Chapter 6 Reading RAYUWATA BOOK COMPELET BY BILLY PINKY.txt Arewa Novels

RAYUWATA BOOK COMPELET BY BILLY PINKY.txt

Author :  Billy Pinky Category :  Arewa Pen

Chapter   6 / 29

15K to 18K   out of 84.6K words

sani ba tafada tana ficewa da gudu tana dariya itama ta rufa mata baya dan ta gane nufin ta,
Haka sukai ta zagaye parlour nan kamar wasu yara,

"Wai 'kalan ku kuwa kunga Safiyyah da buhaisa Allah yashirya min ku mekuma ya faru?

"Wai ummi kaleta fa shopping yah saif zai Kai mu, wai shine hijjab zata sa kullum tana manne da hijjab shine nace tasa mayafi wai a'ah kuma fa ummi hijaban duk ba wankka ku bane bama guga.

"Takare sa maganar tana kallon safiyyah da ta tsaya tana hararar ta"

"Kinga safiyyah kisa mayafi kema kya huta da sa hijjab din nan.
Tom ummi! Yauwa ko kefa, jeki sawo mayafin kafin ya fito.
Gwalo buhaisa tamata kingani fa ummi gwalo take min,
Ke buhaisa kibar mata gwalo nace ma tasa Hijabin hajara ai,
Sorry ummi!
Tafada tana sake mata gwalo tai sama da gudu tana dariya.
Baya safiyyah ta rufa mata
Naga randa zaku Dena wannan abin kamar wasu yara cewar ummi tana murmushi.
(Like nida sis Waleeda 😅)

"Tsaf su fito gunin burgewa cikin doguwar riga ta material red,
Sai ma dai-dai cin mayafi da tayi rolling dashi tsaf ta fito kamar wata balarabiya,

"Haka su iso shop rite din shiga suyi yah saif ya dauki keken yana jah sukuma suna sawa, safiyyah dai rabin kayan data dauka turaruka ne sai kayan za'ki dan ita buhaisa tafi auki a gurin kayan kwalliya.

"Haka sugama da ganan su wuce gurin Shan ice cream da yawo,
Da ganan ya ajesu gida ya wuce gurin kallon ball.

*Washegari...*
Kasancewar jiya mun gaji bamu tashi da wuri dan tunda muyi salah mu koma.
Anty hajara da ummi ne suyi breakfast bayan sunga ma anty hajara tazo ta tashemu,
bathroom nashiga nayi wanka buhaisa ta shiga,
Tare mu fita muna dariya"

"A dinning area mu sa mesu muma can mu nufa"

"Muna gama wa mudawo parlour muna fira har Abba ya fita shida yah saif baki sunzo,
muje mukai musu drinks da snack's"

"Har Isha tazo aiko nayi murna na rungume ta su gaisa da ummi da anty hajara daga baya ma bathroom mu wuce.
Aikuwa musha shafta ta bamu labarin MD buhaisa dai bata so wai tana Taya yah saif kishi"

"Ansa ranar auren anty hajara nan da wata daya zamu sha biki tun ranar mu fara tsararen biki"

"Ina sallah yah saif ya kirani ni Isha ta dauka suka gaisa, ta bani lokacin na idar kasancewar anguwa za muje yau"


_______________

*Abuja🤍*

"Kowa part din su yanufa itakuma zaituna part din granny tayi.
Aa ke kuma daga ina da wannan tsinan nun kaya? "

"Kai tsohuwar nan daga gida mana"

"Amah zakiyya na ganin ki kifito haka?

_____

"Yah majeed na Shirin fita office suna sallama da Ammii.
saiga addah nan a'ah my son yaushe andawo ne ba azo an gaishemu ba?
Birkitatun idon shi ya dago yana kallon addah,
Sorry addah yanzu nake shirin shigowa.
Yafada kamar bai son magana,
Aa my son bakomai wallahi ai gajiya ce to yah hanya?
Alhamdulilah! munsame ku lpy?
Yafada yana shirin barin parlour"

"Wai dama bakaje ka gaishesu ba da kaje gaida granny?

"Uhm lokacin sallah ne yaye shiyasa,

"Yafada alamun ya gaji da maganar, murmushi kawai Addah tayi.............✍️




*Please🙏 comment and like 👍and share fissabilah👏👏👏*





*🌹 RAYUWATA 🌹*

*Story and written✍️*

*Bilkeesu .S. Aliyu*
_💞(Billy pinky)💞_

*🤝 Amanar nazari writer's association📚🖊️*

*[07070260240]*

_WhatsApp number or call_

_📚N.W.🖊️_

*Book 1 📖*

*Page 20&21*




"Yanzu zakaje ka gaishesu ne koh sai ka dawo?

"Saina dawo yanzu time ya kure"

"Allah yah tsaremin Kai ya dawo da kai lafiya Allah yabada sa'a"

"Ameen yah Allah cewar Addah, shima Ameen yace yana sunbatar goshin ta kana ya fice cikin nutsuwa, dolene inka kaleshi ka 'kara kallo .
Tunda ya fito compound din gidan tight security d'in dake zagaye da harabar wurin suka wani irin kamewa tare da sara mishi,
Had'i da gaishe shi"

"Hannu kawai yadaga musu tare dace wa kun tashi lpy?
Cikin harshen turanci.
Bai jira amasa warsu ba ya nufi"

"Gurin shegun manyan car's d'in dake jibge wuri guda su nufa shida security d'insa.
Zu'ke'kiyar ba'kar motar da juseph ya fiddo,
Wanda ko makaho ya shafa yasan eh lallai kudi yayi aiki wurin siyenta. Dan sai wani irin kyalli da sheke take mai daukar ido.
Gatan dai bata cika hayaniya ba kuma Bata mamaye waje ba. Tsaf take kala da yanayin matasan zamani irinsa dake gara kan nera bisa ga damar da ubangiji ya basu."

"juseph ne ya bude masa motar ya shiga sanan Yuoseef ya shiga suma sauran security d'in shiga nasu suyi su fita a jere susa motar da Aj yake a tsakiya juseph ke driving"

"Kai tsaye company su nufa"

"Ganin katon company dasu zo yasani furta masha Allah gaskiya company ya hadu ga girma, a saman company dauke yake da wani tambari Mai kamar tauraro irin tambarin dake jikin motocin shi"

"Har ciki su shiga guys d'insa su bude Mai motar,
Saida yadau tsawon lokaci kafin ya fito gaba daya ma aikantan sai girma mashi suke."

"office din danake kyautata zaton nashine, dan yafi ko ina tsaruwa, kuma security's ne aciki da wajen shi. ya shiga youseef beye dashi"




✨🤍✨

Uhm dan Allah meye ai bin wanan shigar granny? bama wannan ba ace yah majeed ya dawo amah baki gayama mummy ba?

"To ban fada ba kinga daga ke har uwar taki inbaku rabu dani da zancen Abdulmajeedu ba wallahi zan saba muku.
Kedashi kwata-kwata baku dace da juna"

"Kamar zaituna zatai kuka tace granny kina nufin nida yah Aj bamu daceba?"

"To banda abinki inake ina Abdulmajeedu?
jikifa yara ba tarbiyya, jifa shigar dake jikin ki da sunan wayewa, shiyasa yaran 'kauye sufiku hankali wallahi.
Takare maganar tana cigaba da damun furar ta,"

"Zaituna nashirin sake magana, granny ta zuba mata wani kallo, wuce ki bani guri kin wani tsayamin aka"

"Harara itama tazuba ma granny tana wuce bedroom din ta,"

"Kwafa granny tayi tacigaba da abin da take tana mita"

"Tana shiga ta danna ma mummy kira wayar na fara ringing ta fashe da kuka.
Aikuwa mummy na dauka taci karo da kukan zaituna, nanfa hankalin ta ya tashi an ta'bamata shalele.
Kinga ya isa haka fadamin meya faru?
Nanfa ta shirya karya da gaskiya tafada mata, kuma granny ma wai nida yah Aj bamu daceba takai karshen maganar tana sake fashewa da kuka"

"Kinga ki kwantar da hankalin ki, wallahi indai ina numfashi a doron kasar nan bamai auren majeed sai ke,
Inko kiga baki aure Shiba to saidai bana numfashi wallahi.
Bari Yaya ya dawo"


"Yauwa mummy na shiyasa nake kara sonki wallahi sosai Allah ya barmin ke"




____🤍💗
"B'angaren Ammii kuwa bayan Aj ya fita ne take karaba addah hakuri.
A'ah aminiya bakomai Nima jiya basma take sanar min ya dawo, kuma yau ina Shirin zuwa saiga fennah tashigo raibace, nake tambayar basma wai fada suke da zaituna.
Yaushe zaituna nan tazo gidan nema?

"Saida Ammii taja numfashi kana ta bude baki tamkar Bata son maganar tace.
Okay nima fitowa ta kenan natar suna yi maybe yau tazo,
Fitowar majeed nema sudena.
Takai karshen maganar kamar bata so"

"Ai kinsan yaranan sai addu'a wallahi Allah dai yashirya Mana"

"Ameen yah Allah"

"Daganan su cigaba da firar su irin ta aminai"



_____________

*Kaduna✨*

Tsaf su shirya cikin bakar abaya wacce ama kolliya da farin duwatsu sai takalmi Mai dan tudu. Safiyyah datai rolling din gale saita fito kamar balarabiya"

"Sallama suyima ummi anty hajara na musu tsiya aikuma yawo salamu alaikum jiya an fita yauma haka. Dariya suyi su fice suna mata gwalo.
Eyye zaku dawo kusa menine har ke ishan. tafada tana daga murya dan su jiyo ta da kyau"

"A motar Isha mutafi. Kai tsaye gidan anty zainab muje antyn Isha. aikuwa taji dadi sosai anan muka dade dan sai gabda magrib mukoma gida. Isha tayi-tayi Dani naje na gaida momy nace mata insha Allah gobe kan natafi zan zo. Badin taso ba ta ajemu bakin get ita kuma ta karasa gida kasancewar anguwar su daya"

"Koda mushiga ba kowa a parlour cikin sanda mu wuce sama Dan kar ummi taji mu tace yanzu mu dawo. Gab da zamu shiga daki saiga anty hajara nan. murmushi tayi tana fadin ummi!
aida gudu mushige muna dariya.
Itama murmushi tayi ta koma daki"

"Saida muyi sallar isha'i sanan mu fito parlour lokacin ma dady ya dawo amah Banda yah saif. Muna cikin dinner ya dawo, shima nandin ya nufo. nice farkon tashi aikuwa ina zama yah Ansar ya kirani, munsha waya har nake sanar mai gobe zan koma gida, da kuma sa ranar anty hajara. yace ai ummi ta fada mishi,
Har su gaisa da buhaisa da ganan muyi sallama.

Yau bamu wani dade muna fira ba kowa ya tafi daki, koda mu shiga ma bamiyi wata fira ba nida buhaisa kasancewar mungaji ko bacci yake ji,

*Washegari....*
A hankali take bude idanun ta tasauke shi akan agogon dake ma'kale a bangon dakin bakin ta dauke da addu'a tashi daga bacci
A round 8:30 ai da sauri ta duro a gadon Kai tsaye bathroom ta shiga bata wani dade ba ta fito da alamun wanka tayi duban ta takai kan bed din amah ba buhaisa alamun ya riga ta tashi.
Wanka tayi lotion kawai ta shafa ta saka doguwar riga mai dan santsi da hula kana ta fito parlour.

"Bayan sun gama breakfast, su tafi gidan su Isha, ai kuwa taji dadi sosai taja su suje su gaida momyn ta daganan su shige ciki fira su sha kamar baza su hadu gobe ba.
Buhaisa ce dai yau haushi takeji safiyyah. zata tafi gida, saida suyi sallar ashar sanan su koma gida.

"Kasancewar yah saif ne zaikaita"

Tsaf tashirya cikin atamfa riga da siket Wanda d'inkin ya zauna daram ajikin ta kamar dan ita ayi, kasancewar tafi buhaisa kiba, shiyasa kayan su kamata sosai, gogaggen Hijabin ta tasaka hadi eyeglasses, facemask dinta kuma ta mayar jaka ta fito.

Aikuwa buhaisa ta cika tai fam kamar zata fashe da kuka anty hajara ta tasata a gaba tana tono ta.
Saidai da tasata kuka, daga baya su koma lallashin yar auta.

Koda safiyyah ta fito itama lalashin tayi, ki kwantar da hankalin ki, bikin anty hajara fa yazo Kinga tun ana saura sati biyu zanzo to kinga ai na kusa dawowa.

Badi taso ba yah saif yace kinga tashi mu tafi kar yamma ta cikayi.
Sallama suyi da ummi da anty hajara kana su tafi.

Har kofar gida ya kaita shirin fitowa take taji ya rikemata hannun ta waigowa tayi tana Mai zuba mai hararar da ita kanta bata san ta Mai ba,

"Hannun ya saki yana dan wayan cewa, tafiya zaki ba sallama?
Ko kinyi kewarsu ne?
Ya jera mata tambayar ajere.

"Kai kawai ta daga mishi tare da cewa kadan.

"Kiyi kewar tasu?

"Uhm

"Tom shikenan sai yaushe kuma?

"Yatsun hannun ta tadaga mai guda biyu tare da cewa week.

"Two weeks?
ya fada yana kallon safiyyah.

"Uhm

"Yar kurma kenan wato na isheki koh Tom shikenan sai munyi waya.

"Baki tadan turo jin ya kirata da yar kurma,
Amah batace komai ba saida ta fita hannun ta rike da murfin motar kana tace.

"Thank you yah saif Saida safe, ka gaidamin da sisy nah please.
Ta hada hannu wan ta alamun roko.

"Baki ya saki yana kallon ta, saida ta rufe murfin motar, kana ya dago da sauri har takai bakin get.
Saida yaga shigarta ya sauke ajiyar zuciya kana ya tada motar ya tafi.

"Saida motar shi ta tafi ta dago daga leken da take tana sauke ajiyar zuciya, ga baki daya tsoran shiga take amah haka ta dake tai sallama a kofar parlour.

"Gabaki dayan su suna zaune a parlour daga mom har anty Waleeda da yah safwan dashi ba zaman gidan yake ba sai baby.

"Aikuwa da gudu baby tazo ta rungume ni nima rungume ta nayi muna kara sawa cikin parlour.
Tunda nayi sallama su

6 / 29