Author : Asma Baffa Category : Romantic Hausa Novels
tausaya wa yaran nasa irin jarabawar da suke karba,daga wannan sai wannan.Duk abinda sukeyi yau gashi ba uwar tasu a duniya,duk burin Ummansu yau gashi ta tafi tabar duniyar.
Shima wannan ya jawo Su Sadiya sun kara darasi a duniya.kwanan Rahina takwas da rasuwa Haj Binta ma ta cika itama,sosai akayi jimami da ta'aziyya nan ma ansha kuka.duk son duniyarsu yau gashi Allah ya kirasu sun bar komai sun tafi.nan make Tarawa nan ake bari duniya kenan.
Sahar abin nata ba sauki,wata ranar juma'a ta fita waje ba tare da kowa ya sani ba,wani babban mutum ta gani a hanya ta cire zaninta tare da cewa Alhaji zaka siya,bata san liman din Unguwarsu bane ai kuwa limamin nan a fusace yayo kanta dan ubanki tsinaniya tambadaddiyar karuwa,ni zaki mayar dan Iska ni zakiwa maganar banza,ya fara jibgarta ina liman zaki mai dani dan iska,da kyar aka kwaceta,ita kuwa sai gwalo take wa liman,yana kallonta idan suka hada ido sai ta zaro masa harshe ta mayar.
Sai da wani mutum yazo yayiwa liman bayanin yer gidan Gomnace daya sauka last yr,ai kuwa nan liman ya fara yi mata addua ya daina masifa yaji kudi.
Kamata akayi tare da mayar da ita gida. Allahu Akbar duniya,da ace da ne liman bai isa yaga Sahar ba bare ya iya yi mata ko da kallon banza ma.sai gashi harda duka.
2wks da haihuwar Iklas jini ya dauke mata ta fara sallah a boye dan kar Omar ya gani bata San Omar tuni ya hada CCTV a computer dinsa ba, in ya dawo daga Office yana kunnawa ya kalli duk abinda Gomnati keyi a gidan,
Rannan yana dawowa ya kunna yana kallon Iklas,katsam yaganta sadaf sadaf ta sa key a kofar,sadaf sadaf ta tayar da Sallah,wani dadine da farin ciki ya lullube Omar. Ya furta today is my day.Iklas kuma tunda Mama taga yau ta fara sallah sai tace wa Iklas tattara naki ya naki kaf ki koma dakina da zama,Iklas cike da murna ta koma room din Mama.
AsmaBaffa.
Mom walida name sake with maman waleeda na gode naga comment naki.
Jinjina gareku mutanena.
ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
200-205
By
AsmaBaffa
SAFEEYA AHMAD,MAMAN ABBA, wannan page din nakune
Omar shigowa yayi gidan a gajiye,ko wanka baya jin zai iya yiwa kansa shi yasa ma ya aiko Suhaila ta kira masa ita,Iklas an cakare da kwalliya kamar wata queen tsabar kyau,ga mama da Ummi gyarata sukeyi sosai,itama Iklas kullum sai taje gyaran jiki wajen Mero Lallausa,kamar wata Amarya haka ake gyareta,jikinta ya murje sai sheki da kyalli takeyi,gashi abinci me rai da lafiya Mama ke bata,
Koda Iklas taji sakon Omar firgita tayi,mama ce ta bada Amsar je kice aiki na sata. 1mnt da fitar Suhaila kiran Omar ya shigo dankareriyar wayar Iklas,sai da ta kusa tsinkewa ta daga tun kafin tayi magana yace in kin gama kizo am so tired ko wanka bazan iya ba,kuma yunwa nake ji,kamar zatayi kuka tace to am coming.
10mnt kiransa ya kuma shigowa wai har yau me kikeyi haka?tana Ina ina tace I...I...will..be on my way, better dit ya kashe wayar
15mnt ltr call din Omar ya kuma shigowa still dagawa tayi idan nazo room din baza ta miki kyau ba bring ur self to my room quietly nasan abinda kike gudu ki daina tsoro ni ba abinda zan miki sai nan da 2mnths maybe ki saki jikinki ki daina bata lokacinki.
Mama ta kalla kamar zatayi kuka,jeki kinji idan kinga wani abu da bakya so ki gudo,kamar kwai ya fashe mata Iklas ta fita tana sake sake a ranta,ita wahalar Haihuwa take tunawa.
Omar kuwa Ransa ya matukar baci da Iklas,tana shigowa room da masifa yaso Tatar ta sai yaga wani uban kyau da ta zuka kamar ya lashe ta haka yakeji,dan danan ta kwacewa Omar Imani,yama rasa me zaice sai binta da kallo yakeyi,
Gefen bed din ta zauna tana cin magani,sannu da zuwa me zanyi ma?Iklas ta tambaya,jiki a mace yace tashi kije bana so sai wani fushi kikeyi akan nace kizo jeki ki bawa Suhaila ta kawo min Prince,
Gomnati taga da gaske Omar fushi yayi sai taji bata kyauta ba,batayi dai dai ba ta batawa mijinta Rai.
Sumi sumi taje ta dauko Prince da kanta ta kawo masa,a hankali cike da nutsuwa tace masa me zanyi maka dazu?nace ai na fasa bana so cewar Omar,kai dai kace kawai kayi fushi dani banzo da wuri ba kayi hakuri to,
Gani kikeyi wani abun zan miki,dama wanka zaki min ki bani abinci kuma zanyi da kaina.mikewa tayi ta hada masa ruwa wankan.
Dawowa tayi ta karbi Prince da ke hannunsa ta ajiye a kan bed sannan ba tare da tace kala ba ta shiga cire masa kaya sai dadi yake a ransa,amma a fili sai shagwaba yake mata yana gocewa yaki tsayawa kamar yaron yaye,
Pls ka tsaya mana mutum sai rigimar tsiya,sai da ta gama ta daura masa towel tare da kare masa kallon birgewa,dan ita dai a rayuwarta kirar dirin Omar,skin da komai na Omar suna matukar birgeta tare da bata sha'awa,a ranta sai zancen zuci takeyi yanda Omar kullum yake kara kyau da haduwa.
Hannunsa me matukar laushi ta kama ta kaishi har Toilet,wanka tayi masa sosai,sannan tazo ta shiryashi,harda sa masa jallabiyya fara Sol,ka Dade baka sa jallabiya ba kasan kuwa yanda take ma kyau,yau ita nake so kasa min a gidan nan, tsokanarta Omar yayi ai kuwa fita zanyi ni,haba dai duk gajiyar nan da ka kwaso ,sai da ta gama ta kalleshi tana murmushi tace Honey dan Allah Kasan kai me kyau ne kuwa? kana kallon kanka kuwa yanda kake da kyau
Hancinta ya ja ai kinfini kyau wifey,duk Inda ake Neman kyau to azo wajenki,
Ranar Dana fara ganinki a gidan kaji tun a ranar na tabbatar ke me kyau ce wacce ban taba ganin irinsa ba,
Hugging dinsa tayi tare da shakar kamshin juna,tare da cewa hmm wai a gidan kaji dama ka kalleni? Ko mutum baya so sai ya kalleki yanda kika haske gidan kajin gaba daya,ke ake fara gani a ciki da tsangalalliyar rigarki gwiwowin ki da kafafun masu kauri da kyau duk waje suke,kallonta Omar yayi wai don Allah a lokacin ba kya jin kunyar mutane?
Dariya Iklas tayi kai nifa idona a lokacin tar nake ganin kowa,na saba da shiga cikin maza dasu nake gogayya kullum,kaga kuwa ai dole ido ya bushe,
Wai kai ai kadan ka gani danma baka ganni a tsakiyar yan wiwi ba mun kafa daba guga suna zuka tare da bulbula hayaki,to can kuma me ya hadaki da yan wiwi? Dariya Iklas tayi tare da boye fuskarta a kirjin Omar,kasan me a time din babu wanda ke birgeni irin dan wiwi,ni idan baka zuka hayaki ba ruwana da kai,kawai naga ana feso hayaki ga wani kidan Bob marley yana tashi ko wakar ganja fama,ka harde kafafu kawai ka fuske kana bulbulo hayaki malam,
Dariya Omar keyi sosai,amma dai basa cewa suna sonki ko?ai kasan duk wani dan wiwi idan ya shahara ya cika dan wiwi to baya mu'amula da mata,basu fiye neman mata ba,ko budurwa basayi,idan na samu ribar tallana har hamsin nake raba musu a zuka hayaki,ni kuma inyi ta kallo ina jin dadi,
A kunna wakar ganja farmer subhanallah kai kanka zasu birgeka yanda ake zana love da hayaki,murmushi Omar yayi lallai Allah ya kare min matata shi yasa ba a son daurawa yaro talla,idan ba wanda Allah ya tsare ba lalacewa sukeyi,Iklas tace wlh kuwa honey kafin kaga yar talla wacce ke fita tasha,ko titi ta gari sai an tona,duk a tallan maza ke lalatasu,ga shaye shaye yanzu wasu sun waye da sha banalin,codine,da sauran kwayoyin maye duk a sanadin talla,nima Allah ne ya shiryani kuma Ummi tayi mana tarbiya,ga addua ina dagewa amma da tuni nasan nabi duniya.
Za kaga manyan masu kudi suna parker motoci suna neman yan talla,su kashe mata kudi,shike nan idan ba ayi sa'a ba tabi duniya,rayuwarta ta lalace,sai kaga yan majalisu,senate,com,yan kasuwa da manyan masu kudi suna bin yan talla,kafin kace me an rude ta da kudi
Kaga suna tayi mata maganar batsa tun bata yarda har ta yarda,wasu kuma ayi musu fyade,watafa honey me chemist ta kaiwa talla amma ya bata kwaya yayi mata fyade,
Wasu a shaguna,wasu kango,wasu su koma karuwanci,kai alot fa,talla bashi da afani ga mata kawai sai dai wasu sabo da talauci ba yanda za ayi,wasu kuma son abin duniya,wasu kuma rashin gata kishiya ko dangin uba suna rikesu sai su dinga tura su talla suna cin amana,ba Arabic schl bare boko,Allah ma ba a sani ba bare a bauta masa.
Allah kyauta wifey gaskia ya kamata ki fara yiwa mata wa'azi a kasar nan, ta kyalkyale da dariya tare da dan dukansa a kirji cike da shagwaba tana turo lips dinta tace kai honey ba dama nayi magana sai ka ce wani wa'azi,ina fada maka abinda na sani ne kuma kaddarar rayuwa ta kaini kasan ba dadewa ce a duniya take sawa asan rayuwa ba,kaddara ce da mutum zai cinci kansa yake sawa yayi nasa karatun duniyar,
Amma da nayi maga......ba tare da ta ankare ba ya fara kissing dinta a wuya,daga nan ya gangaro lips dinta,tare da shafa mazaunanta masu matukar raushi, kafin kace me wasa ya canja salo,sosai Gomnati ke enjoying, sai da ya lugwigwitata son ransa tana biye masa,sannan ya kyaleta itama ji tayi tana matukar bukatar Omar gaskiya,
A ranta tana anya zan iya 1mnth ba tare da na yarda da Omar ba,can ta tuno wahalar haihuwa,sai kuma tace kau dan wuya ai ba a bar dadi ba.
Omar kuwa da kyar ya saita kansa so yakeyi ta hanyar wayo da salon dabara Gomnati ta bashi abinda yake so,idan ya nuna ta karfi ko yayi mata dole to zata ki yarda ko su sami sabani tunda irinsu Iklas saida lallabawa.
Kallonta yayi cike da sha'awa sai Mirza yatsunta yakeyi, cike da shagwaba yace my heart yunwa,au na manta bari na kawo abincin ta fada tare da mikewa ya jawota a hankali ta fado jikinsa kiss ya manna mata a goshi tare da cewa jeki dawo ki sanmin milk din Prince,bata gane me yake nufi ba tayi waje.
Abincin ta dauko jere a katon tray me mugun kyau na yan gayu ta ajiye a kasa tare da shimfida katon carpet me tsananin kyau da birgewa ga duk Wanda ya gashi,
Zama yayi a kai sannan tayi serving dinsa ta fara ciyar dashi tare da yi masa kalamai masu matukar sa nishadi da jin dadi Wanda ke kankarowa mace daraja a idon mijinta,me kara sa miji yaji gaba daya ya narke,ya tsunduma,tare da cabalbakewa cikin kogin son matarsa,
Shagwabashi Iklas keyi sosai kamar wata Mamansa,shi kuwa Omar jinsa yake kamar yaron goye a wajen Iklas,yaron ma irin danye cakal din nan.
Bayan ya gama cin abinci Iklas tana kasa ta mike kafafunta kusa dashi kanta yana kafadar Omar tana wasa da zaren jallabiyarsa da ke lilo a wajen wuyansa,
Zamewa yayi tare da daura Kansa a saman cinyar Iklas ya kwanta kamar zai sha nono,a hankali ya dage rigarta dukiyar fulaninta suka bayyana farare tas dasu,nipple din jajir dasu,kansa yasa a tsakitarsu wani azababen kamshi ya rikitashi sai fisgar numfashi yakeyi tare da shidewa,
Iklas kuwa lumshe ido tayi tare da zama dagalolo kamar wata doluwa Omar ya fara kaita karshe da salonsa,idon sa jajir yace wifey ki sanmin milk din prince kinji,baki ta bude ta firgice,da karfi take son Jan rigarta tana so ta rufe amma Omar ya rike rigar gam ta kasa,
A rude tace me...me zaka sha nonon Prince kayi dashi wannan ai kazantar taka ta kai karshe,ni ban taba ji ba a duniya,idan babu kyau fa?ni bani da Ilmi a nan,amma ko ya halarta baka kyankyami me zakayi da shi,kuma ma ai shanye masa zaka yi,
Ganin yanda ta rude kamar zata zura da gudu yasa Omar cewa calm down Baby relax kiji mana,shuru tayi tana saurarensa ba a koya muku a Islamiyya ba?baki da ilmi a kansa ni ina dashi,matukar miji bazai shanyewa jaririn ruwan nonon ba a barshi da yunwa,yazo ya cutu ko ya shiga wani hali to ya Halarta miji yasha milk din matarsa,idan kuwa zai shanye masa abarshi da yunwa to bai halarta ba,
Wa'azi ya kunna mata inda akayi wa malaman sunna da dama tambayar kuma suka ba da amsar a haka cewar ya halarta,honey kinga mutanenmu da yawa basu San wannan ba,turawa ne da larabawa da sauran yare suka San da wannan,akwai hausawanmu da yawa basu sani ba.
Shi yasa Neman Ilmi yake da dadi,ya kamata a dage da nemansa ta ko ina.
Yanzu kai baka kyankyami?murmushi Omar yayi muke shan na rakumi,na Saniya Dana akuya ma bare abinda Prince dina ke sha,kuma milk din my heart,liver and my blood.ni ba wani kyankyami sai dai idan baza ki bani ba.
Ni ba ruwana kai kaga zaka iya.
Ai kuwa Omar kamar jariri ya kama zukar milk din dukiyar fulanin Iklas ji kake makwat,harda yin wasa da dayan, dan kadan yasha Iklas ta kwace abinta ta rufe tare da cewa Kazami zaka shanyewa Prince kalli yanda kake lashe lips,to kaga dai a jikina yake ko?to wlh bazan iya sha ba.
Ke kika ce ai,ni as from 2day kullum ki dinga ajiye min milk dina.a'a bazan iya ba kato dakai ga prince kunyi min yawa ai sai kusa na rame.Ummi ce ta sa aka kira mata Ikkas,
Da sauri ta sami Ummi a room dinta Ummi gani lfy?ina fada miki ki kiyaye shigewa miji kinki ji ko? Yaufa satinki biyu da Haihuwa amma ke bakya gudunsa,so kike ki samu wani cikin ko kiyi kwanika.
Dire diren kafafu Iklas ta fara tana make kafada,ni a gaskia abinda kikeyi Ummi bakya kyautawa,kun cika fassara mutum Ku tsofaffi Ku ke jawowa wasu kaga daga sun haihu sai aure ya mutu idan kuka kawo yarinya gida wai goyon ciki sai Ku hana mace ko mijinta tayi hirar kirki dashi,ba kula da miji,ba zance me dadi,kullum ta dinga gudunsa har sai kiga a haka aurenta ya mutu ko kuma ta jefa mijin ya kasa daurewa ya fada Neman mata.ni kinga ina tsoron kara haihuwa amma wlh akanta bazan kasa zuwa na bawa mijina kulawa ba,to naji magana uwar yan wa'azi da an tabaki yanzu kya fara nasiha,naga yanzu tunda kika daina son aikin Gomnatin nan kika daina rubuce rubecen iska sai kika koma wa'azi,ke a dole kinyi hankali kinyi aure ke ga me miji ko,?
dan ubanki jeki ki bashi kanki ke zai bari da wahala,baki Iklas ta turo gaba Ummi pls ki dinga ganewa kina yawa fa Ummi ya za ayi ki dinga kwafsawa ke kullum harkar daa can zamaninku kike kawowa,Iklas tana fada tana yarfe hannu tare da yatsina fuska,ki gane Ummi ba cewa nayi zan bashi kaina ba,nimafa ina da hankalina ba sai kin dinga sa min ido ni da mijina ba,Ummi ce ta jefeta da cokalin da take cin dambu ai kin gaji Ubanki haka yake shima kan matarsa bashi da kunya,jininku haka kuke ai, dariya Iklas tayi tana daga jikin kofa tace Ummi hardake fa haka kenan kika kula da tsohon mijin nan naki ko? Dariya Ummi tayi Ohh ni jikar Hauwa'u naga ta kaina da Iklas
Ummi ki daina damuwa akwai solution ba wani ciki ki daina samin ido yanzu kai ya waye bazan jira haka kawai Ku jawo min salalan tsiya mijina yayi fushi dani,ko aure na ya fara tangal tangal,ko mijina na jefashi hanyar bin mata ba,domin ni Kadai ta shafa,iyakaci idan na kawo kararsa kunyi min mutunci Ku bani hakuri kuyi addua ko Ku lallasheni. Kinga yaushe zan yarda da shawararku.ni nasan halin mijina Ku barni inji da abuna.to Gomnati Allah taimaka fita ki bani waje na gaji.
Ummi ce tace au na manta ban fada miki ba Mama zata tafi Umra ita da Baffa,suleim,da Suhaila wani watan me zuwa,sosai Iklas ke murna,tace kuma Baffa Nima ya biya min aikin hajji bana dani za aje idan muna da Nisan kwana,ke kuma yace ke mijinki yace tare zakuje dashi kafarki kafarsa da Prince. Tsalle Iklas Ta farayi tare da rungume Ummi sai murna sukeyi.kamar ba Ita ta haifi Prince ba sai tsalle takeyi, lafiya kenan inda ita komai mutum gani yake dai dai dashi ne,Iklas ba a Girma cewar Mama da ta shigo ta kama Iklas na tsalle.
Sai godiya Iklas ke wa Mama taji labari.
Ibzzy Boy ne tare da WANKAN TSINKE sun cakare suna shopping a wani katon Mall,wani Babban abokin Ibzzy ne ya shugo suka tafa yana karewa Ibzzy kallon,man kana