Chapter 2 Reading Nafisat Return Book Complete By Ummu Dahirah.txt Arewa Novels

Nafisat Return Book Complete By Ummu Dahirah.txt

Author :  Ummu Dahira Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   2 / 20

3K to 6K   out of 58K words

tayi kana tace, "ok go, idan ka dawo I'll sent you later".


"To Hajiya".


Daga haka juyawa tayi ta nufi cikin gidan, Matashiyar yarinyan itama tabi bayan ta. koda suka shiga ciki Direct Part ɗin su suka nufa, lokacin da suka shiga cikin ɗan madaidaicin parlour'n su da sallama a bakin su


Fadila ce zaune tana kallo ta'amsa musu


"Welcome Aunty"  Fadilan saying


"Yauwa Fadila, ke kaɗai ce zaune?" Aunty Amarya tace hakan cike da fara'a tana kallon ta


Fadila ta bata amsa da "Eh su Umma na General parlour".


"Ok mu ma ai bamu shiga cikin gidan ba nan muka taho, bari in shiga ɗaki in yaso sai in shiga can mu gaisa".


"Toh aunty".


Wuce wa ɗakin ta Aunty Amarya tayi


ita dama tuni Ɗahira ta wuce tasu ɗakin wanda ya kasance tasu tare da Fadila, tana shiga ta'ajiye Jakan dake hannun ta ta zauna gefen gadon ta, zare ɗankwalin da tayi Rolling a kanta tayi ta'ajiye tana bin gadon ta kwanta, kanta na kallon sama yayin da ta ƙure Cilling ɗin ɗakin da kallo, ta ɗan jima ahaka kafin ta sauke ajiyan zuciya tana lumshe kyawawan idanuwan ta, sai kuma ta buɗe ta tashi zaune tana zare Glass ɗin idanun ta ta miƙe ta nufi gaban Looking glass ta buɗe Locker ta'adana, darect Sif ɗin kayan ta tanufa ta ciro wasu riga da wando na Pakistan Milk and Red colour ta zube su saman gado, kayan jikin ta ta soma cire wa kafin ta ɗaura towel ajikin ta tashige toilet, wanka tayi ta ɗauro alwala ta fito, sai da ta shafa Lotions ajikin ta kafin ta saka kayan ta ɗaura Hijab tayi sallan asar da ta wuce su tun a hanya, bayan ta gama ne ta nufi wajen Looking glass ta zauna tana kallon kanta a madubi, tagumi ta zuba still tana ci gaba da kallon kanta


Fadila ce ta shigo ɗakin idanunta ya sauka akanta, sai ta taɓe baki tana ƙarisawa wajen ta tace, "Are you all right?"


Sai a lokacin Ɗahira ta ɗago kanta tana kallon ta, sai kuma takau da kan tare da faɗin "me kika gani?"


Fadila bata ce komi ba ta juya ta tafi, dama wayan ta tazo ɗauka, tana ɗauka ta fice a ɗakin, wannan shi ne halin su su duk ka biyun basu cika kula juna ba duk da duk kan su suna da ƙyaliya, But kasancewar Iyayen su suna kishi shiyasaka su ma suke taya su a junan su, ga dai shi ɗaki ɗaya suke kwana amma sai su wuni su hantse ba wacce zata kula ƴar uwanta, ba me shiga harkar ɗaya sai sun ga dama, ita dama Ɗahira ƴar ba ruwanta ne, bata cika shiga shirgin da ba nata ba, bata da son hayaniya amma tana da fara'a da kirki, komi tana yin abinta ne cikin class, sai dai alokaci ɗaya baza ka taɓa fahimtar halin ta ba sai ka zauna da ita, Fadila ma haka sai dai wani lokacin tana da yawan wulaƙanci a ɗabi'a, domin miskilancin ta yayi yawa don in bata ga dama ba ko kai uban waye baza ta kula ka ba sai taga dama.


Ɗahira cire tagumin tayi ta soma shafe Baby face ɗin ta da kayan makeup, ita gwanar son gayu ne duk sanda zaka ganta bata rabo da kwalliya, Light makeup tayi wanda ya ɗau fuskarta sosai ya ƙara fito da zallan kyawunta, ba maganar wasa ba Ɗahira tana ɗaya daga cikin kyawawan gidan, duk a cikin ƴan matan gidan zan iya cewa tafi su kyau duk da suna matuƙar kama, sai dai ita yanayinta da komi nata ya banbanta da nasu


Buɗe Lockern tayi ta ciro Glass ɗin ta tasanya Wanda ya zame mata ɗabi'a ko yaushe idan zaka ganta tana tare dashi, sai ta miƙe ta nufi gaban gadon ta taɗau wayan ta ƙirar IPhone 11+, takalmin ta kawai ta sanya ta fito batare da ta yafa komi ajikin ta ba baya ga ɗankwali da ta sanya ta rufe tulin gashinta, tana fitowa parlor ta hangi Fadila zaune har yanzu, sai dai wannan lokacin wayan ta take dubawa, ɗakin Mahaifiyar ta tawuce, tana shiga babu kowa hakan yasa ta fito ta doshi cikin gidan, sai da ta wuce wani dogon corridor kafin ta buɗe wani ƙofa ta shige, ahankali ta soma taka Step tana sauko wa sai gata cikin wani kyakkyawan parlour ƙarami, sai tabi ta wani ƙofan ta fito babban parlor'n gidan da ya kasance cike da mutane kowa sai harkan gaban sa yake yi, tana isa ta gaishe dasu sannan ta wuce wajen ƴan matan dake can gefe zaune, zama tayi gefen Shakira da Salma (ƴa ga Hajiya LAILA)


Shakira CE ta soma cewa, "Now I ask Aunty Amarya where are you? She told me kina Sashin ku ai".


Ɗahira She smiled and said,  "na tsaya wanka ne".


Fiddausi da ta kasance ƙanwar Salma tace, "to ya Naga hannayen  ki rabbana suna dukan cinya, ina tsaraban tamu?".


Kallon ta Ɗahira tayi tace, "What are you eating na baka na zuba? Let me rest for a while, sai ki zo ki taya ni kwance jakan".


Gaba ɗaya wajen su kayi dariya ban da Yusra dake faman latsa wayan ta ko ɗago kai bata yi ba


Shakira tace, "kin ji ƙyale wannan yarinyan bata da hankali, ke da akaje Duba marar lafiya kike zancen tsaraba?"


Ɗage gira Fiddausi tayi tace, "to kuma akace idan anje baza'a yi tsaraba ba? Nasan da cewa waɗannan tsofaffin baza su barta haka ba sai sun haɗo ta da abin lasawa".


Shamsiyya (ƴa ga Hajiya Ikram) tace, "ƙwarai kuwa Fido sai dai idan mu baza'a bamu ba, don naga tunda ta shigo Shakira take ƙifƙifta mata idanu".


Salati Shakira ta saki tana rufe bakin ta tare da zaro idanu, sai suka saki dariya suna shewa, wasu suce "eh su ma sun gani" wasu kuma suce "kai Shamsiyya banda ƙarya".


Dogon tsaki Yusra taja ta miƙe ta wuce abin ta, yayinda duk kan su suka bi ta da idanu kana Salma tace, "Oh, that juju girl, what's wrong with her?"


Dawo da idanun ta Ɗahira tayi gare su tana murmusawa tace, "Ni kun ga tafiya na bari inje in miƙa gaisuwata ga Kaka tunda naga ban ganshi anan ba".


Tafa hannu Fiddausi tayi tace, "ai Kaka yau sai dai yayi haƙuri mun hana sa fitowa, cewa yayi bazai iya da surutun mu ba ya shige ciki ya kwanta".


Tashi Ɗahira tayi tana faɗin "ai gwara haka kar ku ƙara masa damuwa".



Daga haka ta wuce batare da ta kula su da sukayi mata caaa ba.
[5/21, 9:54 PM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
             *FAMILY DOCTORS*
                         🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
  *NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
                 _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* 🧝🏻‍


*بسم الله الرحمن الرحيم*


*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞

```( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*


*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈
        

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_


*NATSUWA A SALLAH*
      _Sallah babbar matsala ce. Ganawa ce tsakanin Bawa da mahaliccin sa, Ubangiji maɗaukakin sarki. Saboda haka ana buƙatar cikakkiyar natsuwa, a tattara hankali wuri ɗaya domin wannan ganawa ta musamman._
     _A cikin ayoyi biyun farko na suratul Mu'uminun ana faɗa mana cewa:_
     _"Lalle ne, muminai sun sami babban rabo, wanɗanda suke a cikin sallar su masu tawali'u ne."_
    _Watau, Muminai wanɗanda idan sun tsaya yin Sallah sai gaɓoɓin su da zukatan su su natsu, babu wani abu mai shagaltar da su daga ambaton zatin Allah maɗaukakin sarki, to, irin su suke rabban ta. Natsuwa cikin sallah da ƙasƙan da kai ga Allah su ne alamun imani na gaskiya da Tauhidi tsantsa, don kuwa ko yaushe bawa yayi kusa da Ubangijin sa sai ya haɗa jin tsoron sa, musamman ma dai a sallah inda yake ganawa da shi, yake tunawa da girman sa._





    *EPISODE Three*


      A hankali ta sanya hannun ta ta soma jan gemun sa


Hakan yasaka ya buɗe idanuwan sa ya sauke a kan ta, murmushi yayi yana kallon ta yace, "Ni dama nasan babu wanda zai min haka sai ke, When did you come back?"


Murmusawa tayi tana janye hannun ta tace, "yanzu babu daɗewa".


Tashi zaune yayi yana faɗin "To ya me jikin da fatan ya samu sauƙi?"


Sai da ta dawo kusa dashi kana tace, "Alhmadulillah Kakus suna gaishe ku kowa da kowa".


"Mun gode muna amsawa".


"My Kakus miss you so much".


Murmushi Kaka yayi yana ɗaura hannun sa a kan ta yace, "nima haka Matata, You have left me alone I miss you, kin bar ni da waɗannan yaran mara su kunya masu ido a tsakar ka ko hiran basu taya ni".


Dariyan ta me kyau ta saki tana jingina kanta jikin Kakan tace, "Kakana kenan! don't worry, I'll be back. hira har sai ka gaji daji, akwai labarin ma da na samo maka".


"Well I hear you tell me".


Ƙofar da aka turo ne ya sanya Ɗahira rufe bakin ta without saying a word. Big Dady ne tare da Abbu suka shigo da sallama, amsa musu su kayi yayinda Ɗahira ta tashi da sauri ta nufi Mahaifin nata ta rungume shi tana faɗin


"Abbu na".


Murmushi yayi yana shafo kanta yace, "to ya kin dawo ko zaki fara?"


Dariya tayi tace, "I'm really missing you, Abbu."


Sai kuma ta sake shi, Then she hugging Big Daddy and said, "Daddy, I'm the only one."


Shafo kanta yayi shima yana smiled and said, "my daughter when did you come back?"


"Now Dady".


"To ya me jikin yaji sauƙi dai ko?"


Gyaɗa masa kai tayi tana faɗin "Alhmadulillah".


Big Dady yace, "madalla haka ake so".


Sannan ya juya yana kallon Kaka yace, "Dad, we're here to talk about new products da za'a shigo dasu."


Kaka yace, "to shikenan".


Abbu da ya samu wuri ya zauna yace, "Mamana bamu wuri za muyi magana".


Big Dady yace, "a'a barta kawai ta zauna".


Murmushi Ɗahira tayi tana kallon Big Dad tace, "bari dai inje in dawo Dady, because I have some things to do".


"Well shikenan Daughter".


Daga nan fita tayi ta rufo musu ƙofa, She did not go back to the General Parlor. Sai tabi ta wani Corridor da zai sada ta da Part ɗin su, tana cikin tafiya ta hangi Baffa ya taho shima ɗin, yayi shigan nan nasa na ɗamewa irin shigan wizaye, kansa babu hula sai kwantaccen gashin kansa da ya sha askin zamani, sosai yayi masa kyau ya sake fito da kyawun sa ainun, hannun sa Sigari ne yake sha, shima yana hango ta ya matse Sigarin a hannun sa ya kashe kana ya tura shi cikin aljihu


Murmushi ya saki lokacin da ya'iso wajen ta yana faɗin "Oyoyo My Lovely sister". Ya nufe ta da ninyan Hugging ɗin ta


Tayi saurin ja da baya tana murmusawa tace, "Oyoyo My Lovely Brother".


Sai ya ɓata fuska and looked at her and said, "Why don't you let me hug you?"


Still tana murmusawa tace, "ka san ba na so fa".


Ɗage kafaɗa yayi yana cewa, "ok to ya Hanya? kin dawo ko ki neme Ni, kinsan nayi missing ɗin ki sosai".


Ɗan huro hanci tayi tana kallon sa, sai kuma ta ɓata fuska tace, "Ya Baffa kamar warin Sigari nake ji?"


Waro idanu yayi yace, "Really?"


Sai ta harare sa tana cewa, "Where is our promise?"


He smiled and touched his forehead and said, "Sorry Sis ban saɓa miki ba ai".


"I don't agree, ga shi kana bani haƙuri".


"Da gaske my Sister na Dena sha, sai dai idan hancin ki ya juyo miki wani warin daban".


Kallon sa kawai take yi, sai kuma tace, "ok I Believe You".


He smiled and said, "so where are you now?"


"I'll go back to our Part".


"Mu je ki taya ni hira mana".


Girgiza kanta tayi tace, "No grave until tomorrow, now I have something to do."


Baffa haɗe hannayen sa yayi yana kallon ta yace, "Please Mana my sis".


Ɗahira ɗan kawar da kanta tayi


ya sake cewa, "Please kinji?"


"Ok Muje".


Murmushi ya sakar mata yace, "yauwa ko ke fa".


Itama murmushin tayi tabi bayan sa suka jera suka nufi cikin gidan.


Suna shiga cikin ɗakin sa tabi ɗakin da kallo tana yamutsa fuska, sai kuma ta kalle sa tace, "Wai Ya Baffa kwana nawa ɗakin nan be ga shara ba?"


Shafo kansa yayi yana kallon ta shima yace, "wlh kin san ban da lokaci kuma ga shi ke kinje anguwa, and na saka Shakira ita kuma kin san halin ta ba wani iyawa tayi ba"


Gyaɗa kanta tayi kana tace, "ok bari in gyara maka yanzu ko".


"Ok my sis let me help you".


Zuwa tayi ta soma kakkaɓe gadon yana tayata suna hira, bayan sun gama suka share ɗakin tare da wanke Toilet ɗin ɗakin, ita tayi Moping shi kuma ya koma kan sofa ya zauna yana latsa wayan sa


Bayan ta gama ta dawo kan hannun kujeran ta zauna tana kallon sa tace, "Yaya na gama maka bari in wuce sashin mu kar Mama taji ni shiru".


Ok my sister, Thank you so much, that's why I love you so much coz you are so kind".


She smiled and said, "Yayana kenan! I love you more than anyone else in this house. Kaima kana da kirki."


Tashi tayi tana nufan saman drower ta ɗau wayan ta tadawo tana kallon sa da shima ya kafe ta da nashi idanun, murmushi tayi masa tace, "Na tafi Yaya".


Miƙewa yayi ya rako ta har bakin ƙofa kana ya koma ciki yana zama saman kujera tare da aza kansa ya kwantar kan hannun yana lumshe idanun sa, murmushi kawai yake saki yana tuna ɗan kyakykyawar fuskarta, sosai yake matuƙar son ƙanwar tasa, kuma so na aure, burin sa kawai a rayuwa yaga ranan da zai mallaki Ɗahira a matsayin matar sa domin tayi masa tako ina, sai dai har yanzu ya kasa samun ƙwarin gwiwar tunkaran ta yace mata yana son ta


Ɗahira tana da wani irin kwarjini da zai yi wuya namiji ya tunkare ta da zancen so, shiyasaka tun tasowan ta bata taɓa yin saurayi ba duk da tana da farin jini sosai na mutane, a lokacin da suka je ABU Zaria karatun su na Degree yawancin Friends ɗin ta maza ne, kuma duk acikin su babu wanda ba so yake kawo sa wajenta ba but basu iya gaya mata.


Shima haka Baffa ya daɗe yana ƙaunar ta yana dakon son ta Amma har yanzu be iya sanar da ita ba, kuma duk abinda tace "yayi ko ya bari" yana bari, shi ɗin ma'abocin shan Sigari ne don wani lokacin har Alcohol yake korawa, amma babu wanda ya sani a gidan sai ita kaɗai kasancewar tana yawan zuwa ɗakin sa koda ba ya nan, wani lokacin sai tazo ta kwanta tayi barcin ta, yawan kusancin su dashi ne ya saka tasan wannan sirrin nasa, kuma tun sanda tace ya dena sha ya dena, sai dai har yanzu Sigari ne be dena gaba ɗaya ba, amma idan har zata gani zai yi ƙoƙarin ɓoyewa.





        *WASHE GARI*


         Ranan ne ya kasance ranan Walima, kowa idan ka gani agidan cikin farin ciki yake, sosai gidan ya sake cika sai hada-hada ake yi, har mutanen Maiduguri tushen su kenan duk sun hallaro, duk girman gidan nan sai da aka cika sa da mutane


Ƙarfe 02:00pm. Aka soma tafiya *AL'AMEEN FAMILY HOSPITAL* kasancewar acan ne za'ayi taron, haka motoci manya-manya suke ta jidan mutane suna kai su.










_Kar ku manta da_
*Share*
*Comments*
*Vote*
*Like.*
[5/21, 9:54 PM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTORS*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏻‍


*بسم الله الرحمن الرحيم*


*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞

```( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*


*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈


*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_


*NATSUWA A SALLAH*
_Manzon Allah mai tsira da aminci, ya ce, "sallah ba kome ba ce illa miƙa wuya da tawali'u..." Kuma ya ƙara da cewa, "Bawa bai samun ladan sallar sa sai gwargwadon abinda ya hankalta daga sallar." Watau, gwargwadon natsuwar mutum cikin sallah gwargwadon darajar da yake samu gun Allah. Don haka ne ma ma'aikin Allah ya ce, "Allah ba ya juya wa Bawa baya yana cikin sallah matuƙar bai waiwaya ba; idan ya waiwaya kuwa, sai Allah ya bijire masa."_
_Babu abin da yake kawo waiwayo cikin sallah kuwa sai gafalar Bawa da muƙamin Ubangijin sa, watau ya zama tamkar wanda ya tsaya yana ganawa da Ubangijin sa alhali zuciyar sa tana shagale da wani abin dabam. A kan wannan matsala ne Allah yake ce wa Manzon sa, da al'ummar sa ma, a cikin suratul A'ARAF aya ta 205:_
_"Kada ka kasance daga gafalallu."_
_In muka lura sai mu ga cewa ta ya ya kuwa gafalalle zai iya tunawa da muƙamin Ubangijin sa yana cikin wannan hali na rashin kula har wani abin tsoro ya auku? Bugu da ƙari, daman can ga shi Allah ya yi umarni a cikin suratul Ɗ.H., aya ta 14 da cewa:_
_"Kuma ka tsayar da Sallah domin tuna Ni"._
_In mutum ya Yi haka, ana fata ya rabban ta._
   _Allah yasa mu dace._





*EPISODE four*


    Babban haraban asibitin cike yake da mutane bila adadin, mutane ne kamar tsaki kama daga yara manya masu kuɗi da manyan likitoci duk an gayyace su, har ta da gwamna Malam Nasiru El Rufa'i sai da aka gayyace shi wajen, komi ana yinsa ne akan tsari gunun sha'awa


Ɗahira, Shakira, Yusra da Fadila can na hango su wajen zaman su daban, sosai su kayi kyau cikin shigan su na material fari ƙal da akayi masa ɗige-ɗigen Coffee colour, ɗinkin doguwan riga akayi musu fitted, sai suka yane kan su da Goldeen Veil tare da sanya Hill shoes shima Golden, sosai su kayi matuƙar kyau kamar ka sace su ka gudu sai faman haskawa suke yi kamar taurari


Nan akayi ta gabatar da komi cikin girma da arziƙi, daga ƙarshe aka gabatar dasu a matsiyin waɗanda ake taya murna tare da sauran sabbin ma'aikata da za'a ɗiba.



      Wata kyakykyawar Farar

2 / 20