ANA BARIN HALAL Hausa Novels by Anty Nice.doc

Author :  Auty Nice Category :  Hausa Novels 001

Chapter   28 / 46

81K to 84K   out of 137.2K words

ya kama goggo amma akwai farin fatan nan da kyaun fuska, daga ganin ta macece da lokacin ?uruciya tayi jiki da tsayi, masha Allah, yau kam naga inda M.G ya samo kyaun shin nan, don babu ?arya Matar akwai kyau, ga fara'a,
mummy ko ina ganin idon ta sai da na runtse nawa idon, da sauri na sunkuyar da kaina ?asa, domin sai naga kaman idon ,A.G na kallah, duk da Mummy ba?ace, amma kyakkyawar mace ce, ga ido kaman wanda ta cire nata ta mannawa A.G, hattah lumshewan da yake dashi irin nata ne, sai dai hala farin fatan shi na mahaifin shine, doguwace kuma bata da wani jiki sosai, gefe Waya kuma Heedayah ce, itama kyakkyawa ce amma dai bata kama ?afan A.G ba, duk da dai suna kama da A.G, amma ita bata kai shi fari sosai ba, amma sunyi kama, don hattah idonta irin na Mummy ne, irin na shi, haka kawai naji haushinta a zuciyata, wato akan wannan M.G ya share ni ko waya baya mun, sai naji bana son kallon fuskanta.

Bayan mun gaisa da sune dukkan mu a parlon ummie, sai mummy take mi?o mun wayanta, "Ga A.G ko dougter", a kunya ce na karSi wayan, "Eesha sannu ko, sorry beauty, sannu da rashin da aka mana, wayan ki akashe tun ranan bana samunki, M.G kuma yace mun yazo kina ta kuka shiyasa ya kasa haWamu, kiyi ha?uri Eesha, addu'a take bu?ata, Allah ya ji?anta ya raya abunda aka bari,", ina jin muryan shi sai naji rauni na ya ?aru, hawaye kuma suka soma mun sintiri, ban san lokacin da bakina ya ambaci sunan shi ba, amma murya chan ?asa wanda nayi imanin ko maryam da ta ke gefe na bata iya jiyo maganana, "A.G na rasa habiba, ta tafi ta barni da amanan babynta, bansan yaya zanyi na bashi kula ba, bansan yayah zanyi da ciwon rashinta ba, kadawo please", na faWa sautin kuka na yana fita, a hankali naji hannun mummy shi ta rungumo ni jikinta, shi kuma daga wayan naji yana magana, ha?uri yake ta bani kaman zai mun kuka, a haka na mi?awa mummy wayan ina ?ara fashewa da kuka, rungumeni tayi sosai tana rarrashina, gefe Waya kuma su hafsy suna ta share hawayen su.



Ranan uku su Aliyu suka shigo bayan anyi addu'a tare da Yayah Ahmad da su M.G, ashe kullum da su ake zama bansani ba, sai lokacin naji su Aunty B suna faWa, akan yadda Aliyu yayi laushi sai kuka yakeyi, hattah mummyn su jammy rasuwar ta bugata, gashi ?annen mamie naji fir sun?i basu yaron su gani, ganin kada abu yazama abun magana Mummyn ta share bata tanka musu ba, hatta Aliyun sun hanashi har sai da Abba ya musu jan ido tukun aka mi?a mishi ya mishi huWuba ya mishi addu'a, tunda na Waga ido muka haWa ido da su ban ?ara Waga kaina ba, don ko gaishe mu da sukayi idona yana ?asa, kuma a washe gari M.G ya tafi, don naji Yayah Ahmad yana gayawa Ummie M.G zai koma gobe insha Allahu.

Nidai banje naga babyn ba sai ranan da akayi bakwai, wato ranan da aka raWa mishi suna, kuma yaro yaci sunan Abba wato *USMAN* nan ma sai bayan magrib na shiga side Win mamie, wanda tun ranan da akayi rasuwan ban ?ara marmarin shiga ba, haka na daure muka shiga tare da su Aunty B, domin zasu mata sallama gobe zasu wuce idan Allah ya kaimu, zama nayi a ?asan carpet da muka shiga parlon mamie, don dukkansu suna zaune a parlon, yaron yana hannun raliya tana bashi madara, kallo Waya na mishi na kawar da kaina, nayi-nayi na iya buWe baki na gaida mamie amma na kasa, har sai da ita don kanta ta mi?o mun hannu, kuka naji yazo mun, wanda itama kukan ta fara, sannan raliya ta mi?o mun babyn tana cewa, "Adda gashi ki mishi addu'a ki zaSa mishi sunan da za'a ?ira shi da shi," ta faWa hawaye yana bin fuskanta, "wato Aunty nice idan kikaga mamie da raliya a lokacin zakiyi zaton har abada duk wani gaba ya?are a tsakanin mu, amma ina kibar zuciyar da babu Allah a cikinta, " hannu na saka na amshi babyn da ya buWe idon shi tar yana kallo, babu abun da yabari na kamanni da mahaifin shi, hatta ba?in fatan na Aliyu ne, don duk da jariri ne bai yi wani fari ba, ido na zuba ina ?are mishi kallo, gefe Waya wani ?aunar shi da tausayin shi na cika zuciyata, "SABEER" na ambace shi da shi muryana yana Wan rawa, kuka mamie ta sake fashewa da shi tana furta, "Allah yasa ?azamo mai ha?urin irin mahaifiyarka, Allah yasa ka amsa wannan sunan Wan albarka", mi?ewa nayi da shi a hannuna har gaban mamie, ?asa na dur?usa na furta, "Mamie ki amince na tafi da shi don cika umirnin sisto", bata bani amsa ba sai sunkuyar da kanta da tayi ?asa tana share hawaye, yayarta ce ta bani amsa da, "Aysha kiyi ha?uri ya Wan ?ara tasawa, sai ki karSe shi, yanzu idan ya tashi kuka da dare yayah zakiyi?" ido na ?ura mata bance komai ba, amma abun mamaki sai naji muryan mamie tace, "ta tafi da shi tunda ae ba nono za'a bashi ba, kuma nayi imamo da Allah ummie zata taimaka mata", tana rufe baki mahaifiyarta ta amsa da "a'a bazaiyiwu ace yarinya ?arama ta ri?e ba, kawai ta dinga zuwa da safe tana amsan shi, amma bamda a tattara shi a mi?a mata, ke mai zaki gani zuciyarki tayi sanyi bayan shi"? Ta faWa tana kawar da kanta gefe, babu musu na mi?a shi hannun sister mamie muka musi sallama muka fice a parlon.


Kullum safe kuwa sai na shiga side Win mamie na Wauko Wana, gashi mai ha?uri baida rikici, wuni mukeyi tare da shi, har su raliya suka koma kaduna, idan zanje makaranta ne kawai na kan bar shi hannun mamie, wataran ma mamah ce ko ummie suke ri?e shi, ita dai mamie har zuwa lokacin a sanyaye take.


Habiba tayi arba'in aka raba gadon abun da ta bari, sannan a ranan Aliyu da iyayen shi suka sake zuwa gidan mu gaishe da su Abba, a wannan ranan kam an bar su sun Wauki sabeer, don har video call sukayi da jammy, duk da munsha video call tana ganin shi, Aunty nice zaki sha mamaki idan nace miki sanadin yaron nan har video call munayi da A.G? Murmushi nayi ina kallonta cike da mamaki, itama murmushin tayi ta cigaba da bani labari.

Ranan farko da muka fara, na dawo daga sch yana ta kuka, an rasa me ya same shi, sai na Wauke shi inata jijjiga shi, lokacin wayan A.G ya shigo, a rikice na Wauka, jin kukan da sabeer yakeyi yasa yace bari ya ?irani video call ya rarrashe shi, hummm abun mamaki indai akan Wa nane zan iya komai, ae babu shiri na Wauki wayan da ya sake ?irana video call, duk nayi sukuku doni, matso mishi da fuskam sabeer nayi, shi kuma yanata rarrashi, ranan naga ikon Allah kawai sai yaro yayi shiru yanata sau?e ajiyan zuciya, murmushi A.G yayi yace, "yarona yana missing Winane, ko kuma Ammin shi bata iya bashi kulawa ba, yafi son na Abbin shi", tura baki nayi cike da shagwaSa, sanan ya umurce ni na saka mishi yatsa a baki , ina saka mishi kuwa ya ri?e yana tsotsa idon shi a kaina, a haka har yayi bacci, ajiyan zuciya na sau?e na maida kallona kan A.G, ido ya kashe mun yana murmushi, "yakamata na dawo na baku kulawa sosai ke da Wanmu, don naga wannan rikicin uwa da Wan duk A.G ne zai iya shanyewa," Murmushi na mishi lokacin, sannan nace, "saura kwana nawa kadawo"? Idon shi cikin nawa yace, "saura 2weeks oum sabeer", daWi nake ji idan ya ?irani da wannan sunan, amma sai na wani harare shi, dariya ya Wanyi.
Lokacin da su Aliyu suka zo da mummyn shi takeyiwa Ummie maganan ya kamata su turo manya akan maganan Aliyu, ita dai Ummie bata ce komai ba sai murmushi da tayi, bata kuma gayawa kowa yadda akayi ba har bayan sati biyu da maganan, ana saura 2dys A.G ya dawo, iyayen Aliyu suka zo wurin Abba da maganan Aliyu ya dawo da maganana, a haka ma basu san da wasiyan Habiba, kawai da so da ?auna da Aliyu yake mun da iyayen shi ne, anyi dace kuma ranan da sukazo Yayah Muhammad yana nan, don yazo we?end.

Bayan Abba ya gama sauraron su sai yayi murmushi ya gyara zama, "ALHAMDULILLAHI Naji daWin wannan batu na ku, don duk inda akace ?ar'uwa ta rasu tou daWin zama ya kansa a sake neman auren ?ar'uwarta, duk da ansamu saSani a tsakanin su har ta kai ga batun saki, tou naji daWin zuwan ku, don alama ya nuna Habiba Wiyata bata zalunci Wanku Aliyu ba a zaman takewar su, don nayi imani da Allah da ace ta zalunce shi ko ta cutar da ku, babu wanda zanga ?afan shi a ?ofar gidana don neman auren Waya daga cikin ?a?ana," g?aWa kai kawai iyayen Aliyu sukeyi, Abba ya cigaba bayan yabi kowan su da kallo, "Habiba, Ayshaa duk abu Waya ne yayi su sannan ?a?a nane mafi soyuwa a zuciyana, sanadin halayen su Allah ya saka mun ?aunar su a zuciyata, yara ne dattawa, masu ha?uri, yarah ne masu albarka, Allah ya ji?an habiba", Abba ya faWa da wani yanayi a fuskan shi na jimami,
"Kunzo da maganar neman auren ?ar'iwarta, wanda da ko ba ayi zaman lafiya ba Albarkacin wannan jariri zan iya amincewa da bu?atanku, tou amma gaskiya banji daWin ri?on da Aliyu da ku iyayen shi kukayi wa habiba, tabbas banji daWi ba, amma komai ya wuce zamuyi zumunci a tsakanin mu ko dan albarkacin wannan jariri, amma maganan aure da Ayshaa abune ba mai yiwuba, don a yanzu akwai maganan aurenta da wani yarona, har an saka rana, kunga kuwa duk dattijon arziki baya magana biyu", Abba yana kaiwa nan ya mi?a musu hannu suka sake gaisawa, sannan yace su gayawa Aliyu duk lokacin da yaji yazo ko shi ko iyayen shi da ?an'uwanshi ganin yaro ?ofa a buWe take, amma maganan bashi Wa kuma kada ya saka a ranshi, don ya wufantar mun da ?a da abinda ke cikinta, bai san lafiyan su da komai da suke ciki ba har sai da Allah yayi ikon shi tukun na gan shi gidan nan, bawai na ri?e shi bane a zuciyata, a'a kawai zanyi abun da nake ga shine dai-dai, nagode da zuwanku neman sake haWa iri dani a karo na biyu".

A kunyace Waya daga cikin ?anin baban su Aliyu ya Wan risina yana yiwa Abba godiya, sannan dukkansu suka sake bawa Abba ha?urin abunda ya faru, don gaskiya ne sun san basu kyauta ba, lokacin da Aliyu yayi saki babu wanda ya biyo bayan habiba, haka dai suka fita duk jiki a sanyaye,
Gida suka wuce wurin mummy, bayani dalla -dallah suka mata, gaba Waya ran mummy ya Saci, a fusace tace, "tou ae dama tun farko Aliyu baice yana son habiba ba, kuma bamuce habiba tana da aibu ba, kawai na?ita saboda halin mahaifiyar ta ne, don Aliyu ba'a hayyacin shi ya furta ya amince da auren ta ba, kuma lokacin da ya dawo hayyacin shi ya nuna baya sonta, amma ae dana san habiba tana raya baza'a taSa barin ya auri ayshaa ba ae ban nuna komai ba, amma da habiba ta rasu sai naga akwai dama da Aliyu zai maye gurbin habiba da ?ar'uwarta, wanda dama tun farko itace zaSin mu da shi baki Waya", cikin Sacin rai ta ?arasa maganan, su dai ha?uri suka bata suka tashi suka fice, cike da Sacen rai ta ?ira Aliyu ta zayyane mish komai, dama yayi tafiya baya gari, "mummy wani maganan aure aka tsayarwa Ayshaa da shi? Kawai munafurcin uwar habiba ne ta hana komai, ki ?ira ita ummie kiji komai daga gareta", sallama sukayi mummy ta ?ira ummie a lokacin, nan dai ummie tayi namijin ?o?arin sanarwa mummy akwai maganan aure akaina, wanda zan aura ma cikin satin nan zai gama ya dawo, "duk da haka dai ummin su a duba al'amarin Aliyu, yana son Ayshaa sosai fah, kuma ashirye yake daya ha?ura da wancan maganan auren idan Ayshaa zata amince,"
Murmushi ummie tayi tace, "gaskiya koda zai auri ayshaa bazan so a fasa maganan auren shi da yarinyar da ta ke matsayin ?a a wurinki ba, ga magana kuma yayi nisa, kawai dai mu ?ara addu'a, Allah ya zaSa abunda yafi alkhairi a tsakani", badon mummy taso ba tayi sallama da ummie akan idan Aliyu ya dawo zaizo ya samu ayshaa suyi magana a tsakanin su.

Zuwa dare Abba ya ?iramu nida ummie zuwa parlon hajiya ummah, achan muka same su harda yayah muhammad, nan Abba ya gaya mana yadda sukayi da iyayen Aliyu, kuma ya sake jaddada bai hana Aliyu yazo ya ga Wanshi ba, amma su yayah muhammad su zama shaidah har abada bazai bashi ri?on yaron habiba ba, dom sakamakon izayan da suka yiwa habiba kenan, nan hajiya ummah ta tafka salati hannu ri?e da bakinta tace, "amma dai Aliyu da iyayen shi anyi sokayen banza, yoo sokaye mana, ku wahar da habiban don babu kunya a idonku kuzo kuma neman auren ?ar'uwarta? Da shegen ba?ar fuska kaman na boss Win indian film ya kwaso ?afa yana zabgegen bazawari yace Ayshaa budurwa wanda zata auri saurayi yake so? Tou haram wannan shirmen ba'a gidan Usmanu na ba, don ko Gwamnah ne mahaifin shi bai isa yaja da kai ba usmanu, nera yafi ka ko suna a gari"? Dariya ne ya kubcewa yayah muhammad yace, "ballantana ma besty kam bata son wani Ali black, A.G Winta kawai tace sai shi, bawai don farin fuska bako besty"? Ya faWa yana duba na da murmushi a fuskan shi, sunkuyar da fuskana nayi ina duban fuskan Sabeer da yake rungume akan cinyata yana bacci, ido na ?ura mishi ina jin wani irin son shi alokacin kaman zai fasa mun ?irji na, ummie ce cikin murmushi take zayyana musu yadda sukayi da mummyn Aliyu, nan ma hajiya sake rabka salati tayi tace, "amma kuwa sun tabbata manyan sokaye, daga uwar har Wan", ta maida kallonta kan Abba tace, "ae wannan satin ne dawowan Aminun ko?" Abba ya Waga mata alaman haka ne, "tou kayi aniya sati na sama a sambaWa auren nan", tayi ?asa da murya har tana sunkuyowa kaWan tace, "gama zafin uwar shinnan da yadda tafi ?arfin Hauwa da zuriyarta da suka shahara a yawon bin malamai, tou itama bazata gaza bin bokaye ba, tou bokaye mana, don itama ae Hauwan su tabi ta jawo hankalin Aliyun ya bar Ayshaa ya dawo kan nata ?ar, amma da yake na uwar Aliyun sun fi shahara ae kaga abun baiyi lestin ba, tunin yayi espiya", ta faWa tana watsa hannu.

?ago kai Abba yayi da sauri ya maida kallon shi kan ummie, "dama bada amincewar ayshaa ya fara neman habiba ba ne"?
Ita dai ummie bata ce komai ba, sai kallo na da ta Wanyi ta kawar da kanta gefe, "dama baka da labari ne? Lallai khadijah kin cika cikakkiyar bafulatana, kawaicinki yakai duk inda ba'a zato, tou Ayshaa ya fara gani a bikin ?ar'uwarshi ?awarsu, ya kware yana sonta, ita kuma marigayiya ban san ya akayi ba, don bana ce taci amanar ?ar'uwarta ba tunda ?asa ya rufe idanunta, kuma da kunya ga idon Wanta na faWi wani mummuna akanta, tou haka dai muka samu zance ya juye ya koma kan habiba, amma dai ba wai da yardar Ayshaa ba yadda suka tsara maka, juya kanshi akayi ya bar kan Ayshaa, daga wannan rana kuma uwar habiba ta raba tsakanin ayshaa da habiba, Allah dai masani amma shu'umancin uwarta na shige da fice wurin bokayen da baka son afaWa ne ya tabbatah, shi kuma Aliyu bayan aure Allah ya kuSutar da shi uwarshi ta tashi tsaye ta lalata Wan ?aramin shirkan Hauwa, don daga ganin idon uwar Aliyu gwaska ce, tou komai dai ya karye Aliyu ya dawo hayyacin shi yace baiji ba bai gani ba baya son habiba, don ba ita yace yana so ba, ita kuma marar kunyar ?anwar tatah Raliya ta tsayar mishi rashin kunya ya labga musu uban na jaki, kaga asalin ?iyayyan shi da ita marigayiya kenan, sharrin rashin da ce da uwa ta gari".

Abba ido ya zuba mun kaman bazai sake furta komai ba, chan kuma sai yace, "Aysha ki yafewa ?ar'uwarki, nayi imani ko da laifin habiba tou babbar mai laifin uwartace, don Allah ina ro?on arzikin ki kiyafe mata, taci darajana"!
Hawaye na saka hannu na share, "Abba ni ban taSa rike habiba da zuciya ba Waya ba, kuma ni tun farko ban so Aliyu ba, shiyasa ma ni banja ba, amma ni ban riketa da komai ba tun farko, Allah ya ji?anta da rahma", na ?arasa ina share hawayen da bansan ranan daina shi ba.

Addu'a sosi Abba ya mana na alkhari gaba Waya ?a?an shi , sannan ya umurce ni da na je na cigaba da kula da yaro na, tashi nayi ima rungume da Sabeer na fice, ina ganin hajiya ummah da ummie suna ta share hawayen su.


Ranan friday da 6:00am jirgin su A.G ya sau?esu a garin lagos, 9:00am kuma suka tashi zuwa Abujah, amma A.G bai shiga bauchi ba sai ranan saturday da yamma, don basu samu flight me zuwa bauchi ba, dole suka bugu mota sai bauchi, ya iso ya samu gidan a cike, ga Hudah ga Heedayah da

28 / 46