Author : Billy Pinky Category : Arewa Pen
nadauka nasaka a hand bag na fita,
Su anty Waleeda suna ta sharar bacci harna mu tafi
Muna zuwa ya bani 1k godiya na mai ina karasawa ciki.
Yauma Isha ta rigani zuwa ban dade da zuwa ba mu fita gabatar da program din ranar Thursday da ba muyiba.
"Bayan mun gama mukhtar yake cemin MD na kirana,
Kai tsaye office din nashi na nufa ina shiga,
PA dinshi da sai cin magani take ta min iso gurin shi,
ban damu da kallon da take minba na karasa da sallama.
"Tsaye na ganshi sai zagaye office din yake,
Nima tsayawar nayi ina furta,
good afternoon sir!
Nuna min gurin zama yayi shima yana kai zaune.
Jin ya kafeni da ido ya sani na dago daniyar magana dan nifa na tsani kallo, shikuma ya kware indai gurin kallo nane.
Yah jikin naki?
Ya jefomin tambayar da saida na dago na kalleshi.
Ai naji sauki! Nafada ina kasa da idona .
Masha Allah!
Dama dalilin da yasa na kiraki ina son magana dake ne,
Uhm inajinka na fada cike mamakin wacce magana zaiyi dani.
"Cikin bazata matukar bazata na d'ago ina kallon shi jin maganar da banta b'a tsammani daga gare shi ba.
"Wallahi safiyyah ina son ki ina burin ki zamo uwar y'a'yana tun randa na ganki naji ina sonki wallahi, tinanin ki ya hanani bacci, har gidan ku naje acemin Wai banan bane gidan, ko sawa nayi yau tayi please kar kicemin aa.
Ya karasa maganar kamar zaiyi kuka idon shi na tara kwalla.
Ni wallahi dariya ma yabani da tausayi gami da kunya.
"Na baki lokaci safiyyah kije kiyi tunani da kyau, Insha Allah duk abinda kika yanke zan amsa da hannu biyu, amah kimin adalci please.
Ya 'karasa maganar cike da magiya.
Kai kawai na gyada mishi na fice daga office din,
Kai tsaye office din mu na nufa, mu cigaba da abinda muke,
gabaki daya tunanin maganar nake. to ya akai ma yasan gidan mu, haka dai har atashi takardun dazan kaima ma cewa nayi Isha takai mu hadu a mota,
Koda ta tambayeni cewa nayi bakomai na wuce.
Da ta dawo take sake tambaya ta, meya faru naji MD yace intaya shi rarrashin ki?
Bakomai! Na fada irin banson wata tambayar,
Amah safiyyah baki da wata aminiya data wuce nida buhaisa, haka nima bani da wata aminiya sama dake, kinsan bana boye miki damuwa ta. amah some time kina boye min damur ki bana takura ki da dole saina ji, shikenan.
Ganin taji haushi kuma nima fa banyi adalciba, hannun ta na kama, kiyi hakuri kinji sis wallahi ba haka bane, nafad'a mata duk yadda muyi da shi.
"Uhmm safiyyah ta kira kinsan menene?
"Aa saikin fada isha"
"Wallahi ki amince ta ko ina MD ya can-can ci a soshi.
Don mutum ne nagar tacce wanda yasan ya kamata mai ilimi.
A taikaice wallahi
*🌹 RAYUWATA 🌹*
_Story and written✍️_
*Bilkeesu .S. Aliyu*
_💞(Billy pinky)💞_
*🤝 Amanar nazari writer's association📚🖊️*
*[07070260240]*
_WhatsApp number or call_
_📚N.W.A🖊️_
_*_Masu comment gaskiya comment dinku yana sani nishad'i sosai*_
*_Kuna cikin zuciyar Billy pinky kuna dabbane wallahi my fans_🥰🤗💃💃*
*22&23*
"Kamar ko yaushe ba abinda parlour yake sai kamshi mai sanyaya zuciya mai shaka,
Youseef dake biye dashi ya ajeye mishi laptop wayoyin shi, tare da furta sir baka bukatar komai?
"No youseef kaje Saida safe"
"Thank you sir Allah ya tashemu lafiya"
"Ameen"
Ya amsa asaman labba.
"Bedroom ya nufa Koda ya shiga zama yayi a gefen bed yana bin ko wacce kosurwa da kallo kamar mai san ganin wani abu,
Mikewa yayi ya fara zame kayan jikinsa domin shiga wanka.
Yaja tsawon lokaci kafin ya fito sanye da bathrobe ash calour sabuwa dal dan yadda take wani maski-maski zai tabbatar da hakan karamin towel dake hannun sa ya kai kan ji'ka'kiyar sumar kansa mai tsawo data kwanto masa har fuskar sa.
Kai kace ya hada jini da larabawa,
Tamkar bashi kadai bane a dakin fuskar sa adaure ba alamun rahama a cikin ta.
Gurin mirro ya nufa hand dryer din dake gaban mirror ya jona a socket, cikin 'kan'kanin lokaci ya kammala gyara ta, lotion ya shafa sama-sama sai sprays dinsa masu shegen kamashi
sanan ya nufi close d'insa, fari pyjamas mai shegen kyau da laushi sai boxer shima dai sabo, tsaf yayi shirin nasa ya koma gaban mirror yayi wakan tsaddadun turarukan baccin sa masu kamshi kamar ba dare ba,
Kai tsaye parlour ya nufa tsit yake sai karar tv da yake ta aiki, zaune yakai kan sopa, madarar da auta ta kawo masa yanab wanka, ya zuba a cikin karamin mug yana sha yana aiki a laptop.
Sai 12:pm ya wuce bedroom ya haye bed ya kwanciyar sa kace wanda bashi da wata damuwa a rayuwar sa, saida yayi addu'oin kwanciya bacci ya lumshe idanun sa, kafin wani dogon lokaci ya fara sauke numfashi a hankali alamun yayi bacci.
_____✨✨
Koda zaituna tashiga granny na ganin yadda tashigo rai bace, yasa ko kallon ta batai bahar ta shige bedroom din ta.
Koda auta tazo amsar masa madara saiga tanan ta fito wai tabata takai mishi, a'aa kibarta takaimi shi ita ya aiko, kuma kinsan halinshi basai na fada miki ba, inba so kike daga ke har ita ranku ya baciba.
Kinga habibah ga madarar can acikin fridge ki dauka ki kaima sa, Tom granny auta ta fad'a tana tashi,
Madarar ta dauka kana tai musu saida safe.
Granny ce kawai ta amsa amah zaituna tsaki tayi tana tashi,
Kinga wallahi in baki fita min hanciba zan feto ki, ya zaki zo mun daki kina min tsaki kamar dangin tsaka, akan wanda besan ma kinai ba, kinsan Allah ko yasan kinayi zan hanashi auranki, tinda ku baku da kunya, daga ke har uwar taki kallon ku nake.
A batace ba sai baki da take turowa tashige daki,
Kwafa granny tayi taciga da kallon Indian film din da akeyi, yadda ta kafe tv da kallo zaka dauka tasan me akeyi, lokaci-lokaci takan ja tsaki da fad'in tirr.
(Hajiya granny tamu dama ina ke ina kalon Indian film😂)
"Koda taje kaimai madarar taga bashi a parlour, ta d'an zauna daga taji shiru ta ajiye mai takama kanta, mezata zauna tayi wayace tun rana an kawo mata ita kud'i kuma taji alert.
___________
*Kaduna✨*
Kadan nasha garin kwakin na ajiye shirin kwanciya nake saiga Kira,
Bakuwar number ce kamar bazan dauka ba dan kuwa Saida ayi 2 miss call kana na dauka.
"Assalamu alaikum"
Cikin mamaki na ciro wayar ina kara dubawa kamar fa muryar MD nakeji, jin ance Safiyyah yasa ni maida wayar ina amsa mai sallama,
"Zakiyi mamaki ina na samu number ki koh?"
"Uhm"
"Agurin Isha na amsa, kin koma gida lafiya?
"Lafiya lau"
Mum dade muna wayar shike firar nikam Iya kaci nace uhm, uhm-uhm, kamar wata kurma.
Bayan munyi sallama, yah Ansar da tunda muke wayar ya kirani na kira,
"Assalamu alaikum Yaya nah"
Wa'alaikis Salam little sis yakike?
Lafiya lau alhamdulila!
Kin koma gidan ne?
Eh yah na dawo tun jiya yauma har gurin aiki naje"
Masha Allah komai dai lafiya?
Alhamdulilah! yah Ansar ya aiki?
Mundad'e muna waya kam, har yake cemin ranar Friday zai dawo, naji dad'i sosai dan kuwa kamar na jawo ranar tazo,
Koda muyi sallama bathroom na shiga na dauro alwala, kwanciya nayi ina karanto addu'oi kwanciya bacci ban wani dade ba kowa ya daukeni.
Yauma kamar ko yaushe bayan na gama duk aikin gidan dan har breakfast nayi, tsaf nashiya cikin jar abaya mai ratsin fari, wace amah ado da fararen duwatsu, sai takalmi mai dan tudu white,
ribbon nasa na daure kaina, mayafin abayar nasa nai rolling da face mask da eyeglasses sai takalmi mai dan tudu white,
wayata Dana saka a hand bag ce tafara ringing,
hello yah safwan"
"Kifito mutafi"
Bai jira me zance ba ya yanke Kiran,
Har gurin aiki ya kaini ya bani 1k, godiya na mishi, ina shirin shiga saiga motar Isha nan tare mu shiga da ita
Kasancewar yau munada program akan matasa, mu'az yazo mutafi domin fara gabatar da program din, tini babban bakon mu ya iso, dan haka cikin kan-kanin lokaci mu fara kasancewar an gama shirya komai.
Motsi kadan idon MD akaina dan har ya fara takurani da wannan kallon nashi,
Koda mu gama cafeteria mu nufa domin cin abinci bayan munyi order muna cikin cin abinci saiga MD, kujerar kusa dani yaja ya zauna, hakan da yayi yaba ma kowa mamaki,
kasancewar MD akwai jiji da kai gami da miskilanci dan haka suke mai kallon mai girman kai,
ban dago na kalleshi ba naci gaba da cin abicina, da Isha su gaisa yasa amishi order, sai a lokacin na gaishe shi dan banso yau mu hadu dashi ba.
Aikuwa murmushi kwance a fuskar shi ya amsa,
Shiya biya kudin order bance komai ba sai Isha ce ta mishi magana, a gurin mu barshi mu tafi.
Isha ce yau ma takai ni har gida, mun dade muna fira a mota kana ta tafi ni kuma na shiga.
_________
*Abuja🤍*
Cikin nutsuwa gami da nagarta yake sa'kkowa daga mata'kalar benen,
Sanye yake cikin sute black sai neck tie golden, takalmin kafar sa da yake black kolliyar shi ta kasance golden, sumar nan tasha gyara ta kwanto masa har fuskar sa, hannu ya kai yana matsar wa, ga wani kamshi da yake mai saka nutsuwa,
tun kan ya karaso 'kamshin sa ya riga shi isowa, gaba daya suna dining area har Ammii, ido su zuba mishi a sace har ya 'karasa yaja kujera kusa da Ammii ya zauna,
Cikin girma mawa yake gaishe ta itama cikin farin ciki ta amsa mishi, suma gaishe shi suyi cike da girma mawa tunda yace lpy bai sake amsawa ba, to dama shi haka yake 'kar-'karin amsawa dai lpy. Shiya fara tashi a dinning din sai zaituna yau dai balefi doguwar riga ce ajikin ta,
"Majeed harka gama?
"Uhm Ammii zanje na gaida granny ne"
"Okay jiya dama da naje gaishe ta take tambaya ta nace ka tafi company tom inka fito kaje ka gaida su addah"
Saida fuskar sa ta canja, kai kawai ya d'aga mata kana ya nufi part din granny.
"Murmushi tayi tasan because tace yaje ya gaida su addah ne yasa shi bata rai"
Granny dake zaune kamar ko yaushe ta zuba ma tv ido, ba kamar jiya ba yau program take kalla na gidan tv haske inda safiyyah suke gabatar da program akan matasa
A dai-dai lokacin da Majeed ke shigowa da sallama ciki-ciki, a dai-dai lokacin safiyyah ta sake magana cikin zakin muryarta.
Shawara ga matasa ya kamata ama tsayin ka na matashi kari'ke martabarka ta matashi, wanda a yanzu haka yayi 'karanci ga matasan mu, kullum idanun su akan 'yan mata, burin yin kudi kota halin 'ka'ka, daukar shaye-shaye a matsayin wayewa, raina na gaba dasu saboda suna jin tashen balagar samartaka, rashin yin biyayya ga iyaye saboda jahiltar wayewar zamani, da kaga ka kai tsawo shikenan iyayenka sun zama abokan wasanka, fifita ilimin boko fiye da na addini,
Dan Allah taya za'a samu nasarori a RAYUWA?
Kalilannefa a cikin ku masu irin wannan 'kya'kya'kywan tunanin, 'karancin su yasaka kowa ganin tamkar babusu.
Dan Allah matasan mu ku gyara please, kune ginshi'kin kowacce al'umma, daku duniya take alfaharin, kudena shaye-shaye, domin kullum ruguza ku yakeyi, ya ruguza 'kasashenmu da al'ummar mu, ku Dena zina, kullum durkusar daku take da 'kaskantar daku, ku dena barandar siyasa inba hakaba kullum a 'yan turin mota zaku 'kare,
Dan girman Allah ku farka daga nauyayen baccin daya d'auke ku, ku daidai ta RAYUWAR ku, nutsu kuyi karatu, ku daina karatu domin burin aiki, karatu wata katangace a gareku, idan kun kammala koba aiki ku nemi sana'a kudena girman kai, 'kila wannan sana'ar itace mafi alkairi a gareku amah kullum burinku 'katon office why?
"Dan Allah ku sanja ku zama jarumai"
A hankali ya sauke ajiyar zuciya yana me janye idanun sa akan tv daya kafe safiyyah dasu har tagama jawabi, baya ganin fuskarta sosai, kasancewar sanye take da eyeglasses sai facemask dinta data jawo kasa dan da kadan ya wuce bakin ta,
Masha Allah masha Allah gaskiya yarinyar nan na matukar birgeni, ka duba fa yanda take jan hankali ga matasa bama iyasu ba kawai, da ace matasan mu zasu dauki shawar ta ai sun sauya da yawa,
Allah yamiki albarka d'iyar, nan kaima Allah yabaka mace irin wannan"
Da ameen yah amsa asaman labba kana su gaisa,
Yauma kamar fadi Saida ta kuma mishi maganar aure aikuwa ya hadde fuska yace, kinga granny please kidena min maganar, nan wallahi banaso dan ni har yanzu banga wacce tamin ba, yakai karshe yana sauke ajiyar zuciya.
Nifa bana son iskanci meye wani pilis kace kome oho, nifa in bazaka mun hausa ba to kamin shiru basan wannan cakod'addiyar hausar nan taka.
Takai karshen maganar tana balla mishi harara,
Murmushin gefen baki yasaki tare da fad'in, ayya sorry my granny tafad'a yana mikewa saina dawo,
Fuska ta sake hadewa jinya 'kara mata turanci, saida ya kama handle din zai fita tace Allah yah tsare ya bada sa'a.
"Ameen ya amsa a saman labba kana ya fice, kai tsaye part din uncle Abdullah ya nufa a parlour duk ya same su har uncle Abdullah yana shirin fita, zama yayi su gaisa kana su gaisa da mama matar shi kenan,
Tare su fito uncle abdallah ya tafi shi kuma ya shiga part din uncle sulaiman, su ma dai a parlour ya same su addah sai kuma Umma amarya.
Cikin fara'a su gaisa da addah, ita kuwa Ummu amarya irin miskilan matan nan ne haka su gaisa ba fara'a, koda ya tashi zai fita da wani kallo me kama da harara ta bishi har ya fice.
(Toh🤔ke kuma ummah amarya yada haka)
Fuskar nan a daure kamar wanda a aikowa sakon mutu,
Kallon shin yakai kan agogon dake daure a tsin-tsiyar hannun sa kirar diamond,
Time ya tafi da yawa gashi yau aikwai abubun da yake sonyi da yawa maybe ma tomorrow zai bar kasar,
Gashi ya dawo baije yaga yadda abu-buwan shinsuke ta fiyaba duk da youseef ne tsaye a kan komai.
Tsaki yasake ja akaro nabiyu,
Har ya isa babban parlour, Da youseef ke jiran sa.
Youseef na zaune suna gaisawa da Ammii, shima koda ya shigo sallama suyi da Ammii ta bishi da addu'a har lokacin 'yan matan gidan na parlour. zaituna kam ita tashi ma tayi tabi bayan shi, aikuwa fennah ta hade rai jira kawai take taga dawowar zaituna.
Ammiii kai kawai ta girgiza ta tashi ta haura upstairs,
Koda ya fito tini motocin daza su fita an shiryasu, kasancewar sunji ogan nasu shirune ma su fito suna