Author : Billy Pinky Category : Arewa Pen
da ita kawai tana fada ne insha Allah namayi kusan dawowa verry soon ''.
'' Yaushe zaka dawo Yayana ? '' ta sake fada a wannan karon cikeda zumud'i dauke a fuskarta.
'' Ban san ranar ba amma insha Allah nan kusa ne ina fatan hakan ''
'' Tom Allah ya dawomin dakai lafiya yayanah ''. Da haka sukayi sallama tana ajiye wayar ta jiyo muruyar Mom na kwalla mata kira "Safiyya" . "Na'am Mom '' ta amsa tana mai fitowa dan ganin meke faruwa.
'' Wai meye nufinki bazakiyi girkin bane koh me ? ''
'' Anty Waleeda kaina ke ciwo yau bazan iya girkin ba ''.
Ta lailayo wata ashariya '' ke har kin isah kice ba zaki girka mana abinci ba dan ubanki, to wallahi baki isah ba ''. Tana gama tijarar nata ta fice daga dakin. Ae kuwa tana fita nasa ma kofar key na saka karatu.
Sama² na jiyo muriyar Mom tana sauke nata masifar dan har barci ya far daukana da alama yar lelen nata ce takai karana a gurinta '' Ina mara kunyar nan take bazaki bude kofar ba eyyye, lallai zaki sani karki fito ''. Tin inajin su har bracci ya kwasheni ban san yasu ka karkeba.......
____________
WACECE SAFIYYA ???
Sai mun hadu a page 4
Dan jin cikaken tarinhin Safiyya .
💗 RAYUWATA💗
Written and story by.
Bilkeesu S aliyu.
🌸 Mallakar💋
💕Billy pinky💞
✍️💖 AMANAR NAZARI WRITERS ASSOCIATION📚✍️
📚🖊️ NAZARI WRITERS ASSOCIATION📚🖊️
_Kyawawan Nazari kafin rubutu na damfare da bin'ka'idojin rubutu.
_Nazari kafin rubutu kan'kayata duniyar Adabin hausa.
🖊️🖊️ Alk'alami yafi takobi⚔️⚔️
Page••°°••4&5
"Safiyya A Ibrahim" shine asalin sunnanta .
Malam Ibrahim dan kasuwa ne, annan cikin kaduna yake da zama, matar shi ta farko "Amina" wacce ake Kira da ummah. yar "Niger" ce,
Tazo gurin yayarta N an cikin kaduna, su fara soyayya har yakaisu ga aure,
"Amina" (ummah) ,
Iri buzayen "Niger" ce kyakyawace ajin farko kon dai san ,
Buzayen Niger da kyau .
sun kai shekaraka uku basu sami haihuwa ba,
Danginshi suce lallai sai ya 'kara aure, shikuma bashi da niyar aure, yace Allah shi zai basu haihuwa,
Amah haka suyi ruwa suyi tsaki kafin ya amince zanyi, acikin Dangisu akwai wacce take son, shi wato "Zuwaira"
Ita abashi akasha biki,
Bayan biki baifi da wata biyu ba,
Sai ga "Zuwaira" da ciki, wacce ake Kira da mom, sunyi farin ciki sosai, to daganan Zuwaira wato (mom)
Wulakanci iri_iri takema ummah shi Wai juya, na yau da_ ban na gobe da_ban, duk wannan abin da ake malam Ibrahim wato(abba)
Bai saniba, kasancewar ummah akwai hakuri,
Ana cikin haka sai ga ummah da ciki, ranar missalta muku farin cikin, da "malam Ibrahim" ya shiga 'bata lokacine, da wasu daga cikin danginshi,
Ummah matayi farin cikin sosai dan tahuta da gorin da ake mata na haihuwa haka antyn ta ,
Iyayen ummah duk sun rasu, daga ita sai umma halima yayarta kenan, umma halima tana da yara uku da _Yaya saif,
_anty hajara,
_buhaisa,
Auta kenan itace sa'ar "Safiyya"
Haka suyita rainon cikin su, har Allah ya sauke su lafiya, mom tariga haihuwa, ta haifi yarta mace, ranar suna yarinya taci suna Waleeda,
Ansha suna lafiya,
Ummah dai nada tsohon ciki, bayan suna da wata daya lokacin ma tayi arba'in,
Ummah ta haifi d'a
Namiji, ranar suna yaro yaci suna "Ansar" shima dai ansha suna lafiya, masu farin ciki nayi, masu ba'kin ciki nayi,
Haka dai akai suna aka tashi, washe gari umma halima da yarta
Anty hajara sukai suyar hakika,
Suma dai suka tafi gida,
Saidai fatan Allah yah kai kowa gida lafiya
Ummah ta samu ciki, yafi so biyu amah mom tana zubar wa, kuma ba wanda yasan itake zubar wa, tunda
Bokanta ne ke bata maganin,
Wai ita haushi takeji ta haifi namiji ita kuma mace,
(bayan duk kyautace daga Allah, amah mutane suna mance hakan, duk Wanda Allah ya bashi 'ya'ya mata, ya bashi hallitta mai tausayi, hallitta mai jinkai, hallitta mai cike da hakuri, Allah yasa mudace, ameen🙏)
Haka taita ma ummah, sai daga baya sanda ta samu cikin Safiyya, ba wanda yasan tana dashi, sai abba da umma halima, har saida ciki yayi girma sanan,
Mom ta gani,
Aikuwa ta shiga tashin hankali, sosai
Ta garzaya gurin malaminta,
Yace mata ai yanzu ciki bazai zubeba yayi girma sosai,
Saidai kafin yarinyar tazo duniya su kashe ta tun tana aciki,
Yabata wani magani da zata na samata abinci.
Ko abin sha to dayake Allah ba azalimin bawansa bane, ummah batacin girkin ta saidai in ita tayi, da
Kanta ,
Har Allah ya sauke ta Lafiya, yarinya taci sunan maman abba wato,"Safiyya"
Ummah nakiran tada Mami ,
Duk da haka mom Bata hakura, ba abba yana matukar son safiyya, yana kuma ji da ita, kasan cewar sunan goggon shi taci.
Amah Saida mom ta shiga ta fita taraba su da mahaifinsu,
Dan ko gidan yadawo suna zuwa gurin shi zai korasu, yaran mom kuwa yana jidasu sosai .
Amah duk da haka matar nan, bata hakura ba sai da ta rabasu da farin cikin su,
Dan kuwa tashi sukai aka nemi ummah sama da kasa bata,
Gashi lokacin safiyya tana yarinya, dan bata
Wuce shekara 6year ba,
Ayi neman _anyi neman
Amah shiru, har Niger anje amah bata, dama umma halima da mijin tane akan koma,
Dan shi abba ma baidamu ba,
Kamar ma ya manta da ita a matsayin matarshi,
Haka akayi neman ummah akarasa,
Bata ba labarin ta, ummah halima tashiga tashin hankali sosa,i yar uwar ta guda daya tilo da tarage mata,
Itama tarasa ta, haka Yaya Ansar kamar hankalin shi zai gushe,
Ayita mishi magani, sannan asami kanshi,
Ko "safiyya" dake yarinya abin ya doketa ,
Amah mom ko ajikin ta da taga kamar za'a zargeta,
Shine tasa baki harda Dan kukan ta,
Ummah halima taso amsar "Safiyya" abba da yace yabata, amah mom tayi ruwa tai tsaki, saida abba ya amso ta,
Wahala iya wahala yarannan sun shata tun "Safiyya" tana shekara bakwai 7 aikin gidan gaba daya,
Ita keyin shi, tun tanayi tana kuka, harta saba, ya zame mata jiki, tun asuba take tashin ta da ruwan sanyi,
In Yaya "Ansar" na tayata, shima takawo masa nasa,koka d'an
Bata bari ya tayata aiki, makaranta ma,
Mijjin ummah halima ne,
Yasa su suda su buhaisa, da 'yar abba ya yadda, nan ma dan ance za'a had'ashi da hukuma ne shiyasa mom ta barshi, ya yadda,
Harzu kuwa jami'a ,ba Abin da za suce, masa sai Allah yasaka masa da alkairi,
Mahaifin da ya haifesu, ya kasa tallafar rayuwar su,
'ya'yan mom kuwa, sai makarantar dasu zaba,
Komai nasu da namu ya ban_ban ta hatta gurin kwana,
Tufafinsu, abincin su,abin shan su, komai nasu ya ban_banta
Daga baya ne ma, dasu koma sabon gida, kanwar mom ta bata shawar ta hadasu daki daya da Waleeda,
Kar mutane su zargi wani abun, shine yanzu suke daki daya,
Amah badin Waleeda taso ba,
Gidan ummah halima kuwa, saidai ta saci hanya, taje in ta dawo ta zane ta,
Amah yanzu ta waye, duk wanda ya daga mata yatsa, a gidan saita karya shi, mom kawai take ragawa, wataran,
Dan koba komai ta haifeta, sai abba tayi sati ma bata ganshi ba,
Ita yanzu mom yaranta uku .
_Anty waleedah,
_Yaya safwan,
_Sai baby,
Ita kuma ummah yaranta biyu.
_Yayah Ansar,
_Safiyyah,
Yanzu haka Yaya Ansar yana aiki ne a Abuja, ma aikacin banki ne,
"Safiyya"kuma tagama makaranta, mass communication takaran ta, kuma tasa mu aiki yanzu haka, wani program suke gabatarwa, fannin islamiya kuwa tayi saukar hadda,
Shikuma Yaya safwan, yana aiki anan cikin kaduna, itakuma anty Waleeda har yanzu aiki take nema, amah bata samu ba,
Dan ita gaba daya halin mom ta dauko
Wannan kenan✍️
Sai mun hadd'u a page 6 danjin yadda zata kaya😅
🌹RAYUWATA🌹
Story and written✍️
©️ Bilkeesu .S. Aliyu
💞(Billy pinky)💞
07070260240
WhatsApp number or call
📚🖊️ NAZARI WRITERS ASSOCIATION📚🖊️
Book 1
EPISODE 🌷 {6&7} 🌷
Edited
Cigaban labari....
Washegari. Karfe hudu na asubah, 4:00am ta tashi ta fara gyaran gidan, kasancewar yau Monday, zata gurin aiki, Kiran sallah farko tagama aikin ta, bedroom tanufa,
Kasan cewar anty Waleeda yau ba adakin ta kwana ba,
Saboda jiya ta rife kofar,
Bathroom tashiga tafara wanka tare da dauro alwala,
sanda ta fito ma anshiga sallah dan haka, agurguje ta saka riga, tafara sallah, koda ta idar azkhar tayi, karatun alQur'ani tafara, cikin zazzakar muryarta, cikin natsuwa,
Kowanne harafi tana bashi hakkinshi,
Bayan ta idar ta tashi ta soya musu miya, kamar dai jiya,kana tayi breakfast, har lokacin ba wanda yafito, bedroom Takoma p
L a gurguje, body spray ta fesa da humra ,
Tsaf tashirya cikin abaya baka mai sulbi
Wadda aka mata ado da jajayen dutsina masu sheki,
Ta nannade tulin gashinta, tayi acuci da shi, simple Make up tayi, ta daura agogo na fata baki sai plate shoe mai jane da bakaken igiyoyi, sannan ta dauko gogaggen Hijabin ta milk colour,
Tasaka tare da face mark, da eyeglasses, Masha Allah,
"Safiyya" tako ina Allah ya mata zubi da tsari, Wanda yasanya take burge mutane ba maza kawai ba hatta ga 'yan uwanta mata ma, sai dai gonar miskilanci ce, sam magana bata da metaba, muryarta sanye take dawani irin sirri, wanda idan tai magana take dauke hankalin mai saurare,
Cikin sand'a tafita a bedroom din tana leqa cikin parlour, bakowa dan haka cikin sand'a ta fice a gidan, nappep ta tare tare da fada mishi inda zai kaita, bayan yak kaita ta bashi kudin shi, ta wuce ciki , office dinsu ta nufa kai tsaye "Aisha"
Tasamu a office din oyoyo "Aisha tafada tare da rungume ta, yaudai nariga ki zuwa
Umm Wai duk saurin Nan danayi saida ki rigani zuwa? amah insha Allah gobe saina rigaki, mukullah Mr hijjab cewar "Aisha"tana miko ma
"Safiyya" hannu sasanyan murmushin ta tayi itama tana mai miqa mata nata hannun, atare suka saki dariya,
Ni kiga bani guri in zauna duk kin isheni da surutun ki, au sis haka zakicema ,
Murmushi kawai tayi tana zama agaban computer,
Wai nikam "isha" ina aikimu na wacan satin ne?
Kin manta ba yana gun "MD" ba oohh my God, wallahi na manta.
Amah kinga bari inje in amso dan aikwai abin da ban gama,
Tafada tana mikewa har takai kofa ta dawo
Face mark dinta ta saka da eyeglasses dinta kana ta fice,
Itadai "Isha" kai kawai ta gir_girza ta cigaba da abin da take.
Cinkin takunta na nutsuwa da yanga da mutane da yawa suke fassarawa ta fito,
Duk wanda ta gamu dashi takan daga masa hannu da fadin,
Good morning wasu sukan tsokaneta,
Iyakarta murmushi kawai dan in baka zauna da itaba ba zaka tabba tunanin tana da surutu ba Sam.
Batacika yawan magana ako inaba saidai in ita taga damar hakan, shiyasa dayawan mutane kan daukarta shiru_shiru har wasu kan daganata da hakan a iya yardarsu.
Basu saniba in aka tabota batada ragi Sam.
Koda takarasa office din "MD" PA ce tace ta shiga! da sallama ta shiga office din, yana zaune, idon shi arufe amah yanajin sallamarta ya bude idonshi tare da yin murmushi, harkin karaso?
Umm barka da safiya sir, tafada ba tare da ta amsa masa Question din shiba,
Fatan kintashi lafiya?
Lafiya lau! ta amsa mai tana mai kai zaune a kujera,
Ina fatan dai lafiya? Nazo amsar aikin Dana kawo maka ne wacan satin!
Okay,
Dubawa yashiga yi, Daukowa yayi ya bata ta amsa tafice a office din,
Da kallo yabita harta fice kana ya maida idanunshi yah lumshe,
Itako tana fita ta ballama office din harara tare da jan tsaki, mutum sai kallon tsiya,
Kai tsaye office ta nufa bata tadda "Isha" Aciki ba dan haka tafara aikin ta,
Har "Isha" tadawo sunayi suna hira,
Ahankali sauran members din office din suma suka shigo,
Kasancewar su biyar ne acikin office din,
Aka gaggaisa,
Kowa yakama aikin gaban sa,
Bayan takammala tanufi office din MD
Knocking saida takai minti daya sanan ya bata izinin shiga ciki,
Kallo daya tai masa tadauke kai,
Kasancewar shidin me shegen san kalan mutane kamar zai cinyesu.
Cikin san kawar da kallon dayake mata yace zauna . Zama tai adda _dadare tare da fadin good afternoon sir. Atakaice yace how are you? baijira amsarta ba yace kin gama?
Yeas sir, nagama tafada tana mai mikashi takardun ,
Amsa yayi ita kuma ta Mike tafita, office takoma ta karasa abin da yarage musu sanan,
Su wuce itada "Isha a motar ta, har kofar gida "Isha takaita sanan sukai sallama.
Da sallama tashiga gidan cikin zazzakar muryarta,
amah bakowa atsakar kidan,
A parlour na iske dukka mutanen gidan amah ba yaya "Safwan da abba.
Sai anty Waleeda da baby sai mom.
Mom ce tawa tsomin wata muguwar harara, dayasa ni tacin face mask din na turo mata baki
Mom good evening
Koku good uwarki,dariya anty Waleeda tasa min itako baby tana ta home work dinta kamar ma batasan me akeyiba,
Tsawa ta dakamin kan nazo a hankali na nufi gabanta ina kaiwa kasa, ban ma gama kaiwa qasaba ta shinfidamin wani lafiyayen mari daya gigitani dan har eyeglasses dina Saida ya fadi. Rumtse idanuna nayi hawayen daya cikasu nai kokarin mayarwa Dan bana so nabasu damar zubowa. "K Dan uban uwarki harni zan saki aiki kitafi sabgar gaban ki ki barminshi?"
Karo na farko na dago na kalleta, ina Mai kokarin danne kukan dake kokarin zubo min, wallahi mom ban tafiba saida nagama komai.
Miyar daki bari akan wuta uwarki ce tai fatalwa tazo ta karasmin. Rumtse idanuna nayi ina Mai jin wani takaici ba Abin dana tsana irin inji mom na zagin ummah bana iya daurewa sai na maiyar mata. dan haka yanzu ma cikin kaushi murya nace.
Mom kunsha tabarraki kenan dan kisan komai yafito daga hannun ummah ta mai albarka ne. bare kuma kince fatalwa ai albarka ma saitafi.
Bari inje in sallah inkara rokon Allah in zata dawo gobe har abinci ta kika mana ba iya miyaba ma.
Ba mom kawai ba hatta anty Waleeda ma sakadde suyi suna kallo na. niko ko a kolar rigata na Mike tsam ina Mai nufa bedroom din mu
Wannan kenan✍️
https://chat.whatsapp.com/CiFQHB3CNkRJ8gmX6banlC
*🌹RAYUWATA*🌹
*Story and written*✍️
*©️Bilkeesu .S. Aliyu*
_💞 (Billy pinky)_💞
*🤝🥰Amanar nazari writer's association*📚
[07070260240]
*WhatsApp number or call*📱
*📚🖊️ NAZARI WRITERS ASSOCIATION*📚🖊️
Book 1📖
*EPISODE*🌷8️⃣▶️9️⃣🌷
Inashiga daki kukan Dan banyi agaban suba ya kufcemin. banyi zaman yi saba cire kayana nashiga bathroom, domin in wanka sai da na wanke bathroom din sanan nayi, alwala nayi nafito nasa ka doguwar rika mara nauyi pink coluor mai gajeren hannu,
Sallaya na shinfida nafara sallah bayan na kamalah azkhar nayi tare da karatun alQur'ani da dazu banyi dayawa,
Saida a Kira isha'i na gabatar da ita, kana na idda karatun alQur'ani danake, nadade ina addu'a kafin na mike nacire hijjab din na maida cikin wardrobe,
Dan kwalin rigar na yafa na fito parlour,
suna zaune sai kallo suke abin su ana shewa kamar ba 'ya da uwaba, da'alama ko sallah ba wacce ta tashi tayi,
Dan nalura mom sai taga dama take sallah ,tom itama anty Waleeda haka take,
Ba wanda na kula na wuce kitchen dan daukar abinci na, amah wayam da alama yauma ba abinci na, gashi dare yayi dan wajan karfe Tara tama wuce, fitowa nayi duk da irin yunwa da nake ji amah na hakura da abincin, da harara duk suka bini har na shiga bedroom din, gado na fada hawaye na zubomin, inda ace ummah na gidan nan bazata barni naje gurin aiki na dawo na kwanta banci abinci ba, yah Allah duk inda ummah take Allah katsaremin ita Allah yah sa tana cikin farin ciki da kwanciyar hankali ameen yah Allah.
Duniyar tunani nafada na kara jin sautin yasa nasan Yaya Ansar ne, cikin zumudi na dauka barka da dare yayanah,
Yauwa little sis yakike? lafiya lau yayanah! kaifa? lafiya!
Maiyasa mekine naji muryarki wata kalane uhm?
Yaya ba komai kawai dai natuna da ummah ne nafada hawaye na zubomin. Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi, kana yace kiyi hakuri. muciga ba da mata addu'a ahalin yanzu ita take so agaremu, kuma insha Allah tana cikin koshin lafiya kinji.
Tom yayanah Allah yah sa. ameen yah Allah Little sis,
Tom ya gurin aiki komai yana tafiya daidai ko?
Wallahi Yaya komai lafiya ! ya naka kuma? Alhamdulilah.masha Allah haka akeso ai.
Okay da kudi agurin ki yanzu? eh Yaya! akwai,
Tom zasa miki wasu saboda gurin hawa nappep, ko cin abinci,
Duk da nasan ko Babu bafa da min zakiba,
Kai yaya Allah akwai,
Amah nagode Allah yasaka da mafificin alkairi yayanah,
Ameen little sis.
Kije ki kwanta dan kisan gobe da wuri zaki tashi ko.
Tom yayanah sai da safe, Allah yah tashemu lafiya,
ameen yah Allah.
Bathroom na shiga na dauro alwala, nai nafila raka'a biyu sanan nai addu'a na kwanta.
_______~~
Washegari......
Kamar dai kullum yau ma hakance ta kasan ce karfe hudu 4:00am
Na tashi nai duk wani aiki danake bayan nagama tsaftace gidan, na daura mana breakfast, kiran sallah farko na kamalla duk wani abin da zanyi, Dan har wanka nayi yau nai alqawarin wallahi ba zanyi musu miyar ba, saidai inna dawo su tsireni, ai saima mutum ya gaji da cin abicin miya,
Dan haka alwala na dauro , ina niyar tada sallah natuna anty Waleeda adakin ta kwana, karasawa bakin gado na yi ina tashin ta amah ko motsi, koma tana jinane oho danaji ana niyar tada sallah nima nafara raka'atanul fajir, san nai sallah bayan na idar nai azkhar kana nasake tashin anty Waleeda amah ta'ki tashi daga baya ma sai cewa tai na ishe ta, kyaleta nayi, nafara karatun alQur'ani ban wani dau lokaci mai nisa ba natashi nafara shirin fita aiki.
Cikin atamfa orange da ruwan ganye, dinkin riga da siket ne da fatan din atamfar ai kwalliyar rigar, sai shuwaris da akasa ka.
Simple Make up nayi danko iyakar fauda, sai kwalli, da lips gloos, da maskara, da na taje eyelashes dina dashi, aifa ya fito gadar_gadar masha Allah, dan kwali ta daura saida yadan zame kasancewar gashin daya kwanta luf_luf a goshin ta.
Parlour ta fita tai breakfast, har lokacin mutane gidan basu tashi ba, suna can suna baccin asara.
Gogagen farin hijjab nasaka da face mask da eyeglasses sai plate shoe shima orange, ina shirin wayana na dauka ina Shirin fita sai ga kiran Yaya Ansar murmushi kwance a fuskata na dauka. ina kwan yayanah?
Antashi lafiya? lafiya lau, har an shirya kenan? eh yanzu ma tafiya zanyi dan har nasaka hijjab.
Okay natura miki kudin, saiki ciri ki aje saboda kudin transport
Tom yayanah Allah yah saka da alqairi,
Ameen, ki tafi karki makara,