Chapter 11 Reading Nafisat Return Book Complete By Ummu Dahirah.txt Arewa Novels

Nafisat Return Book Complete By Ummu Dahirah.txt

Author :  Ummu Dahira Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   11 / 20

30K to 33K   out of 58K words

miki don nasan halin ta ba wai son ki take yi ba?"


Numfashi Fadila taja sannan tayi murmushi tace, "haka ne.. to Ni zan tafi kin ga nayi late yau ban shigo da wuri ba". Sai kuma ta ɗan ɗago wayan ta tana duba time kafin ta juya ta tafi ba tare da ta sake furta komi ba


Daga Ayush da tun zuwan Fadilan take kallon ta har Shakira bin bayan ta da kallo suka yi har ta ɓace ma ganin su


Tsaki ne ya biyo bayan shirun nasu


Ayush ta kalle ta da mamaki tace, "mene ne ƙawata?"


Sai da Shakira tayi ƙwafa kafin ta buɗe motan tace, "Allah Fadila tana baƙanta min rai idan nayi mata maganar Ɗahira take nuna halin ko in kula wanda Ni ba hakan nake so ba".


Dariya Ayush tayi duk da bata fahimci me take nufi ba, ta nufi ɗayan side ɗin ta buɗe ta shiga, itama Shakiran shiga tayi ta rufe ƙofan tare da jan motan suka bar haraban Hospital ɗin.







           ⚫⚫⚫

               Kai tsaye hawa na uku ya wuce inda a nan ne office ɗin sa yake, Office ɗin na kallon na Ɗahira ne


Buɗe wa yayi ya shiga ya rufe, kallon ko ina yake yi da idanu fuskar sa babu fara'a, ko kaɗan ba ya farin ciki da kasancewar sa a nan ɗin, jin sa kawai yake yi cikin takura kuma hakan ne ya ƙara ɓata masa rai sosai


Duk da office ɗin yana da girma, ga shi ya haɗu tako ina amma shi be burge shi ba ko kaɗan tunda ko kwatan nashi na ƙasan Turkey be yi ba


A hankali ya soma takawa ya nufi kan kujeran ya zauna yana kwantar da kansa jikin kujeran, ya lumshe idanun sa yana jujjuya wa cikin kujeran, numfashi kawai yake sauke wa ba tare da ya motsa ba tsawon lokaci, sai da wayan sa ta soma ringing ne sannan ya buɗe idanun sa yana ɗago kai yabi wayan da kallo a inda ya'ajiye saman table, ganin sunan Dady na yawo a screan ɗin wayan hakan yasa shi sanya hannu ya ɗauka ya kanga a kunne bayan yayi peacking call ɗin, shiru yayi yana sauraron sa kafin ya buɗe baki a hankali yace, "Eh na zo".


Kallon files ɗin gaban sa yayi, sannan ya yamutsa fuska yace, "ok".


Sai ya cire wayan a kunnen sa yana ajiye wa, ya sake maida kansa jikin kujeran ya rufe idanun sa


Bayan mintuna biyar ya jiyo Nocking, iznin shigowa ya bayar ba tare da ya motsa ba


Ɗaya daga cikin staff's ɗin asibitin ne ta shigo, ta gaishe sa but ko amsa ta be yi ba, kamar ma be san da wanzuwar ta ba


"Dr Noor told me to bring this to you."


Hannu ya nuna mata alamun ta ajiye a table


Don haka babu musu tayi yanda yace mata sannan ta juya ta fice


A ƙalla ya ɗau tsawon mintuna goma kafin ya buɗe idanun sa ya ɗago kai yana kallon files ɗin gaban sa, numfashi yaja me ƙarfi sannan kuma ya ɗaura kansa saman table ya sake rufe idanun sa be da alaman yin abinda ya kawo sa.







         ⚫⚫⚫


         Hannun yarinyan ta riƙe tana kallon ta cike da tsantsan tausayi, wai yarinya ƙarama kamar wannan ace an yi mata Fyaɗe, kee duniya ina zaki damu ne? Mene mutane suke nema a kan ƙaramar yarinyan da bata fi shekara biyar ba?


Numfashi taja tana sanya hannun ta kan yarinyan ta soma shafa mata gashi, ko kaɗan yarinyan ba ta motsi, ba ma zaka san tana da numfashi ba sai idan ka ƙura mata idanu sosai zaka ga tana fitar dashi ɗai-ɗai ta cikin Oxgyen ɗin da aka sanya mata


Ta jima tana kallon yarinyan wanda a baɗini tunani ta lula a kan abinda ke faruwa a ƙasar mu, wanda Fyaɗe ya zama ruwan dare a wannan zamanin


Hannun ta tajanye ta miƙe daga kan gadon ta fito waje


Matar dake zaune bakin ƙofan a ƙasa tana kuka ta ɗago kai da sauri tana kallon Ɗahira, sai kuma ta miƙe cikin rawan baki tace, "Likita.."


Kuka ne yaci ƙarfin ta dole tayi shiru


Ƙwallan da ya cika mata idanu na tsaban tausayin matar da ƴarta ta share sannan ta dubi matar a tsanake tace, "Calm down, she will be relieved by God's will, but follow ME and we will talk".


Kallon ta Matar tayi alamun kamar bata fahimta ba


Hakan yasa Ɗahira ta sake maimaita mata da Hausa, "ki kwantar da hankalin ki zata samu sauƙi da yardan Allah, amma ki biyo NI ofiice muyi magana".


Gyaɗa kanta tayi tana saka gefen zanin ta ta share hawayen ta da suka haɗe da majina, sannan tabi bayan Ɗahira da har ta soma tafiya


Office ɗin ta suka zarce, sai da suka zauna sannan Ɗahira ta kalle ta tace, "zan so ki bani bayani a kan abinda ya faru, sam abun be min daɗi ba kuma tabbas dole ne hukuma ta ɗau mata fansa".


Numfashi taja kafin taci gaba, "Mun rigada mun cire spain ɗin waɗanda sukai mata wannan aika-aikan, kuma insha Allahu idan result ya fito zamu miƙa case ɗin ga hukuma domin abi mata haƙƙin ta".


Cikin kuka Matar ta soma magana da faɗin, "Likita mun rigada mun bar su da Allah, sam baza mu iya Shari'a dasu ba domin kuwa waɗanda suka aikata mata hakan sun fi ƙarfin mu nesa ba kusa ba, Ni fata na Allah ya tashi kafaɗun ƴar mu domin kuwa ban san me zance wa Mahaifin ta ba idan ya dawo ya tarda abinda ya faru.." Sai ta fashe da kuka tana ɗaura hannun ta ɗaya saman fuskarta


Kallon ta kawai Ɗahira take yi na tsawon lokaci kafin tace, "kar ki damu dole ne mu miƙa wannan case ɗin ga hukuma, domin a yanzu zancen da nake miki Human right sun shiga zancen nan, kuma ya kamata ki kira mijin naki duk inda yake yazo ya ga abinda ya faru hakan shi ne maslaha, sannan ina so muyi magana dashi". Taƙarike maganar tana janyo Pepper gaban ta taɗau Bairo ta soma rubutu


Matar bata ce komi ba sai kukan ta da take yi


Miƙa mata Peppern da ta gama rubutu tayi, "Ki je ki siyo wannan alluran ina buƙatar su yanzu".


Hannu ta saka ta'amsa tana jan majina, "Na gode Likita Allah ya saka da alheri".


Murmushi kawai Ɗahira tayi mata bata ce komi ba, tana bin ta da kallo har ta fice sannan ta kau da kanta tana sauke ajiyan zuciya, hannu biyu ta saka ta tallabo haɓan ta bayan ta ɗaura gwiwowin hannun saman table, sosai take cikin damuwa akan abin da ke faruwa da yaran mutane


"Wai shin mene ne matsalan hakan? Meke jawo yawan Fyaɗe a wannan lokacin? Sannan mene ne mafita?"


Nocking ɗin da aka yi yasaka ta dawowa hayyacin ta, numfashi taja tana kallon Baffa da ya turo ƙofan ya shigo.
[5/28, 8:08 PM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTORS*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏼‍


*بسم الله الرحمن الرحيم*


*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞

```( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*


*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈


*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_




*EPISODE Eighteen*


      "Yayana baka tafi ba?"


Murmushi yayi ya tako ya zauna yana cewa, "yanzu na tashi nace bari inzo inga ƙanwa ta".


"Allah Sarki Yayana, ina to budurwan taka ko ta tafi ne?" Tayi maganar tana dariya


Shima dariyan yayi yace, "kai sis yaushe nace miki budurwa ta ce?"


Ɗage kafaɗa tayi tana taɓe baki tace, "Ni naga alama ne ai".


"Serious ba budurwa ta bace freindship ne kawai a tsakanin mu".


"Anya Yaya ban yarda ba?"


Langaɓe kansa yayi yace, "shikenan tunda baza ki yarda ba?"


Ɗahira dariya tayi tace, "na yarda to, yaushe ne kuma zaka haɗa ni da budurwan ka ko sai ka kawo ta gida ne zamu ganta?".


"Very soon lokaci nake jira ai".


Ɓata fuska tayi tana shirin magana aka yi Nocking


"Yess come in". Tafaɗa idanun ta a kan ƙofan


Matar da ta fita ɗazu ne ta dawo


"Sis bari in tafi sai mun haɗu a gida". Baffa yafaɗa yana miƙe wa


"Ok Byeee Yaya".


Sannan ta kalli matar tace zauna


Zama tayi kamar yanda ta buƙata sannan ta miƙa mata alluran da ta siyo


Amsa Ɗahira tayi ta duba kafin ta kalli matar tace, "Shin Mijin naki ya zo?"


Girgiza kanta tayi sannan tace, "yana Zaria ne a yanzu haka, sai dai kuma na faɗa masa yace min yana kan hanyan dawo wa".


Gyaɗa kanta tayi kafin tace, "to ki je ki kula da ita, Dr. Rahab zata riƙa zuwa ta duba ta, idan ya ƙariso sai ku taho tare ina son ganin ku".


Jinjina kanta matar tayi sannan ta miƙe tayi hanyar ƙofa ta fice



Waya ta ɗauka tayi kira sannan ta kara a kunne


"Ki zo ina son ganin ki". Abun da tafaɗa kenan kafin ta'ajiye wayan taci gaba da duba files ɗin gaban ta


Babu jima wa wata Nurse ta shigo bayan tayi Nocking an ba ta izni


"Gani Doctor" Nurse ɗin tace hakan bayan ta tsaya a gaban table ɗin Ɗahiran


Lokacin ne ta ɗago kai ta kalle ta, sannan taɗau alluran ta miƙo mata tace, "Yauwa Sister ga shi ki je ɗakin da yarinyan nan da aka kawo jiya take kwance kiyi mata alluran nan, Please yanzu zaki yi mata Dr. Rahab bata kusa ne Ni kuma ban yi sallah ba lokaci ya ƙure, ki kula da ita zuwa sanda zata dawo sabida ako yaushe zata iya farka wa kinji?"


Murmusawa Nurse ɗin tayi sannan tasaka hannu ta'amsa alluran a lokaci ɗaya take faɗin "insha Allahu doctor". Sannan ta juya ta fice


Ita kuma Ɗahira miƙe wa tayi ta cire Labcoat ɗin ta; ta rataye a Hanger, sannan ta zare Eyeglasess ɗin ta tare da agogon hannun ta ta'ajiye ta nufi cikin Toilet ɗauro alwala.






⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫



Sai da suka gama kitumurmuran su na abin da suke ƙulla wa a kan Baffa da Ɗahira kafin Shakiran ta sauke ta a bakin gidan su sannan taja motan ta tatafi


Ayush bata shiga gidan ba sai ta nufi cikin anguwan, gidan ƙawarta Rumanatu


Rumanatu ƙawa ce wajen Ayush tun na yarinta, da gidan su Ayush ɗin da gidan su Rumanatu gida ɗaya yaraba su, sun taso makaranta tare komi nasu tare har zuwa matakin da suka kai NCE, inda daga nan ne Rumanatu ta dakata da karatun nata, yanzu haka shekara biyu kenan da auren ta, ta taɓa haihuwa ɗan nata na da wata bakwai ya rasu


Gidan ba wani babba bane gidan Rumanatun but gida ne na masu hali tunda mijin ta yana da ƙumban Susa, shima a anguwan yake da zama da iyayen sa


Ƙofar gidan ta ƙwanƙwasa tunda a rufe yake daga ciki, babu jima wa aka zo aka buɗe mata


Rumanatun ce da kanta, ganin Ayush a gaban gidan ta sai ta kwantsama ihu tana rungume ta tare da faɗin, "Ayushhhh".


Dariya Ayush tayi itama tana rungume ta ɗin, kafin suka saki juna suka shige ta rufo ƙofan, cikin gidan suka shiga suka yaɗa zango a parlour


"Waiii wata sabon gani ai nayi fushi wlh". Cewar Rumanatu tana ajiye mata farantin silver da ta ciko da drinks


Dariya Ayush tayi bata ce komi ba ta ɗauki Robbern Coke tana buɗe wa


Rumanatun ta sake cewa, "tunda kin zama big girl me amsar Albashi duk wata ai dole ki guje mu".


Still dariyan Ayush ta sake yi kafin tace, "wlh kema kin san ba haka bane, tsakani da Allah idan zaki faɗa gaskiya kema kin san bazan taɓa juya miki baya ba, ai ke kin fi ƙarfin haka a waje na".


Kanta ta ɗaga tana taɓe baki tace, "da dai ban san daɗin bakin ki bane, kar fa ki raina min hankali".


Kwashe wa da dariya Ayush tayi har da ɗan buga ƙafafun ta


Rumanatu ta harare ta tana faɗin, "ke dai kika sani".


Ɗan langaɓe kai tayi cikin muryan tausayi tace, "na rantse da Allah ki yarda dani My Ruman, wlh aiki ne ya ɓoye Ni but kiyi haƙuri ban sake wa".


"To ya na iya, yanzu wuni kika zo min ko kuwa?" Rumanatu tace hakan tana tsare ta da idanuwan ta


Sai da ta yatsina fuska kafin tace, "daga wajen aiki nayo nan fa, wlh damuwa ce dani nake neman me bani shawara".


"Shegiya ashe ba don Ni kika zo ba matsalan ki takawo ki? ke wlh baki da mutunci Ayush". Tafaɗa tana dariya


"Ke dai bani shawara kawai ki ajiye wannan a gefe, babban matsala ce dani wlh".


"To ina jin ki fesa min naji".


Sai da ta sauke numfashi kafin tace, "wlh wani Guy ne nake faɗa miki na kamu da mahaukacin ƙaunar sa, don bazan iya ce miki son da nake masa me hankali bane, yau rana ɗaya na gansa amma wlh baki ga yanda na kasa samun nutsuwar zuciya ba".


Dariya Rumanatu ta sheƙe dashi har da tafa hannayen ta, "Wayyo Allah ki ce yau kin samu wanda ya susutar dake? tirƙashi zamu sha biki kenan".


"Ke ba nan matsalan take ba, bari dai in warware miki komi don ki fahimce ni da kyau". Ayush taƙarishe maganar tana muskuta zaman ta


Tiryan-tiryan tafaɗa mata komi har shirin su da Shakira


Sai da ta gama Rumanatu tace, "lallai kin taro match baki da ƴan wasa, amma kinga Ni shawaran da zan baki tunda har kin samu Baffa ta hanya me sauƙi haka, ga shi har kun zama friend soyayya ce kawai ta rage wanda hakan ba wani matsala bane a wurin ki na sani, to me zai hana ki ƙyale shi wannan Guy ɗin da kika gani, kinga fa kince min Familyn su ɗaya, kar ki je kiyi saki na dafe".


Izuwa yanzu fuskar Ayush ya sauya da matsanancin damuwa, cikin sanyin murya tace, "wlh nima haka na gani Ruman, sai dai kuma matsalan yanda zuciyata ta kamu da ƙaunar Usman na haƙiƙa fiye da Baffa, wlh a yanda nake ji a yanzu dai zan iya rasa komi nawa don in mallake sa, Usman ba irin mazajen nan da mata zasu gansa su ƙyale bane, wlh kinji na rantse miki ya wuce gaban kwatance, amma baza ki gane hakan ba sai idan kinyi ido biyu dashi zaki gane irin su ne mazan nan da samun su babban nasara ne a duniyar mu, kin san me? Wlh kyau dai Usman bazai nuna wa Baffa ba, fari ne kaɗai zan iya cewa Usman ya ɗara Baffa domin babu maraban su, amma kuma wayewan su tasha bamban matuƙa, duk da Baffa shima wayayyen saurayi ne wanda duk macen da ta same sa ta gama Sa'a, sai dai abinda yafi jan hankali na akan Usman kasancewar sa yayi rayuwan out side, that's why dole su bambanta nesa ba kusa ba, uhmmm baza ki gane ba amma wlh zuciyata ta kamu, domin ko wacce zuciya da abun da tafi ƙauna, Ni shi nake so ba wanin sa ba". Ayush taƙarishe maganar da dafe setting ƙirjin ta


Jinjina kanta Rumanatu tayi tana kallon Ƙawar nata cike da tausayi, domin ba kaɗan ba ta bata tausayi don sosai ta hango iya gaskiyar ta a idanun ta, so babban cuta ne ga duk wanda ya kamu da ita dole ya zama abar tausayawa


"Gaskiya kina cikin wani hali Ayush dole in tausaya miki, domin kuwa nima na shiga wannan halin kafin in auri Musbahu, amma Ni abinda nake ganin ya dace kiyi yanzu, ta yanda kika bi da Baffan ta nan zaki bi da Usman ɗin.."


Tun kafin ta gama kai aya a zancen ta Ayush ta katse ta da faɗin, "Ruman yanda nake faɗa miki Usman ya bambanta da Baffa nesa ba kusa ba, a halayyan su daban ne sosai, a yanda Shakira ta faɗa min ta ce mugun me zafin kai ne, yana da tsananin miskilanci fiye da tunanin mutum, be da harka ko kaɗan, wlh Ni kaina da na ganshi na yarda da hakan don banga alamun zai iya saurarona ta wannan hanyan ba". Sai kuma ta girgiza kanta taci gaba da faɗin, "Inaa! kwarjinin sa ma bazai bar Ni inje ba".


Numfashi Rumanatu ta saki tana kallon Ayush ɗin, "To yanzu ya kike so ayi?".


"I don't know Ruman, shawaran ki nake nema".


"Ok Ni dai shawarana a nan kawai kibi sa a social media, idan har ya kula ki sai ki faɗa masa abinda ke zuciyar ki, kar ki tsaya tamkar na wannan ki ce zaki ƙi sanar masa, duk da haka ki bani time sai mu san abun yi ko? Ai shawara bazai gagara ba za mu samu mafita".


Murmushi Ayush tayi tace, "Yauwa my Ruman shiyasa nake son ki, I know zaki iya wlh, yanzu ki bani Numban ki so that mu riƙa communicate, wancan Numban taki idan na kira ba ta shiga".


"Wlh kuwa, wayan faɗi tayi shiyasa ai". Rumanatu taƙarishe maganar nata tana amsar wayan Ayush ɗin ta soma ƙoƙarin saka mata Numban


Daga nan hira suka soma yi don Ayush tace mata "ba yanzu zata wuce ba," don haka Rumanatun ta miƙe domin ta girka mata wani abun, tare suka shiga kichen ɗin tana taya ta.








⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫



Ƙarfe 06:01pm. Ɗahira ta gama komi nata ta haɗa kan files ɗin dake gaban ta, sannan ta ɗau jakan ta tare da files ɗin ta fito cikin Office ɗin nata, rufewa tayi tana juyowa shima Usman ya fito daga office ɗin sa riƙe da kai yana yamutsa fuska


Idanun su ne suka haɗe waje ɗaya yayinda gaban ko wannen su yayi mummunan faɗuwa, musamman ma na Usman wanda ya kasa jurewa har sai da ya runtse idanun sa zuciyar sa na masa wani irin ƙunci


Ya tsani wannan yanayin a koda yaushe da yake rinskan sa, that's why ya tsani ganin Ɗahira sabida duk idan idanun sa zasu shiga nata to tabbas sai ya rasa nutsuwar sa tare da bugawar zuciya


Buɗe idanun sa yayi tare da sake tamke fuska yana kallon bayan ta da har ta buɗe Office ɗin kusa da ita ta shige


Dogon tsaki yaja ya janyo ƙofan sa yayi gaba cikin tafiyan sa na taƙama.



11 / 20