MAAIKACIYAR GOMNATI COMPLETE HAUSA NOVELS PDF BY ASMA BAFFA.txt

Author :  Asma Baffa Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   23 / 38

66K to 69K   out of 113.6K words

Daddynta da naci,su kuma suna son yarsu,farin cikinta suke so,shi yasa Sahar ta lalace da yawa, Omar kamar zai mutu har zazzabi yayi,yace wlh bazai je gidansu ba sai dai a fada mata ta koma,Sahar murna tayi tace ko dan naci uban yarinyar nan bari na koma,tattara kayanta tayi ta koma gidan Omar,gani tayi komai na gidan an canja new kamar ma ba gidan ba,tasha mamaki a ranta tace Ashe dai ya damu dani.
Iklas kuka takeyi kullum an maida Sahar ta zama kishiyarta,shike nan zasu dinga kwana da Omar.

Ummi da Mama ke lallashinta amma kullum bata da sukuni danma tana zuwa schl da damuwarta sai tafi haka,
Tunda Sahar ta koma Omar bai koma gidanba ko sau daya,har ta kwashe 2wks amma mijin nata shuru,Mama ta sa Omar a gaba kullum fada takeyi ya koma gidansa kar ya shiga hakkin Sahar amma yaki,ko ta koreshi wani gidan yake komawa cikin jerin gidajensa.
Satin Sahar 3 da tarewa Baffa ya umarci mama kan ta kira Iklas Ummi da Omar,kafin ta kirasu sai ga yan uwan Baffa Da aka daura auren Omar da Iklas sukayi sheda da kuma Wanda sukayi wakilcin iyaye du sun hallara a falon Baffa

Omar baya gida yana Office sai a waya aka kirashi,minti kadan Omar ya Iso,Iklas sanye da hijab anyi lukui a gaban Baffa,Haj Rahina ma an kirata,Sahar tazo don tunaninta tunda taji Baffa ya nemeta to kudi zai bata,Sultan da Raj an cika harda sauran yaran gidan.
Duk kowa yana wajen,Omar sai mamaki yakeyi ko lfy,

Taro aka bude da addua,sannan Baffa ya fara magana,nasan wasunku basu San me yasa na taraku ba wasu kuma sun sani musamman yan uwana da Mama,Ummi,Iklas, sai Sultan da Raji,ga limamin masallacin da akayi a idonsa shima shaida ne cewar a masallacinsa muka daurawa Iklas aure ita da Dana Wanda kowa ya sani wato Omar,

Omar bamu sanar maka ba sakamakon kana hali na cuta,mukace a bari sai ka warke,nan wajen Baffa ya bada labarin kimai,shedu ma suka tabbatar da hakan,har pics da video Sultan da Raj suka nunawa kowa.
Omar ne ya fara gani ya rasa ma me yakeji a ransa ga dadin Iklas ta zama mallakinsa sannan ga haushin anki fada masa da wuri an ja masa rai,an barshi da damuwa.

Yana so ya danyi koda romancing Iklas ne amma ya dinga tunanin babu kyau,an barshi a duhu maza sun tsaya masa da matarsa sunyi hira,tayi rawa a gaban maza, sai yanzu yaji ya kara jin haushin saleem da yayi hira da matarsa,Ibzzy ma haka tab wannan duk laifin Iklas ne,sai yanzu ya tuno yanda Iklas ba ruwanta take taba jikinsa anyhow Ashe tasan komai ita ba rashin kunya ce tayi mata yawa ba,
Tunani ya shiga yanda zai sawa Iklas sonsa a ranta sannan asha love,tunowa yayi yanda Iklas ta dinga raina masa hankali,a ransa yace dole na rama.Iklas kuwa dake gaban Baffa kanta ta cusa tsakanin cinyoyinta ta dunkule wai kunya,

Sultan sai daria sukewa Omar kasa kasa.yaran Mama harda Suhaila sai jin dadi sukeyi,Haj Rahina ce ta mike tsaye akan wannan aka bata mana lokaci,dan sunyi aure sai me,fasikan banza fuuuu ta ja su najja suka bar dakin cike da takaici,nan take tayiwa Aisha da Sadia waya ta shaida musu komai.Haj binta ma ta bugo waya suna ta gulmarsu ta kulla tsiyarsu idan Iklas ta tare.
Sahar kuwa wani wawan tsaki taja hade da shewa tace ta shigo gidan indai miji ne Mara amfani holoko to gashi nan,kizo kiji dadi mugani.ficewa tayi ta shiga motarta ta bata wuta.

Baffa kuwa kai ya girgiza yace Allah shiryeku sauran mutane sukace ameen,nan taro ya tashi saura Mama,Ummi ,Baffa sai Iklas da Omar ba bata lokaci Baffa yayi musu Nasiha sosai,haka Mama da Ummi ma sunyi tasu Nasihar,an yanke nan da 3days za a kaiwa Omar matarsa,godiya Omar yayi wa Ummi da iyayensa da suka bashi Iklas amma fuskarsa a daure.an kasa gane yanayinsa.


Iklas dadi taji kamar me zasu tafi gidansu ita da Omar dinta,shike nan itama tayi gida,sai kaji ana cewa mun tafi gidan Iklas, ga Omar Allah dole ne ta dinga baccinta a jikinsa me kamshi laushi da santsi,inyi girkina,inyiwa Ya Omar abinci,muyi wasanmu etc
A ranta take zancenta ta
A hankali ta dago da kanta Omar ma a lokacin ya dago caraf suka hada ido,gani tayi fuskar Omar ba alamar Rahma,gabanta ne ya yanke ya fadi wato ma dole akayi masa baya sonta,Inusa me wanki ta tuno zancensa sai kuma taga kamar Omar baiyi farin ciki ba it means ma karya ne baya sonta,
Lallai dole na fara addua da Sallar dare zata fara Allah sawa mijinta Omar sonta ya basu zaman lfy,yasa ta zame masa Alkhairi shima ya zamar mata alkhairi.

Sallamarsu Baffa yayi tare da sanar musu gobe jirgin karfe 6 na safe zai bi ya koma kasar Russia wajen aikinsa,addua sukayi masa sosai kowa ya tafi aka bar Baffah da Mama.

Iklas na bayan Ummi,Omar na binsu a baya hijab din Iklas ya dan ja juyowa tayi amma har yau gani tayi fuskarsa a daure,jawota yayi kiiii kamar zai doketa,ihu Iklas tayi wayyyo.....ta tsorata ta dauka dukanta zaiyi,da sauri Ummi ta juyo ai da sauri Omar ya saki hijab din Iklas,
Ummi ta riga ta ganshi,kara juyawa Ummi tayi taci gaba da tafiya,Omar ya kara fusgo hannun Iklas,da gudu Iklas ta kwace ta sha gaban Ummi,ke wai wacce shashasha ce,cewar Ummi,waigowa Iklas tayi tana kallon Omar tace wlh Ummi wani abu zai min,Allah ki masa magana zaneni zaiyi.

Ke rufe min baki marar wayo wuce muje ciki,an kusa kaiki gidansa ai kuje Ku cinye juna ma,karki sake ko a waya ki kirani komai raunin da yaji miki,Iklas bata gane maganar Ummi ba,ta zata zancen duka da tace shi Ummi take nufi za a ji mata ciwo.

Sun shiga room Iklas zata rufe kofa Omar ya mata irin abu da kafa ya buga kafar a kasa kamar zai kwasa da gudu ya damkota,ai kuwa ta saki kofar ta fada dakin da gudu.

Daria Omar yayi ya wuce part dinsa,misalin karfe 1 na dare,Omar ya kasa bacci,sai yanzu ma yake tsananin son jin dumin jikin Iklas, fitowa yayi yaci Sa'a kofar su Iklas ya ganta a bude yanda Iklas ta barta dazu.

Lallabawa yayi ya leka dakin,Iklas da Ummi kwance gado daya suna ta baccinsu,karfin hali Omar yayi ya matsa kusa da Iklas,a hankali ya kama tashinta ta hanyar Sosa mata kunne,
Firgigit ta bude idonta,alama yayi mata da tayi shuru,saboda Kar ta tonawa Kansu asiri tayi luf tana kallon Omar,tasan idan Ummi ta gansu fadan har Ita.

a hankali yayi rada ki taso muje dakina,kafada ta noke tana masa nuni da Ummi, kara rada mata yayi ni zakiji tsoro,nine mijinki,itama rada masa tayi ummi zata kamamu.

Tsaki yaja a hankali ki taso kawai malama na fada miki,ni lokacin da kike zuwa kina taba min jiki hanaki nayi?lokacin ma fa ban San ke matata bace amma na kyaleki,murmushi Iklas tayi,harara Omar ya watsa mata,ki taso ki biyani jikina da kika dinga taba min,mijinki ne ni Allah ya konaki kinki bin umarnina kinji dai nasihar Ummi ko,
Tsorata Iklas tayi kar Allah ya konata fa,Omar ya kara da kizo ko na kwanta anan Ummi ta kamamu.

Da sauri Iklas tace a'a dan Allah zanzo muje ni,kar ka jawo min masifar Ummi dan laifina zata gani,muje kawai,mikewa tayi a hankali kamar barayi sadaf sadaf suka fara tafiya,Ummi kuwa dake bacci motsi taji kusa da ita ta farka, mikewar da Iklas tayi shine ya tashi Ummi da ga bacci,

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un Iklas yanzu iya shegen da kika dauka kenan,nasan Umaru bazai aikata ba ke kika kirashj a waya,dawo ki kwanta ko wlh na saba miki,mu zaku mayar yan Iska, tuni Omar ya bawa Ummi hakuri yace Ummi cewa tayi nazo na dauketa tafi son dakina.

Salati Ummi ta kara saki jeka Umaru Allah maka Albarka ai nasan halinta,ficewa Omar yayi da sauri cike da kunya.wlh Ummi bani nace yazo ba cewa yayi.....rufe min baki Ummi ta kai mata duka dan ubanki kwanta ki rufe min baki,Iklas kija mutunci ki ina fada miki namiji ba dan goyo bane.

Rushewa da kuka Iklas tayi wiwi take kuka haushi takeji Omar ya kala mata sharri ya zame kansa gashi ya barta Ummi tana jin haushinta,shi kuwa ya wanke kansa tas wurin Ummi.

Gajia tayi da kukan ta shige toilet tayi Alwala ta fara nafila da adduarta Allah sawa Omar sonta,ya sota ita kadai a duniya,Allah bata ikon yi masa biyayya yasa su zamewa junansu Alkhairi.
Tana idarwa harda karantawa Omar suratul Yaseen Allah sa masa sonta,ita gani takeyi Omar baya sonta shi yasa yanzu yasa Ummi tayi mata fada.da yana sonta ai bazai zame Kansa ya kyaleta ba.
A ranta tace Allah kaimu gobe lfy Allah sai na rama zai San nice Gomnati.
Washe gari Iklas da fushi ta tashi cike da shirin ramuwa kan Omar shima sai tasa an masa fada yaji kunya.




Pls kuyi hakuri da wannan bazan iya forcing kaina nayi muku 2 pages ba,typing akwai wahala ga shi akwai schl ba time,Ku danci wannan tuwon Ku kora da ruwa kuyi bacci.
Tnx alot readers ..




Asmabaffa

ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

135-140



By
Asmabaffa




Jira kawai Iklas takeyi taga ta inda Omar zai bullo amma shuru,Mama ce ta fito cikin shiri,tashi maza dauko mayafi zamu fita,ba shiri Iklas ta fito dauke da mayafi,driver ne ya kai su Iklas wurin wani saloon,Mama ta biya kudin komai yanda za a tsantsare Iklas,
Komai da ya dace iyaye suyiwa yarsu Baffa da Mama sunyiwa Iklas kayanta babu banbanci da na su sadiya sai dai color daban,na Iklas Dark brown ne komai,haka kayan kitchen Mama tayiwa Iklas Wanda ya take nasu sadiya,kayan gyara Dana kamshi babu abinda ba a siya mata ba wadatacce,kayan yaji da sauransu du an shirya mata part dinta,

Allah ya taimaki frnds din Iklas da wasu dangin Mama har aka gama shirya kayan Sahar bata nan,kayan sawar Iklas du an kai gidanta an shirya mata lefe kuwa Baffa ya bada kudi Mama ta hada mata akwati 8 ba abinda babu masu tsadar gaske da kyau domin English wears kaf da wasu tarkace a Russia Mama ta hado su murna Iklas keyi za a sha wanka,Omar kuwa gagarumar walima ya hadawa frnds dinsa maza a wani katafaren waje,ranar kai Iklas ranar za ayi walima.

Omar kafin ayi jeren Iklas har ma'aikata yasa suka kara yin adon golden jikin ginin Wanda yafi na da iri iri,ko ina sai ka rantse adon zinari akaiwa ginin wajen Iklas, komai dark brown da Golden ne,har labile idon gari.tsayawa fada muku yanda part din Iklas ya hadu iya haduwa karshe ya zarta tunanin me tunani,sai na gama novel din nan kaf ban gama ba,
Iklas koda suka dawo ma Omar na busy bata Ganshi ba,Iklas manya tsabar gyara duk inda ta zauna kamshinta sai yayi kusan 1wk bai bar wajen ba,ko gidan mutane taje to sai tabar musu tsarabar kamshinta.

Washe gari dangin su Mama mutum biyar sunzo raka amarya gobe,haka dangin Baffa,ga frnds din Iklas zuga guda,Rana ta Uku ranar kai amarya,da wuri Iklas taje wurin Saloon da lalle,masu mata lallen mutum uku ne ,sai mai gyara gashi,Karfe 4pm Iklas driver ya dawo da ita,kunga Iklas kuwa yanda ta koma?tab zankadaziyya kenan,dama gata fara kwal,ga lalle yayi kyau over,
Tana shiga room dinsu mero lallausa tana jiranta,nan itama ta hau nata gyaran,gashi sai bata abubuwa akeyi ta shanye wannan ta cinye wancen,Lallausa da Mama sun koya Iklas harkoki sosai na mata da ake amfani dasu,Mama da Ummi sun hada mata wasu da yawa an kai gidan,store kuwa both na Iklas Dana Sahar an dankareshi da kayan abinci haka kitchen ma.

Karfe biyar su Omar suna can suna Walima,amarya an shiryata tsab jiran angwaye kawai akeyi,Ummi da Maman saleem sun sa Iklas gaba da nasihar bin miji,idon Iklas Kamas ko kuka babu tunda wajen Omar ne bata da Matsala.
Ummi tace to kinji dai abinda muka fada miki kishiya gareki wlh kija mutuncinki,ban son tsokana nasan halinki,kuma ba a dambe da kishiya jahilci ne,ki kiyaye,zaman aure ne ba jin dadi kikaje ba ibada ce,dole sai da hakuri da juriya,ki farantawa mijinki,komai ba musu,sannan kinji na rantse Iklas kikaje kika tashi hankalin Omar da fadace fadace da kishiya Allah sai na saba miki,
Ki rike mijinki nasan dole kin San dai dai da rashin dai dai abinda ya shige miki duhu ga Mama ga ni ki bugo mana waya,haka dai suka dinga yiwa Iklas fada,kawayenta ma sai nasihar iya shege suke mata,
Amarya banda rowa a wangalewa oga cinya etc.
5:30 yan daukan Amarya suka zo,motoci Jere na alfarma aka dauki amarya da yan rakiyarta zuwa gidanta,Iklas fa har yau idonta tarwai har hira takewa angel kawarta,,
Gida ya hadu kowacce sai kallon tsaruwar gidan sukeyi,gidan Omar dan gayu gidane na alfarmar gaske,upstairs kadai part uku ne,haka downstairs ma karshen haduwa ce,bare compound ba a magana,kayan da akayi ginin Omar wasu da yawa basu zo kasar mu Nigeria ba,domin turawa ne sukayi masa ginin gidan.

Sahar da kawayenta yan magaa tantiran yan banaline da codine ne suna Palo sai shewa sukeyi hade da habaici kala kala,idan suka ga wata cikin yan kawo amarya sai kaji zagi da ashar na tashi.

Kowa tausayawa Iklas yakeyi sabo da Sahar da suka ga abinda takeyi,ita kanta Iklas ta shiga damua sai taji duk ta tsorata,gwiwowinta sunyi sanyi,gashi bata San ya Omar zai karbeta ba tunda ba sonta yakeyi ba,
Ummi na kusa da Sahar sunyi jugum jiyo muryar Sahar da sukayi tana ta zunduma Ashar.Iklas ji tayi dama bata yarda an daura aurenba,tasan Sahar watarana maybe kasheta ma zatayi.tsoro ne ya kama Iklas,amma har yau zuciyarta bata yi raunin da zatayi kuka ba,

Yan kawo amarya duk sun mata sallama sun tafi har Ummi amma still Iklas ko kuka babu.
Tana zaune tana tunani 9pm Omar, sultan,Raj sai Usy suka shigo dakin amarya Iklas,tana ganin Omar taji wani sanyin dadi,idon amarya kiri kiri mayafinta a kai amma bata rufe ido ba,haka aka bude da addua,sukayi musu nasiha da barkwanci,suka ajiye mata kudi Omar yaje ya Rakasu sannan ya dawo wajen Iklas fuskarsa a sake,ita kuwar gogar ji takeyi kamar ba aurenta akayi ba,normal tunda ta saba da Omar dama

Gyalen kanta ya cire mata yanmata Amarya,ya kk,a hankali tace lfy,yau najiye miki dadi abar da kika Dade kina kallon shape dinta a boxers ko a towel gata yau har gida,sai kin gaji,yau zan baki ita,tunowa Iklas tayi da kallo tabi Omar kamar zatayi kuka,
Cike da shagwaba tace ban taba kallar maka abu ba,kawai bangon dakin nake kalla amma kake ganin kamar idona a kanka yake, murmushi Omar yayi ganin yanda Iklas ta tsorata,bai taba sanin tana da tsoro haka ba sai yau,dama tsokanarta yayi.
Tausayinta yaji ganin bata San kowa ba sai shi,bata saba da kowa ba sai shi,kwantar da hankalinki amaryas tsokanarki nakeyi,da Sauri ta rufe idonta tana daria,tare da furta ai nasan Sir dama tsokanata kakeyi,

Omar a ransa yace zakiga tsokana yarinya nan da wasu kwanaki bazan iya jure kallonki ba ga sonki da ke ragargaza min zuciya,a fili yace dama ni salihi ne uztazu kece kike Neman lalatawa Mama ni,
Je kiyi wanka muyi Sallah,ko na miki?murmushi tayi ba yanzu ba sai watarana,zaro ido Omar yayi yau ga amarya Mara kunya wai Iklas yar yarinya amma tasan zasuyi wanka ma wato nan gaba,inda take birgeshi ba boye boye irin na mata dan a kallesu a nutsatsu, abinda ke ranta zata fada koma wanne kallo kayi mata kai ka sani.

Iklas ta saba da Omar bare ace zata ji kunyarsa,dama kuma ita bata cutar kanta da kunya a cikin arna ta taso shi yasa ba komai ke bata kunya ba,gogayya da mutane bata tsoro da Shakkar mutane bare ta bari a cuceta tayi fa talla a kwalta readers kar a manta.Iklas kwai wayo sai ta siyar da mutum a gabansa bai san anyi cinikinsa ba...
Mikewa tayi ta tube gaban Omar daga ita sai towel ta Shiga wanka,ta dan jima ta fito,Omar ya fita yana Room dinsa ko takan Sahar bai bi ba,tunda ya shigo shi da frnds dinsa ta kama zage zage,shi Sam bai dauki Sahar a me

23 / 38