Author : Billy Pinky Category : Arewa Pen
da zaman gun.
Granny da Ammii na lure dashi tausayin jikan nata take daya kasance shi kadai namiji a gaba ɗaya family, tun kan takai ƙarshe a maganar tata ya musu sallama ya fice yana dafe kanshi dake masa tsananin ciwo.
Da kallo duk su bishi tausayi kwance a fuskar wasu daga ciki, dan granny da Ammii ma kamar zasuyi kuka har ya ƙarasa fice wa a ɗakin, dady ma kai kawai ya girgiza su cigaba da firar su, fuskar wasu daga cikin su ba fara'a.
(🤔 To me kuma yake faru wa dashi ne dasu bishi da kallon tausayi🤭 bari dai nayi shiru mu zuba ido👀)
Ita kuwa mummy kawai jira take taji dady yayi magana akan Auren su Majeed, amah shiru har kowa ya kama gaban sa.
*Washe gari*
Cikin nutsuwa gami da nagarta yake sakkowa daga mataƙalar benan,
Tun kan ya ƙaso ƙamshin sa ya riga isowa, gaba ɗaya family zaune suke suna breakfast, da kallo su bishi fuskar su dauke da murmushi har ya ƙara so ya gaida iyayen nasa cike da girmamawa, duk da dai sun gaisa tun a masjid yaja kujera ya zauna kusa da uncle Sulaiman.
Suma su Zaituna gaba ɗayan su gaishe sa sukayi cike da girmamawa. Ya amsa fuskar nan a haɗe,
Lokaci-lokaci yakan yakan shafa kan shi da runtse ido, Ammii da dady na lure dashi.
Shiya fara tashi, cikin damuwa Ammii tace "Majeed ina zaka" a hankali ya ɗago dara-daran idanun sa ya sauke a kanta cikin ya mutsa fuska alamun ya gaji da zaman gun yace,
"Ammii zanje gaida granny ne".
Ya faɗa yana ɗan fara tafiya, cikin damuwa ta girgiza kai har ya hau upstairs, suma da kallo duk su bishi har ya ɓace ma ganin su.
Zaituna ma tashi tayi tabi bayan sa part ɗin granny, Fennah da Azima su bita da harara.
Bayan sun gama, kowa ya kama gaban sa masu zuwa gurin aiki su tafi.
Majeed kuwa koda ya ƙarasa zaune yasami granny tana kallon tasher haske Tv idan Safiyyah ke gabatar da program, tunda yayi sallama ta ɗago ta amsa mai cikin fara'a yana zama kusa da ita, hankali ta mayar kan Tv shima sanin yadda take mutukar son wannan gidan Tv da kuma program ɗin da suke gabatar wa ne yasa bai sake cewa komai ba ya maida hankalin shi gun, inda Safiyyah yauma take gabatar da program akan taɓarɓarewar ilimi tare da abokin aikin nata. Inda take cewa,
*Taɓarɓarewar ɓangaren ilmi a tarayyar Najeriya* ta daɗe ta na haifar da illoli da janyo nakasu ga harkokin ci-gaban ƙasa musamman ma dai yankin arewa,a sabili da yadda darajar ilmin ke ci-gaba da zubewa ƙasa warwas. ƙwararrun masana sun nuna takaicinsu, dangane da matsalolin ilmi daban-daban da suka tattaro suna ciwa hukumomi da malamai tuwo a ƙwarya,al'amarin da ke ƙara nunar da cewa malamai da yawar gaske a Najeriya sun fara yin bankwana da harkan koyarwa sakamakon tsananin talauci da rashin biyan su alabashi bakan lokaci,da kuma wulaƙancin da malaman ke fuskanta daga iyayen yara. Safiyyah ta ci gaba da bayyana rashin jin daɗin ta kan yadda manyan Najeriya ke kwashe 'ya'yansu daga ƙasar suna fitar da su ƙasashen ƙetare neman ilmi.
lokaci yayai da dukkanin shuwagabannin Najeriya dake kwashe 'ya'yan su suna zuwa karatu ƙasashen ƙetare da su daina,su dawo mu tattaru wuri ɗaya dan gyara darajar ilmin yaranmu. Duk da cewa a yanzu haka dai kashi 75 % na makarantun jihohin arewa masu zaman kansu na jama'ar kudancin Najeriya ne,kuma akwai baragurbin malamai da yawar gaske dake a makarantun gwamnati suna koyarwa,wannan ya sanya gwamnatin jahar kaduna ta fara yin waje da dukkanin malaman da basu cancanta su koyar a cikin makarantunta dan ya zamo wani mataki na farko na tsaftace harkan koyarwa a dukkanin makarantunta.
Haka dai su cigaba da tattaunawa itada abokin aikin nata har su gama, suma masu sauraro sallama.
"Masha Allah yarinyar nan tana ƙoƙari sosai saidai fatan Allah ya kareki a duk inda kike Safiyyah"
granny tayi maganar tana waigowa tana kallon Majeed yadda ya haɗe fuska bazaki gane ma yasan me granny take cewa ba amah dai ya amsa da "Ameen" asaman labba. Daganan su cigaba da fira wacce rabi ita keyi sai Zaituna dakan sa musu baki data shigo tun suna kallon program ɗin. Sallama yama granny kana ya fice.
kai tsaye part ɗin Ammii ya nufa. Koda yaje bata mama Rabi'ah take cemai tana part ɗin dady, saidai ya runtse ido jin ta ambaci dady kamar zai juya sai kuma ya nufi part ɗin nashi
Zaune ya se sa shida Ammii shima ƙara sawa yayi yana zama a ƙasa daga can gefe kamar me tsoran wani a cikin su. cikin ladabi yake sake gaida iyayen nasa batare daya ɗago ya kalli dady ba sai shafa gefen kanshi yake dake masa ciwo, magana kaɗan suyi da mahaifin nasa akan kasuwanci lura da halin da yake ciki ne yasa shi cewa.
"Majeed kaje ka huta ma ƙarasa maganar a waya zuwa anjima"
Kai kawai ya kaɗa ya tashi ya nufi hanyar fita, ganin yadda yake tafiya ne kamar zai faɗi yasa Ammii tashi ta ɗan rungumo sa jikin ta su nufi part ɗin ta dashi. Dady ya bisu da kallo kwalla cike da idanun sa.
Kai tsaye bedroom su nufa ya kwanta a gadon ta, kana ta fara mishi addu'a tana shafa mishi a hankali ya fara sauke ajiyar zuciya alamun bacci ya ɗauke sa. Auta dake zaune tun ɗazu ta zuba uban ta gumi tana kallon su, ta sauke ajiyar zuciya tare da cewa "Allah sarki yayah Allah ya baka lfy" da "ameen Ammei ta amsa kana tace.
"Kije parlour ki zauna ni zanje gurin dadyn kune saiki riƙa lekowa kiga koya farka"
Da "to" ta amsa kana su fita tare Auta ta zauna a parlour Ammei ta wuce part ɗin dady.
_________
*Kaduna✨*
Shirye shiryen bikin anty Hajara muke ba kama hannun yaro dan yau da yamma za muyi ƙauyawa. Gaba ɗaya yan matan dangin Dady duk sun zo dan kusan sa'annin mune.
*In the evening*
Buhaisa ce cikin shirin ƙauyawa take kwalla kiran sunan Safiyyah.
"Wai Safiyyah mekike nufi ne tun ɗazu muna ta jiranki mun kintsa ashe ke kina nan kina bacci wai ustaziya bazaki gurin ƙauyawa ba, batin kinsan time ɗin Abu nan yayi har ya fara wucewa".
Safiyyah da tun da Buhaisa ta fara magana har ta gama tana kallon ta kana ta balla mata harara itama cikin ɗaga murya tace.
"Ke dan Allah meye kizo kina mun ihu a ka batin kaina ciwo yake eye?"
Buhaisa na niyar magana Isha ta shigo tana faɗin
"Wai lfy kuke kuwa ya ke Safiyyah da muke jiran ki naganki haka Bama ki kintsa ba lfy kuwa?"
"Kyale yar rainin wayo wai kanta ke ciwo" Buhaisa ta faɗa tana hararar Safiyyah.
"Uhmm bawani ciwon kai malama places tashi ki kintsa dan ke muke jira haba dan Allah. Kuta wani abu kamar yara"
"Uhmm bazaki gane bane kawai tazone ta sani a gaba tana min masifa" na faɗa ina kallon Buhaisa.
"To sorry sisi nah wallahi raina ne ya ɓaci dana ganki a kwance nan amah shikenan please tashi ki shirya".
"Dama fa ninayi wanka kaya kawai zansa kuje inna kintsa zan fito". Na faɗa ina kallon su.
"Wallahi baki isaba malama kedai kwai kintsa kizo muje" Isha ce tai maganar tana zama, ba tare dana ce musu komai ba nashige bathroom.
Cikin ƙanƙanin lokaci na gama shirya cikin kayan ƙauyawa, kasan cewar a harabar gidan za'ayi tuni komai ya kamala kasan cewar masu daya decoretion sun zo sunyi dan sanda ma mu fita anty Hajara na gurin da ƙawayan ta.
Haka ayi ƙauye day aka tashi lafiya inda washegari akayi Fulani day. Yau kam ba'ai fama daniba kasan cewar ina mutukar ƙar son fulani day inda muka shirya cikin fararen kayan fulani amar kuma tasa blue.
Abun ba'a cewa komai yadda kayan su min kyau dan saida su Buhaisa su matsa muyi hoto aikuwa anyi hotuna kam ba lefi. Shima anyi lpy inda washegari daya kasance day 3 akayi Arabiyan night, kasan cewar sai dare yasa mu fita dan sai gab da magrib mu dawo inda mu kintsa cikin bakar abaya tare dayin rolling ɗin mayafin ta dukan mu aikuwa munyi fito kamar larabawa.
Toh shima haka ayi lpy a tashi lpy. Day 4 kuma ayi Bridal shor inda gaba ɗaya muyi ankon kaya purple amah banda amarya shima haka ayi lpy a tashi lpy.
Washegari kuma daya kasance day 5 ayi walima amarya tasha kyau cikin les blue inda malamai magada annabawa suyi wa'azi mai kashe jiki da ɓargo anty Hajara kam ansha kuka inda ƙawayan ke mata dariya daga baya su koma lallashin ta. Antashine gab da magrib, dan haka kowa ya tashi muma muje miyi sallah. Gajiyar dana yine yasa na kwanta da wuri dan so nake na huta ko dinner ma yau bazan yiba waya tace ta fara rigging ganin sunan daya fito
ɓaro-ɓaro akan screen ɗin wayar wato حببي yasani sakin murmushi na ɗauka da sallama a baki nah, daga can ɓangaren ya amsa min sallamar har ina jiyo sautin murmushin sa, haka mu cigaba da waya cikin soyayya da nisha can yace. "Albishirinki my princess".
Ido na lumshe kana nace goro.
"an shirya komai tsaf gobe in sha ALLAHU za'a tsaida date. Jinai duk wani iri, amma a ƙasan raina ina farin ciki da hakan. Koba komai ai zan samu ƴancin kaina. Daga nan mu cigaba da fira bajima muyi sallama.
*Washegari*
Yau ta kasance ana i gobe ɗaurin aure kuma yau za'a sa amarya a lalle mukam tunda mu fita wankin kai dan acan ma amana namu lallen baki da jah sai dai ace Masha Allah kam dan lalli yayi kyau. bamu dawo ba sai gab da magrib. a gajiye mu shiga ciki inda mu tarar parlour cike da baki. gaishe su muyi mu wuce sama inda kai tsaye ɗakin anty Hajara mu nufa. Zaune take tasha lalli ƙawayan ta sun sata a tsaki sai zolayarta suke. Muma zama muyi a ɗaura damu daga baya ma data gaji tashi tayi wai zata amsa waya. Dariya muyi Nabila ke cewa "ba wani waya dama kin dawo" bata kulata ba ta fice muma mu tashi mu nufi bedroom.
Wanka nayi tare da dauro alwala bayan na gabatar da sallah magrib ban tashi ba na fara karatun Alqur'ani ko wanne harafi ina bashi haƙƙin sa saida akira isha'i na tashi na gabatar, lokacin yaya Ansar ya kirani a waya da rabon dami waya dashi tun shekaran jiya. Cikin farin ciki na ɗaga tare dayin sallama. Daga ca ya amsamin tare da tambaya ya nake, mun dade muna fira yake cemin ɗazu ya dawo yanzu haka ma yana gida. Cikin shagoɓɓa nace.
"Yayah zaka zo nanne yau?" Daga can ina jiyo murmushin sa kana yace.
"Safiyyah kenan dare yayi saidai zuwa gobe ran daurin aure insha Allah"
"Toh yaya nah Allah ya kaimu lafiya". Da "Ameen" ya amsa kana muyi sallama.
Tun muna waya dama md ke kirana sai bayan mun gama na kirasa bai dauka ba sai ya sake kirana. Mun daɗe muna waya tunda najisa cikin farin ciki nasan da walakin goro. Yake cemin.
"My princess yau fa ansa rana nan da wata ɗaya insha Allah kina gida na"
Dama tuni yaya Ansar ya faɗa min ansa rana, amah bai faɗa min wata nawa ba. Cikin jin kunya nayi ƙasa da kaina kamar yana gaba na nace.
"Allah yah kaimu"
Da "Ameen yah rabbi" ya amsa kana mu cigaba da waya cikin farin ciki.
Buhaisa ce tazo ta kirani wai yayah Saif na kira na. Koda naje ba abinda yamin saima fira dami dashi yanda muke firar nagan shi wani iri cikin damuwa nake cewa.
"Yaya Saif baka da meke damun kane nagan ka wani iri?"
"Uhmm bakomai kawai dai rabuwa da Hajara ne"
"Allah sarki yayah ai sai hakuri haka aure ya gada. Kai da kake babba kai zaka ƙarfafa mana gwuiwa. Please yayah ka kwantar da hankali ka kaji".
Tunda ta fara maganar ya zuba mata yana kallon ta a zuciyar sa yace.
"Uhmmm bazaki gane bane Safiyyah"
(Allah sarki 😥Yah saif)
Suna zaune har Buhaisa tazo su cigaba da fira.
________
Ɓangaren mom kuwa tunda a kawo kayan sa rana take ta tasa Abba a gaba tana masifa sai hakuri yake bata amah sam taƙi saurarasa ta yadda take shiga a tannan take fita ba. daga baya daya gaji sai ficewa yayi ya bar mata gidan, inda anty Waleeda ta saka mata kuka.
"Wallahi mom in ban sami Suraj ba itama Safiyyah bazata same saba. dan wallahi nafi karfin inrasa abu ita ta samu impossible mom wallahi bazai taba yiwuwa ba"
takai ƙarshe maganar cikin tsawa kamar wata mahaukaciya. Ita dai mom da kallo kawai tabi ɗiyar tata cikin sauke ajiyar zuciya tace.
"Toke Waleeda banda abinki ai koh bakya son wannan yaron wallahi bazan taɓa barin Safiyyah ɗiyar Amina ta aure saba. kenan ma Amina tafini koda bata raye yanda yaron yake ɗan gidan manya ta aure shi ai Amina tamin nisa tafini, wallahi indai ina raye Amina bazata taɓa finaba ko da yaushe saidai ta kasance a bayana. Ke Safiyyah ma bazan barta tai aure sai dai ta ƙare a me min bauta, daga baya na haɗa da wanda nasan bazai barta ta huta ba. Dan haka ki kwantar da hankalin ki auren ki dashi ba fashi inko baki same saba itama bazata same shiba wallahi.
Takai ƙarshen maganar rai bace inda anty Waleeda ta rungume ta tana zuba mata kirari. Wayarta ta dauka tana neman layin Umman ta aikuwa baifi ringing ɗaya ba aka ɗaga daga can ɓangaren, bako sallama ta fara faɗin.
"Umma komai fa na shirin lalace wa gashi har ansa rana nan da wata ɗaya bikin wannan matsiyaciyar".
Shiru tayi na ɗan wani lokaci tana sauraren mahaifiyar tata, can kuma tace.
" Anya Umma na kan kwari kuwa yayi aikin nan cewa fa yayi baza ma asa rana ba balle biki gashi har ansa rana saura biki, gaskiya Umma ki neman mana wani dan so nake nanda gobe komai ya wargatse wallahi".
Shiru ta kumayi nadan wani lokaci alamun tana sauraren ta kana cikin taɓe baki tace.
"Uhmm tana can gidan wannan ƙanwar uwar tata Halima ana bikin wannan shegiyar yar tata data ƙi aure sai yanzu. Dan wallahi yanzu haka nasan itake zugata duk iskanci da take amah bari ta dawo zan gyara mata zama".
"Toh Umma saikin zo ɗin" ta kareshe maganar tana yanke kiran hankali kwance.
(Ni koh nace ayi dai mugani☹️)
__________
A ɓangare Suraj kuwa wato (MD) musalta muku irin farin cikin daya shiga bata lokaci ne, daga shi har iyayen sa. Inda tuni dangin sa sunji daga ciki akwai yarinyar ƙanwar mahaifinsa dake mutukar sonsa amah shi kwata-kwata bata gaban sa. Aikuwa da suji labari har gida tazo ta zazzage momy ita da ɗiyar tata.
Ana haka Suraj ya dawo cikin farin ciki domin ganin mahaifiyar tasa ya tarar su lubna da mahaifiyar ta suma ma momyn sa wulaƙanci. Tsawa ya daka ma lubna tare da sauke mata lafiyayyen mari, ya mata tatas ita da mahaifiyar tata dakyar su fice tare da cin alwashi kala-kala. Kasan cewar momyn tashi macece mai hakuri ta lallaɓa shi da kwantar mai da hankali.
___________💫
Rana bata karya sai dai uwar ɗiya taji kunya inji masu iya magana dan kuwa yau aka daura auren anty Hajara da angon ta Ahmad. Inda bayan daurin aure da gama hotuna a fara shirye-shiryen tafiya da amarya Abuja.
Can na hango ƙannin amarya wato Safiyyah da Buhaisa da Isha, gurin su yaya Ansar da yaya Saif dan harda MD ma. inda su haɗe cikin ankon shadda yar uban su pink calour. sunsha make up sunyi kyau saidai ace tabarakallah. Kasan cewar Safiyyah ba gonar kwalliya bace dan saida Ummii ta matsa amata kana ta yarda, aikuwa tayi matukar kar kyau kamar itace amaryar kowa sai yabawa yake. Bayan sun gama gaisawa da MD akayi musu hotona. Ummii ma uwar amarya ta haɗe cikin fitinanne Les ɗin ta ɗan ubansu marron colour and white saidai ace Masha Allah amah fa tasha kyau. Inda ta shiga cikin tsakiyar yaran nata amusu hotuna. kana a fara shirye-shiryen tafiya da amarya.
Inda akaita gurin dady ya mata faɗa da nasiha mai ratsa jiki aikuwa taita kuka za'a tafi da amarya da kyar a ɓanɓareta a jikin Ummii ta rungume ta tana kuka. Muko dariya muyi ta mata daganan mu ɗauki hanyar Abuja.
Ankai amarya gidan ta lafiya gida yayi kyau saidai ace masha Allah. 8pm mu fara shirye-shiryen zuwa gurin dinner, inda akawo me mana make up bayan angama ma, amarya da ƙawayen ta sai mu.
Kasan cewar mu uku ne sai kwalliyar tai sauri, dan danan simple makeup akayi mana, amma komai iri d'aya, dama haka mukeyi, komai namu kullmun iri d'ayane.
Munyi k'yau mukayi shiri cikin material blue doguwar riga dan ta matseni da kyar nake motsi, kamar yanda aka tsara sai veil shi kuma pink.
Na jujjuya ina kallon kaina a mirror, “kai jama'a nikam bazan iya fita hakaba gaskiya”.
Buhaisa dake kwance tana danna waya tad'ago ta kalleni, “kai amma kuma wlhy kayan sun miki k'yau, kinganki kuwa? dan ALLAH ki barsu, kiyi rolling veil naki kawai”.