Author : Billy Pinky Category : Arewa Pen
maganar tace.
Okay nima fitowa ta kenan natar suna yi maybe yau tazo,
Fitowar majeed nema sudena.
Takai karshen maganar kamar bata so"
"Ai kinsan yaranan sai addu'a wallahi Allah dai yashirya Mana"
"Ameen yah Allah"
"Daganan su cigaba da firar su irin ta aminai"
_____________
*Kaduna✨*
Tsaf su shirya cikin bakar abaya wacce ama kolliya da farin duwatsu sai takalmi Mai dan tudu. Safiyyah datai rolling din gale saita fito kamar balarabiya"
"Sallama suyima ummi anty hajara na musu tsiya aikuma yawo salamu alaikum jiya an fita yauma haka. Dariya suyi su fice suna mata gwalo.
Eyye zaku dawo kusa menine har ke ishan. tafada tana daga murya dan su jiyo ta da kyau"
"A motar Isha mutafi. Kai tsaye gidan anty zainab muje antyn Isha. aikuwa taji dadi sosai anan muka dade dan sai gabda magrib mukoma gida. Isha tayi-tayi Dani naje na gaida momy nace mata insha Allah gobe kan natafi zan zo. Badin taso ba ta ajemu bakin get ita kuma ta karasa gida kasancewar anguwar su daya"
"Koda mushiga ba kowa a parlour cikin sanda mu wuce sama Dan kar ummi taji mu tace yanzu mu dawo. Gab da zamu shiga daki saiga anty hajara nan. murmushi tayi tana fadin ummi!
aida gudu mushige muna dariya.
Itama murmushi tayi ta koma daki"
"Saida muyi sallar isha'i sanan mu fito parlour lokacin ma dady ya dawo amah Banda yah saif. Muna cikin dinner ya dawo, shima nandin ya nufo. nice farkon tashi aikuwa ina zama yah Ansar ya kirani, munsha waya har nake sanar mai gobe zan koma gida, da kuma sa ranar anty hajara. yace ai ummi ta fada mishi,
Har su gaisa da buhaisa da ganan muyi sallama.
Yau bamu wani dade muna fira ba kowa ya tafi daki, koda mu shiga ma bamiyi wata fira ba nida buhaisa kasancewar mungaji ko bacci yake ji,
*Washegari....*
A hankali take bude idanun ta tasauke shi akan agogon dake ma'kale a bangon dakin bakin ta dauke da addu'a tashi daga bacci
A round 8:30 ai da sauri ta duro a gadon Kai tsaye bathroom ta shiga bata wani dade ba ta fito da alamun wanka tayi duban ta takai kan bed din amah ba buhaisa alamun ya riga ta tashi.
Wanka tayi lotion kawai ta shafa ta saka doguwar riga mai dan santsi da hula kana ta fito parlour.
"Bayan sun gama breakfast, su tafi gidan su Isha, ai kuwa taji dadi sosai taja su suje su gaida momyn ta daganan su shige ciki fira su sha kamar baza su hadu gobe ba.
Buhaisa ce dai yau haushi takeji safiyyah. zata tafi gida, saida suyi sallar ashar sanan su koma gida.
"Kasancewar yah saif ne zaikaita"
Tsaf tashirya cikin atamfa riga da siket Wanda d'inkin ya zauna daram ajikin ta kamar dan ita ayi, kasancewar tafi buhaisa kiba, shiyasa kayan su kamata sosai, gogaggen Hijabin ta tasaka hadi eyeglasses, facemask dinta kuma ta mayar jaka ta fito.
Aikuwa buhaisa ta cika tai fam kamar zata fashe da kuka anty hajara ta tasata a gaba tana tono ta.
Saidai da tasata kuka, daga baya su koma lallashin yar auta.
Koda safiyyah ta fito itama lalashin tayi, ki kwantar da hankalin ki, bikin anty hajara fa yazo Kinga tun ana saura sati biyu zanzo to kinga ai na kusa dawowa.
Badi taso ba yah saif yace kinga tashi mu tafi kar yamma ta cikayi.
Sallama suyi da ummi da anty hajara kana su tafi.
Har kofar gida ya kaita shirin fitowa take taji ya rikemata hannun ta waigowa tayi tana Mai zuba mai hararar da ita kanta bata san ta Mai ba,
"Hannun ya saki yana dan wayan cewa, tafiya zaki ba sallama?
Ko kinyi kewarsu ne?
Ya jera mata tambayar ajere.
"Kai kawai ta daga mishi tare da cewa kadan.
"Kiyi kewar tasu?
"Uhm
"Tom shikenan sai yaushe kuma?
"Yatsun hannun ta tadaga mai guda biyu tare da cewa week.
"Two weeks?
ya fada yana kallon safiyyah.
"Uhm
"Yar kurma kenan wato na isheki koh Tom shikenan sai munyi waya.
"Baki tadan turo jin ya kirata da yar kurma,
Amah batace komai ba saida ta fita hannun ta rike da murfin motar kana tace.
"Thank you yah saif Saida safe, ka gaidamin da sisy nah please.
Ta hada hannu wan ta alamun roko.
"Baki ya saki yana kallon ta, saida ta rufe murfin motar, kana ya dago da sauri har takai bakin get.
Saida yaga shigarta ya sauke ajiyar zuciya kana ya tada motar ya tafi.
"Saida motar shi ta tafi ta dago daga leken da take tana sauke ajiyar zuciya, ga baki daya tsoran shiga take amah haka ta dake tai sallama a kofar parlour.
"Gabaki dayan su suna zaune a parlour daga mom har anty Waleeda da yah safwan dashi ba zaman gidan yake ba sai baby.
"Aikuwa da gudu baby tazo ta rungume ni nima rungume ta nayi muna kara sawa cikin parlour.
Tunda nayi sallama su zuboma kofar ido harna karasa ina gaida mom,
"Abin mamaki saida na ta'bata ta d'ago firgigit.
Kuma ta amsamin harda tambaya ta yasu ummi,
Amsa wa nayi ina gaida yah safwan shima dai amasa wa yayi tare da cewa ina kishiga ne safiyyah?
"Naje gidan ummi ne .
"Oooh shiyasa abincin ma sai anga dama akeyi a gidan kenan?
Bance komai ba na tashi na nufi anty Waleeda na rungume ta, duk da tana tureni amah ban damu ba dan ba karya nayi kewar su.
Yadda nai tsam mani hakan ce ta kasance Dan parlour dai sai addu'a wallahi.
Ina mamakin san jiki irin na mom da anty Waleeda.
"Bedroom nashiga na barsu da mamakin dawo wata, dan itafa mom batai tsammani zan dawo ba.
To shima dai bedroom din sai addu'a dan yama fi parlour datti,
Jaka tana ajiye ina Mai leka bathroom wayo Allah, na furta ina mai fitowa da sauri.
Parlour na fito na wuce kitchen na dauko kayan shara, bedroom din na share tare da yin mopping.
Na koma bathroom shima share shi nayi abin takaici ga pad nan haka duk na hada na share kana na wanke bathroom din.
"Saida akira magrib na gama aikin, yah safwan nata min sannu da yake shi ba halin mom ya biyo ba.
"Around 4:00
Natashi, raka'a atul fijir nayi kana nai sallah asuba tare da azkhar, nafara karatun alQur'ani ban wani dau lokaci ina yiba natashi nafara gyaran gidan kafin karfe 7:00am nagama komai har girki,
Wanka nayi har na fito anty Waleedah bata tashiba bare tayi sallah tashinta na kumayi, me hali baya fasa halinsa dan yauma masifa ta hauni da ita kyaleta nayi na cigaba da kintsawa.
"Tsaf na shirya cikin less pink wanda amai ado da fararen duwatsu, dinkin riga da siket,
simple makeup nayi dan kuwa daga fouda, sai kwalli, da lips gloos, and maskara, da na taje eyelashes dina dashi aifa ya fito gadar-gadar Masha Allah, kalba na hade na daure da ribom,
Parlour na fita dan na karya bakowa a parlour sai yah safwan, gaisawa muyi tare mu karya dan shima zai fita gurin aiki,
Jeki dako mayafi na ajeki,
Tom yah safwan.
Gogagen milk hijjab nasaka da face mask da eyeglasses sai plate shoe shima pink waya ta nadauka nasaka a hand bag na fita,
Su anty Waleeda suna ta sharar bacci harna mu tafi
Muna zuwa ya bani 1k godiya na mai ina karasawa ciki.
Yauma Isha ta rigani zuwa ban dade da zuwa ba mu fita gabatar da program din ranar Thursday da ba muyiba.
"Bayan mun gama mukhtar yake cemin MD na kirana,
Kai tsaye office din nashi na nufa ina shiga,
PA dinshi da sai cin magani take ta min iso gurin shi,
ban damu da kallon da take minba na karasa da sallama.
"Tsaye na ganshi sai zagaye office din yake,
Nima tsayawar nayi ina furta,
good afternoon sir!
Nuna min gurin zama yayi shima yana kai zaune.
Jin ya kafeni da ido ya sani na dago daniyar magana dan nifa na tsani kallo, shikuma ya kware indai gurin kallo nane.
Yah jikin naki?
Ya jefomin tambayar da saida na dago na kalleshi.
Ai naji sauki! Nafada ina kasa da idona .
Masha Allah!
Dama dalilin da yasa na kiraki ina son magana dake ne,
Uhm inajinka na fada cike mamakin wacce magana zaiyi dani.
"Cikin bazata matukar bazata na d'ago ina kallon shi jin maganar da banta b'a tsammani daga gare shi ba.
"Wallahi safiyyah ina son ki ina burin ki zamo uwar y'a'yana tun randa na ganki naji ina sonki wallahi, tinanin ki ya hanani bacci, har gidan ku naje acemin Wai banan bane gidan, ko sawa nayi yau tayi please kar kicemin aa.
Ya karasa maganar kamar zaiyi kuka idon shi na tara kwalla.
Ni wallahi dariya ma yabani da tausayi gami da kunya.
"Na baki lokaci safiyyah kije kiyi tunani da kyau, Insha Allah duk abinda kika yanke zan amsa da hannu biyu, amah kimin adalci please.
Ya 'karasa maganar cike da magiya.
Kai kawai na gyada mishi na fice daga office din,
Kai tsaye office din mu na nufa, mu cigaba da abinda muke,
gabaki daya tunanin maganar nake. to ya akai ma yasan gidan mu, haka dai har atashi takardun dazan kaima ma cewa nayi Isha takai mu hadu a mota,
Koda ta tambayeni cewa nayi bakomai na wuce.
Da ta dawo take sake tambaya ta, meya faru naji MD yace intaya shi rarrashin ki?
Bakomai! Na fada irin banson wata tambayar,
Amah safiyyah baki da wata aminiya data wuce nida buhaisa, haka nima bani da wata aminiya sama dake, kinsan bana boye miki damuwa ta. amah some time kina boye min damur ki bana takura ki da dole saina ji, shikenan.
Ganin taji haushi kuma nima fa banyi adalciba, hannun ta na kama, kiyi hakuri kinji sis wallahi ba haka bane, nafad'a mata duk yadda muyi da shi.
"Uhmm safiyyah ta kira kinsan menene?
"Aa saikin fada isha"
"Wallahi ki amince ta ko ina MD ya can-can ci a soshi.
Don mutum ne nagar tacce wanda yasan ya kamata mai ilimi.
A taikaice wallahi koni MD yace yana so tuni zan amince ba kiga yadda PA ta mutu akanshi ba amah bata gaban shi.
Please kidai kara tunanin amah wallahi kun dace da MD sosai.
"Murmushi nayi tom sisy nah nagode sosai muje to"
"Itama murmushin tayi never mind sis nidai fatana ki amince wa bawan Allah nan,
Tafad'a tana tada motor,
Har kofar gida takawo ni kana ta wuce tana kara rokona murmushi kawai nayi na shiga bakina dauke da sallama.
Mom ce da anty Waleeda kawai a parlour, ko firar mai suke ina shigowa suyi shiru dan ko sallamar basu amsa ba,
To nasan hali tunda basu san mahimmanci taba.
Gabanta naje ina fadin good evening mom, murmushi kwance a fuskata.
Sanin ba amsawa zatai ba yasa na mike na wuce bedroom.
Tom dama yaudin fa gaskiya na gaji. kasancewar program biyu nayi ga kaina har juyawa yake.
Bathroom na shiga na wanke kana nayi wanka tare da dauro alwala,
Bed nafada ina sauke ajiyar zuciya ga yunwa na kwakular cikina, amah nasan ba abinda zan samu a gidan nan,
nikuma bazan iya girki ba dan kaina ciwo yake.
Ganin fa zan cutu yasa na tashi, mayafi na daura akan towel din na fito kai tsaye kitchen na nufa.
"Kamar yadda nai tsam mani hakan ce ta kasance dan kuwa bakomai hattana miyar basu rage ba,
Garin kwaki na jika da Madara na zuba gyada, na fito duk da kallo su bini anty Waleeda na dariya kasa-kasa har nashige"
________
*Abuja🤍*
Motocin shi ne su shigo gidan kai tsaye parking lot su nufa ajere su tsaya, kasancewar parking lot din akwai girma.
Da sauri Samuel ya Kara so ya bude mai motar.
yadau tsawon lokaci kafin ya fito gaba daya kamewa suyi har ya bargun youseef beye dashi,
Kai tsaye ta babban parlour yabi.
Aikuwa gaba daya 'yan matan gidan suna zaune,
wasu sunyi group din fira, wasu waya, wasu chat, wasu koma iya su biyu ne, wato zaituna da azima kenan dan yanzu ma riga da wando ne ajikin ta.
"Da sallam ciki-ciki ya shiga dan inba kallon bakin