AKWAI SILA HAUSA NOVELS BY AMANARCOOL.doc

Author :  Amanar Cool Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   1 / 11

1 to 3K   out of 32.7K words

??ࡱ?>??  
????
???????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? P?'KSKS?.?????????JJm JT???,
1 $? h? B?? ?U  =ئ? AKWAI SILA=ئ?


BY AMANARCOOL


YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION/ YOTA ID/O21


Godiyata ba za ta gushe a gare ki ba Aysharcool. A matsayin ki na uwa a gare ni a Duniyar marubuta, kuma ?ar uwa amintacciyata, na tsinci kaina cikin wani gata da ba kowa ke samu ba. Kin ri?e mini hannu da gaskiya da amana, kina faWa min abin da ban sani ba cikin natsuwa da kulawa. Duk irin hasken da zan samu a harkar rubutu ki ce sila, akwai gudummawarki, akwai tausayi da jajircewarki. Ina alfahari da ke, kuma ina yi miki godiya mai yawa wadda baki ba zai iya faWa ba. Allah ya saka miki da alkhair, ya ?aro miki Winbin nasarori a rayuwarki.


Ina mika godiya ta musamman ga shuwagabannin ?ungiyarmu, musamman Aunty Sarauta da Aunty Zee Kumurya, bisa irin kulawa, gyara da shawarwari masu daraja da kuke bani a kan rubutuna. Goyon bayan da kuke bani ya ?ara mini kuzari da ?arfin gwiwa sosai. Allah ya saka da alkhairi, ya ci gaba da Waukaka ku a duk inda kuka dosa.


(3E 'DDG 'D1 -EF 'D1 -JE

PAGE 1-2



Misalin ?arfe goma na dare, daren ya yi duhu sosai irin duhun nan da yake cinye inuwa ya bar zuciya. Garin ya yi tsit ba ka jin motsin komai, cikin tashin hankali da kaWuwa take tsala gudu na fitar hayyaci, gudu take irin gudun da ba a iya sarrafa shi, gudun da ba ?afa ke yi ba, tsoro ne ke tura ta gaba kamar an Waure ta da iska. Idonta na kallon gaba amma zuciyarta ta ma?ale a baya. Jin sawun ?artin mazan nan masu kama da samudawa na binta cikin kaifin mugunta. Zuciyarta na bugawa tamkar za ta yi tsalle ta fito daga ?irjinta. Kowanne mataki da take Wagawa yana yi mata nauyi saboda tsananin firgici, sai dai duk da haka ?afafunta ba su tsaya ba, sai ?ara hanzari suke yi.

A bayanta take jin ?arar takun takalmin waWancan ?artin nan suna biye da ita kalmomi masu ban tsoro kamar hadari na fita daga bakinsu,  Ki tsaya mana, ba zamu cutar da ke ba . Sai dai muryarsu ta nuna akasin haka, tana Wauke da ?iyayya da mugunta. Can kuma jin Waya ya ce  Idan ta kuSuce mana wallahi za mu gamu da bala'i .

Dim! ?irjinta ya ?ara ba da wani sauti mai nauyi, ta ?ara ?arfin gudunta, hawayen tsoro na taruwa a idonta. Ta juya gabas sai ta tarar da duhu, ta nufe arewa sai ta ga daji mai ban tsoro. Ta rasa inda hanyar da ke gaban ta take, gudu kawai take yi jikinta na rawa sai ta ji ?asa ta canja a ?ar?ashin tafin ?afarta kamar ba ita ce hanyar da ta saba gani ba. Wata iska mai sanyi ta daki fuskarta, a take gashin jikinta ya mi?e tsaye. Ta kalli gaba sai ta ga wata hanya siririya, tamkar ba za ta kaita ko ina ba, sai dai ba ta da zaSi ta shige cikin hanyar da gudu.

A daidai lokacin da take son tsallake wani ?aramin dutse, ?afarta ta zame. Ta ji ?asa ta yanke kamar wani abu ya huda sararin Duniya a ?ar?ashinta. Ba ta yi aune ba ta afka cikin wani guri mai zurfi da faWi, ihu ta yi wanda sai da ya karaWe gurin gabaWaya har sautin ya doki kunnen ?artin mazan dake bin ta.

...............


?aramar yarinya ce, da ba za ta wuce shekaru goma ba. A hankali aka ji saukar takunta daga saman bene, ?afafuwa masu sanyi, kamar wadda zuciyarta ke kiranta, ?asa ta sauko ta bayyana a falon da murmushin kuka a muryarta ta ce

 Sorry Dady, na fito

Dady ya Waga kai yana kallon ta murmushi mai cike da soyayya ya bayyana a fuskarsa.  Haba shalelena, ki daina ba ni ha?uri ai ko kin yi tsawon awa ba zan ji haushinki ba. Kin yi wa Momy sallama? .

Ta girgiza kai cikin Wan wasa. Ya ri?e hannunta suka nufi harabar motoci. Ita ce ta zaSi motar da zasu shiga. Ya buWe mata ta shiga, sannan ya zagaya shiga ya ja motar da kansa suka bar gidan.


Wani matashi ne da ba zai wuce shekaru sha takwas ba. Zaune yake a cikin bola tamkar wanda Duniya ta manta da shi. Busasshen biredi yake taunawa, ya haWa uban gumi saboda rana. Wani lokaci yana wasa da hannayensa, wani lokacin yana zabura kamar wanda tsoro ya taso masa daga ciki, daga ?arshe ya mi?e ya fara wata irin rawa mara kan gado, rawar da ba ta da wata ma ana face irin ta mutanen da hankali ya rikice musu, sai da ya haWa gumi, ya koma ya zauna yana tsinkar tarkacen datti yana ci. Sai kuma ya yi shiru. Ya fashe da kuka mai tashin hankali, ya kwanta yana birgima kamar yaro ?arami da aka tsane shi da ciwo.

A hanya kuwa Joriyya da Dadyn ta na hira cikin nishaWi babu wanda ya kai Joriyya ?ima a zuciyar Dady. Ita ce autar gidansa, kuma ita ce abar son zuciyarsa. Duk abin da zai faranta mata rai zai yi. Suna wucewa kusa da gurin mahaukacin, ta sauko da gilas Win motar. Idonta ya tsinci matashin nan da yake birgima cikin datti yana kuka a cikin zafi.

 Dady

 Na am shalelena?.

 Duba can ga wani yana kuka a rana .

Ya Wan kalli bangaren ya ce  Eh na gani rabu da shi, ai mahaukaci ne

 Mahaukaci kuma? Ta tambaya idonta cike da tausayin da ba ta ko tunanin na mene ne.

 Eh. Ina yawan ganin shi. Wani lokaci dariya yake, wani lokaci kuka.

Joriyya ta ja numfashi, ta ce  Dady mu koma gurin shi.

Ya kalleta da mamakin shagwaSarta  Shalele me za mu yi masa?

 Wata?ila yunwa yake ji. A siya masa abinci Dady mu koma don Allah

Ya yi shiru sannan ya ce  To ina ruwanki da shi?

Ta zumSura baki ta juya kai ta yi shiru. Nan Dady ya gane ta yi fushin, sai ya yi dariya.  To shikenan bari mu juya ta saki murmushi mai cike da jin daWi. Suka koma inda matashin yake. Dady ya fita, ita ma ta fito. A can gefe ya hango wata mata mai saida abinci, suka nufe ta. Dady isa gurin da sallama ya ce  Dan Allah abinci mai yawa nake son ki bawa wancan mahaukacin ki kai masa .

Ta firfita  Alhaji? Kai masa? Gaskiya bazan iya zuwa ba in dai kai zaka je ka karSa, gaskiya ni bana shiga inda yake D
duka yake . Wani saurayi can gefe ya ce
 Kai ka ji mugunta ke ba za ki kai masa ba saboda kina gudun duka, amma shi ki ke so ya je? . Ta harare shi ta ce  Ni mace ce, shi kuma namiji ne ai ya fi ?arfin irin abin da zan yi Dady ya tambayi mai abincin
 Duka yake?.

 ?warai kuwa, babu wanda ke zuwa kusa da gurinsa

Ya Wan yi shiru sannan ya ce  To zuba min kawai ta zuba ya biya suka Wauki ruwa da lemo, Joriyya ta nufi mahaukacin, sai Dady ya ja ta baya ya ce  Shalele ki tsaya, ki bari zan kai masa .

Ta girgiza kai  A a Dady ni zan ba shi .

Mahaukacin ya zauna yana kallon su. Idonsa jawur, fuskarsa cike da gumi, sai ya mi?o hannu kamar yaro mai ro?o, kafin Dady ya yi magana, tuni Joriyya ta mi?a masa abincin idonta ?ur akansa tana kallonsa da tausayin da ta kasa Soyewa. ya karSa sannan suka juya za suka wuce, sai mahaukacin ya Waga ?afa ya hankaWe Dady, taga-taga ya yi zai faWi Allah ya tsare bai faWi ba. Ya ce  Kin gani ko Shalele wannan nake gujewa, yanzu da ya karya ni fa? . Ya ja hannunta da Wan zafi suka shiga mota. Joriyya ta yi shiru har suka yi zagaye da yawa. Duk da ta ga yadda ya kusa cutar da Dady, hakan bai rage tausayin da take ji masa ba.

Sun daWe suna zagaya gari Dady dauriya ce kawai yake yi, saboda ?afarsa tana yi masa ciwo sosai, ya yi mata siyayyar kayan ciye-ciye da yawa. A gajiye suka koma gida. Nan suka tarar da Junior ya zo gidan, cikin farin cikin dawowarsu ya gaishe da Dady, Momy ma sannu da zuwa ta yi musu, Dady ya zauna a nan falon, Joriyya kuwa ganin Junior yasa ta yi kicin-kicin da fuska. Yana yi mata magana ta yi kamar ba ta ji shi ba, ta fara ?o?arin hawa sama.

Momy ta ce "Auta ba ki ji Yayanki na yi miki magana ba?".

"Momy bacci nake ji ne" daga haka ta yi haye sama, Momy za ta kuma yi mata magana, Dady ya Waga mata hannu alamar ta yi shiru.

"Haba Dadynsu wannan yarinyar na rasa me yake damunta ne? Ni lamarinta mamaki yake ba ni, yarinya ?arama da ita sai shegen girmankan tsinya, kwata-kwata ta raina Jiniyo ba ta ganin girmansa ko kaWan, indai ya zo gidan nan haka take yi masa wannan iskanci kuma ta san saboda ita yake zuwa gidan, tunda na haifeta yake matu?ar sonta da ba ta kulawa amma ita ba ta gani, ai ko tana yarinya ta san mai sonta da kuma kyautata mata" Momy ta shiga masifa Dady ya yi mata shiru daga ?arshe shima tashi ya yi ya haye sama Win.vMomy ta ce "Jiniyo yi ha?uri ?yaleta ka ji, kaima ka daina damuwa da ita, tunda ba ta san harkar arziki ba" . Ya ce "Ai babu komai Momy, Joriyya yarinya ce sai ana ha?uri da ita, ni banji hsushinta ba, kinga ai a gajiye take".

"Duk da haka Junio Joriyya akwai raini a cikin lamarinta, kusan shekara goma ka bata amma take yi maka wannan rashin kunyar, son da kake nuna mata ko yayunta basu nuna mata shi" shi dai Jiniyo ya shiga bawa Momy ha?uri, akan ta daina yi wa Joriyya faWa ?uruciyya ce ke damunta. Ya daWe a gidan kafin ya yi wa Momy sallama ya bar gidan.

Tashi Momy ta yi ta shiga Wakin Joriyya a zaune ta tarar da ita saman gado ta baje kayan ciye-ciyen da Dady ya siya mata tana ci tana game a wayarta. Zama Momy ta yi tana kallonta ta ce

 Auta halin da kike yi wa Jiniyo ba daidai bane. Tun kina jaririya yake miki gata amma kin raina shi da yawa .

Shiru ta yi, sai can ta ce
 Momy kin san wani abu kuwa? .

 A a sai kin faWa .

 Mun ga wani yana kuka a cikin datti yau sai da na sa Dady ya siya masa abinci. Amma bayan mun kai masa sai ya hankaWe Dady .

Momy ta firfita  Subhanallah! Dadynku kuwa? Me ya kaiku can? .

 Ni ce na takura .

Momy ta ri?e haSa ta ce
 Auta ki daina irin wannan halin. Ko da kina tausayi, ki kula da kanki . Daga haka Momy ta bar Wakin tana girgiza kai.

Momy ta fito daga Wakin Joriyya kai tsaye Wakin mijinta ta nufa. A hankali ta tura ?ofar Wakin, Dady na zaune gefen gadonsa yana shafe ?afarsa da ruwan sanyi, fuskar nan tasa mai Wauke da girman kai da alfahari da dukiya tana cike da gajiya da Wacin ciwo. Bai Wago ba har sai da ta ?araso ta tsaya gabansa. Ta ce da siririyar murya mai cike da damuwa
 Alhaji na ji abin da ya faru yau .

Ya Waga kai a hankali ya dube ta ya ce  Kin ji komai kenan? .

 Eh Joriyya ta faWa min, yadda mahaukacin nan ya hankaWe ka to me ya kai ku gurin mahaukaci? .

Dady ya yi ?asa da murya  Kin san halin yarinyar nan. Idan ta saka abu a ranta ba ta da sau?i, ni ma ba son raina na je gurinsa ba, sai don gudun rigimarta, kuma kin san ba zan iya jure kukanta ba". Momy ta zauna kusa da shi tana kallon fuskarsa.
 Amma Alhaji mahaukaci fa? Ka san haWari ne da shi. Babu wanda ke shiga inda yake, kai kuma ka je, ka san ba mu da hulWa da irin waWannan mutanen. Sun fi jawo bala i fiye da alheri .

Dady ya Wan yi murmushi mai Waci, ya ce  Shi ne fa dalilin da ya sa ban son su. Ni ba ruwana da talakawa, Shafa babu abin da ya haWa mu da su. Su na kawo bala i da nauyi. Ina kuka da su? Amma ita Shalele.." sai ya yi shiru, ya shafa gemunsa. "Wannan yarinya tana da zuciya mai tauri, ai dole na biye mata, amma ba zan kuma kuskuren bari ta kusanci wannan mutumin ba .

Momy ta ce  Ka yi a hankali, ai ya kusa cutar da kai yau, wannan rigima ta Auta daga ganin mutum baki san asalinsa ba ki ce sai an siya masa abinci . Ta mi?e tsaye ta ce  Allah ya tsare ya tsare gaba zan je in duba maka abincinka .

Jiniyo na zaune a harabar gidansu yana sosa kai kamar mai jiran hukunci. Fuskar nan tasa ta matashi mai ?ananun shekaru ta nuna alamun damuwa fiye da shekarunsa, mahaifiyarsa Hajiya Munira ce ta fito, wadda ta kasance ?anwar Momy ta ce  Hamma me yake damunka haka yau? Tun da ka dawo daga gidansu Aunty Shafa kake ta kai kawo kamar wanda aka faWa masa mugun labari? .

Ya sauke numfashi mai nauyi ya ce
 Mama Joriyya ce .

Ta Wan yi dariya ta zauna kusa da shi, ta ce  To ita kuma wane sabon abin da ta yi maka yau? .

Ya Waga kai da murya mai sanyi ya ce
 Mama ban san me ya sa ba amma tun da na balaga zuciyata ta tsaya a kanta. Amma ita ko kallona ba ta son yi . Da nayi magana sai ta yi kamar ba ni bane, kuma idan na je gidan su, sai in ji kamar ina Waure zuciyarta kamar ba ita nake so ba .

Mahaifiyar tasa ta girgiza kai ta kuma cewa  Hamma ka san wannan gidan dukiya ce kawai da girman kai ke Wawainiya da su. Ita Joriyya ta taso tsakanin gata da shagwaSa ne. Ka yi hankali kada ka cutar da kanka akanta .

Ya ce  Ni dai ban iya daina tunanin ta. Kuma Mama tun tana ?arama nake jin kamar ita ce matata . Murmushi ta yi cikin murya tausayi ta ce  Allahu ya kyauta. Amma ka ri?e kanka, kada ka nuna wa kowa" ya yi shiru, zuciyarsa na tafasa da soyayyarsa marar gata, mara amsa.

Da daddare Joriyya na kwance saman gadonta, kayan wasa da kayan marmari a warwatse, amma hankalinta bai kan su. Idonta a lumshe, tana sake hasko hoton fuskar mahaukacin da ta gani yau, ta tuna jajayen idanuwansa, da birgimarsa cikin ?ura, yadda ya ri?e abincin da ta mi?a masa kamar wanda bai taSa ri?e komai ba a rayuwa. A hankali ta ce "Shi ma wani ne ya haife shi, me ya kawo shi haka? Wai me ya sa ya fashe da kuka kamar yaro? Me ya sa babu wanda ya kula da shi? Ya ci abincin kuwa bayan mun tafi?". Nan take ranta ya soma nauyi.Ta zaro numfashi, zuciyarta na cike da wani sabon abu na tausayin da bata san dalili ba. Har kwanciyarta ta kasa nishaWi tunani ya rufe mata ido gabaWaya.


By Amanarcool
'?
08163516796



=ئ? AKWAI SILA =ئ?


BY AMANARCOOL


YOTA ID/O21


*SHIN RAMA CE MATSALARKI? BUSHEWAR JIKI KO KUMA MATSALAR SANYI? TO ALBISHIRINKI, NA ZO MUKU DA INGANTACCIYAR SABAYA DA AKA SARRAFATA DA NATURAL GRAINS, HERBS DA KUMA SPICES, WADDA ZA TA INGANTA LAFIYAR JIKINKU, TA CIKO DA JIKI, SAMAR DA RUWAN NONO GYARAN BREAST, TA KUMA YI MUKU MAGANIN SANYI DA MA SAURAN GYARAN JIKI NA MATA, DUK A KAN KU?I ?ALILAN. SABAYARMU BA MA SANYA ?WAYA A CIKINTA, DA TSIRRAI KAWAI MUKE SAMAR DA ITA. SANNAN AKWAI MAGANIN SANYI GA MASU FAMA DA MATSALAR INFECTION KOMAI DA?EWARSA. AKWAI COMPLETE SET NA GYARAN BREAST, SPECIAL PACKAGE, KU NA IYA TUBTU?A TA KAI TSAYE KU TUNTU?E NI AYSHERCOOL TA LAMBOBIN WAYATA 08081012143*.


PAGE 3-4


Washegari tun kafin gari ya fara yin haske Joriyya ta farka da wani irin Waci a zuciya. Tunanin mahaukacin ya rufe mata ido kamar mafarkin da ya?i Sacewa. Ta tashi ta wanke fuska, ko breakfast ba ta jira ba ta nufi kitchen. Mai aikin gidan Lami ta taso da mamakin ganin Joriyya ta shigo kitchen cikin sauri fuskarta Wauke da damuwa.  Lami ta faWa da ?aramar murya mai nuna umarni  ki girka min tuwon semo da miyar taushe. Ki tabbatar kin saka nama da kayan ciki sosai .

Lami ta kalle ta da mamaki ta ce  Amma Auta ke ba ki cika cin irin wannan ba, ko dai Dady ne ya bu?ata? .

 Ba don mu za ki yi ba ta amsa tana haWe hannuwanta, ta kuma cewa  Wani mutum ne wanda muka kai wa abinci jiya ina so a ?ara kai masa yau. Yunwa yake ji . Lami ta tsaya cak, ta ji duk jikinta ya yi wani irin sanyi.  Auta wancan mahaukacin da na ji Hajiya na magana akansa? Ko ni ba zan iya tsayawa kusa da shi balle ke, ko nesa da shi ba zan iya tsayawa ba .

 Ba ke za ki je ba Joriyya ta katse ta  ni zan kai amma tare da Dady zamu je . Daga haka ta juya ta fita da sauri kamar wata wal?iya. ?akinta ta kuma ta shirya, bayan kamar awa Waya ta fito.

A falo ta ga Momy zaune tana shan tea, Dady na gefenta yana duba wasu takardu. Joriyya ta sauko a hanzarce tana takowa kamar mai son sanar da wani abin gaggawa, ta ce  Dady ta tsaya gabansu, idonta ya cika da wani irin abu mai kama da kuka.  Dady don Allah mu je wajen mutumin jiya. Lami ta girka masa abinci . Dady ya Waga kai a hankali, ya Wan yamutsa fuska, ya ce  Auta ban shirya shiga bala in wancan mutumin ba yau. ?afar nan tawa har yanzu tana yi mini zafi . Momy ma ta Waga

1 / 11