni bahijja hindou tasa ta dawo nan sashin nasu ɗakin nurayya kamar yadda nurayyar ta buƙata,ba irin abin arziƙin da hindou batai mata ba,ayko bahijja ci gaba tayi da kulawa da prince da nurayya,dan tausayi yake bata halin dayake ciki.




07044600044
[8/14, 06:48] Ummu Fadila: https://chat.whatsapp.com/DQsgTQR1BnJJlytCN4E670

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*KWANAN TURAKA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra surbajo*


*500 ne vip 1k kisiya kisamu damar karanta littafin tantabara kyauta*

*Zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*07044600044*


*13*



Tunda hindou ta dawo kusan matsalolin cikin fadar ta roman cikin kashi ɗari kashi hamsin sun warware,sabida wazeer yanzu ya koma bakin aykinshi,hakan ya taimakawa sarki umar a fanni da dama na gudanar da mulkinsa.

Hameed na samun kulawa daga bahijja da kuma hindou da kanta,ta hanyar zama dashi suna hira.

Nurayya tunda tasan hameed ɗan uwantane take tausayinshi kullum fatanta taganshi yasamu lafiya shiyasa ta ɗauki tsanar duniya ta ɗorawa uwarmasarauta duk da batasan koma wacece hakanva,kawai de tunda itace silar faɗawar danginta cikin masifa taji ta tsaneta.

An sauyawa nurayya makaranta, inda aka maidata ta ƴaƴan manya kuma tana da ƙoƙari sosai ba laifi.

Duk sanda ta dawo makaranta tana zama gurin hameed ta dinga koya masa abinda aka koya mata,duk da baya magana amma haka ze dagale yana kalkonta,itako taita bayaninta.


Sannu a hankali ta dinga bin labarin uwar masarauta inda ta fahimci aljanace,kuma tasha alwashin ganin bayanta da yardar Allah.

Duk wata aya dake cikin Qurani me girma saida nurayya ta rubuceta ta kuma karanta ta tofa aruwan zamzam ɗin data tanada,ganyan magarya tasamu shima ajikinshi saida ta rubuta ayoyin Qurani akan kowanne ganye inda ta shanya ya bushe ba tare da kowa yasan tanayo ba,ta ɗaure abunta a laida.
*********

"ranka ya daɗe kasan wannan taro dolene ayishi tunda uwar masarautace tai kiransa,bama hakaba ay abune da aka saba duk shekara anayi,kaga shekaru sun shuɗe da yawa wanda baayiba"cewar boka lokacin daya isarwa da uwar masarauta saƙonta fa sarkin roman umar.

Gyara zama sarki yayi yace"banƙi ta taka ba boka,inaso kasani wazeer yace bazashi taron ba,kaga hakan matsalace tunda dokarta dolene ahalin gidannan kowa yaje, na rasa yazan ɓullowa lamarinnan"cewar sarkin cikin yanayin damuwa.

"to nide nawa dama isarwa ne kuma na isar dan haka,ni na wuce"cewar boka sannan yawa sarki sallama yatafi.

Sarki jiki ba ƙwari ya koma cikin gida,inda kai tsaye ya isa ga wazeer,lokacin yana zaune da nurayya da hameed tana vasu labarin abin dariya sunayi.

Ganin sarki da kansa a falon nasu ne yabawa wazeer tabbacin ba lafiya azuwan nasa.

iso yay masa sannan suka gaisa nurayya ma tagaisheshi shiko hameed sede kallo.

"Salman uwar masarautace take nemanmu gobe a fadarta"cewar sarki umar kamar yana tsoron faɗin saƙon.

Murmushi wazeer yayi sannan yace"to base kujeba tunda ta nemeku ni meye nawa aciki?".

"Wazeer dole kaje gurinfa inba hakaba komai zai iya faruwa"cewar sarki yana kallon wazeer ɗin.

"ashe ko zata nannaɗe ƙasar roman da abinda ke cikinta baki ɗaya kenan in har sai naje gurinta"cewar wazeer batare da damuwar komai ba.

Duk yadda sarki yaso shawo kan wazeer ya amince da halartar taron ƙi yayi dole ya haƙura ya ƙyaleshi dan taurin kan wazeer bame sauƙi bane.

Sallama yay masa yatafi haushine yasa wazeer ko taka masa beyiba,yabarshi ya tafi da fadawansa.

Nurayya dake zaune can kusa da hameed ba abinda batajiba,dan haka ta lashi takobin zuwa ga uwar masarautar gobe koba da izinin kowaba na gidansu.

Washe gari da wuri tai shirin makaranta kamar gaske tai sallama da gida bayan ta ɗauki ruwan adduarta da ganuen magaryarta da Quraninta ajaka,direbantane ya ɗauketa suka tafi,suna fita a fada tace"kaini gurin taron uwar masarauta"

Ayko direban beyi ƙasa aguiwaba yayi abinda ta buƙata,

lokacin da suka isa gurin taro yayi taro,dan tuni anfara gabatar da abun alada.
Fita tayi ta kutsa cikin taron batare da kowa ya lura da itaba Har taje gaba.


"Uwar masarauta name umartarka daka kawo mata ɗanka hameed a mazaunin hadayar karya duk wata doka tata dakukayi,da hakane kawai zata ƙyaleku."cewar boka ga sarki.

"Ƙarya kike azzaluma,hameed ba rabonki bane,baƙar munafuka,daga yau sena shafe tarihinki a wannan ƙasa koda kuwa zan riski ajalina"cewar nurayya cikin ƙaraji gamida fitowa gaba sosai ta yadda zaa ganta.


wata tsawace ta bayyana agurin gamida rugugin aradu kamar zaai ruwa,sannan wannan bishiya kawai saita kama da wuta,ayko Nurayya laidar rubutunta me ɗauke da tofinta na littafi me tsarki ta wurga da ƙarfinta cikin wutar,

Wata irin ƙarace me firgitarwa ta fara amo agurin,sannan wutar ta dinga harshe kamar zata laso jamaar gurin da gudu kowa yaja baya ciku ko harda sarki umar da mamakin nurayya yacika masa kai.

Ledar ganyan magaryar ta wurga cikin wutar ba tare da tsoron komaiba,ayko faruwar hakan keda wiya ganyan bishiyar ya fara kaɗawa,da ƙarfin gaske inda ya faɗo ƙasa duka,itama bishiyar ta fara girgiza wannan ƙara na ƙaruwa.

Da ƙarfinta ta ɗauko Quraninta ta nunawa bishiyar sannan ta fara karanto ayoyin cikinsa da kanta da ƙarfi,

Boka da gudu yafaɗa cikin mutane jiki shi na ɓari dan yasan yau ƙarshen uwar masarautane yazo,tunda adokar zuwa gurinta baa zuwa da Qurani to yau gashi karantashi ma akeyi.

Cikin abinda be wuce minti gomaba bishiyar ta kakkarye ta faɗi agurin sannan ta kama da wuta, bata dena ci da wutaba har saida ta zama toka nurayya bata dena karatunba.hawaye na biyo idonta sabida zafin wutar sosai yake ƙonata amma taƙi barin karatun.

Bishiyar na gama zama toka,kawai saiga ruwan sama kamar da bakin ƙwarya yawanke tokar gurin ya koma kamar baa taɓa halittar wata bishiya ba agurin,.

Kowa da gudu yafara gabatowa kusa da nurayya dan ganin ta kawo musu ƙarshen uwar masarauta,cikin sauƙi,shiko sarki umar hawayen farinciki ne ke biyo idanunsa ya kasa motsawa agurin,

Itako nurayya yanke jiki tayi ta faɗi agurin sumammiya.



07044600044
[8/14, 06:48] Ummu Fadila: https://chat.whatsapp.com/DQsgTQR1BnJJlytCN4E670

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*KWANAN TURAKA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra surbajo*


*500 ne vip 1k kisiya kisamu damar karanta littafin tantabara kyauta*

*Zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*07044600044*


*14*




A mota sarki umar yasa akasata sannan yashiga direba sa masu tsaron lafiyarshi sukai gida da ita.

Kai tsaye ɓangaran iyayenta yasa aka kaita inda tun kan su iso labarin abinda ya faru acan ya iske su hindou,amma tashin hankalin da suke ciki na buge bugen da hameed keyi shiya hanasu zuwa gun nurayyar.

Aman wani koren abu yake kamar ze amayar da komai na cikinsa,duk sun firgice sun ruɗe ba ita ba ba bahijja ba na wazeer ɗinba.

Shigowar me martaba ɗauke nurayya jazbeer na binshi abayane ya ƙara ɗaga musu hankali,suma iyayen hameed ɗin hankali atashe sukai gurinsu ganin halin da yake ciki.

Nanfa hindu tashiga tofa musu ayoyin Allah,tana shafa musu ruwa akai da fuska,ayko a hankali nurayya ta sauke ajiyar zuciya,ta miƙe azabure ta ɗauka a can fagen dagar take.

Rungumeta waxeer yayi yana shafa kanta ahankali ta dinga sauke ajiyar zuciya har ta samu natsuwa ta shigeta.

A hankali ta ɗago kanta tana ƙare musu kallo har idonta ya sauka kan hameed.azabure tayi kanshi tana faɗin"me yasamu yayana,wayyo Allah."ta faɗi lokacin data kamo hannunsa,zafin datajine yasata miƙewa da sauri zuwa toilet ta ɗauro alwala sannan taxo ta fara karanta masa ayoyin ruqya.

Ayko fa nan ya dinga gunji,yana kakari,yana aman kore,har ya dena,ya koma ya kwanta laƙwas bayan ya jera atshawa ƙwarara guda uku.

Ga mamakin kowa na gurin hannu da ƙafarsa da suk shanyene suka koma daidai da ɗayan me lafiya wayyo jazbeer ganin haka kawai saita fashe da kuka ta rungumeshi tana yiwa Allah kirari da manxonsa.

Sarki umar ko sujjada yayi yana faɗin"na tuba Allah ka yafeni biyayyar da naiwa uwar masarauta,ta jefani a halaka na manta da ƙarfin mulkinka,Allah na tuba ka yafemin na tuba Allah"ya faɗi cikin muryar dake nuna danasaninsa.

"Ranka ya daɗe ay godiyar Allah zamuyi kawai daya dawo mana da farincikinmu cikin ahalinmu,kuskuren da mukayi abaya Allah zai yafe mana"cewar wazeer cikin matsanancin farinciki.

Ranar guri guda suka yini,inda hameed be tashi a bacci ba se bayan laasar,inda ya tashi ya koma kamar baƙo acikinsu binsu kawai yake da ido dan abun ya bashi mamaki ne gwada miƙewa yayi yaga yayi hakan normal,ayko seya zabura ya tashi tsaye,yaganshi dire kan ƙafafunsa ba qata nakasa,ay kawai sai yasa kuka ya rungume sarauniya jabeer ya na ɓoye fuskarsa a jikinta.

Kowa saida ya zubda kwallar tausayinsa,kamun arakashi ɗakinshi.

********


Hameed lafiya tasamu,ɗan shekara Ashirin da uku amma zaka ɗauka yakai talatin sabida yadda yake kama kansa,karatun da nurayya tadinga koya masa lokacin dabeda lafiya ashe yana ɗauka.

Bayan watanni huɗu da samun lafiyarshine ya buƙaci fita zuwa ƙasar Nigeria dan fara karatun yaƙi da jahilci,sabida a ɗan zamansa da nurraya ya fahimci karatukan data ɗannƙoya masa ya riƙesu dan nurayya tana da ilimin addini daidai gwargwado wanda tasameshi daga bahijja da hindou wainda duk ƴan nigeria ne,shiyasa ya buƙaci zuwacan karatu badan komai ba saidan yasamu wadataccen ilimin sanin Allah.

Tun bayan samun lafiyarshi kotazo tana masa hira ɗan ɗauke mata kai yake dan shi ɗin mutum ne miskili dabe son hayaniya itako nurayya akwai surutu shiko beson hakan.



Nurayya uzuri take masa,dan gani take duk sanadin rashin lafiyarshine yasa yake hakan.

Goyon bayan wazeer kawai ya samu amma sauran iyayenshi basu goya masa bayan tafiyarba a farko amma da suka ga ba sarki sai Allah sai suka sa masa alvarka kan batun.

Nurayya ma fatan alkhairi tai masa,ba yabo ba fallasa ya ansa mata gamida mata godiya.


**********


A farkon shigowar hameed nigeria beyi zaton ze iya zamanta ba amma da yake an sakar masa kuɗi daga gidan su can roman.

Hakanne ya bashi damar mallakar mshalli kalar wanda yakeso badan komai yajure zamanba sai dan ilimi addini da yakeson koya,dan ƙarancinshine ya jefa iyayenshi halin da suka shiga shiyasa shi yakeso yasan komai game da ubangijinsa..


Besha wiya sosaiba ya samu gurbin karatu, a makarantar da hindou tai masa hanyarta bayan tasaki kuɗi .

Ya fara karatunsa cikin saa danshi yaje yi shiyasa be kula ƴanmatan da suka ga farar fata suke kawo masa hari.

Nurayya ma acan cigaba tayi da karatunta dan antsaya mata sosai akan makaranta bahijja da hindou basa mata da wasa in taƙi zuwa.



07044600044
[8/14, 06:48] Ummu Fadila: https://chat.whatsapp.com/DQsgTQR1BnJJlytCN4E670

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*KWANAN TURAKA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra surbajo*


*500 ne vip 1k kisiya kisamu damar karanta littafin tantabara kyauta*

*Zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*07044600044*


*16*



Da sallamarta ta shiga falon,dukansu suka amsa mata saɓani

4 / 11