ANA BARIN HALAL Hausa Novels by Anty Nice.doc

Author :  Auty Nice Category :  Hausa Novels 001

Chapter   26 / 46

75K to 78K   out of 137.2K words

a parlon ummin mu, wallahi idan baki bar kukan nan ba zan tayaki,"
?ago kaina nayi da sauri jin yayi ?asa da murya kaman zaiyi kukan, kallon shi nayi ido waje nace, "nifa ba kuka nakeyi ba, please ka kuma chan kada yayah ya fito".
Ajiyan zuciya kawai yayi ya ?ura mun idon shi duka da suke lumshe, "Eeshaa kina da kyau sosai, banda ni banga wanda yafi ki kyau ba a duniyan nan, idon ki masu kyau kawai nawa ne yafi naki kyau", hararan shi nayi ina kallon shi nace, "kafini kyau?" Waga kai yayi alaman haka yake nufi, hararan shi nayi nace, "nafika dogon hanci fah," murmushi yayi yaa kan kallo na da lumsheshhen idon shi, bai ce komai ba sai idon daya kura mun yana wani smilling, hararan shi nayi na sau?e idona ?asa, don gaskiya ne yana da wani mahaukacin kyawawan ido, tun ba yau da ya matso kusa dani kuma yayi maganan kyaun ido yasaka na kalle shi da kyau, ga idon manya da su amma baya iya buWesu dukan su, "nidai ka koma chan", na faWa ina kawar da kaina gefe.
Hancin shi ya Wan shafa kaWan yana kallona, "Beuty kinsan kyaun hanci na kuwa? Baki san yafi dogon hanci kyau ba, kalla kiga hancin mu fa kusan iri Waya ne fah dake, don kema naki daidai ne mai kyau, don har ya kusa iso nawa a kyau", dariya ne ya Wan suSuce mun, "ni ban taSa jin mai yaba kyaun shi ba sai kai, kuma har kana tunanin ina mace ka fini kyau" na faWa ina maida kallon na fuskanshi, marairaice mun fuska yayi cike da alaman shagwaSa yace, "Allah akwai wata ?ar Eathoupia da muke course Waya da ita, kullum sai ta Wauki photo na idan ina zaune, har friend Winta ?ar India ce ita kuma, wata rana ta daure tazo har inda nake ta zauna, chan sai tace, "an taSa gaya maka irin baiwar kyaun ido da kake da shi"? Kallon ta nayi shiru bance komai ba, sai ta cigaba, "friend Wita AFRAH kana mata kyau, tana so kuzama friends da ita, amma ta kasa gaya maka", tou ni tunda ga ranan na ?ara yadda ni mai kyau ne, saboda ?an eathoupia da india har suka ga kyau na, ae kuwa kyaun nan ya kai inda ya kamata ya kai", ya ?arisa faWa yana wani shafa fuskan shi, ido shi kuma akaina.

Lokaci Waya naji wani mumunan Sacin rai, wanda har akan fuskana ma bai Suya ba, kallon shi nayi ya ?ura mun ido nace, "kuma kayi accepting Winta kun zama friends Win"?
Girgiza kai yayi alaman a'a, sanan ya buWe baki har lokacin cike da wani basarwa yana wani ya mutsa fuska yace, "ina zan accepting mata? Kalan duk ranan duniya ta dinga kallona tana yaba kyau na? Ko amsawa friend Win nata banyi ba, tashi nayi na wuce room Wina, a zuciyata nace, "wallahi baku isa ba, sai nazo naji daga bakin Beauty nah, idan haka ne tou sai naji gaskiyan batu, idan bakiga kyauna ba kuma sai na koma nayi accepting Winta, don ima son naji ance ina da kyau, da kyaun ido", ya faWa yana kara shigar da idon shi cikin nawa.
Ajiyan zuciya mai Wan ?arfi na sau?e, wanda har sai da yasaka shima ya sau?e, "ita Win tana da kyau ne"? Na tambaye shi, Waga kai sama yayi alaman ehh, Sata rai nayi nace, "kenan dai ta maka kyau"? Girgiza kai yayi alaaman a'a , harara na aika mishi da shi, "mekake nufi tou? Nasan ae ta burge kane shiyasa baka manta fuskanta ba", na faWa ina tura baki gaba, du raina ya Saci.

BuWe baki yayi ya saka hannu a haSan shi yace, "nifa ke kaWai nake ganin kyaunki, kawai ina so ke danafi so da ganin kyaunki naji daga bakinki kafin wasu kuchakai su dinga gaya mun, nafi son jin nako, ina da shi ko bani da shi"? Ya faWa muna ara haWa ido da shi.
Yamutsa fuska nayi sannan nace, "kana da shi kaWan, amma dai baka wani fini ba", na faWa ina kallon yatsun hannun shi da yake Wan lanlan?wasa su.
"Nifa nayi tunanin nafiki kyau wallahi, tou idan na koma zanje na samesu sumun bayanin yadda zan fahimci nawa kyaun, don ni tunani na nayi irin sosai Win nan ne".
Da sauri nace, " ba sai ka sake neman bafa, kana da kyau sosai, idonka ma mai kyaune sosai, kada ka sake kula su, kaga ance kai mutumin kirki ne kada kuma azo a ga kana kula mata", na faWa kaman zan masa kuka.

Dariya yayi sosai yana lumshe ido, sannan ya Wan sunuya sosai da kanshi yace, "dare yayi zan gudu wurin mummy, gobe insha Allahu zanzo muyi sallama, sai naji sauran bayanim, don ma Soye miki ne, tave ma tana sona, amma nafi so naji daga gareki, idan sonki yafi burgeni, tou xanyi warning Winta, idan kuma ke baki sona sai na duba yayah natan yake", ya faWa yana mi?ewa tsaye, dama sanye yake da wasu jean da shirt mai layi layi, ya mish kyau sai ?amshi yakeyi, nima tashi nayi tsayen don jin da nayi yace bari dai ma na koma sai na ?irata mu gaisa a waya don kada tace na shareta, kin san sun bani number wayan su".
?ata rai nayi nayi gaba don rakashi zuwa bakin ?ofan fita, hanya na bashi ya fita, yana fita ya tsaya ya maida hannayen shi cikin aljihun wandon shi ya karkatar da kanshi gefe kaWan ya ?ura mun ido, duk narasa mai yake mun daWi, a hankali na kalle shi fuskana cike da damuwa nace, "ka ?irani idan ka isa zan gaya maka wani abu", risinar da kanshi yayi kaWan yace "angama Beauty nah, inaga muna gama waya da ita zan ?iraki, ko kuma sai munyi da ke"?
Bansan lokacin dana fara buga ?afana a ?asa ba, "nikan bana so ka ?irata, ka ?irani sai nagaya maka tukun", na faWa ina shirin mishi kuka.
Matsowa yayi kusa dani yace "mummy kawai na miki al?awarin zan kula a duk matan duniya sao na ?iraki, ko sister na yau ta kalle ni sai na ran?washeta ballantana ta mun magana, ina shiga Waki ke zan ?ira ranki ya daWe".
Dariya ya bani babu shiri na juya cikin parlon da sauri, shima ina jin sautin dariyan shi.

Ina shigowa kuwa na haWu da yaya Ahmad wanda fitowan shi kenan daga Wakin ummie, kallo na yayi yana murmushi yace, "barrister ya tafi kenan?" murmushi nayi na Waga kaina sama alaman ehh, murmushin ya sakeyi yace, "A.G mutumin kirki ne ayshaa, ki so shi xakiji daWin zama Wa shi, dattijo ne sosai, kuma bayida hayani, idan Allah yasa yazama mijinki zakiji daWin zama da shi", murmishi kawai nayi ina zama akan Waya daga kujerun parlon, muna haka ummie ta fito hannun ta Wauke da filet, da sauri na mi?e na karSa na wuce kitchen, sallama sukayi da shi ya wuce gidan shi.
Ina fitowa naga ummi bata parlon, wucewa nayi har Wakinta na sameta suna shirin kwanciya ita da hafsy, don Wakinmu sai da ba?i sosai a gidan muke kwana, Wakin ummie hafsy ke kwana ni kuma Wakin hajiya ummah, sai da safe na mata, sannan na wuce side Win hajiya ummah, bayan ummie ta biyoni domin rufe musu ?ofa.
Wuraren 10:00 na dare kuwa sai ga ?iran shi Wan halak, dama na shiga Wakin hajiya umma Waya wanda muka mai da shi namu, a zuciyata nake maganan shi akan ya?i ?ira, hala ma ya ?ira wancan Wayan ne, tsaki naja bayan na kashe wutan Wakin na hau zan fara addu'a, kawai sai ga wayan shi ya shigo, ido na zubawa wayan yayita neman agajin Wauka ban kula shi ba, yana katsewa wani ?iran ya sake shigowa, shima har ya kusa yankewa tukun nasaka hannu na Wauka.

Ajiyan zuciya ya sau?e mai Wan sauti, shiru mukayi dukkan mu babu wanda yayi magana, amma kowa yana sauraran sautin bugun zuciyar Wan'uwan shi, mun Wauki sama da mintuna goma babu wanda yayi koda tari ne, har nayi niyyan kashe wayan, amma kuma kaman wanda yake duba sai naji muryan shi a Wan sha?e yayi magana, "beauty na dawo gida, mummy ta Wan tsayar da ni muna hira", ajiyan zuciya na Wan sau?e a hankali, sannan nace, "bakayi wayan ba kenan"? Shiru yayi kaman mai tunani, don shi gaskiya a gefen shi ya manta da maganan wata da yayi bayan Eeahan shi, chan kuma abun ya faWo mishi a rai yace, "ni na isa na ?ira wata bayan na miki al?awarin ke zan ?ira? Heedayah ma tana gaishe ni nayi kaman ban san tana wurin ba, ganin haka itama tayi ta kanta".
Dariya ne ya suSuce mun, "ni fa bance maka har da sisters Winka kada ka kula ba", na faWa ina ri?e dariya na, don yanayin yadda yayi maganan ya sakani dariya, "ok tou nagane, banda su heedayah, tou ?irgamun wanda baki son na dinga kula su beautyn A.G".
Gyara kwanciya na nayi nace, "wannan yarinyar da friend Winta", ina jin shi yace, "one",
Murmushi nayi nace ko wacce mace idan ba ?an gidanku ba ko kuma tsufaffi, har ?an office Winku", ina gama faWa na saka hannu na toshe bakina, "insha Allahu zan kiyaye beauty, sai dai ina neman alfarma guda Waya a wurinki", ya faWa da mugun nutsuwa a muryan shi, ban amsa mishi ba naji yafara mun bayani, "Eesha ni mai tsare kaina ne sosai, kuma zan ?ara fiye da yadda nake a baya, ni lawyer ne dole wasu matan zasu neme ni akan damuwan su, insha Allahu na miki al?awari daga abunda ya haWani da su babu wani abu da zai biyu baya, sannan Ina da family both side, mummy da daddy nah, kuma akwai mata, insha Allahu zan tsaya dai dai da yadda shari'a ya umurce mu dayi, wata mace insha Allahu bazata ga dariya na ko murmushi naba idan bake ba, sai dai a bisa kuskure, zan tsare miki kaina yadda bakiyi zato ba, amma kema bana son ki kula ko wanni saurayi please."
Wani irin nutsuwa ne yazo mun a zuciyata, wanda bansan meye dalili ba, "ni ae bana kula samari, ni basu ma burgeni," na faWa ?asa-?asa da murya, "amma dai ni ina burge ki ko"? Naji muryan shi yana tambaya na, runtse ido na nayi, sannan nace, "ni tausayinka kawai nakeji".
"Alhamdulillah" naji ya faWa, sannan kuma naji yace, "Eesha kin gama mun komai a rayuwata, duk macen da take tausayinka tou ba ?aramin so zata maka ba, Allah na gode maka", ya faWa da Wan Waga muryah.
Zaro ido nayi ina rufe bakina da hannu Waya, "nifa ciwon kanne yake sani tausayi bawai sonka.....", sai kuma nakasa ?arasawa, saboda yau Waya kawai naji ina jin kunyan nace bana son shi, haka dai mukayi ta hira wanda bansan ma 12:00 am yayi ba, sai da naji yace nayi ha?uri ya jani muna hira har 12, sallama mukayi kowa ya kashe wayan shi.


********
Washe gari yazo amma a parlon hajiya ummah muka zauna, sallama ya mun akan gobe zai wuce Abuja, don tanan zai tashi, yau banji yana jana da hira ba kawai shiru yayi ya ?ura mun ido, har narasa yadda zanyi da kallonshi, duk Wago kaima kuma sai ya Waga mun giran shi sama, haka dai har 9:00 tayi sai yace nayiwa hajiya umma magana suyi sallama zai tafi gida, tashi nayi naje Wakin na mata magana, sallama sukayi tana ta saka mishi albarka, da al?awarurruka Kaman itace mai auren shi, bunch na 500 ya ajiye mata ya fice, tana ta zabga mishi addu'a, nidai nabi bayan shi, muna fita yace muje yayiwa ummie sallama, haka naja tsummukaran ?afana jiki a sanyayae na raka shi har parlonta, suna tare da hafsy da yayah Ahmad, hannu ya mi?awa yayah suka gaisa, sannan ya gaishe da ummie, nidai gefen hafsy naje na zauna kaina a ?asa, hira suka Wan taSa kaWan, sannan yayiwa ummie sallama akan gobe zasu wuce tare da yayah Ahmad, flight na ?arfe 9:00am zasu bi, hafsy ya ?ira sukayi waje, chan sai gata ta dawo, hannunta ri?e da envelop an saka 100k wa ummie, sannan tace mun naje yana jirana a waje, ni dai tashi nayi na fice, ina jin ummie nayiwa hafsy faWan meyasa ta karSo, ita kuma tana cewa, ko da wa ita yabayar karSewa zatayi wallahi, tana faWa tana dariya abunta, haka dai na wuce nayi waje.

A jikin motan na tsaya hannu na ri?e da murfin motan, shi kuma yana zaune a driver sit, ?afan shi Waya a waje Waya a ciki, hannun shi akan stearing motan, dukka ida nun she a zube a kaina, munyi shiru babu wanda ya tanka a cikin mu, chan dai nayi ?arfin hali nace, "kana ta hidima dasu ummie da hajiya ummah, an gode Allah ya ?ara buWi", baice uffan ba sai ido dai da yaci gaba da zuba mun su, Wago kaina nayi muka haWa ido da shi, "Beauty zakiyi mssn Wina"? kawai naji ya faWa ido a lumlumshe, Girgiza kai nayi alaman a'a, da sauri ya daga kanshi yace, "shiyasa nakeso nayiwa yarinyar nan tambayan gaskiya, idan ta amsa mun kawai zanyi ha?uri na amsheta".
"tambayan me zaka mata"? Na tambaye shi, "ko da gaske tana sona, idan har da gaske ne zan bawa kaina ha?uri kawai ayi da ita", ya faWa yana wani ya mutsa fuska, sama na Waga kaina kawai ia kallon taurari, batare da na sau?e kaina ba nace, "idan ta amsa maka kuma zaka sota? Bayan kache mun bazaka sake kula wata mace ba"? Kallona na mayar kanshi jin yace, "tou ae kene beauty, ni so nake kawai a soni, ke kuma kin nu?e kin ?i ki soni", ya faWa idon shi na kaina, idona cikin nashi ina jin yadda zuciyata take wani irin mugun harbawa, a hankali na Wauke kaina saboda yadda nake jin wani irin yanayi idan muna kallon juna, baki na tura gaba nace, "tou ni dai bama son kayi magana da ita, bana son ma ka koma school Win", "tou please Eeshaa ki soni", ya faWa kanshi tsaye, shiru nayi ina tunani, chan kuma sai nace, "shine zai saka bazaka so wata ba" ido na akan shi, lumshe ido yayi ya Wan Waga mun kai alaman ehh, "tou zanyi tunani, amma..... Sai kuma nayi shiru ganin Yayah Ahmad ya fito, ?urawa Yayah Ahmad ido nayi, _Sai da ya Kusa isowa inda muke sai nayiwa A.G sallama na wuce, anan suka Wan tsaya kaWan, sai kuma naji tashin motan kowan su.



Washe gari suka wuce Abuja, zuwa dare kuma jirgin su A.G ya Waga, kafin ya wuce ya ?irani munyi waya, washe garin ranan tafiyan shi kuma ya ?irani wuraren ?arfe shida na asuba akan sun isa lpy, daga wannan ranan kullum sau biyu a rana sai munyi waya da shi, wataran ma sau uku zuwa huWu, amma bamu wani dogon hira da shi, M.G kuma shiru banji ko sau Waya ya ?irano a waya ba, nima haka sai na share shi.



*********
Kwanci tashi asaran mai rai haka dai rayuwa ta lula damu har december, har satin bikin raliya, wanda har zuwa lokacin mamie bata san da maganan aure na ba, ana sauran 2weeks auren raliya kuma Aunty j ta haihu, itama Wa namiji aka samu, wanda yaci sunan Yayah Auwal, wato *MUHAMMAD AUWAL* amma suna ?iran shi da Affan, a zuwan mu sunane nasan M.G yana ?asan yana Abuja abun shi, domin ranan sunan ma hafsy tace mun sun haWu da shi, yace ta gaishe ni suna saurine zasu fita da yayah, nidai naji haushi, saboda meyasa M.G ya wani ?aurace mun, babu waya babu ziyara, gaskiya Al?awari baice haka ba, haka dai nima na share batun shi, mun dawo kuma bikin raliya.

Mudai babu ruwan mu da wani rawan kan bikin, yayun mi dai duk sunzo daga Abuja, kuma har da Aunty B da Areef, maijego kawai aka bari da wata ?ar'uwar ta, Adda ma tazo, Aunt? ma'u ma tazo, gida dai ya cika da dangi sosai, ranan da za'ayi walima, da safe hadiza suka zo da ?an'uwa na chan, zuwan tane ma ta jani muka shiga side Win mamie, anan naga habiba, tayi wani irin ?iba, ga cikin ya fito sosai, tana zaune a ?asa tana shan kankana, gaisawa sukayi da hadiza, ni kuma ta kalleni fuskan ta Wauke da fara'a, murmushi na mata, itama ta maida mun da gaggawa, sannan naga ta kalli gefen da mamin ta take zaune, ganin bata ganinta sai ta mum alaman nazo nasha kankanan, murmushi nayi na mata alamamn na gode tasha kawai, haka dai tayita ?ureni da idon ta, har muka gama muka fita fatar bakin mu bai furtawa juna komai ba, tausayin ta cike da zuciyata.
A haraban gidan mu akayi haWaWWen walima, wanda yafi na habiba ?ayatuwa, amaryah tasha kyau sosai, tayi shiganta mai kyau, sit Waya muka zauna da ni da hadiza da maryam, domin tazo mana, hafsy da ummita suna chan cikin friends, don raliya bata tsoron mamie irin habiba, ita da taga bikinta ya matso kusa sai ta jawo hafsy ajiki suka cigaba da sha'anin su, duk Waga kna da zanyi sai mun haWa ido da habiba, kuma sai ta mun murmushi, nia sai na mayar mata, har magrib tukun aka watse, washe gari aka Waura aure, akayi wuni, bayan la'asaar aka

26 / 46