Chapter 3 Reading Nafisat Return Book Complete By Ummu Dahirah.txt Arewa Novels

Nafisat Return Book Complete By Ummu Dahirah.txt

Author :  Ummu Dahira Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   3 / 20

6K to 9K   out of 58K words

mota ce ta shigo haraban asibitin, a hankali motar take tafiya har zuwa inda sauran motocin suke fake, tsawon mintuna 5 kafin aka buɗe motan ya zuro kyawawan ƙafafun sa kana ya fito a hankali yana rufe motan, kyakykyawar saurayi ne da aƙalla bazai wuce 32yrs ba, fari ne tarrr kamar kalatsa shi jini ya fito don har wani ɗaukan idanu yake yi, yana sanye da Milk ɗin riga me gajeren hannu da ya matse sa sosai, sai Blue Jeans tare da sanya Combat a ƙafafun sa shima blue, yana da yalwan gashin kai kwantacce baƙi siɗik tare da ɗan siririn sajen sa, Kallo ɗaya idan kayi wa Guy ɗin zaka tabbatar da ya haɗu ne tako ina, *USMAN NOOR AL'AMEEN* kenan, *(The Younger Doctor)* yaro kyakykyawa me Izza da Son nuna shi wani ne, ma'aboci Son gayu da son hutu


A hankali ya taka ya soma tafiya cike da taƙama ya nufi inda su Big Dady suke.


Har aka gama taron sannan kowa ya soma tafiya gida, sai yamma duk yawancin ƴan uwa suka soma watsewa sai gidan ya rage daga ƴaƴan Kaka sai jikokin shi suka rage waɗanda basu tafi ba, su ma ɗin a gobe duk za su watse su tafi


Washe gari ƙarfe 05:00pm. Na Yamma gaba ɗaya a halin gidan sun hallara a babban parlour bisa umarnin Kaka


Ɗahira ce tafito daga Part ɗin su don ita bata riga ta tafi ba, tana sanye da doguwar rigan atamfa kalan ja da ratsin Milk da ruwan ƙwai, rigan iyakan ta ƙwaurin ƙafafuwan ta kuma sosai tayi mata kyau ta sake fito da tsantsan kyawunta da kwarjinin ta, sai tayi Rolling da ɗan ƙaramin Veil da iyakan sa kafaɗun ta, Slippers ne a ƙafanta tana tafiya tana latsa waya, hira take yi da freinds ɗinta na Facebook sai faman doka murmushi take yi, gab da ta iso ƙofan da zata sada ta da General parlour taji tayi karo da mutum wanda hakan yasaka wayan ta ya zame ya faɗi ƙasa, a hankali ta ɗago kanta tana kallon sa


haka zalika shima ɗin dai-dai da sanda ya sauke nashi idanun cikin ƙwayan idanuwanta da yafi tsana cikin rayuwan sa


kallon sa kawai take yi babu ko ƙyafta idon


While shi kuma ya ɗaure fuska tamau yaja jikin sa ya wuce, gab da zai buɗe ƙofa ya tsinkayi zazzaƙan muryan ta tana cewa


"Ba ka ganin kayar min da waya ne?"


Cak ya tsaya yana juyowa ya kalle ta da tsananin mamaki da ya nuna a face ɗin sa, ita kuwa a lokacin kallon wayan nata da ya fashe take yi cike da tsananin baƙin ciki sannan ta ɗago kyawawan idanun ta tana kallon sa itama fuskarta a ɗaure


A hankali ya tako ya'iso gaban ta still yana ci gaba da kallon ta, duk da ya daɗe be ganta ba kuma tayi masa girma ainun but be yi tunanin cewa ta kai matsayin da har za tayi masa irin wannan maganar ba, shiru yayi yana ƙare mata kallo yayinda itama ɗin shi take kallo batare da ko alaman tsoro ya nuna a fuskarta ba, abinda ya ƙara ba shi matuƙar mamaki kenan, domin yasan ada babu wanda tafi tsoro sama dashi, idan har zata gan shi ko za taji sunan sa tsoro ne da fargaba suke kawo mata cafka, ko kaɗan bata haɗa hanya dashi bare magana ya haɗa su, duk inda akwai shi to ta haramta wa kanta wurin har sanda zai bar wajen


Kuma hakan ya samo asali ne tun sanda ta tashi da wayon ta take matuƙar tsoron sa, ba don komi ba sai tsananin azaban da yake gana mata da tsanar da yake nuna mata afili ko a ɓoye, shi kuwa tun sanda aka haife ta ya haɗa idanu da ita shikenan yaji ya matuƙar tsanar ta, ba don komi ba sai don ƙwayar idanun ta da ya kalla, sabida idan har zai kalle ta sai yaji faɗuwar gaba me tsanani tare da tsoro wanda hakan ne ya saka mishi muguwan tsanar ta cikin ran sa, sosai cikin ƙwayar idanun ta da suka kasance sky green suke bashi tsoro da fargaba, hakan yasa tun tana ƙarama ko ɗaukan ta ba ya yi, da zaran ya ganta duka ne abinda ke haɗa shi da ita, har zuwa kuwa girman ta da ta gane shi ɗin mugu ne, koda laifi sukayi ƴan gidan gaba ɗaya, to ita yake kamawa ya fanshe kaf dukan da zai yi musu akan ta, ko agaban waye babu wanda zai iya hana sa, kuma koda an hana sa sai ya san yanda yayi ya haɗu da ita ya gana mata azaba, Ɗahira ta tashi cikin tsoron sa matuƙa wanda ya haddasa mata tsanar sa fiye da wanda yake mata, kwata-kwata bata ƙaunar sa bata ƙaunar ganin sa koda jin sunan sa ne, ta saka wa kanta shi ɗin maƙiyin ta ne wanda babu wadda tafi tsana a duniya sama dashi


Wajen shekara 9-10years kenan babu shi a ƙasan, yana can ƙasar Turkey yana aiki acan, tun sanda ya tafi karatu ya zauna can sai dai yazo gaishe su, Ɗahira ta dena jin tsoron sa ne don kawai daɗewan da tayi ba ta ganin shi, and sai kuma girma da yazo mata, yanzu baza ta taɓa juran abinda yayi mata a baya ba, domin ita tana ganin ta wuce matsayin da zata zauna wani banza wanda ba iyayen ta ba ya duke ta bare har taji tsoron sa.


      Sauke kansa yayi kan wayan yana kallo, sai kuma ya mayar da idanun sa kanta yana sake ɗaure fuska ya ɗaga ƙafan sa ɗaya ya ɗaura saman wayan ya soma murje ta da ƙaton takalmin sa da ya kasance tamkar irin na sojoji, babu abinda ake ji sai sautin ƙaran fashewan wayan


Ita kuwa Ɗahira sauke idanun ta kan ƙafan sa tayi tana kallon wayan yayinda taji hawaye sun ciko mata idanu sabida tsananin baƙin ciki da yazo mata iya wuya, still ɗago kanta tayi tana kallon sa cike da zallan tsana da ya nuna a cikin ƙwayan idanun nata


shi kuma hawayen da ya gani a idanun nata shi ya saka shi jin wani farin ciki tare da sanyi a ransa, magana ce a bakin sa yake son faɗa mata amma girman kai da Izza sun hana sa buɗe bakin, illa juyawa da yayi ya nufi ƙofa ya buɗe ya shige..


Ƙaran rufe ƙofan ne ya saka ta ƙyafta idanun ta wanda hakan ne yasa hawayen ta daman zubowa suka sauka kan kuncin ta, ahankali ta sake mayar da idanun ta kan wayanta da ya gama murƙushe ta duk screan ɗin ya farfashe babu kyan gani, wasu zafafan hawayen ne suka soma sintiri a face ɗin ta, tayi saurin saka hannu ta soma sharewa domin baza ta bama kanta daman nuna raunin ta kan shi ba, dole ne ta nuna masa yanzu ba irin da bane, dole ta nuna masa ba ta tsoron sa, kuma duk abinda yayi mata BASHI ne ya ɗauka dole sai ya biya, don haka ɗaukan wayan tayi ta nufi ciki itama da sauri.











_To fa nan ake yinta, bari muga me zai faru?_


_kar ku manta ku suburbuɗo min Comments ta hakan ne zai bani daman ƙara muku yawan Page._


Plz
*Share and Vote.*
[5/21, 9:54 PM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
             *FAMILY DOCTORS*
                         🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
  *NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
                 _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* 🧝🏻‍


*بسم الله الرحمن الرحيم*


*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞

```( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*


*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈


*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_





       . *EPISODE Five*


Da shigan ta darect wajen Kaka ta nufa, ta sami waje kan hannun kujeran dake kusa da Wheel chair ɗin sa ta zauna tana sauke kai ƙasa


"Matata lafiya wa ya taɓa min ke?"


Abinda ya saka yayi mata tambayar ya santa idan har tazo wuri dole sai ta tsokane shi, ƙa'ida ne sai taja masa gemu kafin ta nemi wurin zama


Ɗago kanta tayi tana kallon sa sai kuma ta soma wurwurga idanun ta tana kallon mutanen wurin da duk suka nutsu suna kallon ta, a kan Usman dake zaune kusa da Abbun ta ta sauke idanu, yayin da shi kuwa wayan sa yake latsawa ko sanin Allah yayi ruwanta be yi ba


"Tell me my wife. I can't calm down idan ban san abin da ke damun ki ba?"


Dawo da idanun ta kan Kaka tayi cike da marairaice fuska tace, "Kaka Ya Usman ne ya fasa min waya, kuma ya saka ƙafa ya tattaka shi da gangar".


Kaka salati yayi yana kallon wayan dake hannun ta kana ya mayar da idanun sa kan Usman da har yanzu yaƙi ya ɗago kansa duk da yana jin abinda ake yi, shi har a lakocin mamakin yarinyan yake yi ainun, "yaushe har ta samu ƙwarin gwiwar da har zata kawo ƙarar sa? Lallai yarinyan nan dole ya koya mata hankali".


"Fodio, why did you break my wife's phone?"


Shiru yayi batare da ya ɗago kan sa ba, kuma be dena latsa wayan ba


"Kai ba magana ake maka ba? Are you crazy? Uban meyasa ka fasa mata waya? Ka dawo kenan zaka soma takura mata ko?" Big Dady yayi maganar a zafafe yana kallon sa


Sai a lokacin ne Usman ya ɗago kai fuskar nan a ɗaure yana kallon su, sai dai be iya cewa komi ba


Abba yace, "miƙo wayan mu gani uwata".


Miƙa masa wayan tayi, ya'amsa yana juyawa sai ya ɗago yana kallon ta yace, "Agarin ya yafasa miki wayan?"


"Mun yi karo ne shine ya faɗi, da nayi masa magana shi ne ya dawo ya tattaka min da takalmin sa".


"It's your fault, why did you talk to him then? Stop following her shit please". Abbu yayi maganar yana amsan wayan daga hannun Abba and put it aside


Big Dady said, "why doesn't she talk and break her phone?"


Sai kuma ya mayar da kallon sa ga Usman ɗin yace, "Make sure you buy her her phone and pay for it, idan ba haka ba zan mummunan saɓa maka kana jina ko?"


Gyaɗa kan sa kawai Usman yayi yana kallon Ɗahira da kanta ke ƙasa, kawai tunani yake yi a ransa abinda zai yi mata idan har ta shigo hannun sa


Kaka ne yace, "ya isa haka Lawal (Noor), karka ɗau abinda zafi haka mana, yanzu mu mayar da hankali kan abinda ya tara mu. Alhmadulillah and Allah show us this time to see my grandchildren finish their studies and become doctors now, don haka na tara ku in sanar muku da Albishir da na tanadar muku".


Murmushi yayi yana kallon su ɗaya bayan ɗaya kana yaci gaba da cewa, "Zuwa nan da Sunday motocin ku da na siya muku za su iso sai kowa ya zaɓi wanda yake so, wannan shi ne kyauta na a gare ku, sannan ina jan hankalin ku ku mayar da hankali wajen aikin ku, abinda ya kai ku shi za kuyi ba na son wasa,
May God help you all. May God bless you."


Duk ka parlour'n suka amsa da ameen ban da Usman da har yanzu latsa wayan sa yake yi, nan ɗaya bayan ɗaya suka yi ta mishi godiya kana ya kalli Usman yace


"Kai kuma Fodio, the opportunity I have given you is enough. dole ne ka dawo Nigeria kaci gaba da aiki a asibitin mu, domin baza mu zira idanu ace kana can kana ma Nasara aiki suna ƙaruwa mu nan ka bar mu haka ba".


Usman da ya ɗago kansa yana kallon Kaka, a karo na farko yace, "wai Kaka meyasaka kake son takura min ne? I don't want to work here. I want to.."


Be dire maganar ba Big Dady ya daka masa tsawa, hakan yasaka shi yin shiru yana kawar da kai still fuskan sa ba walwala


"Umarni ake baka ba shawara ba ka ajiye aiki ka dawo nan kaci gaba, karka sake mu ƙara ja'inja da kai". Big Dady ya faɗi maganar da kakkausar murya


Murmushi Kaka yayi yace, "ka bar shi nace Lawal; ba na son kana nuna masa zafi, ai ba cewa yayi bazai dawo ba, abi shi a sannu, kowa zai iya tafiya. idan kuma da me magana ko ƙorafi akan wani abu sai yayi magana".


Kafin Kaka ya rufe baki Usman yayi saurin tashi ya fice, haka sauran ma su kayi ta tatashi suna ficewa ya rage daga Kaka sai su Big Dady





               *****


      Hajja Fatu ce ta shigo parlour'n Hajiya da sallama


Hajiya wacce ke zaune a parlour ta'amsa mata sallaman sannan tayi mata maraba


Zama Hajja Fatu tayi tana kallon Hajiya da murmushi a face ɗin ta tace, "Oh ashe haka abu ya faru? Na zo miki jajen abinda Ɗahira tayi wa Usman ne, gaskiya bata kyauta ba".


Hajiya tace, "Haka ne. amma shima da laifin sa ai, da be taka mata wayan ba baza ta kawo ƙarar sa ba".


Ɗan taɓe baki Hajja Fatu tayi tace, "eh Haka ne kamar yanda ki kace, amma abinda tayi ai be kamata ba, wannan ai kamar tana so ta haɗa Ɗa da uba ne, ko ba kya ganin yanda Mahaifin sa ya nuna fushi dashi? Kuma da ba haka yake nuna masa ba, don Ni kai na shaida ce wajen ƙaunar da yake masa, amma a kan ta ya rufe idanu ya suburbuɗa masa faɗa a gaban ƙannin sa, wannan abun ba yi bane, idan ma uwarta take zugo ta ai zamu gani".


Shiru Hajiya tayi tana sauraron maganganun Hajja Fatu, kuma da alamun sosai zancen yake shigan ta duba da yanda fuskarta ta sauya, domin abinda aka yi wa ɗan nata dama be mata daɗi ba, amma kuma maganganun Hajja ya sake saka ta taji haushi matuƙa


Ita kuwa Hajja Fatu ganin haka ya saka ta sakin wani shu'umin murmushi tana cewa, "Ai sai haƙuri amma dai na san yarinyan nan yanzu hure mata kunne ake yi, ada ai ba ta yin haka duk kuwa da cewa yana dukan ta, amma yanzu tunda ana son haɗa sa da ubansa ai an koya mata yanda zata riƙa kawo ƙarar sa, kin ga hakan zai sa Mahaifin sa ya riƙa fushi dashi".


Hajiya kallon Hajja Fatu tayi don da alamun kalaman nata sun gama ratsa ta sosai tace, "nima naga alamun haka Hajja, sai dai ko ma wa ya koya mata da duk abinda suke nufi da ɗana sai dai ya koma kan su, babu wanda ya'isa ya shiga tsakanin ɗana da mahaifin sa, dole ne ma in ja masa kunne babu ruwan sa da ita tun wuri ya fita harkan ta, ba na son abinda zai saka mu sami saɓani, domin akan ɗana babu abinda bazan iyaba, kowa ya san da cewa ina matuƙar ƙaunar sa; don zan iya yin komi akan sa".


Ajiyan zuciya Hajja Fatu ta saki tana kallon Hajiyan da alamun nuna damuwa a fuskarta tace, "gaskiya ne Hajiya, gwara dai ayi wa tufkan hanci tun kafin magana tasha banban, Allah ya kyauta gaba to, Ni bari in tashi na tafi".


"To shikenan Nagode sai nima na leƙo". Cewar Hajiya da murmushi a fuskarta


Tashi Hajja tayi ta nufi ƙofa ta fice tare da barin Hajiya cikin tunani. Tana fita ta saki wani shu'umin murmushi fuskarta cike da farin ciki, dama abinda take so kenan kuma tana ganin da alamu tarkon ta ya fara kamawa, taku ɗaya zuwa biyu tayi ta tsaya tana juyowa ta kalli ƙofar parlour'n Hajiya, a fili ta furta


"Now the game has started. If I am Hajja Fatu, I will open the heart of everyone in the house. I will make everyone hate you, A'ishah. tare da ƴarkin da kika ƙwallafa rai a kan ta, zan maye gurbin zuciyar kowa da ƙauna ta a ran shi, zaki san kin shigo cikin Familyn da ba na ki ba, mu zuba dani dake.."


"Hajja ke da wace ce zaku zuba? Me tayi miki?"


Da sauri Hajja ta juyo tana kallon ta, wani irin bugawa zuciyar ta tayi, nan da nan tsoro da fargaba ya ɗarsu a cikin zuciyarta har bata san sanda ta fiddo idanu waje ba suna kallon kallo..













_Hhhh to Fans shin wa kuke tunanin wacce Hajja ta gani haka har ta sorata ainun?_


_karku manta da Comments, domin comments ɗin ku shi ke saka na ƙara yawan post._
[5/21, 10:02 PM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTORS*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* 🧝🏻‍


*بسم الله الرحمن الرحيم*


*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞

```( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*


*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈


*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_


*TUNATARWA*
```Manzon Allah mai tsira da aminci, ya yi mana bayani a kan sallah da abin da Bawa yake iya samu. Cewa ya yi, "Yana yiwuwa mutum ya kawo sallah ga baki ɗayan ta amma a ba shi lada wadda ba ta wuce sudusin ta ko ushurin ta ba." Abin da yasa haka kuwa shi ne  rashin nutsuwa cikin sallah.
   Allah yasa mu dace.```




*EPISODE Six*


Murmushi Hajja Fatu ta ƙirƙiro cikin tsananin ruɗewa da son ɓoye halin da take ciki tace, "am..uhmm babu, auhm Ni da wata ƙawata ce da taci amana ta". Taƙarishe maganar tana sake sakin murmushi


Ɗahira kuwa kallon ta kawai take yi, domin kuwa duk abinda ta faɗa ta riga taji, sai dai tayi tsananin mamaki da al'ajabin abinda Hajja Fatu take faɗa akan Mahaifiyar ta da ita kanta. ita ma ɗin nuna mata tayi kamar bata ji maganar nata ba illa sakin murmushi da tayi tace, "But Hajja, why don't you forgive her? I don't see the point in keeping a person

3 / 20