Chapter 20 Reading Nafisat Return Book Complete By Ummu Dahirah.txt Arewa Novels

Nafisat Return Book Complete By Ummu Dahirah.txt

Author :  Ummu Dahira Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   20 / 20

57K to 58K   out of 58K words

sa, yawan jama'a bazai bar sa ganin su ba, shi duk a tunanin sa da ita ake bikin

Dole aka ɗaura mata drip, sabida sosai take jin jiki, duk hankalin su Kaka ya tashi matuƙa, irin su Hajja Fatu kuwa murna fal ciki, domin duk a ganin su baƙin cikin rashin auren ta ne ya saka mata damuwa


Su ma su Kaka abinda suke tunani kenan, shiyasa tayi matuƙar ba su tausayi, a ranan Kaka ya zauna da ƴaƴan sa meeting, inda suka yanke shawaran kawai za su haɗa auren Ɗahira da Usman, tunda dai baza su zuba musu idanu suna kallon su sun ƙi aure ba, sai dai babu wanda ya tayar da zancen, sun bari sai nan da kwana biyu, lokacin an gama huta wa da bikin nan da suka yi.


Itama Ɗahiran sosai take samun lafiya, tunda ana kula da ita sosai

Baffa dai sau biyu yana zuwa gaishe ta, yanda Ɗahiran ta nuna masa ne, yasa shi jin daɗi, domin ko kaɗan bata sauya masa daga yanda suke da ba, gaba ɗaya ta nuna masa tamkar wani abu be faru tsakanin su ba, duk da a zuciyarta tana jin ƙaunar sa. Hakan sai ya mishi daɗi sosai, shima sai ya saki jikin sa yana jan ta da hiran da suka saba

A ranan na ukun ne da zai zo, suka taho da Sa'adatu don ta duba ta, amma daƙyar ta taho, don sai da suka yi faɗa da Baffa ɗin, da cewa tayi, "ba ta zuwa" amma da ya nuna mata ɓacin ran sa, dole ta biyo sa

Suna zuwa tayi mata ya jiki ta miƙe zata tafi, sai ta ga Baffa ma gyara zaman sa yake yi be da ninyan tafiya, ta kalle sa tace, "a'a ya haka kuma? Kai da za mu tafi kuma kake shirin zama?"

Kallon ta yayi, sai ya harare ta, sabida akwai Aunty Amarya a wajen, dayake suna zaune a Parlour ne har Ɗahiran. Kawar da kansa yayi ya soma jan Ɗahira da hira

Sai ta ja dogon tsaki tana faɗin, "Da kai fa nake yi ka zauna ina magana?"

A fusace Baffa ya kalle ta yace, "Ni sa'an wasan ki ne wai Sa'adatu? Ni ne zaki tasa a gaba sai ka ce ɗan ki?"

Murguɗa baki tayi ta hau jijjiga jiki, sai dai bata iya cewa komi ba sabida ganin yanda ya taso mata a fusace

Aunty Amarya ce tace dashi, "ya isa haka Miji na, tashi ka tafi tunda baka san me take buƙata ba, ka je kaji ka dawo anjima".


"But wlh Aunty Amarya this girl..."


"ya isa tashi ka je kaji?" Ta katse sa da faɗan haka cikin lallami


Miƙe wa yayi yana kallon Ɗahira da ta kawar da kanta yace, "Sweet sister I'm leaving, I will be back soon, we have something to talk about, Allah ya ƙara lafiya kinji?"


Gyaɗa masa kai tayi, a wannan karon tana kallon sa tayi masa murmushi tace, "to Yaya na, na gode".


Fuuuu Sa'adatu ta wuce ta bar parlour'n


Shima bin bayan ta yayi bayan ya sake yin ma Aunty Amarya sallama


Aunty Amarya ci gaba tayi da ɓare lemon dake hannun ta, a ranta sosai take mamakin abinda yasa Sa'adatu take kishi da Ɗahira, domin tuni ta gane abinda ke zuciyar ta, sai dai kuma bata san cewa da Baffa Ɗahiran tayi soyayya ba

Ɗahira kuwa gyara wa tayi ta kwanta kan two sittern da take kai, tana lumshe idanu tare da faɗa wa duniyar tunani, ita ko kaɗan abubuwan da Sa'adatu take yi ba ya damun ta, amma duk idan ta tuna da yanzu ita ce a makwafin Sa'adatu ɗakin Baffa, abun na mata zafi sosai a zuciya, har ta zubar da hawaye.




⚫⚫⚫⚫


Kai tsaye gidan su suka nufa, Sa'adatu tariga shi isa, inda ta zauna a kan ɗaya daga cikin kujerun parlour'n ta tana faman karkaɗa ƙafa, sosai ta cika tayi maƙil tsaban kishi, ita ko kaɗan yanzu ba ta ƙaunar Baffa ya raɓi Ɗahira, gani take yi hakan zai saka mutanen gida su san me ke faruwa tsakanin su, kuma ta san ako yaushe za'a iya kawo mata ita a matsayin kishiya, tunda ita ɗin ƴar uwan sa ce, baza su yi la'akari da daɗewan auren ba ko rashin sa.


Shigowar Baffa ne ya dawo da ita daga guntun tunanin da ta afka


Kallon ta yayi kamar yanda take kallon sa yace, "ke wai Sa'adatu wani irin baƙin kishi ne kike son ki shigo min da shi gida na? Wato rashin hankalin naki ya kai har ki shiga tsakani na da ƙanwa ta? A kan me zaki riƙa min haka? Ke fa baki isa ki hana Ni abinda nayi ninya ba, kuma idan Allah yace Ɗahira mata ta ce, wlh daga ke har wacce take ɗaure miki gindin baku isa ku hana ba".


Sai kawai yaga ta fashe masa da kuka, cikin kukan take cewa, "wlh tallahi kamar a kunnen Hajja, wato kana nufin Ni da ita ba mu isa mu hana ka kula wancan yarinyan ba ko? Kenan Hajja bata da mutunci a wajen ka? Da kake cewa kar na shiga tsakanin ka da Ƙanwar ka; ai ba Ni ce na raba ku ba, wlh na gaji da abinda kake min, tunda ba ka gani na da mutunci ƙarar ka zan kai". Tana ƙare zancen nata ta tashi fuuuu ta fice tana ci gaba da kukan ta


Direct cikin gidan ta nufa, inda ta wuce Part ɗin Hajja don Kai ƙaran sa.


Ta bar sa nan tsaye da sakakken baki, sosai ransa ya ɓaci da abinda ta faɗa, "kenan shi be da ikon da zai mata faɗa, sai ta ɗibi ƙafafu ta kai shi ƙara wajen Mahaifiyar sa? Anya zai iya wannan auren kuwa?"











_to ba mu dai sani ba baffa. 🤷_

20 / 20