ANA BARIN HALAL Hausa Novels by Anty Nice.doc

Author :  Auty Nice Category :  Hausa Novels 001

Chapter   3 / 46

6K to 9K   out of 137.2K words

?asa-?asa don tana shakkanta kuma tana tsoronta,
Abba ne duk ya dakatar da su idon shi akan mamie yace, "matsala ta da ke baki da wayo, baki da dabara, huruminane ko kuma dole nane akan ?a?ana mata? Kinga anyi auren su sun wofinta ne? Don Allah Halima bana son rashin hankalin ki, shiyasa abu dayawa bana son sanar dake sbd ?orafinki da nuna kishinki akai". Ya faWa yana barin wurin ya wuce wurin motan shi.


Ummin mu batace komai ba sai murmushi dake sau?e akan kyakkyawar fuskanta, haka zalika daga Yaya mohd, Ahmad, umar, ni da sauran ?an'uwa na mata babu wanda tace wani abu, sai duk muka juya mukabi wurin mototi guda biyu da mukazo a ciki, Raliya ce kawai cikin mu take ta wani harare hararenta na banza da wofi, mudai cike da farin ciki.


Bayan ankai amaryah gidan ta, ana ta saka albarka, a gidan da musu fatan zama lpy, kaii Aunty nice gidan yayi kyau, ranan na ?ara tabbatar da ?an maiduguri ?arshe ne a wurin ?yale, gidan nan kaman kada mu tafi ga wani ?amshi kaman babu gobe, inda muke tsaye nida Habiba da maryam wata yar Aunty Bintu ce tsaye, suna ce mata yah falmata, nidai matsawa da hanci nakeyi ina shinshina laffayanta Aunty nice, tafaWa fuskanta Wauke da dariya, nima ina dariyan nake ?ara maida hankalina kanta, sannan nace mata ae Hajjajo ?amshi rahma ne, tana dariya tace rahma Waya ko biyu, ae nidai tun ranan naji babu abinda nake so irin ?amshi, muna ji muna gani Yayah umar ya tiso ?eyar mu muka dawo gida, wanda har ga Allah bamu so ba, a wautar mu bamu ?i kwana a chan ba.


Da safe kuwa bayan sun karya sun shiryah suka biyo gidan mu domin yin sallah ma da mutanen gidan mu, saboda ranan duk zasu juya maiduguri, wurin 11:00am duk sun kama hanya cike da karamci irin namu na ?an bauchi da iyayen mu suka shiryah musu.


Bayan biki da sati biyu yayah mohd ya kawo Aunty Bintu gidan mu ta gaishe da iyayenmu, murna kaman babu gobe, don muna dawowa gida daga school muka ganta a parlon Ummin mu tana zaune, a gefe Waya kuma ummin ce zaune suna Wan taSa hira kaWan kaWan, tunda dama akwai sabo a tsakanin su, da gudu naje na mata oyoyo baki na kaman zai tsage don murna, itama fuskan ta cike da farin ciki tace, "ae nayi fushi daku Aysha, daga ke har habiba babu wanda ya le?oni"? Ina dariya nace zamuzo Aunty Bintu, mun koma school ne ga kuma Haddan mu an matsa mana zamuyi sau?a this year.

"Masha Allah" Aunty Bintu tace, sannan na mi?e nayi Wakin mu domin na chanja kaya.


Har sao wurin nine na dare tukun yayah mohd ya Wauke ta suka tafi, nida hafsy da habiba har wurin mota muka rakata, muna mata al?awarin Win zuwa mata ranan friday.

Motan su bai gama fita ba motan yayah Ahmad ya shigo gidan ,muma fasa wucewa mukayi cikin gida domin mun jiran ?arasowan shi, don yamana al?awari bai cika ba, gara kafin ya bar garin a san nayi.

Bayan sun gaisa da yayah mohd ya ?araso ciki da motan shi, yana buWewa muka ganshi bashi kaWai bane ashe, tare da wasu abokanshi muka gansu.


"kaiiii" naji muryan Habiba tana faWin, sisto juyo kiga wasu farare tare da yayah Ahmad kaman wasu halfcast, da sauri na juyo ina duban su, nace "hala twins ne, ina Yayah Ahmad ya samo fararen mutane haka? Har sun fishi fari" muka haWa ido nida Habiba, sbd kowani magana Waya tayi tou Waya tasan ina maganar Wayan ya dosa, ri?o hannu na habiba tayi muka ?arasa wurin Yayah Ahmad, hafsy na binmu abaya tana cewa, "inaga fah inyamure ne, don farin su yayi yawa, ko kyau basu mun ba sbd farin su yayi bauu, amma kukuma nasan sun burgeku, mayun farare kaman ku ba fararen bane", babu wacce ta kula ta muka ?arasa wurin yaya Ahmad.


Hannu ya mi?o mana yana "?an biyu Abba yyh kuke? Fuskan mu ciki da farin ciki muka mi?a mishi hannun mu mukayi musabaha, ran?washi ya kaiwa hafsy yana cewa, "jerry ina tom"? Baki ta turo tana "Allah sarki yayah Ahmad ni?an a gidan nan kaman kowa bai damu dani ba wlh, kowa Sai ?an biyun Abbah"? Ta faWa tana hararan mu nida habiba, mudai dariya mukeyi muda Yayah Ahmad, juyawa yayi yana duban abokanshi cikin shiru-shirun shi da rashin son sakewa da dogon magana yace, M.G, da A.G ga sisters Wina, yana nuna mu yace wa?an nan sune favourite sister Wina, suWin kaman twins suke ga hankali, wannan kuma yana nuna hafsy yace autar mu kenan, ita kuma twin sister nata halin su Waya basuji, yadda kasan tom and jerry haka suke, basujin magana basu son zaman lpy", ya faWa yana ri?o hannun hafsy data turo baki tana hararan mu.

Wanda naji yayan mu ya ?ira da M.G da AG Win muka juya muna gaishe su, suma cike da murmushi a fuskansu suka amsa mana, inda Wayan bayan gaisuwan bai sake cewa komai ba, saidai fuskanshi Wauke da murmushi yana duban mu, shima Wayan fuskanshi cike da murmushi yake ?ara mana tambaya akan ajin mu nawa? Habiba ce ta gaya mishi ajin mu da sunan mu, bayan ya sake tambayanta, sannan ya dubi hafsy yace ke kuma kece tom Win ko jerryn?

Dukkan mu dariya muka kwashe da shi, banda ita da tasake turo baki gaba tana cewa, "wallahi sunana hafsy ne"
Kawai dai kowa a gidan yafi son sune shiyasa ba'a ganin laifin su, amma wlh manyan ?an tawayen gidan mu kenan, kuma basu ji ga iya haWa munafurci," ta faWa tana ture hannu na da nakawo kusa da ita, yana dariya yace, "tou nidai banga alama ba, nima ina ga sune favourite sisters Wina, ke kuma inaga friend Wina zaki zama" still dai fuskan shi cike da fara'a, daga gani shi yana da Wan surutu, amma Wayan tunda ya amsa gaisuwan mu bai sake cewa komai ba, saidai yana bin dukkan mu da kallo, shima kuma fuskan shi cike da murmushin, amma dai bai sake tankawa ba.


Wucewa side Win su Yayah Ahmad sukayi, bayan muma mun juya side Win Hajiya Ummah, hafsy ko hararan mu tayi ta wuce cikin gida, kaman wasu munafukai, muna shiga parlon hajiya umma muka zauna a kujeranta two sitter muka haWa kanmu wuri Waya domin tattaunawa, kallo ta bimu baki a buWe tace, "wannan munafurcin da baya sakin ku kuma fah" kudai yaran nan kullum aka ganku cikin nu?u-nu?u na gulmah kuke, nidai duk wacce tayi gulma na nabarta da Allah, domin duk abun mutum da gulmanshi nan gidan Wanane, iko nane, idan ma hassada kukeyi ya kawo ni nan sai kuyi tayi" ta ?ara faWa tana hararan mu.

Mu dai dariya muka kwashe da shi muna kallonta, habiba ce ta bata amsa da, "in banda ke hajiya ummah gorin na menene? Muma idan muna raye zamu haifi yaran da zasu mana gida gidan sama ma mu wataya, bake da aka miki Wan akurki ba," ta faWa tana taSa ?afa na, don mun san yau zamusha gori iri-da kala, don hajiya ummah ji takeyi mu kishiyoyinta ne a wurin Abban mu, don ko shigowa mukayi tare da shi ta dinga hararan mu ?asa-?asa, watar tace amma dai kai kan jakin ?a?a nane, baka kama gabanka suma su kama gaban su? Amma kullum kana nani?e da su, su hanaka yin abun kanka?


Aiko kaman habiba ta jefa mata ?arfe a tsakarka ta zabura tana nuna mu da yatsa, "ahir Winku wlh, don babu wacce zata haifi Wa irin wanda na haifah, don ni Wana Waya ne tamkar da dubu,don ko gwabna bai kai shi kuWi ba, gwamne me a kusa da a kusa da usmanu nah? Ae inaga idan gwamnaty ta kasa biyan albashi usmanuna zai iya bawa gwamna bashi yayi albashi na wata Waya kam, kuma arzikin shi bai taSu ba, don kaf Tafawa Salewa ba'a taSa haihuwa irin nawa ba, kawai dai ya haWu da jarabawan tara mata marasa abinyi ne sai abun da ya musu", ta faWa tana mana kallon banza.

Dariya muka kwashe dashi, habiba tana cewa, "a tafawa mahaifiyar ?angoten bauchi" bakuyi gatse ba marasa kunya ni nan da kuke gani nafi uwar Wangote farin cikin haihuwar Wa mai albarka,

Hajiya Aysha tana duba na cike da dariya tace, "Aunty nice kinsan kakarmu irin mutane ne masu son nasu, kuma har cikin zuciyarta ji take duk ?asan nan babu wanda yakai Abban mu sukuni, shiyasa muke manna mata hauka akan Abban mu yafi gwamna kuWi, kuma ta hau ta zauna," Dariya nayi ina ?ara maida hankalina wurin Hajiya Aysha, ina kuma ?ara jinjina irin baiwar kyau da Allah ya mata, domin murmushi fuskanta ba ?aramin kyau yake ?ara mata ba


Tun ranan da mukaga abokan Yaya Ahmad bamu sake ganin su ba, kasancewar shima ba a gari yake zama ba, amma rana WaWWaya ne bamu hiran su nida Habiba, wanda har ta kai mun bawa Maryam labarin su da irin farin su, cikin zolaya maryam ta kalle ni tana dariya, "amma dai Ayshaa ke kike koyawa habiba ganin kyaun farin mutum? Kuma daga dukkan alamu kin ?yasa? Inaga gara a sanar da yayah Ahmad"'

Hararan ta nayi nace, "ban dake maryam yaushe ma na girma da har zanga wani nace ina so? Soyayyan ma ae bamu kai ba, kuma bani da class ne zan ce ina son su? Kawai ni fararen mutanene bana gajjiya da ganin su, kin san bana son ba?in fata", dukan da habiba ta kai mun ne na hankalta da kwafsin da nayi, don mantawa nakeyi mamie ba?ace, haWa ido mukayi muka kwashe da dariya dukkan mu.


Babu wasa rayuwar tana wani irin gudu, a haka yau muke kammala waec Win mu, kowa a cikin mu cike da farin ciki da burika kala-kala a zuciyar mu, ranan dukkan mu huWun, ni, habiba, maryam, jamilah muna zaune kafin driver yazo ya Wauke mu, a yanayin mu bamu da hayaniyah dukkanmu, sai dai nida habiba da maryam idan mun haWu mukan taSa surutu sosai a tsakanin mu, amma idan wanda bai sani bane bazai taSa yadda muna da surutu ba, amma ita jamila da wuya kaji maganan ta, sai dai kawai ta biku da ido, jamilah bata da matsala ko kaWan, shirunta yayi yawa, amma akwai azaban kai, domin kanta yana mugun ja sosai.


Maryam ce ta dubi jamilah tace, "yanzu besty da gaske auren za'a miki? Tou karatun naki fah"? Ta faWa fuskanta cike da jimami, domin duk munyi shawaran karatu zamuyi a wuri Waya, wato ATBU, don ko jamb Win mu shine first choice Win ko wacce a cikin mu.


"Besty tou an yanke muyi auren saboda na bishi chan na fara karatuna, nima kuma gaskiya hakan yafi mun, don ina tsoron yana tafiyan nan wata ta mun wuff da shi", dukkan mu dariya muka kwashe da shi, ni kuma na zabga tagumi ina duban Jamilah cike da mamakin wai zatayi aure, cousin Winta ne, kaman wasu zamu shiga SS 3 yace yana sonta, kuma cikin hukuncin ubangiji yagama masters Win shi a London kawai ya samu aiki achan, shine iyayen su suka yanke kawai ayi auren su tafi tare, idan yaso karatun sai tayi achan.


"ikon Allah" kawai na furta ina kallon ta, sannan nace, "jamilah kuma zaki iya rayuwar auren da Wan ?aramin shekarunki?" kallo na tayi tana murmushi tace "me zai ban tsoro, yayah nane fah, kuma zai Waga mun ?afa sai na ?ara girma yace mun".


Dariya dukkanmu muka kwashe da shi, habiba ta dubeni tana Waga kai cikin salon mu idan zamu zolayi mutum tace, "dogon magana" kwashewa muka sakeyi da dariya, maryam da jamilah na taya mu.

Maryam ce ta dube mu tace tou yanzu me zamuyi na event? Kun san muma yanzu bebs ne, don mun girma ta faWa tana wani juya idanunta, shiru mukayi na zuwa wani lokaci, sai jamila ta gyara zama tace, "mummy na zasuyi liyafa ne kawai, nima bana son wani event sosai, tunda angon yace shi babu wani event da zaiyi bayan recieption da zasuyi, saboda haka ya kamata mu gwangwaje adon mu a liyafar nan.

Da yake nima bana son wani damuwa sosai sai kawai na bada ?arfin ayi hakan, babu yadda habiba da maryam suka iya kowa sai ta amince, a haka drivern su yazo ya Wauke ta, muma babu daWewa aka zo aka Wauke mu.



Bikin jamila ya gabato sai shirye-shiryen ashobi mukeyi, inda muka haWu da wasu friends Winta guda 6, sai cousins Winta guda 2, muka zama mu 11, muke ta shiri da tsare-tsaren mu, ranan da mukaje sallon a *SHAGARI SHOOPING COMPLEX* Yayanta Aliyu ne yazo Waukan mu, shima yadda kika ga jamila da kyau da shiru tou shima haka yake, sai dai ba fari bane, kuma baza'a ?irashi ba?i ba, saboda yana da haske wanda wasu zasu iya kwatanta shi da fari, amma a wurin wanda basu ganin fari sosai, lecturer ne a Federal polytechnic bauchi, yana Computer depertment, Wan gayu ne na nuwa, kuma daga ganin shi mai tsafta ne, don motan shi wani irin azaban ?amsh yakeyi, ga kuma sanyin A.C

Gidan mu aka fara wucewa ya sau?e mu, sannan suka wuce tare da jamila da wata cousin Winta Ummitah, daga kaduna suka zo, kuma sun sha?u sosai da jamilah, saboda kullum hiranta Ummitah ne.


Muna shigowa gate Win gidan mu Habiba ta juyo tana kallona, fuskan ta cike da gulmah tace mun, "sisto naga daga dukkan alamu Yayan jamilan nan hankalin shi yana kanki, duk wani nutsuwar shi ina hankalce da shi, sai kallonki yakeyi, ita kuma ummitan nan inaga sai wani rawan kai take mishi, har da wucewa gaban mota ta wani zauna, bayan duk hankalin shi baya tare da ita,"

Hararanta nayi nace, "ke kuma cutar gulmar ki ta motsa duk kin kafe shi da ido, saidai in kece ya miki har ya birge ki, don ni wnn ba layi na bane, fari nake jira", ina faWan haka na juyo ina kallon habiba na kama haSa na, "habiba niko ina dai labarin fararen abokanan yayah Ahmad Winnan? Kullum yazo ina hankalce ko zan sake ganin su amma shiru, ko dai aljanune?" na faWa ina Wan zare ido.


Dariya ta kwashe da shi tana cewa, "inaga wannan karon idan yayah Ahmad yazo dole ayi cikiyar su, kada naje sun kama kurwar ?anwata," hararanta nayi nace, "me kike nufi? Kina tunanin sun shiga raina ne? Kuma waye ?anwarkin?" Allah sarki habiba na, wato Aunty nice kullum kika ga faWan mu tou akan shekaru ne, kowa bata so ace itace ?arama, a haka ma habiba da tasan ta Wan fini da kaWan wataran ta kance ta bar mun girman, ta ?ara mun shekara uku ma bayan wata ukun, ni kuma na dinga tsokananta ae tunda na fita tsayi tou na rigata zuwa duniya, a haka muke kullum cikin soyayyar junan mu, donni son da nake yiwa habiba ko hafsy da muke ciki Waya bana mata.


Washe gari tun safe muka tafi gidan su jamila, saboda wacce zata mana make-up da wuri zata zo.



*EVENT CENTRE* a wurin aka shirya yin liyafan, masha Allah amaryah tayi musulmin kyau ita da ?awayenta, sai wani jin falli mukeyi irin muma mun girman nan, har mun fara aure, da yake shine biki na farko da muka farayi na ?awayen mu sai abun ya ?ayatar da mu sosai, sai wanni basarwa mukeyi muna wani rangwaWa irin ?awayen nan, Aysha ta faWa fuskar ta kaman alokacin ake hidiman, ga kuma wani rangwaWa kanta da takeyi, kaii ni Aunty nice ina ga mata mai yanga kam, don ?uri na mata ina kallon yatsun hannunta yadda take watsa su kaman wata Wawisu, ga magana Waya tana juya idon nan kaman ka sace ta ka gudu, gaskiya macen da bata da yau?i ta rako mata duniya ne, na faWa a cikin zuciyata.


Aunty nice ina baki labari, maganan habiba kuma sai ya tabbata, domin Aliyu yayan jamilah gaba Waya ya takura ni, duk inda nayi idon shi yana kaina, tun lokacin da muka fito za'a tafi wurin liyafan yakasa ya tsare dole sai na shiga motan shi, haka ya aiko Fatie ?anwar su mai bin jamilah ta ?irani, gashi ba mai son magana ba, ina fitowa yace na shiga motar shi, ido na zuba mishi ina Wan kame-kame da ri?e gyalen jikina, a haka na daure nace mishi zan bi motan amaryah ne, ya kallo ya bini da shi cikin nutsuwa da kwantar da kai yace, "amaryah ma da angon ta zasu tafi, kema kibi naki angon kawai ku wuce tare", ya faWa bada wani damuwa ba kaman dama muna tare.


A razane na kalle shi nace, "ni kuma? Ni ae banida aure, yana duba na ido cikin ido yace, "ehh kema ae zakiyi tunda ba tabbata xakiyi ba, babu yadda na iya da shi, dole naje na jawo habiba da maryam akan mutafi tare, kafin kuma kiyi haka ummitah ta fito tayi jikin motan Aliyun tana wani rangwaWa, gata kaman zata Salle don rama, "Bro bari nazo mutafi, tun da kaima chan kanufa.
Dubanta yayi kai tsaye yace, " bana son takura ki wuce ki nemi wani motan, akwai wanda zan tafi dasu", kuma bai wani Sata lokaci ba ya buWe mun gaban motan fuska a Waure ya mun alaman da na shige, sannan ya dubi habiba da maryam ya musu alaman su shige bayan motan, ko takan ummitah da ta buWe baki tana kallon mu bai bi ba.


Ummin mu da maman maryam da mamie duk sunzo wurin liyafan, mamah kawai aka bari a gids, duk inda mukayi idon ummi yana kanmu.


Bayan an buWe fili da addu'a an fara programm babu daWewa ango ya iso da rakiyar abokan shi guda uku, bayan sun zauna babu daWewa D.J ya basu umurnin fitowa filin, aka saka musu wa?an aure, haba zokiga iyayen zamani, ba uwar amaryah ba bana ango ba, duk Sarin kuWi sukeyi, damu abu duk Waya, kai ranan naga matan manyan bauchi, kowa Sarin naira kawai takeyi don ace ita ce tafi burgewa, bayan fili ya Wan lafah amaryah sun koma sun zauna, sai D.J ya sake bada daman ?awayen amaryah su fito fili.

Da ?yar maryam ta ri?o hannu na muka fito, domin

3 / 46