Chapter 21 Reading RAYUWATA BOOK COMPELET BY BILLY PINKY.txt Arewa Novels

RAYUWATA BOOK COMPELET BY BILLY PINKY.txt

Author :  Billy Pinky Category :  Arewa Pen

Chapter   21 / 29

60K to 63K   out of 84.6K words

dan a silent take, murmushi nayi ganin Suraj ke kiran dan kwata-kwata ba muyi waya dashi ba. Hannu nakai da niyar ɗaukar wayar Buhaisa ta ɗauka tare da cewa.

"Ango Ango kasha kanshi".
murmush yayi mai sauti kana yace.

"Na'am bestyn mu ya ranki".

"Fari tasss".

Cewar Buhaisa tana dariya, shima dariyar yayi kana su gaisa cikin barkonci dan dama haka sukeyi da ita sannan yace.
"Ina ginbiyar tawa ne?".

"Ga tanan tayi wani iri kamar wanda in akai maka ita ta tafi kenan dan kwana biyun nan haka take har yar rama tayi, yanzu ma lallaba maka ita nake dan jiya ma take cemin gaskiya na sami Ummi na faɗa mata itafa ta fasa aur.....".
Wayar dana fisge ce a hannun ta tare da zuba mata harara ya hanata karasa maganar da take sonyi tare da kyalkyalewa da dariya tana ficewa a dakin.
Nima murmushin nayi tare da kai wayar kunne na. Murya kamar zaiyi kuka yace.
"Babe da gaske wai?"

"Uhm uhm fah".

"To yayane?"
Ya sake faɗa cikin sanyin murya, nima cikin shagoɓɓa nace.
"Sharrin bestie nefa kawai".

Ajiyar zuciya ya sauke mai karfi tare da faɗin "Alhamdulilah" ni saima yaso bani dariya wato shi harya yadda da zancen Buhaisa, Katsemin tunani yayi wajen cewa.

"Babe kinsan meye".

"Uhm uhm"

"I swear I love you Soo much please don't leave me alone babe".

Saida gabana ya faɗi jin yadda yayi maganar tamkar zaiyi kuka ni saima ya bani tausayi, nima cikin sanyin murya nace.

"Insha Allah muna tare FARSI"

"Allah yasa sai nakejin kamar....."

"Kamar me".

Na faɗa cike da shagoɓɓa idona cike da kwalla. Dariya yayi tare da cewa "ba komai babe" Nima jin haka sai nai murmushi. Shiru muyi na wani ɗan lokaci kowa na sauraren bugun zuciyar ɗan uwan sa can naji yace.

"Bebeee"

"Uhm"

"Kinyi dinner"

"Uhm"

"Yauwa tom yanzun ki tashi ku dan yi hira da bestyn mu dan bana son kiyi baccin yamma kinga magrib ta kusa nikuma zan shiga gurin momy ne".

"Tom kagaida min da ita"

"Zataji insha Allah"

Da haka mukai sallama ina shirin fita parlour saiga Luba nan hannun ta ɗauke da wani ɗan mug inda ta mika min tare da cewa.
"Oya maza shanye ki bani kofin".
Yadda kisan zanyi kuka anty Billy haka na kafa kai inasha cikin two minutes na shanye dan abun cikin mai daɗi ne. Kana na bata ita kuma tayi murmushi ta fice inda na rufa mata baya......





____________

*Abuja 🤍*

*A A SARAKI HOUSE*



............. Monday tushen aiki kasan cewar Monday ranar aiki ne . Gaba ɗaya family zaune suke a dinning area dake babban parlour cikin shirin aiki mazan su da matan su suna breakfast inka cire Yah Majeed sai kuma granny da sam bata yadda da zaman dinning ba a cewar ta tafison taji ta Mike kafa. Amma daga kan Uncle Sulaiman, Uncle Abdallah, Dady, Ammei, Addah, Mommy, Mama, sai anty Amarya, sai kuma Yan matan gidan da ko wacce hankalin ta yake akan bama cikin ta abinci wasu kuma anayi ana latsa waya. duk da doka ce kana cin abinci kana latsa waya to amma ba wanda yasa dokar a gun Dan da alama ma bai fito ba.
Tsit ka ke jin gun ya dau shiru sai karar spoon dake tashi dan wasu da yawa a cikin su sun kusa gama cin abincin.

Tun kafin su ganshi mayataccen ƙamshinsa daya gama manne jikinsa da komai nasa ya iso hancinansu. Gaba ɗaya sun zuba ma hanyar da suke kyautata zaton ta nan mamallakin kamshin zai fito.
A hankali ko yake sakko wa daga upstairs din cikin nutsuwa gami da nagarta. Yayi matuƙar ƙyau cikin Maroon suit sai long sleeve shirt fara tas. sai da zuciyar Zaituna da finnat ta ɗan motsa da wasu daga ciki.
Kai tsaye Ammei ya nufa da itama ta zuba mishi ido fuskar ta ɗauke da murmushi.
       “hannun ta ya sumbata yana mai ɗan bata side hug. Sai kuma murya ƙasa-ƙasa ya furta, “Good morning my everything”.
      Murmushi Ammei ta sake masa, tana mai amsawa da, “Ka tashi lafiya ?”.
        “Alhamdullahi Ammei nah”.
 
  “Masha ALLAH”.
Zaune yakai kan ɗaya daga cikin kujerun dinning din kusa da uncle Abdallah. Ya fara gaida iyayen nasa cikin natsuwa gami da girmama wa, suma su amsa masa cike da kulawa. Kana ya koma kan matan suma ko wacce fuska ɗauke da murmushi su amsa mishi. Haka kannin nashi shima su gaidashi cike da girmama, yayin da hannu kawai ya daga musu kana cikin coll vioce ɗin shi yace "kun tashi lafiya" daga haka bai sake cewa komai ba, suma bayan sun amsa basu sake magana ba dan sun san iyakar amsawar kenan. Mama ce ta dube shi cike da kulawa tace.
"My son har yanzu shiru kak'i fito mana da matar aure kuma gaskiya ni jika nake so".
Dariya su sanya gaba ɗaya inka cire shi Majeed ɗin daya kara haɗe tashi fuskar, da kuma wasu daga cikin su da dariyar ba takai zuciya ba.
"Faɗa mishi dai Mama ni kaina nagaji da zuba ido kamar ma tsoron matan yake".
Cewar Anty Amarya. Yayin da cikin taɓe baki Mummy tace.
"In tsoran matan yakeji basai a zaɓa mishi a cikin dangi ba".

"Aaa ku dena takuramin ɗa haba dan Allah kamar ba iyaye ba". Cewar Addah Kana ta waigo tana kallon Majeed cike da kulawa tace. "My son please mu basu kunya kafin sabon wata ya shiga dan naga sa idon ya fara yawa".

Murmushi yayi irin na gefen baƙin nan tare da gyaɗa mata kanshi dake dan masa ciwo sama-sama kasan cewar zaman su guri ɗaya da dady tare da furta. "insha Allah" asaman labban kana ya tashi ya koma can cikin parlourn inda kai tsaye rukunin kujeru Black and White ya nufa tare da ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya.

Duka da kallo suka bishi har Ammei da tunda su fara mishi tsiya batace komai ba saidai kowa da nashi manufar kallon da yayi mishi. Inda Addah ta katse su gurin kiran sunan Zaituna.
"Na'am Addah".
Saida Mummy ta d'ago dan gani me za'a sa Zaituna. Yayin da Addah tace.
"Yauwa Zaituna haɗa ma my son breakfast din shi ki kaimai".
Da "toh" ta amsa farin ciki kamar zai mata me danji take kamar ta rungume Addah dan farin ciki, kana ta mike ta haɗa mishi duk wani abu da tasan nashine, kasan cewar Ammei ke mishi girki dan baicin na masu aiki. Ta nufi inda yake bakin ta ɗauke da sallama. Doguwar riga ce a jikin ta ta bacci amma sai dai bata matseta ba sosai saboda tasan halin shi dan tuni ya hana su sa matsatsun kaya.

Harta dire tiren data haɗu mishi breakfast din akan table ɗin dake tsakan kanin sofar da yake bai ɗago ba. Kana ta fara ƙoƙarin haɗa mishi komai dan tsaf sunsan halin yaya na su akan abinda yake so da wanda baya so. Yadda ta duko sosai kusa dashi ga wani uban turare data bula a jikin ta dan har hannun ta na gogar kafadar shi, kana ta kashe murya tare da cewa.
"Done!"
Wani kallo ya watso mata da yasa hajin cikin ta kada wa, cikin sauri kuma tabar gun ta nemi guri ta zauna a kan lallausan cafet ɗin dake shimfide a cikin parlourn.

Ammei ce ta kalli Finnat cikin kulawa tace. "Au Finnat ɗauki madarar nan ki kaima yayan ku kinga Zaituna ta manta da ita.
"Toh Ammei"
Finnat ta faɗa tare da ɗaukar jug din ta nufi cikin parlourn bakin ta ɗauke da sallama. inda Zaituna ta ɗago tana binta da wani irin kallo mai kama da harara itama ramawa tayi kana ta ajiye mai tare da zuba wa a ƙaramin mug ta nemi guri itaka kan cafet ta zauna.

Saida ya mula dan kansa kana ya ɗago ya fara da madara duk da haka kusan hankali sa na'a kan laptop ne dan da alama wani aiki yake mai mahimmanci.
Youseef ne ya shigo cikin shirin sa nafita aiki kai tsaye dinning area ya nufa inda ya samu su dady na shirin tashi dan gama wayar su kenan da Uncle Kabeer dake can Saudiya, gaishe su yayi cikin girmamawa su amsa mishi cike da kulawa.
Ammei ce ta faɗa mishi inda Yah Majeed yake dan shima tunda yaga dady yasan toh fa ba Majeed a gun Kai tsaye cikin parlourn ya nufa inda ya sameshi zaune yana breakfast yan mata biyu zagaye dashi ko wacce da kallon da take mishi kamar zasu cinye shi. Shi abinma saiya nemi bashi dariya amma ba tare da yayi dariyar ba yayi sallama tare da zama a ɗaya daga cikin kujerun.

Bayan sun gaisa da Majeed suka su Zaituna su gaidashi. Youseef bai wani daɗe da zama ba Majeed yah kammala breakfast din, ba tare daya kalli kowa acikin su ba ya ƙarasa gurin Ammei inda take zaune a set ɗin kujeru masu white and purple.
Har kasa ya duƙa tare inda ta shafa kanshi tare da mai maganar dani kaina banjin me take cewa, amma da alamu harda addu'a take mai. Yanzu kam fuskar tashi adan sake take ba kamar ɗazu ba cikin nutsuwar shi ya fara tafiya yana mai daga mata hannu, Youseef biye dashi bayan sunyi sallama da Ammei, inda Mama ma ta bishi da addu'a dan daga ita sai Ammei a parlourn dasu Zaituna Addah ta tafi gurin aiki anty Amarya ma haka sai Mummy data shige part din granny su dady ma basu daɗe da tafiya ba.
Harya kai kofa Ammei ta kira sunan shi bai waigo ba amma ya dakata daga tafiyar da yake.
"Kaje kun gaisa da Hajja kuwa?"
A hankali ya juyo kamar me ciwon wuya kana ya girgiza mata kanshi murya ƙasa-kasa yace.
"Ammei munyi latti saina dawo".
Kai kawai itama ta jinjina mishi tare da cewa. "Allah yah tsare".
Ya amsa da "ameen" a saman labba suna idda ficewa shida Youseef. Zaituna da finnat na binshi da kallo kamar su hana shi tafiya toh amma ya su iya...............



_____________

*Kaduna ✨*



...............Mom tace "Toh ni ba wannan ba, Murja shirye shirye dai sai gaba yake a gidanmu don yau ma aka kawo lefe karkigan shi..." Murja tace "Saura sati ɗaya fa Zuwaira, ba sai a xuba ido ba a ga ikon Allah, idan fa mutum ya fiye axar6a6i da kyar ya dinga ganin abubuwa yanda yake so, ke dai kawai ki xuba masu ido ki daina damun kan ki, auren nan ance ko an daura bai fi na minti goma ba in ma an daura kenan to me xai dameki, ni ba san halin malamin nan nawa tunda na gaya miki shike min aiki kuma kice na kaiki tunda naku shiru, dan haka kawai mu zuba ido mu gani, amma gaskiya malam yana da gaskiya sosai, duka duka nawa ya amsa wajen mu..." Mom ta sauke ajiyar xuciya tace "Ban son in sakankance ne da maganar mutumi a xo ayi abun nan Ina ji Ina gani, wllh da na shiga uku, shi sa gwara in buga nan in buga can, yanxu ma xan je gidan Hajiya Balaraba" Murja ta tabe baki tace "Toh ni dai sai mun yi waya amma da kin hakura ki jira mu gani koda ace baiyi ba bayan an daura zamu iya gurgude shi koh" ajiyar zuciya Mom ta sauke tare da cewa.
"Tom shikenan sai munyi wayar Aminiya". Daga haka suyi sallama.




________★


Yau anty Hajara ta sauka a garin Kaduna dan tare ma su taho da Yah Ahmad kasan cewar jirgin safe su biyo yasa su sauka da wuri, an shirya musa tarba sosai dan Ni lokacin dasu zo ina ciki Luba ta hana ni fitowa sai bayan nayi wanka da ruwan data haɗa min daya ji turaruka dan ba abinda nake sai kamshi ko yaushe kuma dashi nake wanka dan haka kamshi ya kama jikin na sosai dan ko abu na taɓa sai kaji kamshi. Bayan fitowa ta wanka na kintsa cikin abaya marron sai dan kwallin ta. ba abinda na shafawa fuskata sai mai na fito domin musu sannu da zuwa dan koh parlour Luba ba barina na figo take ba, sai dai innaci sa'a in kuma Ummi taganni tace na koma daki shiyasa zaman dakin ya gundire ni sosai.
Sosai anty Hajara data kara kyau da yar kiba ta tasani a gaba tana zolayata ita da mijin ta Yah Ahmad.
Nikam tun ina sunne kai har idona ya fara tara kwalla dan Buhaisa ma taya su take yi sun taranmin su duka. Fitowar Ummi cikin shiga ta alfarma yasa na koma jikin ta ina sakin kuku, cikin lallashi take tambaya, "waya taɓa min ke Safiyya". Su anty Hajara na nuna mata ina kara sakin wani kukan dani kaina nasan na shagoɓɓa ne.
Murmushi itama Ummi ta saki irin na manya dan sak Safiyyah ba abinda ta bari na kamanni yar uwarta Amina. sai dai ace ita ta dara Safiyyah haske amma komai nata ta ɗauko cikin son danne kewar yar uwar tata saboda gaban siriki take duk da dai kamar ɗan ta yake. Da ƙuwa Ummi tama Buhaisa dake dariya ƙasa-ƙasa tare da cewa. "Kinci gidan ku wato kece kisa min 'ya a gaba koh?". dan su anty Hajara tunda ta fito suja baki suyi shiru sai Buhaisa ce baki yaƙi mutuwa. Cikin dariya tace "Allah Ummi bani kadai bace harda su yah Ahmad ma". Ta idda maganar kuma tana kwabe fuska. Dariya su sanya gaba ɗaya sai Ummi da tayi dan murmushi kawai inda Yah Ahmad yace "kai Autas harda sharri" cikin dan zaro ido Safiyyah tace. "Laaaa Allah Yah Ahmad ba sharri bane" dariya su kuma yi wannan karon harda Ummi sai dai Tata bata kai tasu ba. Sannan tace "Rabu dasu kiji Auta ai Bama kulasu kuma zasu zo su sameni ne dukan su".

Daga haka kuma kowa ya saki jiki aka sha fira danshi dai Yah Ahmad baya surkuta da Ummi, gashi akwai wasa da dariya itama a fannin ta hakan ne saidai dan nauyi kaɗan. Suna haka Yah Saif ya dawo yadda ya samesu cikin farin ciki har Safiyyah data zake kamar ba Amarya ba ana fira da ita, dan Safiyyah akwai surutu idan ta samu fira saidai kasan cewar ta taso ne cikin gidan dako damuwar kama baza a zaunar dakai ajiba balle aje ga babin hira.
Kallon ta yake irin kallon nan dake nuna tsantsar soyayyar da yake mata amma kash wani ya riga shi, ya riga shi a lokacin da yake gab da faɗa mata. Ya tabbata ya rasa Safiyyah har abada toh yaushe ma ya rage mishi ya dena ganin ta tunda bikin dududu kwana nawa ya rage 5 to 4 nefa, "Yah Allah". Ya faɗa yana dafe kanshi inda gaba ɗaya su ɗago su zuba mishi ido saboda maganar karshe da yayi ta fito fili. Tambaya su shiga jira mishi idan ba tare da yace komai ba ya samu guri ya zauna cikin son boye komai yake ma su anty Hajara sannu da zuwa. Suma yadda suga yayi suna basu sake tambayar sa ba.
Sai Buhaisa ce data gir giza kai zuciyar ta cike da tausayin ya'yan nata dan tuni ta gano yayan nata son Safiyyah

21 / 29