ANA BARIN HALAL Hausa Novels by Anty Nice.doc

Author :  Auty Nice Category :  Hausa Novels 001

Chapter   2 / 46

3K to 6K   out of 137.2K words

Baban mu kuma baya yarda, don shi yace bai yadda da asiri ba, shiyasa take tsula tsiyar ta yadda taga dama, gashi ko kaWan Aunty Rakiya basu shiri, inda Allah yayi taimako kuma tsoro da shakkan Aunty Rakiya ta keji.



Yaya mohd muna tsananin shiri da shi, domin komai nashi ni yake nema, muna jss 3 nida Habiba aka fara maganan auren shi da wata budurwar shi ?ar maiduguri, ?anwar abokin shine, tazo service bch sai ta zauna a gidan mu, sunan ta Bintu, gaskiya zan iya cewa na daWe banga mace mai kyau da tsarinta ba, gata ?ar gayu na nuwa, naji daWi da farin ciki danaji Yayah na danafi so zai auri Aunty Bintu, a site Win Ummin mu ta zauna, gashi tana bala'in kyautata mana, kullum da safe idan tana shirin fita inda take service bana gajjiya da ganinta, ga wani ?amshinta kaman nayi yaya nakeji.
"Aunty nice ranan dana fara ganin ki naji kaman da Aunty Bintu na haWu, saboda ?amshin kanuri da naji kinayi, sai naji kema ina ?aunar ki kwatan kwacin yadda naso ta" Ayshaa ta faWa tana kallo na, nima cikin ?ara walwala fara'ar fuskata nace, "Aysha kina koWani dayawa fa, yanzu matan *MUYI NISHA?I* idan sunji ki sai su Wauka haka nake fa da ?amshi, har naje mrs Al'ameen Da takwararki Aisha jewal, da maman fodio sukawo mun ziyarar bazata" na faWa ina ?ara murmushin fuskata.

Itama Aysha cike da fara'a a fuskarta tace, '"gaskiya ne ae Aunty nice, nidai haka kawai kina burgeni kuma ?amshin ki yayi daWi, dole ma ki haWani da wacce kike sayan turarenki a wurinta, duk da dai Aunty Bintu bata rageni da turare ba har yanzu.


lokacin da maganan auren Yayah mohd da Aunty Bintu ya taso gadan-gadan, lokacin tagama Service har ta koma Maiduguri, Ummin mu ta wakilta Adda ?ar gaban Mama da wata ?anwar Ummin mu wacce ake ce mata Goggo, itama anan bauchi take aure, suka wuce lagos domin acan Aunty Rakiya take aure lokacin, acan suka haWu aka haWo kayan aure na garari, kinsan auren ?an maiduguri da ?aryan kaya dai Aunty nice?

Girgiza kaina nayi alaman hakane,ina ?ara saurarenta, domin ni gaskiya bana gajjiya da kallon Ayshaan nan, don ni mace mai yanga burgeni takeyi sosai, ido na zura mata ina sauraranta.


Kaman tasan abinda yake raina, sai ta sake juya kyawawan idon ta cike da rausaya ta kalleni tana ?ara gyara zaman ta, "kina ji ko Aunty Nice, lokacin da suka dawo daga haWa kayan auren ranan anyi tashin hankali agidan mu da Mamie, domin dama tana cike da bala'in tafiya da Adda da akayi lagos Winnan, tana jin haushi ba'aje da ita ba, ganin kayan kuma ta tada wani bala'in kan wai ana so duk kuWin Baba ya ?are, don ita bata yadda Yaya bane ya haWa wannan uban kayan, ta manta Yaya Mohd a NNPC yake aiki, kuma mutumin nan yakai 5years yana aiki a wurin, gashi darajan Baban mu yasamu wuri mai mai?o, Yaya Ahmad Barrister ne, shima yana Abuja da zama, Yaya Umar ne kawai Walibi, don shi kam da saura.
Duk yadda mamie ta kai da son ta raba tsakanin ?awancen mu da Habibah abin ya gagara, don rana WaWWayane bata shigowa side Winmu tayi masifa wa Ummi, akan dole idan mun shigo Ummi ta kora Habiba, sbd ni babu yadda za'ayi naje side Winsu sai mamie ta kore ni, har nadawo ma bana son zuwa, saidai ita Habibah tazo wurina, amma ko sau Waya Ummi bata kula ta, watarana ne ma Yaya Umar yazo suna zaune da Yayah ishaq a parlon mu sai ga Mamie cikin bala'inta ta shigo neman Habibah, inda ta shiga batanan ta ke fita ba, gashi bata san Yayah Umar yana ciki ba.


Ranan na tabbatar Yayah Umar gwarzo ne, don tsabar masifah da ?yar Hajiya Ummah ta shigo da Mamah suka fitar da shi, don rantsuwa yayi akan idan Mamie ta sake shigowa tayi rashin kunya wa Ummin mu ko ta nemi shiga tsakanina da Habiba wlh sai ya mata dokan tsiya, jikin shi har wani rawa yakeyi kaman wani Wan gunda.

Ita dai mamie jiki a sanyaye taja tsumman ?afarta ta juya tayi side Winta, ?asa-?asa ta ke magana akan yajira dawowan Abban mu, wlh bazata yadda ba, aiko batayi nisa ba, ya biyo bayanta idon shi kaman zasu zazzago yana zare su yace, "wlh ummi na rantse miki da Allah idan baki gayawa Abba baki cika mai sharri ba, kuma ni da kaina zan gaya mishi, ya kuma ja miki kunne akan zuwa gefen mahaifiyata, don wlh idan kowa bai Wauki mataki ba ni nan".... Yana buga ?irjin shi da hannu yana nuna kanshi yace "zan Wauki mataki mai tsauri akan ki da shegiyar munafukar ?ar ki mai kai miki rahoto".. Ya juya da sauri yana neman Raliya.

Ganin haka Ummie ta ?aeaso wurin ta kama shi, "Umar na baka umurnin ka fita kada ka taSa yarinyar nan," daga nan ta haWa hannun shi da Ishaq tace sufita zuwa wurin Hajiya Ummah su zauna, bata son fitina.

Tsaki Mamah taja tana hararan Ummie tace, "amman ummin su ke ina ruwanki ne? Ki bar shi ya chasa mana munafukar yarinyar nan mana, itama uwar munafukan ae shine daidai ita", tana gama faWa ta juya ta tafi side Winta, aka barni nida Habiba muna tsilli-tsilli da idanu, don Allah yana gani muna son junan mu sosai, kuma kullum Abban mu yana nuna muna musu junan mu, yana jin daWin yadda muke tafiyar da rayuwar mu, haka ma Ummie da Yayah mohd, gashi ko sch class Win mu Waya sit Winmu ma yana bayan nasu Habibah.

Ma?waftan mu muna da wata ?awar mu mai suna Maryam, maryam itace sit Win mu Waya da ita, ita kuma Habiba suna zaune da wata friend Winmu Jamilah, ita jamila a fadamar mada suke, maryam kuma unguwar mu Waya da ita, wato G.R.A, gida Waya ne tsakanin mu da su, kuma tun shigan mu primary class Winmu Waya sit Winmu Waya, har zuwa yanzu da muke shirin rubuta junior weac.

Ana gama watsewa a wurin muka haWa ido da Habiba, kaman wasu dolaye muka kwashe da dariya, Habiba ta matso kusa dani tana zare ido tace, "sis yau kam zanci na jaki a wurin Ummie babu mai karSa na, yau kam jikina zaiyi yakuwa", tana gama faWa muka sake kwashewa da dariya, nima cikin zare ido na sunkuya dai-dai fuskar ta, don nafita tsayi sosai, Habiba guntuwa ce kaman Mamanta, ni kuma daga Abba har Ummie dogaye ne, sai yazama gaba Waya Wakin mu muna da tsayi, kuma dukkanmu farare ne sol, su kuma kasancewar maman su guntuwa ne sai Habibah ta Wauko guntancin maman ta, amma farin Abba ta Wauko, sbd haka banbancin mu babu yawa a haske, don ita har taso ta fini, don ni na sirka da Wan jaja haka, amma Raliya ba?a ce, ta Wauko kalan fatar Mamie da kamannin mamie, sai dai ita doguwa ce, don tsayin su Waya da hafsy, "Sis kawai mu gudu wurin hajiya ummah, har sai Abba yadawo munga abun da hali yayi, idan ba haka ba ina tsorata miki na jaki da zaki sha yau", na faWa ina kama hannun ta mukayi wurin kakarmu.


Ana daf za'ayi sallan magrib Abba ya dawo daga tafiyan da yayi zuwa Abuja, ta window muka le?o nida Habibah muna ganin masu aiki dasu hafsy da suke masa sannu da dawowa, inda ya rungume hafsy da Raliya a jikin shi, Abba yana son mu, wani irin son da ko iyayen mu mata basa nuna mana, da gudu muka fito mukayi wurin shi, fuskar shi cike da fara'a yana, "oyoyo ?an biyu na," mukaje ya rungume mu, muma muna mishi oyoyo Abba, Yayan Ahmed ne ya fito a motan shima fuskar shi cike da farin ciki yana kallon mu, hannun shi ri?e da hannun hafsy da raliya, don tare suka dawo da Abba, farin ciki kaman zanyi yaya ganin an fito da kwakwa daga boot Win Abba, ina kallon Habiba nace, "sis gobe akwai kwakumeti a gidan nan", Abba ma yana dariya yace, "ae saboda ku na ce dole a sayo kwakwa a gidan nan, ?an biyu na zasu mun kwakumeti naci,"

"Abba mu kuma fah"? Cewar raliya da ta zunSuru baki gaba, tana sake hannun yayah Ahmed ta taho wurin Abba, "ku kan ae baku da tsaraba sbd yawan masifar ku da faWan ku, shiyasa ma ku bana ganin ku kaman ?an biyu," Abba ya faWa yana wuce side Win Hajiya Ummah, sannan yacewa Yayah Ahmed yayi alwala bari yagaida jatumar sa sai su wuce masallaci.


Yayah mohd da Yayah Ahmed basu da hayaniya, amma na Yayah Ahmed har ya Saci, sbd shi komai kukeyi baya tankawa, maganar ma da ?yar yake iya buWe baki yakeyi, don kullum ina jin Ummie tana cewa yayah yake iya magana a kotu?
Wucewar Abba kaWan raliya ta juyo ta zabga mana harara, sannan taja tsaki tace, "wallahi duk iya munafurcin ku kwakwan nan namu ne mu duka, tare za'ayi kwakumetin, ko kuma kunayi na faWawa Ummie ta ?wace ta raba mana dai-dai wa dai-dai, kunga ku da shan wahala mu kuma da morewa"' ta faWa tana murguWa mana baki kaman sa'o'inta.


Mari hafsy ta kai mata a bakinta tana, "mumafuka mai zubin shaiWanu, shiyasa kikayi ba?i ke kaWai a gidan nan sbd ba?in zuciyar ki" aiko raliya ta juyo zasu kama dambe da masifar su, Yayah Umar ya daka musu tsawa wanda lokacin fitowar shi kenan daga side Winsu, marasa kunyan banza da gudu sukayi cikin gida, amma bakin Raliya bai rufa ba tana cewa, "wallahi sai na haWaki da ummie, kince a wurinta na Wauko ba?i da ba?in hali", mudai kallon mamaki kawai muke musu nida habibah.


Kama hannu mukayi muka wucce side Win hajiya ummah, dai dai lokacin kuma yayah umar suna gaisawa da yaya Ahmed, hannun su ri?e da na juna, sbd gaskiya yayuna ukun nan akwai ?auna mai girma a tsakanin su, idan ka gansu kaman abokaina, muma wucewa mukayi side Win Hajiya Ummah inda muka haWu da Abban mu yana shirin fitowa.


Bayan anyi sallan ishaa an haWu a dinning wurin cin abinci, ido na nida Habiba zuru-zuru muna jiran ko mamie zatayi wani magana akan faWan Wazu amma shiru bata ce komai ba, sai dai hararan mu da takeyi a kaikace nida Habiba.


Ana gama cin abinci Yayah Umar ya dubi Abban mu da ke shirin tashi ya wuce cikin parlon yace, "Abba ina son magana da kai" da Waurarren fuskan shi kaman shine maigidan ba yaron gida ba, da sauri Mamie ta Wago tana duban shi, ita kuwa Ummi baki ta buWe tana, "Ubanah bana son dogon magana fah" babu Sata lokaci Abba ya Waga mata hannu, da nufin ta mishi shiru, yana bada hankalin shi gaba Waya kan Yayah Umar.

Girgiza kai Mamah tayi irin alaman Abba ya mata dai-dai, tana hararan Ummie.

"Abba dama alfarma nake nema a wurinka, ina so kayiwa mamie magana akan duk wani abu a gidan nan da ya faro ko akan yara ko na cikin gidan nan, kada ta sake zuwa kan ummie da faWa, idan ba haka ba wlh Abba wataran labarin da za'aji bazaiyi daWi ba, don gsky ni ha?urina yana gazawa," ya faWa yana hararan Raliya ?asa-?asa.


Kaman Abbah bazaice komai ba, har zuwa wani lokaci idon shi yana kan Yayah Umar, zuwa wani lokaci kuma ya maida kan ita mamin, gyaran muryah yayi sannan yace, "Baba nah kafin kagaya mun kai Ummah ta gaya mun, kuma insha Allahu zamu zauna da iyayenkan, kuma zanyi maganin komai, zan kuma kawo ?arshen komai insha Allahu, kaima ina son ka dinga ha?uri da wani abun, kana kuma kawar da kanka akan su", da sauri mamah ta buWe baki cikin Sacin rai tace, " sai an kai uwarshi ?asa tukun zaiyi magana? Wannan ae ba shari'a bane, shiyasa kullum Hauwa takeji a ranta abun da takeyi dai-dai ne, don ba tsawatar mata akeyi ba" ta faWa tana mi?ewa tsaye da niyyan barin wurin, Abba ya dakatar da ita, "Zainab bawai bana lura da abinda yake faruwa bane ko bazan Wauki wani mataki akai bane, nan ae ku da yaranku ne zaune, kuma naji ?orafin Baba na, insha Allahu zan zauna daku muyi magana, ba lallai sai a gaban su ba", ya faWa yana mai da kallon shi kan mamie da ta wani tura baki gaba kaman zata zunduma ashar, sai dai babu dama, don daga Mamah har Yayah umar tana shakkan su, haka kowa ya tashi yayi side Win shi, amma Yayah mohd, yayah Ahmad, Yayah Umar, Hafsy duk mi?ewa sukayi suka wuce side Win Ummin mu, mu kuma ganin Abba zai tashi da wurin mukayi hanyar Hajiya Ummah, don gaskiya yau babu mafaka a wurin Habiba sai chan, munafukar kuma Raliya muna shirin fita tana hararan mu, mudai bamuyi takanta ba muka wuce.


Hajiya Ummah tana ganinmu ta harare mu, cikin hararan mu tace, "nice rumfah sha shirginku ko? Idan ana zaman Allah da annabi ne ina binku kuzo mu kwana sai ku?i, ku masu iyaye sai ku gudu chan, idan sun gallabe ku kuma sai ku kwaso mun ?azamin jikinku kuzo ku takurani ni da gidan Wana," ta faWa tana maida kanta da hankalinta kan T.V, dariya muke mata Habiba ta faWa jikinta tana dariya, ni kuma na zauna wurin ?afanta ina nawa dariyan, Habiba tana neman tsokano mana ita tace, " hajiyar mu maganin kukanmu, idan bamu zo wurinki ba wurin wa zamuje? Kinyi na Abban mu kina namu, ae kin muri duniya da abunda yake cikin duniyan, ?a?anki su miki jikoki su miki", nima ina dariya na chabke da "gashi muna haihuwa ?a?anmu na fari masu sunanta zamu saka".


BuWe baki tayi tana kallon mu cikin mamaki tace, "amma Allah yayi manyan ma?aryata a nan, ae idan na samu kuka cigaba da zumunci dani ma ae nayi sa'a, da shegen bakin ?aryanku ae kuna haihuwa kowa wa uwarta zatayi wa mai suna, babu ma ya wa?ennan gardawan Umar da Ishaq, duk sun lotsa mun gado da kujeru na, amma nasan sunayin na kansu bazasu taimakeni ba, ballantana mai suna, sai gatan kashe mun kujeru da yawan zamansu" ta faWa fuskanta a murtu?e, dukkan mu dariya muka kwashe da shi, habiba tana ?ara ingiza magana da cewa tun ba ma Yayah Umar ba, don naga ya sakoki a gaba da labcecen jikin shi, juyawan da zanyi kawai sai na ganshi a tsaye a bakin ?ofan parlon, ae banbi takan Habiba ba na rantama Wakin Hajiya ummah da gudu na murWa key, ina jin dariyar Hajiya Ummah don babu abinda takeso irin taga yayah umar yana labtan mu, ina jingine da ?ofan ina dariyar Habiba ko ita ina tayi, don naji ihun ta da gudun ta.
Muna shiga SS 1, first term Win mu aka fara shirin biki Yaya mohd, wanda bai wuce 2weeks ba ayi,
Wani farin ciki nakeji sbd bikin da za'ayi a gidanmu, gashi Yayah Ahmad ya mana Winkuna kusan kala biyar-biyar mu da su Raliya, abun daWin ma har da Maryam friend Winmu, mudai shagali babu kama hannun yaro, gashi dodon mu baya nan, don sai ana satin Waurin auren naji ance zaizo, kuma fah Yaya Umar duk zafin shinnan yana mana so na ban mamaki, shidai daga mamie tayi wani rashin hankali ne zaki ga ya wargaza hankalin kowa a gidan, don ni gaskiya bansan wani irin so yakeyi wa Ummie ba.

Biki ya kankama Aunty Asma'u tazo haka ma Adda ta iso, abun farin cikin ma nida Habiba an bar mu zuwa maiduguri wurin event Win amaryah, wanda tafiyan mu da Aunty Asma'u ne.

Aunty Asma'u , Adda, da goggo ?anwar ummin mu duk zasuje, sai kuma wata ?ar ?awar ummin mu, sai ni da Habiba za'ayi tafiyan, mota biyu zai Wauke mu, Yayah ishaq zai ja motan Aunty Asmau, Yayah Umar zaija motan Adda, sai kuma gayyan motan abokan ango da zasu Wauko amare, Yayah Ahmad dai da Abba zasu haWa hanya, su kuma ana gobe Waurin aure zasuje da tawagar Abba.


Maiduguri munga karamci munga kara, an mana karSa na ban girma, munga shagulgula na har kan arziki da mutunci, a mutunce akayi komai aka gama, ranan Waurin aure muka kama hanyar Bauchi cike da farin ciki, ga kyakkyawar amaryar mu Aunty Bintu.


Mun iso bauchi wuraren ?arfe uku na yamma, haka kuma a gurguje aka shiryah domin buWan kai da za'ayi a gidan mu.

Aunty Rakiya ne ?irjin biki, sai kai kawo takeyi a filin gidan mu, inda ake decorating wurin saboda buWan kai, ana sallan la'asar wurin ?arfe biyar aka fito wurin buWan kai, ranan naga washe baki a wurin Yayah Mohd, ashe yana fara'a haka? Mudai muyi nan muyi nan, gaba Waya farin ciki cike da zuciyar mu, anyi taro lpy an gama lpy, inda amaryah da ango sunga karamci, su kansu ?an maidugurin sun yaba da kar??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????San da aka musu.


Bayan sallan ishaa akayi rakiyar amarya gidan ta dake *TAMBARI ESTATE* Gida ne mai Wauke da flat guda uku, ko wanne yana Wauke da three bedroom da parlor 2, Abba ne ya gina musu su uku ?an samarin shi, wanda ansha artabu da mamie lokacin da Abbah ya Wauke su sukaje ganin gidan, don ko gaya musu yana ginin baiyi ba, sai da aka saura 1month bikin ya kaisu, ya kuma shaida musu halak malak ya dam?a su, amma na yayah mohd ne kawai akayi penti, sauran biyun yace kowa ya tashi auren shi ya fente.


Mamie kasa daurewa tayi a lokacin, zuciyar ta kaman zai fashe tana huci tacewa Abba, "amma dai Abban su duk wani dukiyarka anan ka ?arar ko? haba jama'a idan mutum yace ba'a mishi adalci ace ba haka ba, yanzu namu yaran idan sun tashi aure sai ace komai ya ?are, kuma ana magana ace kishi ne", ta faWa kaman zata fashe da kuka.

Tana rufe bakinta, mamah tayi charaf tace," wa na zaice kishi? Sai da ace hassada da jahilci, idan bake kanki baya saiti ba mutum da ?a?an shi har kina da bakin cewa wani abu idan ya musu har kan arziki? Wannan hassada naki akanki zai ?are, naki yara matan cewa akayi ya basu wurin zama idan zasuyi aure ko me?"

Harara mamie tayiwa Mamah

2 / 46