Author : Ummu Dahira Category : New Hausa Novels 2026
Shaƙiyanci suna yaɓa mata magana, sai abin ya soma damun ta, amma babu yanda zata yi haka take barin abun a ranta, duk da ita bata cika iya ɓoye damuwa a ranta ba, ko ya ya ne idan har tana da damuwa sai ka gane..
Gida fa ya sake cika maƙil inda har an soma events, duk da ba kowa bane ke wajen, wasu sun tafi can Katsina, Hajiya Laila ma can ta tafi, sai su Firdausi da sauran ƴaƴan ta masu aure da suka zo nan, Aunty Zainab ma da ita da Aunty Amarya, ana gobe suka wuce can a bisa umarnin Kaka, tunda ba za'a bar Hajiya Ikram ita kaɗai tana biki babu ƴan uwa ba, kowa ya zo nan ya shantake, wasu ma zuwa gobe ranan bikin za su wuce idan za'a kai Fadila can, sai su kwana biyu wasu kuma su yi kwana ɗaya.
Tun ana kwana biyu Sa'adatu ta koma Legos, sai ranan bikin za a kawo ta.
⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫
Dafa ta Fadila tayi, hakan yasa tayi firgigit tana kallon ta
"What are you thinking sister, I'm talking to you are you quiet?"
Murmushin yaƙe Ɗahira tayi, sai ta gyaɗa kanta tana son mayar da hawayen dake cikin idanun ta tace, "nothing".
Cike da tausayin ta Fadila tace, "don Allah ki dena saka damuwa a kan maganganun su Inna, ko ma su waye ne zasu yi miki gori don Allah ki dena saka damuwa kinji, ke baki ga yanda kika faɗa bane? Ana bikin mu amma gaba ɗaya kin tsame kanki a cikin mu".
Shiru Ɗahira tayi, don bata san me zata ce mata ba
Sai itama Fadilan tayi shiru, sai dai bata tashi a wajen ba. Tsawon lokaci suna a haka kafin Fadilan ta kalle ta tace, "Sister, there is something I want to tell you, akwai maganar da naji wajen Hajja da Shakira, shiyasa naga dacewan in faɗa miki".
_What do you think Fadila will tell her? 🤔_
_mu je zuwa yanzu aka soma._
[6/8, 8:45 AM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR'S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* 🧝🏼
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
```( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattapad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_
*EPISODE 29 & 30*
Idanu Ɗahira ta zuba mata tana jiran taji me zata faɗa
Fadila tace, "na lura a gidan nan Hajja ba ta ƙaunar ki, kuma ba ita kaɗai ba har ta da Shakira, domin tasha sanar dani abu game dake domin ta haɗa mu faɗa, ban taɓa biye mata ba, sabida narigada nasan abinda ke cikin ranta. A kwanaki biyu da suka wuce na ji su suna zancen ki, maganar rashin samun tsayayye ne da baki dashi, suna faɗin hakan yayi musu daɗi, har suna cewa Allah yasa ma ki dauwama a haka baza ki taɓa aure ba, sannan Hajja take cewa koda ma kin samu, ita tayi alƙawari baza ta taɓa barin ki ki zauna da mijin ki lafiya ba, duk yanda za'a yi sai tayi don raba ki da Mijin, sai ta mayar dake ƙaramar bazawara idan kin yi aure, idan kuma baki yi ba, zata bi duk hanyan da taga zata iya wajen hana ki aure".
Tun soma maganar nata Ɗahira take tsiyayar hawaye, sosai zuciyar ta ke suya da zancen nan, "wai dama tsanar da Hajja take mata har ya kai haka ne?"
Bata san cewa a fili tayi tambayar ba, sai jin muryan Fadila tayi tana cewa, "yafi haka ma, baza ki san haka ba sai nan gaba kaɗan idan kin san wani sirrin. Sister Ni abinda nake roƙon ki dashi har na sanar miki da zancen nan, saboda ki san maƙiyan ki ne, ki san yanda zaki zauna da su, sannan ki san hanyar da zaki ɓullo wa al'amarin, ki riƙe addu'a domin baki san ta ina za su biyo miki ba, don Allah ina sake roƙon ki, duk wanda zaki aura Sister, ki kasance me mishi biyayya, ki zauna da mijin ki lafiya ko don ki ba ma Maƙiya kunya, Ni ƙanwar ki ce, but I beg you by God, ki tuna magana ta ko bayan ba na nan".
Sosai a wannan lokacin Ɗahira take hawaye, har da shashsheƙan kuka
Itama Fadila tuni nata hawayen sun zubo, cikin rawan murya tace, ""I miss you Sister, please .. please ki nemi kariyan Allah domin ki guje wa afkuwar wani abu, ba na son wani abu ya same ki ta silan maƙiya.."
"Keee Fadila meye haka? Me kuke yi haka? Kukan meye?" Ƙanwar Umma da suke kiran ta Inna Sailuba take faɗar hakan, shigowar da tayi
A tare suka bi ta da kallo, sai dai babu wanda ya tanka mata, illa ƙoƙarin share hawayen da suke yi
Tsaki taja tana bin su da kallo itama tace, "tashi dalla kin zauna ta saka ki gaba tana kukan muna-furci, idan ba ta son rabuwa dake ne itama tayi auren mana, in ba hassada kuma take miki ba. Ki tashi nace ga Naja'atu can ta dawo ku je gidan me lallin".
Kamar yanda basu ce mata komi ba ɗazu ɗin, haka yanzu ma babu wanda ya tanka mata, sai dai Fadila ta miƙe tsaye ta wuce zuwa waje. Itama Inna Sailuba ɗin sai bin bayan ta tayi tana sababi har da kumfan baki, "wai Fadila ta raina ta, tana faɗa mata gaskiya amma Ɗahira ta fi ta a wajen ta". Duk da kuwa tasan cewa halin Fadilan ce ƙyaliya da Miskilanci. Kankace me sauran jama'an da ke zaune a Parlour sun amshe zancen, nan suka soma aibata Ɗahira da ita da uwar ta tunda sun san ba ta nan, suna me zagin su da yin musu gori akan Ɗahiran.
Lumshe idanu Ɗahira tayi tana me sake jin zafi sosai a ranta, sosai take kukan zuci babu me rarrashin ta. Ganin baƙin cikin su zai iya kashe ta, sabida ita bata saba jure irin waɗannan ƙananun maganganun ba, sosai suke damun ta a zuciya, sai damuwar kuma ya haifar mata da ciwo, shiyasa ta tashi tafito ta nufi cikin gidan, kasancewar yamma ta soma shiyasa babu wasu mutane sosai a waje, ta inda tasan ma baza ta same su ɗin ba ta nan tabi ta wuce sashin Hajja
Akwai mutane sosai a parlour'n suna zazzaune suna aiki, kasancewar parlour'n akwai duhun magriba har ta wuce ɗakin Baffa babu wanda ya kula da ita, bare ma a shaida ta, bare kuma gidan biki kowa sha'anin gaban sa yake yi.
Keey ta saka ta buɗe ƙofan bayan ta taɓa taji a rufe yake, ta tura ta shiga sannan ta mayar ta rufe, Direct Kan gadon sa ta nufa ta faɗa ta soma rusa kuka, kawai so take yi ta fitar da duk wani ƙuncin da ke damun ta, domin kuwa muddin bata fitar ba, dole ne tayi ciwo. Sosai tayi kukan babu me rarrashin ta, sai da ta gama ta miƙe zaune ta buga tagumi tana me ci gaba da tunanin zuci
"Ita bata ga makusa a jikin ta ba, duk inda mace me ji da class, me ji da kyawu da tsafta, gami da ilmi ta kai, to meyasa har yanzu ta rasa masoya? Meyasaka har yanzu ta rasa wanda zai ce mata zai aure ta? Ta san tana da farin jinin jama'a, kama daga mazan har matan, babu wanda ba ta harka da su, amma kuma babu wanda ya taɓa buɗe baki yace mata ya zo gare ta ne don soyayya, wanda kuma zai kai su ga aure, sai dai su zo a matsayin tana burge su, tunda tana burge su why baza su sanar mata suna ƙaunar ta ba? Ko kuma dama tana da makusa ne wanda be dace ta samu mijin aure ba?"
Runtse idanuwan ta tayi hawaye na sake silalo mata, cikin muryan ta da ya dishe sosai sabida kukan da tasha tace, "Allah gani gare ka, kai kace a roƙe ka zaka amsa, har yanzu bazan gajiya ba, kuma na san cewa kana ji na. Allah ka zaɓa min abinda yafi alkhairi a rayuwa ta, idan har auren nan ne alkhairi a gare Ni, ya Allah ka zaɓa min miji na gari, idan kuma babu alkhairi a tare da Ni, ya Allah zan rayu ina me gode maka, saboda haka ka tsara min rayuwa ta. Zaɓin ka kaɗai nake nema ya Allah, a duk sanda kaso ikon ka a kaina, a lokacin Ni kuma zan amsa ina me godiya a gare ka ya Allah, Allah na tuba ka yafe min". Ta ƙare maganar tana sakin wani sabon kukan
Ta jima tana yi kafin ta tsakaita tana me miƙe wa, sai hannun ta ya bigi drowan gadon wani abu ya faɗo, kasancewar ɗakin da duhu sai ta saka hannu zata laluba, hakan yasa ta kama wayan da tayar hannun ta na latsa wa a rashin sani, take a nan hasken ta ta kawo
Ƴar ƙaramar waya ce Nokia, wayan tabi da kallo, kamar ta ajiye sai kuma zuciyar ta ta bata umarnin latsa wa, take a nan ta danna ta ta cire ta a keey, nan ya bayyana wajen Text message, kasancewar daga wajen ne ba'a fita ba ta shiga keey
Rawa jikin ta ya soma saboda ganin text ɗin da ake turo mata, take ta koma ta zauna tana ci gaba da karanta wa, tabbas gaba ɗaya text ɗin da ake turo mata ne anan
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un... Kar dai ace Ya Baffa shi ne Masoyin ta na ɓoye?" Tayi maganar a fili tana ɗaura hannun ta ɗaya dake rawa a baki
"Ya Allah..." Ta sake faɗa tana kai idanun ta dake tsiyayar da hawaye kan wayan, ci gaba da karanta text ɗin tayi, sai kuma ta koma ta shiga ta duba Numban, take a nan taga Numban nata ne
Lumshe idanu tayi tana jin wani irin raɗaɗi a ranta, babu abinda ya faɗo mata a rai sai text ɗin sa na ƙarshe
"Hajja..!" Ta furta a laɓɓan ta tana me buɗe idanun ta
"Why Hajja? Me nayi miki? Dama ke ce kika hana Ni aure a wannan gaɓar? Ke kika raba ni da Masoyi na na haƙiƙa? Me nayi miki da zafi haka?".
Miyau ta haɗiye sabida jin wuyan ta ya cinƙushe da tuƙuƙin baƙin ciki, cikin kuka tace, "Ya Baffa meyasa ka kasa bayyana min kanka a matsayin wanda kake so na? Meyasaka ka zaɓi ɓoye min kan ka? Ashe dama da kai ne nake soyayya ban sani ba? Tabbas da baka ɓoye min kan ka ba, da duk haka be faru ba, ga shi Hajja taci galaban raba mu. Meyasa?.." ta kasa ƙarisa maganar dole tayi shiru
Tun soma maganar nata Baffa ya buɗe ƙofan ya shigo, yana tsaye bakin ƙofan yana jin komi, cikin tsananin ƙaunar ta tare da zallan tausayin ta yace, "Ƙaddara ce Ɗahira".
Saurin ɗago idanuwan ta tayi tana bin sa da kallo, duk da kuwa bata ganin sa sosai, amma hakan be sa ta kawar da idanun ta a gare sa ba
Yaci gaba da faɗin, "Nima sai daga baya na gane nayi wauta, tabbas da na bayyana soyayyar ki a fili, da duk hakan be faru ba, da mutanen gida sun goya mana baya, da Hajja bata ci galaba a kan mu ba. sai dai yanzu kuma babu yanda zan yi, sabida Hajja tarigada tayi min iya ka da hakan, idan har na bari wani yaji, tsinuwar ta shi ne zai ta bibiya ta, ban san ya zan yi ba Ɗahira, amma wlh ina tsananin ƙaunar ki, ke nake so a zuciya ta, kuma har na mutu bazan taɓa dena son ki ba".
Da gudu ta tashi tana toshe bakin ta, ta zo ta wuce sa ta bar ɗakin
Shima be hana ta ba, ko motsi ma be yi ba, illa runtse idanun sa da yayi hawaye na zubo masa kan kuncin sa.
⚫⚫⚫
Direct ɗakin Maman ta tawuce, ta shiga ta kulle kan ta ta hau rusa kuka babu ji babu gani, kukan da ke taɓa mata zuciya, yake ƙara mata raɗaɗin da ke cinkushe a zuciyar ta. Sosai tayi kukan wanda har ya haifar mata da ciwon kai me tsanani
Ita da kanta ta rarrashi kanta tayi shiru, sai dai duk yanda taso ta danne abun da take ji a ranta, ta kuma jure baƙin cikin dake zuciyar ta, ta kasa, gaba ɗaya rauni ne a zuciyar ta, waye zai rarrashe ta? Waye zai kwantar mata da hankali har taji sanyi a ranta? Ya faɗa mata tayi haƙuri haka ƙaddaran ta take?
Lumshe idanuwan ta tayi, hawayen dake maƙale a cikin idanun ta suka zubo saman kuncin ta, ta saka hannu ta share tana me miƙe wa zaune, kanta ta riƙe tana jan majina
"Allah Sarki Mamana, da ace kina nan ke ce zaki share min hawaye na. Meyasa ne Ni kuwa bani da Sa'a a rayuwa ta? Menene aibu na? Shin me na tare wa Hajja da ta tsane Ni har haka? Ya Allah.. ka saka min juriya domin in tsallake wannan jarabawar taka".
Miƙe wa tayi ta wuce Toilet ta ɗauro alwala ta fito, sallan magriba da isha'i ta gabatar, sannan tayi shafa'i da wutri, ta jima tana kwararo addu'a tana hawaye kafin ta shafa ta miƙe
Ta san Abbun ta ba anan zai kwana ba, sabida jama'a masu biki, kuma dama Aunty Amarya ce ke dashi, shiyasa ta kwanta a ɗakin tunda tasan ba ma zai zo Part ɗin ba.
Daƙyar a ranan barci ɓarawo ya ɗauki Ɗahira.
⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫
Ranan Saturday 25 March 2021. Aka shaida ɗaurin auren *AL'AMEEN ABUBAKAR AL'AMEEN* tare da Amaryan sa *SA'ADATU ABDULLAHI*
*SHAKIRA ABUBAKAR AL'AMEEN* da Angon ta *SAHABI MAHMUD*
Sai *YUSRA NOOR AL'AMEEN* tare da Angon ta *SULAIMAN HABIB*
*FADILA AL'AMEEN AL'AMEEN* da Angon ta *KHABEER ALH. MUNIR.*
Ɗaurin auren da ya tara dubban jama'a ta ko ina, sai dai mu ce Masha Allah.
Zuwa huɗu ko wacce aka kai ta ɗakin ta bisa umarnin su Big Dady, Fadila aka wuce da ita Katsina da sauran jama'a. Yusra kuma da Shakira duk a nan Kaduna za su zauna, gidan Yusra ma ya fi kusa da gidan su, kuma duk ka su biyun za su ci gaba da aiki a Hospital ɗin su, sabida sai da aka yi yarjejeniya da mazajen nasu kuma sun amince.
Inda Baffa zai zauna kusa da gida ne, gini ne da aka yi musu shi da Usman a gefen gidan su, ga Gate ɗin gidan su ga nasu, sai dai kuma ta ciki a kwai ƙofan da aka yi wanda zai riƙa kai su cikin gidan su, ba sai sun yi wahalan fito wa ta Gate ba, wannan duk tsarin Kaka ne, shi ya siya filin kusa da gida, sabida yafi so iyalan sa su zauna waje ɗaya, har filin Fadil da yake ƙarami akwai shi an ajiye masa, idan ya tashi aure sai ya zauna a nan ɗin
Part ɗin Baffa dana Usman suna kallon juna ne, komi iri ɗaya aka yi musu, ɗakuna uku ko wanne da Toilet a ciki, sai babban Parlour da kichen a ciki da kuma wani Toilet, sannan idan ka fito waje ko wanne yana da faranda a ƙofan ɗakin, komi dai masha Allah, domin ba kaɗan ba an kashe kuɗi a ginin nan, su Big Dady duk suka yi musu komi babu ko ƙwandalan su, kayan ciki kuma suka bar musu su yi da kan su
To Part ɗin Baffa dai ya tsaru sosai, domin zance kuɗi yayi kuka a nan, iyayen Sa'adatu sun kashe mata kuɗi sosai, don ganin sun fito da ɗiyar su, itama zuwa dare aka kawo ta, can babban gidan aka fara kai ta, sai da aka kai ta wajen Kaka yasa mata albarka, sannan su Big Dady suka haɗa su da Baffa suka yi musu nasiha sosai. Daga nan kuma suka wuce wajen Hajja, inda itama tayi wa Baffa faɗa da nasiha sosai, akan "ya riƙe ta da amana, kar taji kar ta gani wajen ya muzguna mata, domin ita ɗin ƴar uwan sa ce, idan kuma aka ce ta kawo ƙarar sa, to wlh sai ta ɓata masa rai".
Shi dai be ce komi ba, har ta ƙarashe faɗan ta ta sallame su, suka nufo gidan su.
Sai mu ce Allah ya ba da zaman lafiya Amare.
⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫
Ɗahira dai taci bikin nan ne ba a daɗin rai ba, domin kuwa fama take yi da matsanancin zazzaɓi me zafi, kowa be san halin da take ciki ba, ko Kaka da take zuwan mishi hira, ƙin zuwa tayi bare ya san me ke faruwa da ita, shima be neme ta ba tunda ya san sha'anin biki ne
Fadila ita ke matsa mata tasha magani, domin sosai take bata tausayi, ita duk a ganin ta tana damuwa ne saboda rashin auren ta, bata san cewa Ɗahira ta kasa jure rabuwan da suka yi ne da Baffa ba, har yanzu abun na cin mata rai, shiyasa dole ciwo ya kamata.
A haka Aunty Amarya ta dawo ta tarar da ita babu lafiya, hankalin ta yayi matuƙar tashi, duba da yanda ta dawo ta ganta gaba ɗaya ta rame a ɗan kwana biyu kacal da ba ta nan, babu wanda ya duba lafiyan ta, har kuka sai da Aunty Amarya tayi, nan ta kira Abbun su take sanar mishi
Shima hankalin sa ya tashi sosai, tare da ɓacin rai da ya nuna a kan Umma, tunda ai ita ce take zaune da su, amma ta kasa kula da ita, ga shi gida ya hargitse da ƴan biki, shi kansa ba kwana a Part ɗin yake yi ba, kuma ko da yana son ganin yaran