Author : Billy Pinky Category : Arewa Pen
jiran fitowar sa, youseef biye dashi gaba daya kamewa suyi su na gaishe gaisawa suyi ya shiga mota, because tini Yuoseef ya bude mishi, a jere motocin suka fice.
Kaitsaye wani katafaren company su nufa, masha Allah shine abinda nafurta gaskiya company ya had'u,
A saman shi an rubuta AA SARAKI MOTORS, da manya baki idan blue ta kawo, sai pink, sai
red, kalolidai da yawa.
__________
*Kaduna✨🤍*
Tini na amshi soyayyar MD because MD ya can-can ci a soshi,
Soyaya muke cike da aminci dan har a gurin aiki sun lura da haka,
PA d'insa ce dai haushi kamar ya kashe ta, to ban masan tanayi ba saidai naji ana fada,
Iyakacin ta harareni bana nuna ma nasan tanayi.
Yau Friday cikin farin ciki na tashi because yau yah Ansar zai dawo, gurin aiki ma jinake kamar kar naje,
Amah haka natashi nafara aikin gidan, bayan nayi sallah nai azkhar da karatun alQur'ani,
Tsaf nagama komai na gyaran gidan dan kuwa har breakfast nayi,
Yau so nake in ma yah Ansar girki mai dadi, shiyasa na'kiyin miyar dan nasan muddin mom tasan yah Ansar zan ma girki wallahi ba barina zatai ba,
Bayan ko kayan abincin shike siya, wataran yah safwan inya gadama yayi cefane amah ba a sanran mom ba,
Tsaf nashirya cikin doguwar riga ta atamfa, pitet sai goggagen hijabi na saka har kasa sai facemask da eyeglasses sai plate shoe,
A gurguje na shirya saboda yah safwan na jirana,
Turaruka kwai na fesa sai hand bag dana dauka nasaka waya ta aciki na fita,
Ina fita parlour naga Abba da mom Abba na karyawa da alamun yau fitar wuri zaiyi,
Danni rabon danasa Abba a idona ma na manta.
Har kasa na duk kusa ina gaishe shi,
Yau kam da d'an fara'a a fuskar shi ya amsa,
harda min addu'ar Allah yabada sa'a, cikin farin ciki na d'ago ina kallon Abba, kwallar data taru a idona ban bata dama zubowa ba,
Ameen yah Allah Abba nah,
Ganin yadda mom ta hade girar sama da ta kasa tana kallon Abba, murmushin takaici nayi nafice a parlour dan bata dago ta kalleni ba bare in saran amsawa,
To da yake yanzu ma wasan buya muke da ita, tace min waya zo nemana, nace bansani ba kuma nasan akan MD take magana, da yazo lokacin dana tafi gidan ummah halima.
Har gurin aiki ya kaini
koda ya ajeni na shiga ciki dan Isha yau tarigani zuwa,
Office din MD naje domin ance yana nema na,
da harara PA din tasa ta bini har na shige,
Koda nashiga gashe sa nayi tare da fad'in gani sir.
Murmushi kawai yayi tareda nuns min gurin zama, ba musu na zauna ina gyara fuskata, ganin yadda nayine yasa,
Yafara min bayanin program din da zamu yi ranar Monday,
"Please baby ki nutsu kiduba da kyau,
"Insha Allah nafada ina ficewa daga office din.
Yau da wuri mutashi aiki kasancewar yau Friday,
Har gida MD ya kaini kasancewar yanzu shike maidani gida yace Isha ta huta. Kuma har yanzu mom batasan shike kawoni gida ba,
Har nakai hannu kan handle din kofar najita a rufe, juyowa nayi ina kallon sa ganin shima kallon nawa yake yasa nai 'kasa da kai, meya "samekine yau naganki cikin farin ciki baby?
"Uhmm maybe yanada nasaba because yah Ansar zai dawo.
Wow, baby shine baki fad'amin ba?
"Sorry farin ciki ne yasa na manta afwan"
"Shikenan dama inaso na tambayeki amah naga kin kosa ki tafi mayi waya kawai"
Okay kawai nace murmushi kwance a fuskata,
Bye nace ina fita a motar,
saida nashiga gida sanan yatada motar ya tafi.
Koda nashiga bakowa a parlour, naji dad'i hakan kuwa, bedroom nashiga kaya kawai na cire nasaka doguwar riga mara kauri,
Kitchen nashiga girki nafara mishi cikin kan kanin lokaci nagama na gyra kitchen, har lokacin banji motsin su mom ba dan alama ya nuna basu gidan, nakin shi naje nakara gyara shi duk kan natafi gurin aiki na gyara nasaka tsin-tsiyar kanshi.
Koda nakirashi ma yana cikin kaduna ya kusa 'karasowa.
Bathroom nashiga nai wanka koda na fito doguwar riga nasa nara nauyi,
Ina gaban mirror inasa turare saiga kiran Buhaisa, bayan mun gaisa take cemin inan zuwa gobe sisi!
Allah yah kaimu amah dai zani islamiya kinsan wancen week din banje ba?
Nima sai yamma zanzo saboda wannan shugiyar matar!
Kai sis mom dince shegiya?
"Ai tamafi haka wallahi"
"Umm Allah ya shirya yaufa yah Ansar zai dawo.
"Eh yafada ma ummi dalilin zawana da yamman kenan kinga ko dare nayi ya maidani"
"Hakane tom Allah yah kaimu goben ki gaidamin ummi da anty hajara jiyama miyi waya da ita"
Ameen tom zasuji, amah amah yah Ansar dinfa ko kuna wayane?
Uhmm munayi"
Da gaka muyi sallama da ita.
Tunda shigowar mota nasan yah Ansar ne naje na dako mishi jaka,
Shikuma ya shiga wanka, kafin ya fito na shirya mishi abinci, koda ya fito zaman ci yayi, muna fira irin ta yayah da kanwa saiga mom nan kamar an jefota, motar uban wa nake gani a gidan nan ?
Ko kulata banyi ba bare innu na nasan tanayi, sumar tsaye tayi tana bin yah Ansar da kallo.
__________
*Abuja 🤍*
Kasancewar yau dady zai dawo sai aiki ake a gidan, gaba daya 'yan matan gidan ma suna part din Ammii har Addah ma nacan, da mama, amah ba banga umma amarya ba, masu aiki kam sai kai kawo suke.
Wata motace tashigo gidan ko parking bata gama dai-dai tawa ba ta kashe motar ta fito.
dattijuwar matar data fito wacce kamar su daya sak da zaituna sai kuma uncle sulaiman, fuskar nan kwata-kwata ba alamun fara'a acikin ta, cikin shiga ta alfarma, security dake harabar gidan sai gaisuwa suke mi'ka mata amah bata dago ta kallesu ba bare susa ran amsawa,
Taku take cike da izza hadi da takama kamar wata sarauniya, tinda tashi go main parlour gaba daya su zuba mata na mujiya, wasu kam mamakin ganin tane ya bayyana 'kara-ra a fuskar su...............✍️
_Taku har kullum da ko yaushe_
_🤝 Amanar haske writer's association📚🖊️_
*Please🙏 comment and like and share fissabilah👏👏*
*🌹 RAYUWATA 🌹*
*Story and written✍️*
*Bilkeesu .S. Aliyu*
_💞(Billy pinky)💞_
*🤝 Amanar haske writer's association📚🖊️*
*_[07070260240]_*
_WhatsApp number or call_
*📚N.W.A🖊️*
🅿️➖24&25
Dagudu zaituna tazo ta rungume ta,
"Oyoyo mummy"
Sai time din tasaki murmushin gefen baki tana shafa kan 'yar tata, kujera mai zaman mutum daya ta zauna ta d'ora kafa daya kan daya.
gaba daya 'yan matan dake parlour suka gaisheta cike da girma mawa, ta amsa fuska a tsuke, zaituna kuwa na ma'kale da ita kamar wata jaririya.
(Too🤔 da alamu ke majeed ya gado a miskilanci, duk da dai Ammii ma ba daga nan ba kamar jinin sarauta)
Barka da zuwa su addah da mama su mata, ta amsa cike da isah tana ma Addah wani kallo.
Ammiii ce ke sauko daga upstairs cikin shiga ta alfarma, shadda ce sai maiko take, taji aiki sai wal'kiya take dinki abuja bubu, sai k'amshi take zubawa kamar wacce tai barin turare,
ga wata uwar sar'ka da dankune, abun hannu, harma da zobe sai zuba kyalli suke daganin su na gold ne, waya ma'kale a kunne ta, har ta karaso ta zauna, yanda duk subita da ido har mummy sai tabe baki take zai tabbatar maka da tayi kyau,
" A'aa zakiyya yaushe ki zone?
" Umm wallahi yanzu nazo naga Yaya ma bai 'karaso ba "
" Oooh tom sannu da zuwa ai ya kusa shigo wa "
" Okay "
Kawai mummy tace tacigaba da latsa wayar ta,
Fira Ammii suke da su mama har papa ya dawo.
Gabaki dayan su harabar gidan su fita, kyakkyawan dattijo daya fito daga mota fuskar sa kwance da murmushi,
Kamar su daya da auta dan da gani kamar sa ta d'ako, taje da gudu ta rungume shi tayi tana zuba mishi shagobba, itada su azima,
bayan sun shiga ciki zama yayi ya gaisa da kowa, kana yace bara na dan watsa ruwa yafada yana mikewa,
" To Yaya a fito lafiya cewar mummy.
" ya amsa da ameen ya nufi upstairs Ammii tabi bayan shi"
wani kallo mummy ta bisu dashi me kama da harara. sai lokacin ta nufi part d'in granny zaituna beyi da ita, suma su addah part din su nufa. 'yan matan kuwa ba wacce ta tashi saima fira dasu dora, har auta da bakinta ya'ki rufuwa saboda farin ciki.
Ranar duka family a mai parlour suyi dinner, ana fira cikin farin ciki, anka cire granny, da yah majeed da kwata-kwata bangan shiba, da alamun bashi ma a kasar, ita kuwa granny tana ji da kafarta,
Bayan duk sun kamala da dady dasu uncle sulaiman kai tsaye part granny su nufa har matan nasu, fira suke cike da farin ciki, da nishad'i, saidai k'alilan a cikin su da sai kalura zaka gane nayin fuskar su,
Sallama suyi mata kowa ya nufi part din shi, because dare yayi,
"Mummy dan Allah kima dady magana auren mu nida yah Aj, wallahi mummy jinake kamar in rufe idona inga na zama matar shi, takai karshen maganar hawaye na zubo mata.
Gabaki daya hankalin mummy ya tashi, itafa a rayuwa ta tsani taga hawayen diyar ta tilo kwallin kwal,
Ki kwantar da hankalin ki ai wallahi indai inada rai majeed bashida wata mata sai ke, meyasa kike tada hankali kine wai akan abinda kisan bazai gagare niba,
Yanzu dare yayi zuwa gobe za muyi magana da yayan, ki kwantar min da hankalin ki kiji dear,
" Tom mummy nah "
" Tashi kije ji kwanta "
*Washegari...*ma gabaki dayan su tare suyi breakfast, bayan sun gama masu zuwa gurin aiki su tafi mazan su da matan su.
Mummy ce dai tunda su gama bata tashi a parlour ba, itada 'yan matan gidan, har dady ya wucce dakin shi, shigarsa baifi da minti arba'in ba tabi bayan shi,
Da sallama tashiga tana bin 'kayatacen parlour nashi da kallo dayaji kayan more rayuwa,
sai k'amshi yake mai sanyaya zuciya, wannan gyaran Ammii ne dan ita macece wacce tasan mahimmanci tsafta, kuma take bata muhimancin, shiyasa k'amshi da yake part din ta daya ne dana yah majeed.
Bakowa a parlour sai sautin k'ira'ar dake tashi a TV, kujera tasa mu ta zauna ta daura k'afa daya kan daya tana bin ko ina da kallo,
B'angaren su amah suna zaune suna fira da dady suji sallamar mummy, koda su fito suma zama suyi dady yace,
" Zakiyya ce ashe?
" Eh Yaya nice dama magana zamu yi tafada tana kallon Ammii "
" Oooh to bara na baku guri Ammii tafada tana mi'kewa "
" Aa yi zaman ki Bilkeesu, dady ya fada "
" Yaya barta ta bamu guri maganar mai mahimmanci ce, ta karasa maganar tana bin bayan Ammiii da kallo da tuni takai kofa.
Shidai dady kai kawai ya gyada tare da fad'in,
" ina sauraren ki "
"Dama Yaya akan maganar majeed ne, ace yaro ya girma har yanzu ba aure duk ga sa'oin shi na dangi kowa da yaron shi,ba daya ba ba biyu ba, amah Yaya haka zamu zuba mishi ido yana abinda yake so. kaima ai zaka so ganin jikokin ka tunda Bilkeesu tayi majeed, tayi habiba, shikenan shiru akeji da alamu ma s,
"Hannun da dady ya daga mata ne yasa ta hadiye maganar data ke son fada ta daro da fad'in"
Yaya ai gaskiya ce wallahi, in baida buduwar ma ai mu saimu zaba mishi ba ma zuba ido muna kallon shi yana abinda ya gadama ba,
ga 'yar uwar shinan zaituna sai hada shi da ita ai baya k'i jinin shi ba, itama kuma tana mutukar sonsa, kaga Yaya sai ayi tuwona maina, akara kulla zumunci wallahi.
Dafa irin auren 'kauye ne da tini majeed yanada jika wallahi bama 'ya ba,
Hajja ma kullum fadan ta akan rashin auren shi, ga uban dukiya ai yasamu magaji nan kusa shima ya huta.
Amah Yaya gaskiya ya kamata a duba magana ta sosai, kuma wallahi zaituna na mutukar son shima tunda kamar tsoran matan yake, ina bashi ita bazai damu ba kuma 'yar uwar shi, koya kagani Yaya?
Takai karshen maganar tata murmushi kwance a fuskata tana kallon dady ganin kamar ya gamsu da maganar ta.
Okay shikenan zakiyya kije zanyi tunani, kuma zan tun tubi su sauran da kuma hajja duk yadda mu Kai shikenan,
Nima rashin auren nashi na damuna, amah inkiyi dubi da kwata-kwata becika samun zama ba, yau yana can gobe nan, kuma auren ma kwata-kwata bashi a gaban shi ne, anya kuwa zai amince?
"Dady yakai karshen maganar damuwa kwance a fuskar sa"
" To Yaya yazai yi in bai amince ba a dole ma saiya amince, tunda in mun zuba mishi ido to wallahi bayi zaiyi ba, tunda shima yana shirin kamawa d'abi'ar turawan nan wallahi, kuma daka kyale hajja in komai ya kamalla shikenan ni zan fara mata magana.
" A'ah kinsan hajja ce ya kamata tariga kowa ji, Allah dai ya zaba abinda yafi zama alkairi "
" Ameen yah Allah Yaya bari naje a huta lafiya Allah yakara nisan kwana "
__________
*Kaduna✨*
Oho ashe kaine ka daowo dole ka cike mana tsakar gida da waccan shegiyar motar,
"Barka da dawowa mom"
"Kai dakata ban bukata,
ke kuma tunda Yayan naki zai dawo shiyasa ki tafi bakiyi miyar ba koh? kinga safiyyah ki fita idona in rufe, kuma abincin in shikadai kima to yadena ci yaje waje ya siya dan da yunwa na dawo.
Tunda tafara maganar har takai karshe ban kalleta ba itama saida ta ida sanan ta karoso parlour tana bin ko ina da kallo,
Da gudu baby tazo ta rungume yah Ansar kanta ya shafa tareda cewa baby kin girma,
"Fuska ta rufe alamun jin kunya kai yah Ansar a hakan primary 6 fa nake"
"Eh mana baby daga primary 6 din basai jss ba?
"Ke dalla zoki wuce banza mara zuciya wuce muje twssss"
ta fizgi hannun baby tana turjewa zata kwace bata saurare taba su shige bedroom din ta.
Kai kawai yah Ansar ya girgiza ya cigaba da cin abinci shi muna fira,
Ranar har sha biyu muna fira yah Ansar har na bashi labarin MD, kodama ya kira maganar daya ce zamuyi cewa nayi mayi waya da safe.
*Morning*
Bayan nagama komai na aikin gidan dana sabayi, dan har breakfast munyi nida yah Ansar because shi zai kaini.
Tsaf nashirya cikin goggagun uniform din islamiya ta, na daura nik'ab sai eyeglasses da nasa alQur'ani na dauka na fice,
Yah Ansar ne ya kaini har islamiya, ya zauna su gaisa da yah sayyadi mu because abonkin shine daganan kuma ya tafi.
Koda nashiga class mu gaggaisa da yan ajinmu suke min korafin rashin zuwana waccan week din,
nace wallahi naje anguwa ne shiyasa.
________
B'angaren MD kuwa tunda safiyyah ta amshi soyayyar shi kullum fuskar nan cikin fara'a, har momyn shi ta lura,
"Waini Suraj Mike damun kane naganka kwana biyun nan cikin Koda yaushe cikin fara'a, kodai wani abun kasamu a gurin aiki naku?
"Duk yadda suyi da safiyyah ya fada mata
"Waikana nufin wacce take program akan matasa Suraj?
" Eh momy ita "
"Alhamdulilah momy ta fada tana daga hannun ta sama gaskiya naji dad'i sosai Allah ya tabbatar da alkairi
Zan ma Abba ku magana sai aje ayi magana da manya, Dan abinda na dade ina jirane ace ka fito da matar aure. Tunda 'yan matan dangi da yawa na sonka ka'ki, to Allah ya amshi addu'a ta"
Mennat ma cikin farin ciki take taya yayan nata murna, harda ya bata number safiyyah.
_______
"Mom wai kuwa kinsan safiyyah yanzu ba wannan kawar tata bace ke kawo ta gida?
Anty Waleeda tayi maganar cike da gulma tana kallon mom.
"K ban gane mekike nufi ba inba k'awar tata ba to kenan takoma karunwanci ne komai?
"To mom wama yasani, nidai jiya bayan kin tafi Nima na fito zan tafi gidan su lubna naga ta fito a wata mota, kuma bata Ishan bace, ke kinga kallon da murmushin da take yine?
da kingani kinsan ba mace bace, dan naga kamar ma namiji na hango aciki to da yake glass din me duhune banga waye a cikiba, dan saida ta shiga ya tada motar, wallahi kidau mataki a kanta.
Yadda mom ta rike baki tana bin anty Waleeda da