Chapter 18 Reading Nafisat Return Book Complete By Ummu Dahirah.txt Arewa Novels

Nafisat Return Book Complete By Ummu Dahirah.txt

Author :  Ummu Dahira Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   18 / 20

51K to 54K   out of 58K words

waya


Sai dai shi gaba ɗaya tunda suka haɗa ido ya rasa sukunin sa, wayan kawai yake yi amma hankalin sa ba ya tare da shi, duk da kuwa ya kawar da idanun sa daga kanta. Ɓata lokaci yayi yana wayan yaƙi ya yanke, sai kamo wani zancen yake yi kasancewar da abokin sa yake wayan.



     Ita kuma tana tsaye ta harɗe hannayen ta a ƙirjin ta tana kallon sa, shiru tayi kawai idanun ta a kansa, sosai take ganin sauyi a tattare da Baffa, gaba ɗaya yanzu ta ga kamar ya sauya mata, kwata-kwata ba ya son ganin ta, idan ba haka ba tasan babu yanda za'a yi a kwana a hantse be nemi ganin ta ba, koda kuwa ta waya ne, amma yanzu tsawon satikai kusan uku kenan ana shirin wata ba ya neman ta, tana ganin kamar akwai wani abinda ke damun sa, yanda gaba ɗaya ya sauya har wani rama yayi...


"Keee!"


Tsawan da aka daka mata ne ya sanya ta dawo hankalin ta cikin matuƙar tsoro


Ba ita kaɗai ba, har ta Baffa da ya juya baya a yanzu ɗin yana ci gaba da wayan sa, sai da ya tsorata da tsawan da aka yi


Sa'adatu ce tsaye ƙiƙam gaban Ɗahira, ta kame ƙugun ta da hannayen ta biyu tana faman huci tamkar zaki, ba komi ya fusata ta haka ba illa fitowar da tayi tana shirin fita, sai ta hangi Ɗahira gaban Baffa ta ƙure sa da idanu ko ƙyafta wa ba ta yi, ga shi kuma har ta iso wajen tana mata magana amma bata ji ta ba, hakan ya sa ta daka mata tsawan nan


Bata bari kowa yayi magana a cikin su ba tace, "uban meye kika tsaya kina kallon sa tamkar zaki cinye sa? Ko dai wani makircin zaki ƙulla iyeee? Ki faɗa idan ba muna-furci da makircin da ke ran ki ba; meye ya kawo ki bayan shi kina kallon sa be ma san kina yi.."


"Kee Sa'ada are you crazy? Kin san da wa kike magana kuwa?" Cewar Baffa a matuƙar fusace da ɗaga murya


Kallon sa Sa'adatu tayi, sai ta zaro masa ido tace, "hankali na ƙalau kuwa Yaya, so nake in San meye alaƙan ka da wannan yarinyan? Ina ce Hajja ta raba ku meye kuma ya sake haɗa ku? Ok har yanzu kana son..."


Mari ya yarfa mata, wanda har sai da yasa ta soma ganin taurari, ba ita kaɗai ba har Ɗahirah dake kusa da ita, bata san sanda hannun sa ya gilma ta gefenta ba, hakan yasa ta tsorata taja baya da sauri tana shirin faɗi


Saurin taro ta Baffa yayi, hakan yasa ta faɗo kansa tamkar ya rungume ta.


      A wannan lokacin shi kuma Usman ya fito gida, babu inda idanun sa ya sauka sai a kansu, tsaya wa yayi kawai yana kallon su cike da mamaki. Janye idanun sa yayi daga kallon su yana jan tsaki a fili, a zuciyar sa kuwa cewa yake, "dama daga gani idan wannan sheɗaniyar yarinyan bata ja hankalin maza sun faɗa tarkon ta ba ai ƙarya ne, waye ya san ma ranan da kuka soma hakan". Motan sa ya ƙarisa ya shiga ya ja ya bar gidan.






     A can kuwa wajen su, Baffa ya kasa cire Ɗahira a jikin sa, while itama ta kasa motsa wa, domin sosai ta tsora ta, sai da ta gama dai-dai ta nutsuwar ta kafin tayi yunƙurin janye jikin ta.


     Sa'adatu da tayi mutuwar tsaye na daga tsantsan mamakin marin da Baffa yayi mata, ga kuma takaicin ganin su haɗe da juna, shi ne yasa ta kasa koda ƙwaƙƙwaran motsi, illa bin su da kallo da take yi.


        Ɗahira na janye jikin ta ta juya ta wuce ba tare da ta furta komi ba


Baffa be iya dakatar da ita ba, duk da kuwa yana son tsayar da ita ɗin, har ta shige mota yana bin ta da kallo, sahun gudun Sa'adatu da kukan ta kawai ya ji, ya juya yana kallon ta wanda har ta kai ƙofa ta shige cikin gidan. Ajiyan zuciya ya sauke yana bin wayan sa dake ƙasa da kallo, be ma san sanda ya wuntsilar da ita ba garin taro Ɗahira. Lumshe idanun sa yayi a hankali ya furta, "Ina son ki Ɗahira! Ina matuƙar ƙaunar ki! Kuma ba zan taɓa dena ƙaunar ki ba har na koma ga mahalicci na".







           ⚫⚫⚫


     Ɗahira motan ta kawai take ja tana tunani, ko kaɗan ta kasa gane takamaiman abinda ke damun ta


Tsaki kawai ta ja ganin tana son damun kanta da tunanin banza, ƙara Speed ɗin motan tayi tana kallon agogon hannun ta


Dai-dai ta isa kusa da Hospital ɗin, tana shirin shan kwana ta shiga, bata kula sosai ba, Ashe wata mota babba na ɗan gote ta dumfaro. shi kuma can ɗaya side ɗin me machine ya dumfaro da gudu yana shirin gilma motan, sai motan tayi ciki da shi, Wanda machine ɗin da me machine ɗin tuni sun yi hanyar su daban, inda machine ɗin ta zo kan motan Ɗahira da har ta kusa tura kan hancin motan ta cikin Hospital ɗin, sai ji kake yi motar nata tayi ƙuuuuuuu.. saboda wani wawan burki da taja kasancewar buguwan da machine ɗin tayi a kan motan ta, yayi matuƙar tsorata ta har ta rasa nutsuwar ta gaba ɗaya taja burki a take tana salati


Can kuwa wajen babban motan nan tuni tayi ciki da wasu motan da suka dumfaro ta,  nan da nan motoci da mashina suka harhaɗe aka haɗa babban hatsari, jini ya soma ambaliya a titin, machine ɗin nan na saman motan Ɗahira, inda wata motan kuma ta bugi motan nata tuni tayi ratsa-ratsa.


Kankace me mutane sun soma zuwa ceton rai, nan da nan wajen ya hargitse da hayaniya. Allah yasa kusa da asibiti ne, nan akai ta zaro mutane ana nufan asibiti da su.
[6/7, 8:19 AM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
              *FAMILY DOCTOR'S*
                         🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
   *NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
                 _NAFISAT ISMA'IL LAWAL._

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏼‍


*بسم الله الرحمن الرحيم*


*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞

```( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*


*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

        
*SADAUKARWA*
𝑁𝑎 𝑠𝑎𝑑𝑎𝑢𝑘𝑎𝑟 𝑔𝑎 𝐹𝑎𝑚𝑖𝑙𝑦 𝑛𝑎 𝑔𝑎𝑏𝑎 ɗ𝑎𝑦𝑎. 𝗚𝗢𝗠𝗔'𝗦 𝗙𝗔𝗠𝗜𝗟𝗬.


_Wannan shafin naku ne Masoyana, kar ku ce ban gaishe ku ba😅, to ku shaƙata da wannan na ku ne kyauta, ina ƙaunar ku nima, har da waɗanda suka ɓoye kansu, Ni *JIKAR LAWALI* ina matuƙar jin daɗin nuna soyayyar ku gare Ni, idan baku Fans to babu Ni ce._





        *EPISODE Twenty Eight*


        Su Abbu na cikin Office ɗin Big Dady, inda suke meeting a kan shigo da magani da za'a yi musu, da sauran abubuwan da asibitin yake buƙata. A lokacin ne labarin mummunan hatsarin da ya afku a wajen Hospital ya iso gare su, ai tuni sun fito don zuwa su ba da agajin gaggawa


Sai da suka sauka downstairs ne, labari ya riske su da Ɗahira hatsarin ya ritsa. Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un tashin hankalin da suka shiga baki ma bazai iya bayyana shi ba, kankace me sun ruɗe gaba ɗaya kowan su sai sharce gumi yake yi, musamman da suka ga yanda ake shiga da masu hatsarin rai a hannun Allah. Nan su ma suka bi ayari fannin emergency rooms


     Su Baffa da Fadila basu fito gida ba ma, labari ya kai musu, tunda shi Baffa dama be yi ninyan shiga ba yau, sai yamma, amma tuni sun ruɗe da su Aunty Amarya sun taho asibitin, sai dai an kasa sanar wa Kaka tunda ba'a san halin da take ciki ba yanzu.


     Lokacin da suka iso asibitin, a reception suka tarar da su Aunty Zainab da Yusra da Shakira, tunda su ba fannin su bane, su Big Dady kuma na ciki.


   Haka DOCTORS da staff's suke ta sintiri suna ba da taimakon gaggawa


Baffa wuce su yayi ya bar su nan, shima ya nufi emergency rooms ɗin, duka tagumi suka yi har Hajja Fatu, domin itama taƙi shiga tunda itama ba fannin ta bane. Aunty Amarya ne kaɗai a wajen take share hawaye, sai Fadila da tayi zugum tana tunanin ƴar uwan ta a ranta, har bata san sanda ƙwalla ya zubo mata ba, babu abinda take tuna wa sai fitowar ta gida yanzu da abinda ya faru, dayake ta side ɗin windown ɗakin su suka tsaya, shiyasa tana kallon draman da suka yi da su Sa'adatu daga saman bene. haka Allah ke lamarin sa, da mutuwa ne sai a aiko musu a ce ta mutu.



       Allah ya taƙaita, Ɗahira bata wani ji rauni sosai ba, sai dai suman da tayi ne har yanzu bata farka ba, ta samu buguwa a kanta har da ciwo, sai kuma gwiwar ƙafafuwan ta da suka ƙuƙƙurje. Alhmadulillah gaba ɗaya ahalin sun samu kwanciyar hankali musamman da suka shiga suka duba ta, time ɗin tana barci tunda an yi mata alluran barci, ba'a haɗa ta da kowa ba a ɗakin da take, sauran suna can rooms ɗin, sun daɗe wajen ta, inda suka je ɗaki-ɗaki suka duba sauran mara su lafiyan.


    Sai da ta farka kafin su Aunty Amarya suka bar asibitin, tare da masu aiki suka koma tunda sun kawo musu abinci.



     Ɗahira tana samun kulawa sosai wajen su Abbu, barin ma kar ace Doc. Sa'id, domin kasancewar fannin sa ne, shi yayi ruwa yayi tsaki yana kula da ita, abu kaɗan ya matso kusa da ita yana tambayan ta abinda ke damun ta, sai hakan ya faranta ran iyalan gidan, musamman su Abba, don a tunanin su akwai wani abu a tsakanin su, tunda itama Ɗahira sosai ta saki jikin ta dashi, ta yanda ma ta nuna sanayya a gare sa.



     Hakan ko kaɗan be ma Baffa daɗi ba, shiyasa be wani zauna ba ya bar wajen, domin bazai iya zama yana kallon wani banza yana hira da ita ba, da kuma bata kula wa sosai.


      Usman kam koda ya san abinda ke faruwa, ko leƙowa be yi ba, yana Office ɗin sa, sai da Big Dady ya kira sa yayi masa faɗa, sannan ne ya zo ya duba ta, kuma komi be ce mata ba, kamar yadda itama bata ko kalli inda yake ba. Haka ya juya yabar ɗakin yana taɓe baki.


    Babu wanda ya sanar wa Kaka, har sanda su Abbu suka dawo gida, sannan ne suka sanar masa cikin nutsuwa, amma duk da haka sosai ya ɗaga hankalin sa, cewa yayi "dole sai an kai sa ya duba ta". Ga shi lokacin dare ne. Dole haka suka fito gaba ɗayan su, Big Dady Abba da Abbu suka nufi asibitin.



      Umma ce da ɗaya daga cikin ƴan aikin su za su kwana da ita, bisa umarnin Abbu. time ɗin ma tayi barci sanda suka zo


Sai a nan hankalin Kaka ya samu sukuni tunda ya ganta a kyakykyawar yanayi. Sun jima kafin suka baro asibitin.



    Washe gari da safe ma ya saka aka sake kawo shi


Lokacin Ɗahira na zaune tana shan tea da aka haɗa mata suka shigo, taji daɗin ganin su, nan tabi su ɗaya bayan ɗaya tana gaishe su


Kowan su na amsa mata cike da kula wa, tare da tambayan ta ya jiki?


Murmushi tayi tace, "it's so easy".


Big Daddy yace, "Are You sure my daughter babu abinda ke damun ki?"


Gyaɗa kanta tayi tana sake tabbatar masa da cewa, "Yes my Dady".


Murmushin farin ciki gaba ɗaya suka yi


Kaka yace, "ai gaba ɗaya kin ɗaga min hankali Matata, a jiya kasa barci nayi, ban ma karya ba na taho duba ki, ashe ke ga shi har kin samu saka abinci a cikin ki, kin bar Mijin ki cikin tashin hankali".


Ɗahira murmushi ta sakar masa, tana langaɓe kai tace, "eyya Miji na, ban sani bane ai, ka ga da ban ci komi ba nima kamar kai, na tausaya maka matuƙa tsoho na".


Dariya gaba ɗaya suka yi har Kaka da ke faɗin, "Ja'ira".


Itama dariyan tayi cike da farin ciki. Haka suka ci gaba da hira na ɗan wani lokaci, inda su Big Dady suka tafi Offices ɗin su suka bar Kaka a nan, don ya ce, "ba yanzu zai koma ba".


Doc. Said ne ya shigo da sallama a bakin sa


Suka amsa mishi suna kallon sa, musamman ma Kaka


Shi kuma murmushi yayi ya iso wajen yana durƙasa wa har ƙasa ya gaishe da Kaka


Kaka ya amsa cike da fara'a da jin daɗin girmama sa da yayi


Ɗahira bata bari ya sake magana ba, ta gaishe shi itama


Amsa wa yayi yana kallon ta yana murmushi, sannan ya tambaye ta "ya jikin nata?"


"Alhmadulillah". Ta amsa mishi da shi


Zama yayi gefen kujeran da ke kusa da gadon ta yana kallon ta, kafin kuma ya ce, "Yakamata a wanke miki ciwon idan kin gama ko?"


Ajiye Cup ɗin hannun ta tayi tana cewa, "ok Doctor I'm done ai".


Miƙe wa yayi ya soma haɗa magunguna


Ita kuma suna hira da Kaka, inda yake tambayan ta "wane ne wannan?"


Dariya tayi tace, "Kaka Doctor ne shima ai".


Gyaɗa kansa yayi yana bin Doctor Said da kallo


A haka dai har Doc. Sa'id ya gama abinda zai mata, sannan ya zauna ana hira da shi


Sosai a nan Kaka ya sake fahimtar akwai wani abu a tsakanin su, inda lokaci ɗaya ya ji farin ciki a ransa, shiyasa ya sake jan Doc. Sa'id a jikin sa, ko ba komi nan da lokaci kaɗan zai ga auren Jikar tasa, ko kaɗan ba ya son ƴan uwan ta su yi aure su bar ta, sosai hatsarin nan ya sake ɗaga masa hankali.


     Ana haka su Aunty Amarya suka zo


Ɗahira taji daɗin ganin su sosai, nan ta sake sakin jiki ana ta hira gaba ɗaya, ga shi sosai take farin cikin yanda ake ba ta kula wa, musamman su Big Dady, da zaran mintuna ƙalilan ya wuce za su taho duba ta.


     Sai yamma duk suka tafi har Kaka.


     Kwanan ta biyar a asibitin tana samun kulawa, kafin aka sallame ta, ta koma gida tana ci gaba da jinya. A haka har ta samu sauƙi sosai, inda ta nemi ta koma bakin aikin ta, amma sai Abbu ya hana ta tunda har yanzu ɗingishi take yi.


    Sai da aka shafe kusan sati Uku kafin ta warware, sannan ta koma bakin aikin ta, zuwa yanzu sosai Ɗahira da Doc. Sa'id suke mutunci, koda aka sallame ta a Hospital be taɓa zuwa gidan su ba, amma kuma suna waya sosai, hakan yasa suka saba, har ita Ɗahira tana tunanin son ta yake yi, sabida yanda yake ba ta kula wa ainun, shiyasa ma ta sake sakin jiki sosai da shi, sai dai har yanzu kalman da take so taji a bakin sa ya ƙi ya sanar mata, ko kaɗan ba ta ƙaunar a sake zaman meeting ba tare da tana da tsayayye ba, sai dai babu yanda zata yi tunda be ce yana son ta ba har yanzu, sai ma daga baya ta gane yana da mata har da ƴaƴa biyu, amma hakan be ɗaga mata hankali ba, a ganin ta idan yana son ta zata iya auren sa, tunda duk wani ɗabi'u na kirki shi yake nuna mata, sai dai lokaci na ta ja babu wannan kalman a bakin Doc. Sa'id, ga shi har yanzu saura sati biyu auren ƴan gidan.


       Kamar yanda suka saba meeting ranan Lahadi, haka wannan Lahadin aka tara su, Ɗahira aka soma tambaya, amma tace musu "bata da wanda take so" maganar ya girgiza su


Kaka yace, "kina nufin wannan Doctorn har yanzu be yi miki ba?"


Kallon Kaka tayi tace, "Kaka ai ba soyayya muke yi da shi ba, it's just Friendship".


"Uwata dama ai ta hakan ne soyayya take ƙulluwa, ke dai kawai ki sanar mana idan da akwai wani abu a tsakanin ku, kar ki zauna ki ce zaki ja mishi aji kinji ko?"


Gyaɗa kanta tayi kafin kuma tace, "amma Abba wlh be taɓa cewa yana so na ba, kuma ma yana da iyalan sa".


Shiru suka yi duk kan su, kafin kuma Kaka ya sake Tambayan Usman da cewa, "to kai kuma Fodio aina taka take?"

"Nima Kaka har yanzu ban samu wacce nake so ba".


"Kana nufin har yanzu maganar da muka yi maka baka ɗauke ta da muhimmanci ba?" Big Dady ya faɗa yana kallon sa


Shiru Usman yayi kansa a ƙasa


Nan Dady ya dinga faɗa kamar zai ari baki, kuma ya ce "dole sai yayi aure da ƴan uwan sa, idan be samo matan ba shi yana da hanyar da zai samo masa"


Kaka ne ya tsayar da shi da faɗin, "ƙyale shi Noor, duk hakan be ta so ba, yanzu dai aci gaba da hidiman biki kar a fasa, su kuma Allah ya kawo musu na gari, lokacin su ne be yi ba babu yanda zamu yi da su".


Daga haka ba'a sake yin wata maganar ba, aka sallami kowa.


     Inda daga ranan gadan-gadan aka ci gaba da hidimomin biki, ko wanne fanni suna nasu, tunda kowa a cikin su zai aurar, illa Aunty Amarya ce kaɗai da babu ita, amma kuma komi da ita ake yi ana Fadila, duk ita take shirin komi, sai ƴan uwan Umman dake nasu, duk da suna yaɓa mata maganganu amma ko bi ta kansa ba ta yi, abinda yafi ɗaga mata hankali yanda gidan duk ya cika da mutane, babu hiran da suke yi sai na Ɗahira, wai "har yanzu bata da mashinshini, tayi kwantai, maza ma tsoron zuwa wajen ta suke yi, bare su furta mata suna son ta." Kowa ba ya lura ba ita kaɗai bace a gidan da baza ayi auren ta ba, har da Usman, shi da yake ma babban su amma yaƙi auren, amma ita kaɗai ake gani


Sanda Ɗahira ta soma jin ƙananun maganganun nan bata wani damu ba, sai dai yanda ƴan uwa suke taran ta da maganar, har wasu suna mata

18 / 20