Author : Asma Baffa Category : Romantic Hausa Novels
da wasu yan biki suke shiga ba,sauran rooms du Mama tasa musu key.
Dolenta ta jira Omar sai abinda yace.9pm sannan Omar yace tayi wanka,10pm sun gama shiri tuni frnds din Iklas sunje can,sai waya suke mata,Sultan da amaryarsa Yasmin, Raj ma yaje.
Kwaalliyar su Iklas fa
INA TARE DAKU MUTANENA
Asmabaffa
[9:10AM, 4/10/2018] +234 810 468 7075: ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ
125-130
By
Asmabaffa
Iklas ce tayi shiri idan ba mugun saninta kayi ba baza ka gane ta ba,wani tsadajjen material tasa na nunawa a gari,Red ne da zanen Arsh color jiki, yayi mugun kyau,duk yafi na amare kyau da tsada,dan Omar ba karamin kudi ya zuba ya siya ba,Riga da skert ne,tasha kyau kamar Ku saceta dan tsayawa ma fadar yanda shape dinta ya fito bata baki ne, Omar yasan size dinta mayene.takalmi me tsini arsh da wata shegiyar pose yar gaske same color da shoe,Omar ya fito daga wanka sai da kyar ya tabbatar wannan Iklas ce,
Iklas fa har gwagwaro itama ta kai aka Nada mata na kece raini,gashin nan ta gyara jelar na reto a tsakiyar baya murtukekiya,ta fito da ita ta tsakiyar goggoro,dama ga jiki yasha gyara ko ina kyalli takeyi,turaruka kuwa sai da Omar ya koreta,zama tayi tana jiransa yana shiryawq tana ta guntse dariarta wai ganin sandar girman Omar a short wando,yana kalonta ta gefen ido,kin San Allah zanyi maganinki ki koma Palo ki jirani kan me zaki sani gaba ki dinga kallona kina daria,baki ta rufe da tafin hannu nayi shuru to.
Harara ya watsa mata yana ta shirinsa tana satar kallon jiki da kira me kyau irin na Omar, Allah ya bashi diri da kyau ga skin dinsa kalarta ta kwashewa Iklas Imani,
Wani rantsatsen yadi me taushi Omar ya sa,shara shara sosai arsh color kalar material din Iklas komai Arsh yasa,dinkin zamani dai dai jikinsa wandonma,Omar uban yan wanka suma taci wani gyara me kyau,tayi luf,turaruka ya fesa sosai,ya fito kwas rike da waya,Iklas ma wayarta fankaceceiya a hannunta,mikewa tayi daram ta isa wajensa yaya Omar kalli fa kayanka shara shara har singlet ana gani,wandonka ma dan an masa landing daga samane amma ai sai adinga hango uhmmm.....uhmm....da ka canja shadda ma ,ke jikinki ko nawa ina ruwanki cewar Omar.kowa ance miki irinki ne me kurawa mazan wasu ido,let's go idan zakije if not na tafi,
Ita Iklas kar a kallar mata kyallin fatar miji,gashi tasan dole Sahar tana can.
Hannunta ya rike suka fito duk gidan Shuru sai yan aiki da suke aikin gyara gida kafin a dawo.
Wata sabuwar mota fil arsh color itama Omar ya bawa driver key a baya suka kame kamar sune amarya da angon,kajifa yan fassion
Har wajen driver ya kaisu,tun daga waje zaka San wajen ya girmi me karamin karfi.
Sahar da frnds dinta an kwafe a kujera tana baza idon ganin Omar,dama su gulma ce ta kawosu da niyar wulakanta Iklas gaban mutane,
Amare da Angwaye ana kujera an fara shagali suna kallon masu rawa da liki,su Kansu Omar suke son gani saboda frnds dinsu su kalli haduwa,najja da sauran kannensu sai iyayi akeyi a fili ana kada hips,kaji kannen Amarya fa.Iklas ce ta masa rada pls ka fita munzo fa idan ka fita ka bude min kofa na fito a Gomnati ta.
Driver ne ya budewa Omar kofa.
Murmushi Omar yayi tare da fita cike da kasaita,omar kuwa zagayawa yayi ya budewa Gomnati itama ta fito,tana fitowa zuruf ta sakalo hannunta Dana Omar ta kara shigewa jikinsa kamar zata shige jikinsa gaba daya ba space da ko tsinke zai iya shiga.wani kar kar kawai Omar ke ji a cikin jininsa kawai Iklas yake bukata, kara manneta yayi suka tafi domin shiga hole din,
Duk Wanda yayi tozali dasu sai ya saki baki da ido dan kallon kyau irin nasu,ga iya wanka,ga shiga me tsada da ka gani ba sai ance ba,gasu sun birge masoya da gani wannan real love ne,dama Iklas tace bikine daga mota sai hole shi yasa taki daukan gyale,
Sultan da Raj suka fara gani cikin wurin,daria suka dinga yi sun San Iklas sarai, wuyan Sahar da frnds dinta kamar zai tsinke dan kallon su Omar,suma su Najja sai nunawa frnds Omar sukeyi ga yayansu babba,wajen da aka tanadar masa najja ta nuna masa suka zauna,Mama da Ummi suna can baya sunga su Omar har murmushi sukayi,Iklas ba dama cewar Ummi.
Duk Iklas ta kasa sakewa yanda taga yan mata na kallon Omar,kamar tayi kuka,shi kam Omar ta kansa yakeyi ganin Saleem a wajen su Angel kawayen Iklas,
Yayan amare aka kira kan ana so ya chashe a fili dama Iklas ta matsu su shiga fili rawar Igbo zatayi yau tace, ai kuwa kafin Omar ya juyo sai gani yayi Iklas har ta danyi doro kamar zatayi ruku'u tana ta kada hips,tafi da ihu fili ya dauka kafin kace me an rufeta da liki maza da mata,su Kansu su Sadiya ta birgesu rawar,
Maman waleeda ma sai liki takeyi sai da ta karar da yan kudin cefanen da Baban waleeda ya bayar na 1mnths,kinga ta kanki da me zasuyi girki,Jamila sule,Haj jamila duk sai balle bakin jaka sukeyi,Zulaihat da su Juwairiya duk an Hallara a fili,sai Diyar katibi me gyara fili ce tazo ta koresu kasa tukunna.
Omar sannan ya fara likiwa Iklas yan dubu dubu,itama mikewa tayi ta gama rawar ta fara barin kudi musamman Omar ya bata dama,masu DJ sun washe da Naira, Omar ne ya janye Iklas suka koma mazauninsu sai radar masifa yake mata kan tayi rawa,
Angwaye da Amare na fitowa suma sai da su Iklas suka yi ruwan kudi.su Aisha ransu ya fara baci fa anzo gidansu ana satar musu dukiyar Uba ana bawa wata banza,
Sahar takaici ya kamata ganin inda Iklas ke barin kudi Omar ne kuma yake bata,a gabansu ma ta karbi wasu,ita kuwa sahar taga ko time din da take matarsa baya bata haka.
Da kyar ya bar Iklas taje wajensu frnds dinta da saleem suka gaisa sai kiranta yake a waya ta dawo wajensu,komawa tayi ta barsu suma suna kallon ,tana zama Sahar ta karaso wajen,hararar Iklas Sahar tayi,Iklas ma ta rama harda karin Jan tsaki,
Sahar dauke idonta tayi ta kalli Omar how far kwana 2,ko da yake nasan wasu sun manne maka yayan matsiyata,sun hanaku sakewa a gid....saukar ruwan lemo me sanyi Sahar taji a fuska da kirjinta,wacce ba kowa bace tayi sai Iklas,Omar kuwa yaga sanda Iklas zata aikata kyaleta yayi ta rama.
Kawayen Sahar ne suka zo da niyar dukan Iklas Sahar ce ta hanasu Ku bari a gama party tukun,komawa wajensu sukayi suna jiran a gama party su karya Iklas,
Iklas kuwa hankalinta kwance tasan gata ga Omar.
Frnds din Iklas ma sun zo sun gaisa da Omar,dinner party yayi dadi gaskia,haka har aka fara tafiya gida,su Mama ma sun tafi,Saleem da frnds din Omar Dana Iklas duk sun tafi,Iklas ta rakasu ta dawo wajen Omar wani Frnd dinsa ya tareshi yana ta jansa da surutu kuma wannan duk plan din Sahar ne,
Radawa Iklas yayi je ki jirani a motar mu,tana fitowa ta ci karo da su Sahar sunyi da'ira,ta tsure ganin ba Omar gashi mutane sun tafi,ta tsorata sosai, amma bata nuna ba,sai ma murguda musu baki da takeyi tana ja baya,
Sahar kukan kura tayi ta damko hannun Iklas daya, tana danna mata ashar iri iri,
Kawaye na zuga Sahar,da dabara Iklas ta dago kafarta ta Ciro takalmi daya me tsini ai kuwa ta kwalawa Sahar a kanta wajen ya fashe sai jini,arcewa Iklas tayi tare da banke wata kawar Sahar dake kan hanya,da gudu ta fada motarsu tacewa driver sa lock.haka driver jiki na mazari ya danna lock,
Sahar sabo da bacin rai ji tayi kamar ta kashe kanta ta huta,jikin Motar tazo da niyar shako Iklas amma ina a kulle gam,Iklas lekowa tayi tana ta yiwa Sahar gwalo iri iri, ta murguda baki,tayi fari da ido,ta kebe baki,ta tale mata baki,ga gwalo.iya kuluwa Sahar ta kai karshe,juyawa tayi suka shiga motarsu da frnds dinta suka wuce da niyar irin hukuncin da zasu yankewa Iklas idan Sahar ta koma gidan Omar.
Gaba daya Sahar tace sai ma ta kashe Iklas du.
Queen mermu ma kungiyarsu duk sun tafi dama kallon bikin yan gayu suka zo, 2:30am Omar ne ya fito tare da bude mota ya shiga,shigarsa ke da Wuya ya ga Iklas sai gyangyadi takeyi,
Mikar da ita baki isa kinmin bacci ba a mota wa yace kizo sai da na hanaki zuwa amma kika ce ke sai kinzo Ashe burinki kiyi rawa ki kadawa maza jiki,kinci sa'a daya muna wajen mutane da na nuna miki yanda ake ball da mutum.
Cike da jin bacci ta kwanta a cinyarsa pls ka barni nayi bacci,kyaketa yayi tare da Dora hannunsa kan cikinta,dayan hannun kuma yana cire mata goggoro kanta,wai taji dadin bacci,
Munafuka Iklas idonta ras baccin karya takeyi wai dan kawai taga yanda Ya Omar zai lallabata,sai dariya takeyi a boye,
Kara juyi tayi tace wash na gaji kafafuna,takalmi ya zare mata ya Shiga dannan mata kafafun.
Iklas aranta tace inye ni din ba,naji dadina tun ban shiga ciki ba kenan,kai Allah ya Omar so na yakeyi, duk a ranta take zancen ta
Kukan shagwaba ta fara uhm..uhm...uhum..bakinsa ya kara saitin kunnenta yana matsa mata kafafu a hankali yace ya akayi wai?yunwa nakeji ni,tuni Omar ya bawa driver umarni ya kaisu wani tsantsararen eatery suyi take away.
Anzo wajen Iklas ta hana Omar tashi Sam wai ni....ka aiki driver ya shiga ya siyo,haka driver ya je ya kawo gashashiyar kazar hausa,da h-bugger sai chips da kayan sha na sanyi.
Sunzo gida tace Sam baza ta iya takawa ba,abin na Iklas da iskanci cewar Omar kayan ya kwasa yayi gaba abinsa,dole ta fito takalminta a hannu ta shiga part dinsu,kowa yayi baccin gajiya gidan shuru,
Wajen Ummi taje ta ganta tana sallar dare,sallamewa Ummi tayi Iklas ki dawo ki kwanta nan nafa gaji da halinki,kinbi kin nacewa mutum ki ja ajinki namiji ya biyoki amma ke kamar ba mace ba.
Turo baki Iklas tayi in kun San hakane me yasa aka bashi ni,kuka aura masa ni,in hakane Ku kyaleni yazo ya nemi auren da kansa mana sannan Ku bashi ni.
Amma kun masa aure kun hana bawan Allah matarsa,Ku fada masa ma ni matarsa Ce kun kasa, kun hana mu fada,ni wlh in na gaji fada zanyi,kune kuke ganin abinda nakeyi a rashin class mu zamanin mu irinmu ake nema,
Baki Ummi ta saki tana kallon Iklas,carbi ta Zara ta zabga mata a baya yar banza wacce bata da kunya ko daya wajen ubanki kikayi gado bazanga laifinki ba,haka shima yake akan matar sa bashi da kunya.tafi ki bani waje kije kiyi ta kwana dakinsa.
Idan ya miki ciki ke kika jiyo,daria Iklas tayi wlh ni kuwa na haifo Dana kece zaki min wankan jego amma sai ya Omar ya yarda,kuma Allah ki gasa masa cibi ta gasu.
Banda mugunta ki sa yaronmu kuka ki shaka masa sabulu wajen wanka,Ummi ji tayi Iklas ta bata kunya ma,ba shiri taci gaba da sallarta.
Wanka Iklas tayi tana fitowa taga Omar ya kawo Mata take away,Ummi tana ta Sallarta taga Omar ya wuce wajen Iklas sai rada sukewa juna bata San me suke cewa ba.
Iklas ta koyawa Omar rashin kunya cewar Ummi, yaro nutsatse ya susuce kan mace ni na gaji ana gama bikin nan a bawa yaro matarsa su karata can,zan sanarwa mahaifiyarsa.
Abincin da suka siyo ya mika mata yace karba,ki tabbatar kinci da da yawa,zan kiraki anjima na tabbatar kinci,
Ummi ya juya ya kalla Ummi sallah kike yi dan Allah ga amana nan kisa taci da yawa tayi bacci ta huta gobe daurin aure da safe baza ta samu damar yi ba,
Sallamewa Ummi tayi ba shiri tace kaci gidanku Umaru,dan iyayenka kaima ka zama fitsararre ko,Ku kiyayeni,murmushi yayi ya kalli Ummi zanzo Ummi idan na samu time zamuyi wata magana.Allah kawoka fitar min a daki,ke kuma kin tsaya min a kai wuce ki bani waje.a bed dinsu ta zauna ta fara cin abinci ta ragewa Ummi nata.
Omar fa shi ya hadu bazai cewa Iklas yana sonta ba direct kawai zata gani in action, idan tafiya tai tafiya,ya tabbatar ta gane sai kawai a zarce da I love u. Fadar wance sonki nake,ko ina sonki da farkon farawa to kauyancine kajifa Omar. Iklas lallai in hakane jira ya ganki.
Asmabaffa tana jinjina ga masoya novel din nan a duk inda suke. Allah ya saka muku da Alkairi.
ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ
130-135
By
Asmabaffa
Misalin 10am kowa ya gama shirin daurin aure maza da mata cikin kwalliya suke kowa yana ji da kansa,
Iklas tasan Ya Omar farar shadda zai sa tunda sanda ta kai masa breakfast yana shiri,yasha kyau tsayawa fadar kyan Omar bata baki ne
Iklas ma wanka tayi ta shirya cikin farar shaddarta kwal,sai kyalli takeyi taci dauri da dankwalin shaddar,Ummi ce tace haba Iklas kefa matar aure ce karki manta ki dauki mayafi,fafur Iklas taki yarda ita ba fita zatayi ba baza ta sa mayafi ba,
Part din su amare ta wuce,basu mata komai ba sabo da gargadin Umma,kallon yan mata taje yi,itama ana binta da kallo tasha shadda me tsada,wasu cewa sukeyi ko yar Gonna ce,
Sadiya amarya Iklas tasa ta fara linke mata kayan da ta sa,kafin daurin aure,ai kuwa ba musu Iklas ta shirya mata komai,Aisha ma sai da ta aiketa wajen Umma Rahina ta kai mata wasu plates,
Tana tsakiyar yan mata ana hira da ita tana tofa albarkacin bakinta cikin manyan mata,
Sadiya ce tayi magana pls Iklas a fesa roomfreshner a waccen part din an daura aure yanzu angwaye zasu zo mana.
Nan ma da sauri Iklas taje tayi yanda tace,ta dawo kamar yanda yan mata ke kara goga powder da gyara kwalliya haka Iklas tayi amfani da kayan kwalliyar Sadiya tayi kwalliya,
Duk mutanen wajen kallon Iklas sukeyi duk Inda ta juya,tayi kyau ga iyayin tsiya gareta kamar babba,shi yasa suke kara mamakinta.musamman in tana tsara zance da kawo shawarar dabarun zaman aure,
Aisha ce tace Iklas jeki ki bude palon gasunan sun zo,sosai suke mamakin Iklas dama haka take da saukin kai da ladabi,Iklas kuwa komawa tayi ta bude,ta fito zata dawo ta hango Omar da Sultan sai Raj da sauran frnds din Omar da yawa,
Ido suka hada,da ido ya mata alama ta koma ciki,wajen su sadiya ta koma,bayan Omar ya raka frnds nasa sunyiwa mutan gida Allah sanya alkhairi rakasu yayi suka tafi,
Iklas ya kara gani this time around da gyale fari jikinta maza damkam angwaye biyu ko wanne da abokansa sun zo,komawa tayi da nufin shiga palon da angwaye suke,ji tayi an fisgota sai da ta fada jikinsa,kamshin turarensa ne ya sa ta gane Omar ne,har part din Mama ya jata,
Warning ya mata kar ya kara ganinta a waje,hakura tayi ta koma cikin dakin Ummi tayi kwanciyarta ta dinga bacci abinta.
Sai da su Sadiya suka kwashe kusan 1wk suna biki,ana gama shagali aka kai ko wacce hadadden gidanta,aka barsu daga su sai halinsu.
Koda Babar saleem tayiwa Ummi maganar saleem yana son Iklas hakuri Ummi ta basu ta sheda musu anyiwa Iklas miji,har auren Iklas ta fada mata, saleem ya shiga damuwa sosai jin labarin Ashe an Dade ma da yiwa Iklas aure, amma daga karshe ya fawwalawa Allah.
Baffa ne ya kira Omar ya bashi Umarnin lallai ya maida Sahar dakinta,sabo da baban Sahar yana ta bashi hakuri saboda Sahar ta dami