ANA BARIN HALAL Hausa Novels by Anty Nice.doc

Author :  Auty Nice Category :  Hausa Novels 001

Chapter   33 / 46

96K to 99K   out of 137.2K words

sai naji duk zuciyata babu daWi, haka na daure na tsuguna a gabanta, itama yadda akayiwa su ummie haka aka gaya mata, hannunta ta saka ta ri?o duka hannaye na ta ri?e su gam acikin hannayenta, addu'a take mun da fatan alkhairi, amma gaba Waya jina nake kaman na zabga ihu, saboda wani irin matse mun hannaye da tayi da ?arfin gaske, wanda har sai da naji hannayen mu suna fitar da zufa nida ita, saboda babu space Win da iska zai shiga, adda'a tayi ta ja, daga baya kuma ta mi?ar dani ta rungume tana muyafi juna, hannu Aunty Adda ta saka ta Wago ni a jikinta muka fita, hannu na kai sai tin hanci na nasha?i wani warin da naji yana mun kaman na jan miski, ni tun asalina bana son warin shi, sai naji kaman miski kaman kuma wani ?arni-?arni yake mun, muna shiga parlon Abba na goge hannun a jikin cottons WiS parlon da dabara, amma dai har jikin lafayyah na ina jin yana warin abun.
Muna shiga naje na dur?usa a gaban Abba, kuka nakeyi sukuma sunata mun addu'a da nasiha, a ?arshe Abba yace muwuce kada mu Sata musu lokaci, kafaWu na ya ri?o na mi?e tsaye, hannun shi ya saka ya ri?oni muka wuce har waje, motan da aka kawo na Waukan amarya Abba ya umurci su goggo da wasu a family su shiga, motan shi ya saka yayah muhammad ya matso mishi kusa da mu, baya ya buWe ya saka ni, sannan shima ya shiga, ya umurci Aunty Rakiya ta shige gaban nashi motan.

Duk ?an kai amarya ya saka suka wuce, muka bi su abaya, ashe kafin mu isa yasaka yayah Ahmad ya taho tare da A.G, masu rakiya dukka side Wina suka wuce, mu kuma muna isa A.G suka fito a parlon shi suka tarye mu shida yayah Ahmad.

Muna shiga A.G ya rusuna yana nunawa Abba wurin zama, kujeran da Abba ya zauna ya manna ni a gefen shi na zauna, shi kuma yana rungume dani a kafaWan shi, daga nan duk su Aunty dasu yayah suka nemi wuri suka zauna, shiru parlon ya Wauka bayan an gama gaisuwa, ?urawa A.G ido Abba yayi har zuwa wani lokaci mai tsawo, har sai da A.G yayi kaman ya koma ?asa ya zauna, saboda ?asa zai zauna Abba ya hanashi ya saka shi dole ya zauna kusa da Yayah Ahmad, duk sai A.G yaji kallon ya na tayar mishi hankali, har sai da Abba ya gama kallon shi na wani lokaci mai tsawo tukun yayi g?aran murya yace,

"Aminu"!
?ago da kai A.G yayi a nutse ya amsawa Abba da "na'am ranka ya daWe"!
Ya maida kanshi ?asa yana ?ara risinawa, ido Abba ya maida kan Yayah Ahmad yace "buWe mana wurin da addu'a", addu'a sosai yayi daya gama, Abbah yayi gyaran murya yace
"A.G ga Ayshaa ?ata da ka nemi aurenta akan ka ganta ta maka kana sonta, ka zaSeta akan ta zame maka uwar ?a?anka abokiyar rayuwarka right"? A.G ya Waga kai ya amsa da ehh, "a'a ka buWe bakinka ka amsa mun" Abba yace mishi, "hakane Ranka ya daWe, Allah ya ?ara girma," A.G ya faWa.
"good, nakawo maka Ayshaa da hannu na ba sa?o ba, na kawota na dan?a amananta a hannun ka Aminu, na kawo ta na baka amanan ?ata mafi soyuwa a zuciyata, ?ata da idan an taSa tou tabbas an taSa zuciya da rayuwar usman" Abba ya faWa yana nuna kanshi da hannun shi, hakan yasaka dukkan su suka sunkuyar da kansu ?asa suna jijjiga mishi kai.
"Ayshaa amana ce a wurinka Aminu, haka kaima amana ne a wurinta, kuma na jaddada mata ban yadda ba ban ?afe ba idan tayi wasa da amananka da yake kanta, ban yadda ba ta ?unsa ma ba?in ciki, ban yadda ta Sata maka ba sai a bisa kuskure, haka kaima,
Nakawo maka Aysha ne da sharaWin ban baka aurenta don ka wula?anta mun ita ba yadda dayawa maza sukeyiwa matayen su a yanzu, ban yadda ka dakar mun ?a ba, ban yadda ka kashe mun ita da ba?in ciki ba, idan Ayshaa tayi kuskure ka hukunta ta yadda addini ya tsara, amma dis time around duk wanda na bashi auren ?ata ya tozarta tou wallahi zanyi mishi hukunci daidai da abinda yayi, idan mutum yaji ?ata ya gajji da ita, tun wuri ya Wauko ta a mutunce yadda nakawo mishi ita ya kawo mun abata,babu duka babu zagi".
Sannan ya tausasa muryan shi ya cigaba, "Aysha ta samu tarbiyan da nayi imani da Allah ko bayan ranmu bazata bamu kunya ba, haka kaima nake kyautata maka kyakkyawan zaton na bawa ?ata miji nagari Wan manyan mutane, na ro?e ku ka haWa kanku ku zauna lafiya, daga nan Abba ya dinga haWamu yana mana nasiha mai ratsa zuciya daga ?arshe Aunty ma tayi mana, inda take gayawa A.G, bawai Abba bai yadda da tarbiyan shi bane ya kawo ni har yaja mishi kunne, a'a yayi hakane saboda karin magana da hausawa suke cewa, *IDAN MACIJI YA SAREKA.......* idan kaga tsumma dole ka kiyaye, saran da Aliyu yayi mishi ne yake firgice da shi, nan A.G ya nuna shi hakan ma yayi mishi, kuma ya ?ara jin aranshi Diamond mai tsananin daraja da tsada ya Wauko, kuma yayi al?awari da ?arfin shi da lafiyar shi da komai nashi zai kare Ayshaa, insha Allah sai kowa yace gara da akayi.

Tashi Abba yayi tsaye ya Wagoni muka tsaya, nidai ban da kuka babu abinda nakeyi, domin nasan Allah ya mun komai na rayuwa, ya bani gata na iyaye nagari, ?an'uwa nagari , dangi nagari, kuma duk maso ?aunata, gashi yanzu ya bani miji Nagari, mijin marainiya mai ?aunata, Abunda zan nema kawai Allah ya zaunar dani da shi lafiya ya bamu zuriya ta gari, hannu Abba ya mi?awa A.G, da sauri ya ?araso gaban Abba amma yakasa bada hannun shi, har sai da Abba ya rungumu shi, hannuna ya cire a nashi ya Waura akan na A.G, ae kuwa da hanzari ya ri?eni sosai, "Aunty nice nidai aduniya ban taSa jin wani halittah na Wa namiji daya taSa ri?e hannu na bayan Abba dasu yayye na, gashi dai Wabi'ace ta yayuna su rungumo mu, especially ma ni, Abba ma idan munje gaishe shi sau dayawa hannun shi yake mi?owa mu gaisa, amma ko yayah ishaq bamu taSa ri?e hannun shi ba saboda kiyaye wa, amma nidai ban taSa jin hannu mai laushi ba irin na A.G, har tsoro naji a zuciyata nace, hala taurin nawa hannun zaiji, saboda laushim da hannun shi yake da shi banyi tsammanin akwai maza irin haka ba a duniya", Nidai murmushi nayi ina bin hajiya Aysha da ido, matse hannuna yayi cikin nashi, ina jin yadda hannun shin yake rawa, a haka Abba ya sake jaddada mishi amanan da ya bashi, sannan ya umurce shi daya sada ni da Wakin shi, ina jin Abba yana zame hannun shi ajikina na zabura zan chafko shi, amma sai naji A.G yasaka dukka hannayen shi ya ri?e ni, ae kuwa da sauri na ?ara fashewa da kuka murya a sama nace, "Abba na kada ka tafi ka barni," amma sai abba ya dafa kaina ya ?ara saka mana albarka yayi hanya fiya daga parlon, aeko da ?arfi na Waga murya nace, "Abba sisto ka zaka bari da wani"? Tsayawa Abba yayi chak a bakin kofan, ganin haka Aunty Rakiya ta ?arasa ita da yayah Ahmad suka ri?e shi suka fice a parlon batare da ya juyo kaina ba, maida kallona nayi kan yayah muhammad da zaibi bayan su nace, "besty kada ku tafi ku barni tsoro nakeji", shima Wan murmusawa yayi kaWan bai kai chan ciki ba ya juya yayi waje batare da yace uffan ba, da sauri na maida kaina kan A.G, bakina har wani Wan Sari yakeyi nace, A.G nikan kabar ni na biso, tsoro nakeji",
Hmmm A.G duniya ne, kawai Jawo ni yayi ya buWe ?ofan Wakin shi ya shige dani, muna shiga kuwa ya rungumeni tsaf a jikinshi bai bani amsa ba tanbayan da nake ta mishi na ina zai kaini ne? Kuka na fashe dashi kawai mai ?arfi, idan banyi ?arya ba yakai sama da mintuna Goma muna a haka, har sai da aka ?wan?wasa ?ofan tukun naji muryan shi ?asa -?asa yana tambayan waye? "Hudah ce yayah", ajiyan zuciya ya sau?e, bai kuma Salle jikin shi da nawa ba yace, "meye ne kuma Hudah"?
"Mummy tace amaryar ka kaita za'a shiryata saboda buWan kai, su Yayah M.G duk sun shiryah", tou kawai ya amsa mata da shi ta juya ta fice.
Ina jin shi yayi tsaki yace "duk fitar M.G ne wallahi da wasu bidi'a, an Waura aure an kawo amaryah kuma meya saura ne nikan? Basai a ha?ura da bidi'an da baida wani dalili ba? Hala ?an rakiyan kawo amaryan ma Abba ya kafa su sun tafi".

Nidai da sauri nace, "wallahi suna nan, ina jin muryan su ma" shiru yayi baice uffan ba, kuma bai sake ni na tafi ba.
A tsorace na sake cewa, "mummy tace mu shiryah da wuri fa", still dai bai kulani ba, shidai ya manna kanshi shi a saman kafaWa ne, chan naji shi kaman mai barci yace,
"ko na ?ira Abba ne nagaya mishi suna nan basu tafi ba, don nasan yanzu zai umurcesu su tafi, mummy kuma babu matsalah Daddy ya isheta ta ?yale mu da maganan bidi'an nan".
da sauri na har da fashewa da wani sabon kukan nace, "wallahi nayi burin bikina ya zama akwai buWan kai da hawa, udan ba'ayi ba za'a mun dariya, kuma bazan taSa daina damuwan rashin yin ba", aiko ina faWin haka da sauri ya juyo dani ina kallon shi, dukkan hannun shi zube akafaWa na, tsoro naji yadda naga udon shi a lumshe kaman bazai iya ganina ba, a raunane ya buWe baki yace, "zan shirya muje, zanyi abun da kike so, ai naji ance ba haramun bane ma, amma don Allah ana gamawa su tafi kinji beauty", da sauri nake Waga mishi kaina alaman naji, nan kuwa ni kaWai nasan wani irin masifaffen tsoron da nake ji a ?asan zuciyata, har ?ofan da zai fitar da ni daga sashen Shi ya rakani, yana ri?e da dukkan hannaye na ya ?ira Hudah, tana zuwa yace ta wuce dani side Wina na shiryah, da sauri kuwa ta amsa mishi, dukka hannayenta ta saka ta ri?oni muka fice, a parlor na muka samu su Aunty Rakiya da sauran ?an'uwa, nan ta ri?e ni muka wuce Wakina, inda aka fara mun shirin fita wurin buWan kai da za'ayi a haraban gidan su A.G.
Wurin buWan kan ya cika ma?il da ?an'uwa da abokanan arziki, gefen mu M.G ne zaune da amaryar shi, sun sha ankon blue shaddah shida A.G, haka wurin Waurin aure sunyi ankon white shaddah, gefen shi Heedayah ce zaune fuska a rufe, nima gefen A.G aka zaunar dani,
M.G ne yafara buWe fuskan amaryar shi, bayan ya li?a mata kuWi ya koma ya zauna, sannan A.G ya tashi ya biWe nawa fuskan, ina jin shi yana li?a mun kuWi yana Wan taka ?afana a hankali, haka na share shi dai ban motsa ba.

?an uwana da nashi suna ta aikin li?a mana kuWi, gefe Waya ma ?an'uwan M.G suna ta li?a musu, Yayah Ahmad ne ya shigo shida wani aboki, M.G suka fara li?awa, sannan suka dawo kanmu, li?a ma A.G yayi, amma daya dawo kaina key Win mota ya Waura mun a tafin hannu na, aiko gaba Waya fili ya Wauki tafi, har sai da A.G ya mi?e tsaye ya rungume yayah Ahmad, M.G ma tashi yayi ya rumgumeshi fuskan su duka cike da farin ciki, hannu A.G ya mi?o kan cinya na ya Wage key Win, aljihun shi ya saka, gaskiya buWan kan ya ?awatar, ko dan motan da nasamu abun ya mun daWi sosai.

Daga nan motoci ne suka Wauke mu zuwa kallon hawa da zasuyi, shima hawan babu laifi yayi kyau sosai, ni dai dayake bai dame ni ba ko kaWan, so ba wani burgeni sosai abun yayi ba, A.G nah yayi kyau da shigan da yayi, a ido na ma kaman yafi kowani namiji a wirin kyau.


Zuwa ?arfe 10:00pm na dare dukkan jama'a sun watse, kowa ya kama gaban shi an gajji da ganin gidan amaren, haka ?awaye da dangi duk sun tafi gida, daga ni sai hadiza da zainab, sai hafsy da Aunty j da suke jiran yayah Ahmad yazo ya Wauke su, sun ?ara gyara gidan sun saka turaren wuta, ko ina ?amshi mai daWine yake fita, nima daidai lokacin na fito a wanka, Aunty j tana tayani kintsawa sai ga yayah ya ?irata akan su fito yana waje, batayi saurin fita ba sai dana shiryah acikin wata doguwar rigar atamfah mai kyaun gaske, ta gyara mun fuska da Wan light make-up, ta yafa min gyale ya rufe mun fuska bayan ta fesa mun turare duka jikina, ina jin su duka suka fita suka barni ni kaWai, nidai ban iya nace musu komai ba sai hawaye na da nake sharewa, ga wani irin fargaba da nakeji yana cika zuciyata, bayan wasu ?an lokuta masu Wan tsawo sai naji an buWe ?ofan Wakin baki cie da sallama, A.G ni ya shigo ina jin shi ya mayar da ?ofan a hankali ya rufe, ya Wan daWe kaWan abakin ?ofan, daga baya kuma sai naji takun tafiyan shi yana shigowa cikin Wakin, duk wani sautin takun shi haka nake jin sautin bugun zuciyata, kafin ya ?araso na haWa wani uban zufa kaman nayi gudun ceton rai.

Zama yayi a bakin gadon ya ?ura mun ido, chan kuma ya saka hannun shi ya yaye lulluSin kan, runtse idona nayi na?i kallonshi, ajiyan zuciya ya sau?e mai Wan ?arfi kaWan, sannan ya sunkuyo da kanshi saitin fuskana ya sumbaci goshina, "*MARABA DA KYAKKYAWAR SALIHAR MATANA, MARABA DA RAYUWAR A.G, MARABA DA HASKEN ZUCIYA DA GIDAN A.G, MARABA DA ?AWISUN A.G*"
ya ?arasa faWa yana haWa fuskanshi da nawa, nidai har lokacin ido na duk suna kulle, sai hawaye ne kawai suke bin kumatuna, harshen shi ya saka ya fara lashe hawayen, hakan da yayi ya sakani fashewa da kuka, shiru yayi ya dakata da abun da yakeyi, muryah a hargitse yace, "Eeshan A.G meyake faruwa? Kukan kewan su ummie ne ko kuma na farin cikin kasancewa da A.G? Idan na kewa ne nima na koma gefe nayi tagumi na kewan mummy nah, idan na farin cikine don Allah ki jirani muyi tare".

Ido na duka na buWesu akan shi, wai kukan farin cikin ganina a gidan shi? Lallai ma, shi bai san kewan ?an'uwana da iyaye na nakeyi ba ko? Rufe idona na sakeyi na ?ara sautin kukan, rungumoni yayi jikin shi sosai ya na lallashi na, da kyar dai ya samu nayi shiru, daga nan ya kamo hannu na muka fita zuwa parlor.

Kan kujera ya zaunar dani ya kunna mun T.V, sannan ya dawo gefe na ya zauna hannun shi ri?e da nawa yace, "kiyi kallo zanje nayi wanka na dawo, zaki bani labarin abunda kika kallah, ko zaki rakani nayi wankan"?
Juyar da kaina gefe Waya nayi na ?i kallon shi, murmishi yayi ya mi?e ya wuce side Win shi, yakai kusan 45mns kafin ya dawo parlon cikin wasu white kayan bacci, three quater ne da riga armless, sai wani ?amshi a hankali da yake tashi a jikin shi, kitchen ya wuce ya Wauko ledan da ya bansan lokacin da ya kai kitchen ba, a saman tray ya Wauro da filet da cups, ?amshin kajin ne ya cika parlon wanda jin hakan yasaka ni wani mummunan faWuwar gaba, wanda har sai da naji alaman kaman fitsari ya Wan biyo jikina, Wan gyara zama nayi ina mamakin tsoron da nakeji mai sakani mummunan faWuwar gaba irin haka, duk yadda yayi naci naman nan kasawa nayi, daya takurani ma kuka nasaka mishi, haka ya ha?ura yaci naman yasha jus Win shi, daga nan ya tattare su ya wuce ya kai kitchen.

Bayan ya dawo ne yazo gabana ya mi?o mun dukka hannayen shi akan na mi?o nawa ya tayar dani tsaye, kawar da kaina gefe nayi na tashi tsaye ni kaWai, hannu ya saka ya ri?o ni, muryan shi chan ?asa yace, "Beauty kina tsoro nane? Kini cin komai? Tou muje narakaki ki chanja wannan kayan ki saka na bacci a Wakina," Sata rai nayi ina kallon shi nace , "zan iya zuwa ni kaWai," idon shi cikin nawa yace, "kayan suna Wakina ne, su nake so ki saka bana son musu", shiru nayi kaman ina tunani sai kuma na bishi, duk jikina a tsarge da fitsarin da naji kaman yana shirin zubuwa.

muna shiga Wakin shi naji kaman an kwaWa mun guduma a tsakar kaina, dole naja ?afana na tsaya na dafa kan, a Wan furgice yace, "kan yana miki ciwo ne"? Kai kawai na Waga mishi alaman ehh ban buWe baki ba, kuma hannun yana dafe da kannawa, kamoni yayi yana shirin zaunar dani a bakin gadon shi sai naji wani sarawan kan ya ?aru, dole na ja na tsaya na?i, "bana son zama kaina yana ciwo sosai,"
"shiyasa nake son ki zauna ae princess, ina son ki Wan ji sau?in ciwon kan ne"

Raina ne naji yana Saci, ga wani tafasa da zuciyana yakeyi lokaci Waya, ?wace hannu na nayi na fice a Wakin da sauri, ina jin idan ban gita ba zuciyata zata buga, da sauri na koma side dina ina harhaWa ?afafu, ina shiga Wakina na wuce direct zuwa toilet, ina cire panta Wina sai naga period Winane ya dawo, abun sai ya ban mamaki domin banfi 9dys dagamawa ba aka Waura aure na, yanzu dai inaga 10dys ne ko 11dys da gamawa, dama babu abun da basu saka mun a toilet Win ba, sbd haka gyara jikina nayi na cire

33 / 46