Chapter 15 Reading RAYUWATA BOOK COMPELET BY BILLY PINKY.txt Arewa Novels

RAYUWATA BOOK COMPELET BY BILLY PINKY.txt

Author :  Billy Pinky Category :  Arewa Pen

Chapter   15 / 29

42K to 45K   out of 84.6K words

“kai ba Safiyyah kad'aibafa, nima bazan iyaba, after dress zan d'ora wlhy”.
Cewar Isha. Dariya Buhaisa tayi, ta tashi zaune tana ajiye wayar, “waiku miyasa k'auyawane sister's, naga a ke6antaccen waje za'ayi?”.
“amma kuma dai ai akwai maza kema kin sani”.
“to alaranmiya, Ku saka, amma kafin Ku saka ɗin nidai kuzo miyi hotuna”.
Gaskiya koni nasan munyi k'yau, kasancewar mud'in fararene, kalolin duk sai suka kar6i jikinmu blue & pink. Wanda bai saniba saiya ce mu 'yan uku ne. dan muna matuk'ar kama da juna, sai dai Buhaisa tafimu haske niku ma nafisu ɗan jiki.
Sai da mukad'anyi hotuna sannan muka fito. Inda ƙawayan anty Hajara suyi tace wa munyi k'yau,

Kai tsaye gurin taron mu ƙarasa inda abokan ango su ɗi bemu. tunkan mu k'arasa muke jiyo tashin kid'a. wajen dank'am yake da 'yanmata da samari, da yan uwan ango da namu muma, sai abokan ango,
Tunda muka shigo akai mana caa da idanu, wasu tsantsar kamarmu ce tajawo hankalinsu kanmu, wasukuma burgesu mukayi, to dama shi taro ya gaji haka.
Amarya ta sha kyau sai dai ace masha Allah ita da angon ta Ahmad
Nan afara gabatar da shagali sai pictures da'aka d'auka da video, 'yan mata sunata casar rawarsu da samari, mudai muna gefe muna kallo. Dan koda a bukaci muje ba rawar dana yi sudai su Buhaisa sun taka. Inda wani maƙalalle a abokan Yah Ahmad ya nace min, to suma dai su Buhaisa sun sami nasu. gab da magriba taro yatashi lfy, kowa ya kama gabansa. muma gida a maida mu.

*In the Afternoon*

"Wai dan Allah Safiyyah ku fito mu tafi mana bawan Allah nan tun ɗazu yana can yana jiran mu, kuma kunsan anjima zamu wuce".
Buhaisa da tunda ta fara magana saida takai ƙarshe ta tsaya.
"Afwan muje dan Allah karkiyi far feson mu mai saurayi".
Dariya tayi "eh naji ai ya daɗe yana jiran mu koh"
"please ku muje magana nan nu" cewar Isha tana ƙaraso wa inda muke.

Dama saurayin Buhaisa ne yace wai ya kamata mu fita waje mu dansha iska. Dani kwata-kwata banyi niyar fita ba dan saida anty Hajara tasa baki kana na shirya. Shine yanzu tazo tana mana aka-aka.

Duka baya mu shiga ashe harda saurayin Isha aciki, kai tsaye a wani tanƙamemen shopping mall yayi parking. Masha Allah tabarakallah shine kawai abin dana ke faɗa a zuciya.

Wani irin don kulallen ginine mai tsawo da sam baida iyaka gamai kallo. Ganine irin na mutanen ƙetare wanda iya haɗuwa yah haɗu, sai wasu tanfatsa-tanfatsa din glass masu kama da window ko ince kofa. Ginin da yake a dunkule kamar anyi cycle da iya kawai gun da a zagaye, abin kallo, shine a gaba inda yake haɗe da wani wanda ya kasance mai faɗi. Inda nakai kallo na saman wancan ginin dake a dunkule, ajikin sane sunan gurin ke rubuce.
*A A SARAKI SHOPPING MALL*
Nagani a rubuce da Golding colour, dolene kaga wannan gurin ka tsarkake sunan Ubangiji mai girma da ɗaukaka. tabbas na taɓa jin sunan amah a ina shine na manta. A gaba ki ɗaya parking lot ɗin motoci ne na alfarama, wasu na shiga wasu na fita keda ganin gurin kasan sai dan wane da wane.

"Ku muje" maganar da Ishaq saurayin Buhaisa yayine ta dawo dani daga haiyacina daga kallon ginin, bance komai ba mu fito daga motar. Aikuwa muna fira wannan nataccen daya nace min shima ya fito a tashi motar, kallo ɗaya namishi na dauke kaina ina jin gina da motar. Kusa dani ya matso yana cewa "beb muje koh"
Ban ɗago ba bale na nuna alamun naji me yace. Buhaisa ce tazo saitin kune na cikin raɗa-raɗa take cewa.
"Please Sopy karki bada mu mana, kuma kimsan wulaƙanci ba kyau"
Kalmar ƙarshe data faɗa ce ta sani motsawa inda suyi gaba itada Ishaq mu kuma a bayan su su Isha a bayan mu. Kai tsaye cikin katafaren mall ɗin mu shiga.........✍️



_*Taku har kullum da ko yaushe*_

*Billy pinky💞*




ing📲*

_WhatsApp channel_ 👇

https://whatsapp.com/channel/0029VauF15RLNSZvrEQHsL0

_WhatsApp group_👇

https://chat.whatsapp.com/EKFnHpoI54t1MvodB5HgYB


*🌹 RAYUWATA 🌹*

_CREATED AND WRITING BY_

*Bilkeesu Sa'eed Aliyu*
💞*Billy pinky*💞

Amanar nazari writer's ✍️

Page 3️⃣0️⃣➡️3️⃣1️⃣

*A A SARAKI HOUSE*

"Boss ya kamata fa yau kaje kaga A A SARARI SHOPPING MALL saboda tunda ka dawo baka je kaga meke tafiya ba duk dai ina zuwa amah zuwan naka zaifi. Ina ganin kawai daga can sai mu wuce gurin metting ɗin"

Youseef ya ƙare sa maganar yana kallon Majeed cikin fatan Allah yasa ya amince yadda suke kamar yan sama jannatin nan yau suna waccan kasar gobe waccan ya kamata yaje yaga meke wakana kafin su kuma barin kasar. Tunda Youseef ya fara magana har ya gama baice komai ba illa zube shi da rikitattun idanun sa da yayi a hankali ya motsa bakin sa kamar wanda ama tilas yace.
"Okay muje" ya faɗa ya miƙewa sai lokacin na kare mai kallo sanye yake cikin sute silver sai ta ciki data kasance black sai neck tie silver. Gashin nan yasha gyara dan ya kwanta masa luf-luf a gadan bayan sa.

Ba abinda yake sai ƙamshin mayun turarukan sa masu mutukar ƙamshi da sanya nutsuwa, Taku yake cikin ƙasaita gami da izzah Youseef biye dashi har su fice kai tsaye part din Ammei su nufa inda parlour yake shiru dan haka ya nufi bedroom ɗin ta Youseef dama tuni ya wuce Babban parlour yana jiransa a can.

Sallama dauke a bakinsa ya shiga inda ya sami Ammei zaune akan sofa dake cikin bedroom ɗin waya a hannun ta da alama waya ta gama ko kuma zatayi, har gaban ta ya ƙarasa tare da kaiwa kasa yana gaidata cikin fara'a ta amsa tare da kamo hannun sa ta zaunar kusa da ita. "Majeed amah kana shan maganin ka kuwa dan ya kamata ace yanzu komai tsakanin ka da dadyn ku ya wuce amah abin kamar ma gaba yake kuma kace kana sha a ina matsalar take" ta ƙara sa maganar cike da damuwa. Hannun ta ya kama cikin son kwantar mata da hankali yace. "Humm Ammei ki kwantar da hankalin ki insha Allah komai zai wuce kinji Ammei nah" yakai kashe tare da lumshe ido, "Na sani amah nasan halinka fa anya kana shan maganin nan kuwa?"

"Uhmm yanzu dai Ammei bar naje Youseef na jirana za muje mall inna dawo sai muyi magana" ya kai ƙarshe tare da sumbatar goshin ta. Tasan dan baya san maganar ne kawai shiyasa zai tafi addu'a tamishi kana ya fice cikin nutsuwa.

Yana fitowa Youseef ya samu a parlour kasa shida su Auta da Basma suna fira sai Zaituna dake can zaune akan kujerar mai ɗaukar mutum ɗaya cikin riga da wando sai ƙaramin mayafi, dan dama jiran fitowar sa take tana danna waya, sai su fennah dake can rukunin kujeru White and black suna fira, yana fitowa gaba ɗayan su natsuwa suyi Zaituna dake danna waya ma ajiye ta tayi duk suka gaidashi cikin girmama wa. Kyakkyawar fuskarsa ma abociyar kamewa da tsare gida a haɗe ya amsa batare da ya kalli ko acikin su ba su fice shida Youseef.

Da sauri Youseef ya buɗe masa bayan farar zananniyar motar da Samuel ya fiddo, wadda ko makaho ya shafa yasan eh lallai kuɗi yay aiki wajen sayen ta. Dan sai wani irin sheƙi take da ƙyalli mai ɗaukar ido. Gata nan wata ƴar ƙumbula bata cika hayaniya ba, ba kuma ta cika mamaye waje ba. Tsaf take kala da yanayin matasan zamani irinsa da ke gara kan kuɗi ta yanda suke so saboda amincewar UBANGIJI garesu.

Sai da ya zauna Youseef ya maida ƙofar ya rufe sannan kowa ya zabura ya shiga mazauninsa. Youseef da Samuel na gaba kamar koyaushe. Securitys ɗin sa na'a wata motar kamar ko yaushe suma. Da dasu uku ma kawai zaiyi fitar. Samuel na ƙoƙarin tada mota ta fito da ɗan saurinta. Kamar kullum tana a cikin kwalliya dake ƙara fidda mata ƙyawunta da bayyana wayewarta. Youseef ne yay ma Samuel nuni daya dakata, dan haka ya tsaya ɗin harta ƙaraso, kallo ɗaya tai musu ta ɗauke kanta, dan direct bayan ta nufa saitin inda Majeed da bai san ma da fitowar tata ba yake. Dan hankalinsa nakan takardun daya ɗauka a gefensa da Youseef ne ya ajiye masa su dan ya duba. Cikin shagwaɓaɓɓiyar muryata data haɗe da gayu ta furta, “My bro.. please zan bika, nasan dai mall zakaje”.

Idan kujerar motar nan ta motsa shima ya motsa duk da kuwa muryar tata tazo masa a bazata tunda shi bai san da fitowar tasu ba. Kuma inama tasan da zuwan sa mall. Ƙara narke murya tayi cikin nuna damuwa da shirun nasa ta sake cewa, “Please mana Yaya Majeed na shigo?”.

“Kai kana jiran miye?!”.
Ya faɗa cikin yanayin fusata batare daya ɗago ba. Ai jikin Samuel har rawa yake wajen murzama motar key dan ko kallonsu ogansu yayi sun san mi yake nufi balle magana da baki. Da wani kalar mayen kallo Zaituna tabi motar, ga wani irin sanyi ƙalau da jikinta ke komawa kamar an zubama bread ruwa. Dai-dai motocin na isa katafaren golden an black gate ɗin gidan da aka wangale musu wasu hawaye masu zafi suka shiga rige-rigen sakkowa saman ƙyaƙyƙyawar fuskarta. Bata motsasu ba, bata kuma yi yinƙurin barin wajen ba. Ashe turaren da Mommy ta bata duk na ƙarya ne tunda gashi tazo gabansa amma bai kulatan ba.

Azizat dake ta bayansu ce laɓe ta tako zuwa inda take bayan ta gama cin dariya, dan tun fitowar Zaituna daga parlour tabiyo bayanta, dama kuma itace ta ɗauke turaren da Mommy ɗin ta bama Zaituna ɗin dan a kunnenta komai ya faru sanda take bata batare da su sun sani ba. Hannunta ta kama kawai tare da janyota ta faɗa jikinta. Rungumeta tayi cikin sigar nuna lallashi batare da tace mata komai ba, sai dai shafa bayanta kawai da takeyi dan babu wani abu da zata faɗa mata kuma wanda ita bata sanshi ba. Sai dai kawai taƙi yarda ne kamar yanda kowa ya sani. Dan tunda yayansu yaface bayayi tofa babu ubanda ya isa cewa yayin sai Ammeinsa, da dady. Bata ganin laifin Zaituna wani lokacin, dan wlhy ko ita inama-inama. Amma yanda tasan yana mata kallon ƙanwa yasa take dannewa kawai. Sun ɗan jima a wajen kafin ta kama hannunta su koma ciki...

Kai tsaye basu zame ko inaba sai A A SARAKI SHOPPING MALL gabaki ɗaya ma'aikatan gurin ruɗewa suyi ganin oga da kanshi nan suka fara gaidashi cikin girmamawa tare da kaishi guri na musamman duk lokacin daya zo dama gun yake zama.

A ɓangaren mu kuwa saida mu shiga mu sake tabbatar da cewa lallai gurin bana wasa bane dan waje ba komai bane akan cikin inda ya kasance komai da zallar glass akayi, inda ya kasance sama da kasa . gaskiya musalta muku kyau da tsaruwar gurin bata lokaci ne dan zamuci lokaci da yawa amah naba kowa damar ƙiyastawa. (kyau ace kowa yaje ya gani da idanunsa lol😁) mutane ne keta kai kawo a gurin 'yan mata da samari harma da matan aure wasu da mazajen su harda masu jajayen kunnuwa dan ga dukkan alamu sune ma'aikata gurin.

Mun shiga 6angaren kayan kwalliya, suce kowa yaza6i abinda yakeso.
Nidai nace masa a'a na gode.
6ata fuska yayi yana hararata, ya maida kallonsa ga Buhaisa dasu tuni sun mayi gaba.
Ya kalleni yana fad'in “mujeto ni na d'ebar miki”. bance masa komaiba nabi bayansa ganin kamar yayi fushi, da kansa yake za6ar mini duk abinda yadace. Dan iyakar mu ƙasa kiransa ayi awaya ya ɗan matsa gefe domin amsa kiran.

Su Buhaisa ma sunacan suna d'auka, kamar ance nabar wajen saina zagaya tabaya, a dai-dai wannan lokacinne shikuma yake tunkarowa shida mutanen shi, da alama yana zagayene kowani abun daban. tafiya yake cikeda nutsuwa da izzah, sai sautin takunsa dakakeji, tunkam ya ƙaraso gareni ƙamshin sa ya riga shi isowa. Waige-waige na fara ban ankaraba saiji nayi natafi suuuu santsi ya kwasheni.
Kasan cewar shi mutumne mai yawan tausayi da taimako, da sauri yayo kaina kafin naje ƙasa, Dan yasan fad'uwata a wajen babban had'arine dan ba ƙaramin woya zan shaba danni nama sadak'ar na faɗi ido na runtse kawai ina jiran kaiwata ƙasa.

Majeed ya tabbatar idan ya barta ta faɗi zataji mugun ciwo ne, dan haka da saurinsa kuwa ya tarota ta faɗo jikinsa. Jin shiru ban faɗi ba kuma najini kamar kwance a jikin mutum tsabar firgice da tsoratar da nayi yasani buɗe idona dana runtse. Zuruf ya faɗa cikin rikitattun nasa dashima ya kafe fuskata da kallo da sauri na janye nawa.
Cikin tashin hankali na fara mutsu-mutsun kwatar kaina, jikina sai rawa ya ke yi. Shikuma yaƙi sakinta dan ya tabbatar yana sakin nata faɗuwar daya gudar mata a farko sai tayi wadda ta fita a yanzu,
Duk da tsawan da yayi mata bata nutsuba, sai ma cigaba dayin mutsu-mutsunta nason ƙwacewa takeyi, tuni hawaye kuwa sun fara bimata kumatu, dan a rayuwarta da hankalin kanta kuma hakan bai taɓa faruwa da itaba. Ko hannu bata yarda koda Yah Safwan koh Yah Saif wani ya riƙe mata balle akai ga runguma irin haka. Sai gata yau kwance a ƙirjin wani ƙaton, da ko yayunta basu taɓa aikata haka a gareta ba. Ai dama barinta yayi ta faɗin da wannan abin kunyar.........

Saida ya tabbatar ya dai-dai ta yadda koda ya saketa bazata faɗi ba kana ya saketa, ba tare da yace uffan ba yabar wajen, inda su Samuel su take mai baya. A hankali na sauke ajiyar zuciya tare da bin bayan sa da kallo.

Su Buhaisa da akan idonsu komai ya faru, sai Youseef daya tsaya ya mata sannu shida ma'aikatan gurin dasu rako shi kana yabi bayan boss din nasa zuciyar sa cike da wasu-wasi.
Da sauri su ƙaraso gareni suna tanbayata babudai wata damuwa ko?.
“babu komai Alhmdllh”. ‘nafad'a ina gyara tsayuwata’.
Kana nace kuzo mu tafi gaskiya dan daga nan ba inda zan motsa sai gida, Buhaisa da Isha ma atare sukace haka ne gaskiya tafiya zamuyi. da kyar mu yadda muje gurin biyan kuɗin su biya nikam danaga bazan iyaba ma waje na fita batare dana musu magana ba.

Dai-dai zan ƙarasa gurin motar da muzo, suma su fito ta wata ƙofa alamun suma tafiya za suyi dan mun kusa cin karo dashi na maza naja baya. Raɓani yayi ya wuce yabarni da kamshin turaren shi.

, A dai-dai lokacin su Buhaisa su ƙaraso gurin hannu na takama mu wuce mota, a motar da muzo anan mu koma kai tsaye gida mu koma inda anty Hajara tace. "niko ina kujene haka kun daɗe sosai 'yan mata masu samari". dariya su Buhaisa suyi su fara bata labari,

"wallahi anty Hajara karkiga yadda gay din ya had'u anya ba Balarabe bane kuwa isha?" Buhaisa tai tambayar tana rike haba "ke saidai ba indiya harfa gashine kwance a gadan bayan sa irin nawani jarumi bani sunan sa nan Safiyyah" Isha ta fada tana kallo na tsaki naja tare da cewa. "Ke kisanshi kuma" dariya suyi Buhaisa na faɗin "anty kinga kuwa yadda Safiyyah tayi wallahi badin daya sake ta tafiya yayiba dayasha masifa dan karkiga yadda ta haɗe fuska. Kamar ba wacce a temakaba". Takai ƙarshe maganar tana hararata kala bance ba saima wayata dana cigaba da danna wa, inajin firar tasu inda duk akan wannan mutumin ne.

"Oooh wai A A SARAKI MALL kuje badai nifinku mai Company ne ya temake taba da zata faɗi.?"
"Shi kuwa anty wannan A A Saraki nefa da zakiji ana yawan faɗar shi saboda cigaban daya kawoma Arewacin Nigeria inda naji wai duk Arewacin Nigeria harma da kudun bame kuɗin baban shi. Wallahi anty ban taɓa tunanin zan ganshi ido da ido ba sai gashi yau na ganshi danko a mujallah ko gidan TV ban taɓa gannin shiba".
Cewar Buhaisa inda Isha tace "ai kisan baya son magana da yan jarida shiyasa"
"Uhmm amah fa Allah yayi halitta agunan"
Buhaisa da Isha dai sai firar Majeed suke yi inda Isha tace waini kam meye cikakken sunan sane naji anata A A SARAKI koh"

Anty Hajara dai dariya tayi tana cewa "ah lallai wannan guy din ya tafinmu daku toh full sunan shidai kamar danaji ana cewa Abdulmajeed Abubakar Saraki"

"Wow nice name" suka haɗa baki wajen faɗa inda suka tasani a gaba ganin yadda nasha mur naki cewa komai wai. "Wallahi karkiga yadda ku dace" tsaki naja na shige ciki.

Kallo suka bini dashi, Ihsan kawar anty Hajara tace, “Anya yarinyarnan batada aljanu?, ke kowama bai mikiba?, yanzu nan duk had'uwar Majeed Safiyyah tana nufin bai burgeta ba kenan?”.
Dariya Buhaisa tayi, sis... Ihsan har yanzu baki gama fahimtar Safiyyah ba na lura, kyagama abinda yafi haka indai daga wajentane. Yanzu hakama tunda kikaji tace haka ko sau

15 / 29