Author : Asma Baffa Category : Romantic Hausa Novels
iklas da shi suka shiga wani hali na shauki kowannensu ji yake jininsa na masa wani yammmm.....yammmm.
Wani katafaren barbing saloon Wanda yake hade maza da mata omar ya parker,mata maza birjik ciki ana gyaran gashi,matan manya da yaran manya,da manyan masu kudi sune a cikinsa,turawa ne masu aiki a ciki.gurin ya hadu kamar a turai,
Fitowa yayi sakale da hannun iklas kamar chewgum,tafiya sukeyi cike da izza,iklas ta raina kanta kyaune kadai ya ceceta,dan duk tafi matan ciki kyau nesa ba kusa ba,sai kallonsu akeyi,suhaila na kusa da ya omar.bangaren mata ya fara kaisu yana zaune,iklas ta karbe daya hannun ta mika masa daya hannun gashi rike wannan dayan ya samu ya huta.
Kujera aka ba omar yana zaune gaban iklas hannunsa rike da nata haka akayi mata gyaran gashi aka gama,suhaila ma an mata,sunyi matukar yin kyau,su Kansu masu saloon din sunyi jinjina.
Wurin maza suka koma wannan karan iklas aka bawa kujera ta zauna gaban omar rike da hannunsa,masifu kawai take ji a jikinta na kamar sha'awa amma ta rasa gane mene take ji.
Omar kuwa a cikin jininsa yake jin bala'in sha'awar iklas wacce bai taba ji ba,amma haka ya daure ya cije.tunda aka fara gyarawa Omar suma iklas ta fara turbine fuska,idan ta kalli Omar sai ta tabe baki,wlh ka cuci kanka ko kyau bakayi ba,minti daya ko biyu zata kalleshi tace ko kyau,wai dole za a je bikon mata.
Gajia Omar yayi yace tunda sahar na son kalarsa ai alhmdlh dama dan ita nayi.mutumin da ba a sonsa anyi yaji an barshi wooooooo....cewar iklas,duk rashin fara'ar Omar iklas daria take sashi.
Haj rahina ce gaban baffan su omar,pls baffan yara 1million nake rokonka ka bani zan canja motata.hajia rigimarki ta isheni duk motocin gidan nan,omar fa baya bari motoci su shekara yake kawo sabbi,jin baffa ya ambaci omar yasa ummansu sadiya daure fuska,kaga alhaji ni ba zancen tambadadde nazo kamin ba,dan iskan yaro Wanda tsabar bin matane yasa ya bar gida.wa ya sani ma ko a waje tayo cikinsa....bata rufe baki ba taji saukar lafiyayyun mari har uku...kunci ta dafe tare da tsagewa da kuka tana kururuwa ta cukume baffa da kokawa tare da danna masa ashar,ai kuwa baffa ya sa kafa ya harbata gefensa,ta bigi center table,
Takadda ya dauko ya rubuta mata saki daya,tare da dafe kansa da kyar ya karasa dakinsa.faduwa yayi kasa yayi sharab...mama wacce abin ya faru kan idonta da kuka ta dago baffa,sannan ta kira maza masu aiki da driver suka kwashi baffa zuwa hospital.
Gaskia kowa ya ga yanda omar ya hadu sai ya kyasa,mata sai kallonsa sukeyi,da yawa suna so su kawo kokon bararsu na love amma yanda suka ganshi kankame da hannun iklas yasa suka ja baya, sai kallo daga nesa,
Take away ya musu na abinci kala kala sannan ya kamo hanyar gida,dadi ne ya kama iklas sosai ganin baza a je bikon sahar ba.
Sabo da murna sai labari takewa Omar,suna isa gida iklas ta hango saleem, da Sauri ta bude mota zata fita,Omar yaga saleem sarai,rigar iklas ya rike gam, kallonsa tayi yace muje gida waccen dan iskan zaki je wajensa ko?
Naji ai na fasa zuwa,to sakeni muje gida mana,kayan suka shigar gida,a cikin motar omar ya bar key din iklas na kusa dashi ta kwace hannunta taje wajen saleem da gudu ta karasa, har sun fara hira akan business da aikin gomnati yanda ake cuwa cuwa kudi na shigowa, wajensu Omar ya taka yaje cike da takama ya zubawa iklas rankwashi muje gida,cike da shagwaba tace ya omar da zafi fa,gani yayi zata bata masa lokaci kawai ya sunkuceta ya sabata a kafada. mutanen layin sai daria sukeyi GOMNATI ta hadu da dai dai ita.
Asmabaffa
ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ
50-55
By
AsmaBaffa
Daukan da Omar ya mata bai direta ko ina ba sai daya kaita har Palo sannan ya jefata a kujera da karfi tare da shigewa room dinsa,
Sosai Iklas taji zafi yar kara ta saki ohhh tare da dafe hips dinta..ko juyowa baiyi ba bare ya San me take ciki.
Lokacin da su Omar sukaje saloon daya daga cikin yaran Maman Omar tare da wani abokin Omar tabbas suma sunga Omar sun fito daga saloon hannunsa rike da na wata kyakyawar budurwa.
Lallai sunyi mamakin Omar ashe tafiyarsa yayi yana sheke ayarsa da mata,amma ake ta nemansa ana cewa ya bata.
Abokin Omar wato Raj ya daukin alkawarin zuwa ya fadawa Maman Omar cewar sunga Omar a saloon da mace.
Haj.Rahina ta dauki akwati da sauran abubuwan amfaninta kadan tare da Tara yaranta tayi musu hudubar banza sannan ta bar gidan ta koma gidan babban yayansu da ke zaune a garin Abuja shima.
Tasha fada wurin yayanta saboda yayanta Alhaji Magaji mutumin kirki ne sosai ya nunawa Rahina kuskurenta amma Sam ko a jikinta sai ma kara kaimi da tayi wurin son daukan fansa,kuma ta sa a ranta dole sai ta koma gidan Alhaji Mohd.
Tunda su Maman Omar suka dauki Alhj Mohd wato Baffa suka yi hospital dashi gado aka basu bayan aune aune da bincike ya tabbatar yana dauke da ciwon hawan jini kuma ya masa babban kamu,sosai ake kula dashi a hospital Mama ta tsaya tsayin daka wajen mijinta,ita ke jinyar sa,su sadiya ma suna zuwa dubiya amma kullum idan sunje sai sunci mutuncin Mama tare da habaici da zage zage.
Mama na mamakin wai ga mahaifinka a gadon asibiti rai a hannun Allah amma su sadiya suna shirme Allah kyauta.
Sultan ma kullum yana kan hanyar dubiya,kuma shi ke kula da Baffa kasancewarsa likita babba,abokan su Omar ma kungiya kungiya suke zuwa dubiya,kamar yau ma Raj yazo yana dakin da aka kwantar da Baffa tare da wannan yaron me yiwa Maman Omar hidima duk wani aike me nisa da wasu abubuwan wannan yaron wato Nura shi ke wa Mama kusan same age suke da Omar.kuma Nura yana da dangantaka tsakaninsu da Raj.gasu frnds ne shi da Raj,shi yasa suke yawan fita tare duk da cewa Raj me kudi ne,
Raj suna zaune kusa da Mama suna hira sama sama yayin da Sultan ke gyarawa Baffa kwanciya,Raj ya kalli Mama hade da gyaran murya Mama akwai wata magana da nake son fada miki,wato yau kwana uku kenan abin na damuna,gaba daya dakin Raj aka zubawa ido har Baffa da ya samu sauki shima ba a barshi a baya ba,
Naje kusa da saloon in da Nura mun karbi sako a hannun wani Mama wlh munga Omar ido da ido ga Nura nan ki tambayeshi kiji,har kokonto mukayi sai da muka karasa har kusa dashi amma kafin mu is a wajensa sun shiga mota sunyi mana nisa,kuma Mama abin mamaki Omar da mace budurwa zankadediya muka ganshi rike da hannunta da wata yarinya zasuyi same age da suleim dinki,
Sultan kuwa an zo wajen nan ya karbe zancen da cewa haba Ashe nima ba gizo idona ya min ba don nima rannan tabbas naga Omar a garden kingdom sun fito shi da wata charkwadediyar budurwa yarinya karama,Mama kamar yarinyar da ta kawo miki sakon envelop da tace Omar ya bata,kuma kamar wata me tallan kwai a titi da Omar ke taimakawa,
Daga Mama har Baffa Kansu ya kulle,to ko dama maganar Haj.Rahina gaskia ce da tace Omar na gari sheke ayarsa yakeyi bin mata yakeyi,yaushe Omar ya zama haka,maybe zaman London ne ya lalatashi ko kuma rashin samun kulawa daga wajen matarsa ne.
Gaba daya su Mama da Baffa sahar suka daurawa laifi sai kuma Omar da ya biyewa son zuciya tare da zubar musu da tarbiyar gida da mutunci.
Baffa ransa ya kara baci da jin wannan magana,yasan Raj da Sultan baza suyiwa Omar sharri ba,gaskia suka fada,lallai Omar ya bashi kunya zai kuma hadu da hukuncinsa duk ranar da suka hadu.Mama kuwa harda kukan bakin ciki Omar ya watsa musu kasa a ido,amma ya za tayi dole addua ce mafita,
Sosai su Sultan suka Shiga kwantarwa da su Baffa hankali tare da yi musu alkawarin nemo Omar,dan sunce zasu sa ido sosai a kansa.zasu Dana masa tarkon da dole sai ya fada tare da damke wannan tsinaniyar karuwar tasa wato Iklas.
Kwana biyu tsakani Baffan Omar har yau jiki yaki sauki sabida damuwa jinin yaki sauka wahala yake sha wanda sai da su Sultan sukayi Dana sanin fada musu cewar sunga Omar.
Mama abin ya hade mata ga rashin lafiyar miji ga rashin Omar dinta tare da jin mugun labarin yana neman mata.
Su Iklas anyi musu hutu daga Ta boko har islamiyya,sabo da haka Iklas ta rikewa business dinta wuta yanzu ma tace sana'ar saida danyen kifi zata fara,kudin da ta samo gidan Maman Omar su ta tattara kaf ta siyo katuwar freezer sabuwa dal ta ajiye a kitchen,saura kawai ta fara saro kifi,duk tsare tsaren Iklas Omar bai sani ba,
Dukkansu suna zaune a tsakar gida da yamma lis,Iklas na kwance a kan katuwar tabar ma da wata Rigarta doguwa ta atamfa tayi kyau,Suhaila na kan cinyar Ummi kwance tana karanta Arba'una hadith, Omar yana kan carpet gefe tare da laptop sai nunawa Ummi wakar shata me ganga yakeyi,Ummi har gyada kai take tana Allahu akabar oh kaji mazan jiya,Allah sarki jiya ba yau ba,Umaru danno min ta Ali makaho da Dan kwairo naji..daria yakewa Ummi ganin abu ba wani Dandano amma Ummi dadinsa takeji ko dan azamaninsu ne akayi wakar,
Iklas littafinta ta dakko tana ta buga lissafin sana'ar kifi da zata fara domin gobe take sa ran sarowa,juyowa tayi dan Allah Ummi a canja mana wakar zamani amma wannan mu bama fahimtar me suke cewa,kaka Ummi dalla mata harara tayi aike ba hankali gareki ba amma ai sune sukayi wakoki masu ma'ana,tabe baki Iklas tayi pls ya Omar kai mana wakar Timaya ko ta Devido,
Ai kece Timayan see ur mouth anki a kunna miki manya na maga kina shiga ciki cewar Omar,murmushi Iklas tayi cike da shagwaba ta ajiye littafin dake hannunta kajika ya Omar da nawa ka girmeni,ai ko zaka girmen kadan ne,hmm na San da auren wuri nayi da tuni na haifi kamarki,ummi ma tace fada mata Umaru in banda rashin kuya dudu shekararki nawa saboda kinyi tsayin kafa,dadin abun dai a gaban Umaru kika fara Al'ada,ba wani iyayi da zakiyi masa ,kukan shagwaba Iklas ta fara haba Ummi wai mene haka dan Allah,kunya Iklas taji sosai,Omar kuwa masu rayuwar London ko a kwalar rigarsa,saima kafe Iklas da yayi da kallo,idonta ta dauke daga kallonsa a ranta tana kai Sir din nan dan duniya ne harda kallo na.
Su dama Maza munafukaine abinda suke so kenan dama taji frnds dinta suna fada a schl.
Washe gari da wuri Iklas ta saro kifinta Carton daya na gwajin kasuwa,Omar yana bacci bai San Iklas ta fitaba,sai fitowa yayi yaga Iklas na shirya kifi a fridge Omar ya shiga kitchen din dauko furarsa dagashi sai jallabiya fara me hula dai dai jikinsa gashi sabo da baya fita baya shiga rana ya kara haske sosai skin dinsa har wani sheki takeyi,
Kamshinsa ne ya bigi hancin Iklas a take jikinta ya mutu murus,kasala ta sakko mata,ta gefenta ya raba zai wuce jikinsa ne ya gogi nata baisan sanda a hankali yace ushshsh shshi sabo da wani irin yanayi daya tsinci kansa ciki.furar ya ebo a glass cup tare da zuka,ke me kike yi haka,duk wannan kifin da wa zaki cinye?kallonsa Iklas tayi tare da murmushi tace au baka da labari ai kifi zan fara siyarwa danye,da kudin da Baffa ya bani na kafa jarin,kaga sana'a goma maganin me gasa,kaga kala kala nakeyi kenan,
Jinjina son kudi irin Na Iklas yayi a ransa,idanuwansa kyawawa masu matukar haske ya zubawa Iklas Wanda yasa Iklas dimaucewa hade da jin kunya,sunkuyar da kai tayi ta tsinkayo muryar Omar ba a nan gidan za ayi wannan sana'arba,baki isa ki cika mana gida da karni ba,duk sana'ar da kikeyi bata isheki ba sai kinyi kalar wannan,haba mene aibun wannan sai da kifin,ummi ma fa da kyar ta yarda wai bata so nayi,nidai ina son siyarwa sai nayi,
Tamke fuska yayi to baki isa ba,ba a gidan nan ba na fada miki idan kuma kinga ina wasa dake kiyi na gani,da shagwaba tace pls Sir nasan in ka fada Ummi bayanka zata bi,ke kika sani ni kam na gama magana ko ki je ki mayarwa Wanda kika siyo wajensu ko a cinye a gida,ko ki bayar kyauta,tab lallai inyi asara ba riba,sai dai ka biyani kudin Dana kashe in kuna so na daina,
Zare ido Omar yayi ina wasa dake,tsorata tayi ta fara bin bango tana rabewa hade da tafiya kadan Kadan ta fice da gudu daga kitchen din tana ae na fada a biyani kudin Dana kashe tare da kulewa dakinsu.
Daria Omar yayi sosai ya fita shima,washe gari da safe Omar ya fito da brush da toothpaste zai shiga toilet sai ga Iklas ma ta fito tana kallon Omar ta wuce da sauri ta rigashi shigewa toilet din.Ummi sakin baki tayi yau naga yar banzar yarinya,ke dan bantan ubanki fito Umaru ya shiga,kyaleta Ummi zanyi maganinta,daki Ummi ta koma tana cewa kunfi kusa.
Iklas kuwa har ta fara brush Omar ya jawo rigarta kiiiiiii ya jefota waje,kafin ya rufe toilet di Iklas ta kara bankawa ciki,murmushi Omar yayi oh..yanzu na gane me kikeso Ashe wanka kike so na miki,damkota yayi kamar zai fara cire mata kaya tuni Iklas ta fara kuka tana Neman agaji,da gudu ta fito daga toilet din,Omar ya rufe kofar tare da Jan tsaki karamar yar iska da kin tsaya kin gani.
Iklas kuwa a ranta tace kut lallai Sir cikakken dan iskane.yau Iklas shiri tayi tsab domin zuwa gidan su Omar so take ta dubo masa lafiyar su Mama,fito tayi Palo tare da yiwa su Ummi sallama,da sauri Omar yace muje tare unguwar na kaiki,batayi musu ba ya kira a take aka kawo wata new Car din.
Tofa kunji masu karatu.
ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ
60-65
By
Asmahbaffa
MASOYANA READERS NA GAISHEKU,MASU COMMENT AKAN WANNAN NOVEL ALLAH MUKU ALBARKA GABA DAYA INA GANIN SAKON KOWA.
Fafur Omar yaki yarda saima room dinsa daya shige ya bar Iklas waje tana tunanin yanda zata bude kofar,hakura kawai tayi ta kyale Saleem a waje yana jira.tunda Saleem yaji Iklas shuru shuru yasan bazai wuce wannan shedanin yayan nasu bane ya hanata fitowa
Tunda Omar suka bar su Baffa da salati cikinsu ba Wanda ya kara koda tari,Suna a haka Sultan da Raj suka shigo,tambaya suka fara yi Lafiya sunga Mama ta rafka tagumi,da kyar Baffa ya fadawa su Raj halin da ake ciki,suma sosai suka sha mamaki,
Sultan ne ya fara Baffa da kun sani Baku kori Omar ba,da kun barsu sunyi bayani,Omar nasan baya abu ba reason,me yasa ba a fada min a waya ba nazo wajen,Mama kema kin manta halayen Omar masu kyau,na tabbata zai wahala idan Omar zai iya aikata abinda muke zargi,
Raj ma haka ya fada Baffa da Mama sai sukaji dama sun tariyo baya sun tsaya sun saurari Omar,sun yanke hukunci cikin bacin rai,ta leko ta koma ga Omar amma sun koreshi,Baffa ne ya dubi su Raj..Sultan yanzu mafita daya kusa ido a garin nan,da sauran abokan Ku da security duk inda aka ga Omar a kawo minshi har gida,in yaki binsu a kawoshi ta karfi ko da igiya Ku dauroshi a kawo min shi,
Aje a sanarwa mutane,nan take suka fara waya tare da hada connection,shima Baffa haka,kwana 2 tsakani aka sallami Baffa,yana hutawa ya koma gidan su sahar wannan karan sunci sa'a an lallaba iyayen sahar da sahar sun dawo da ita gidan Omar,sahar kuwa dama kudi take so ta karba wajen Omar masu yawa tattalin arzikinta yayi kasa shi yasa ta yarda ta dawo..yayinda da taci gaba da sheke duniyar ta.
Tana nan tana jiran ganin an dawo da Omar gida,bayan dawowar Sahar Baffa da yan uwansa suka je bikon haj.rahina,sai murna su sadiya sukeyi,gogar kuwa dama ta samu rana ta bude mata sai shanya,dama abinda take nema kenan Baffan su Omar ya lallaba ya dawo da ita.
Sultan dasu Raj da sauran mutanensu sun fara aikinsu ba ji ba gani,kullum basa zama Neman Omar sukeyi ba dare ba rana,
Iklas ta gaji ta yanke shawarar sanarwa da Ummi abinda ke faruwa da Ya Omar,tausayinsa takeji sosai gwara ta fada ko Allah zai sa a nemo masa magani,Omar kuwa kullum addua yakeyi sosai akan matsalolinsa,
Yau Ummi ce ta dauko naman