AKWAI SILA HAUSA NOVELS BY AMANARCOOL.doc

Author :  Amanar Cool Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   7 / 11

18K to 21K   out of 32.7K words

ce mata ina sonta, bani da wannan tunanin a raina, don haka ki daina wannan maganar ba na so, ba don ke ce kika zo mini da zancen nan ba da sai na yi mugun saSa ma ko waye ba".

"Yaya ni gaskiya ba zan ha?ura ba, dole ne ka ?ara aure, ni ka bar ni zan nemo maka matar da za ka aur...."

"Ke Mariya" ya katseta a tsawace ya ce "Ba na ce ka da in sake jin wannan maganar ba? Zan yi mugun saSa miki, maza tashi wuce ki bani guri".

"Yaya yau ni kake kora saboda kawai na ce ka ?ara aure? Yanzu kafin son farin cikin matarka akan ni ?anwarka da muke ciki Waya? Yaya ni ce fa Mariyarka" ta ?arasa maganar tana ?o?arin zubar da ?walla.

Sai kuma jikinsa ya yi sanyi, ya sassauta murya ya ce "Kina jina Mariya, ba wai bana son farin cikin ki ba ne, ba ni da ra'ayin ?ara aure ne, ki yi ha?uri kin ji".


"Ni gaskiya da sake, matar nan ba za ta zauna ita Waya a cikin gidan nan ba". Daga haka ta mi?e tsaye ta Wauki jakarta ta fita daga gidan tana ?un?uni.

Alhaji ya girgiza kansa, yana mamakin riguma irin ta ?anwar tasa, yanzu saboda kawai ta Waga masa hankali da wannan maganar ya sa ta yi sammakon zuwa gidansa, tashi ya yi nufi Wakin Maryam da ya ji ta shiru ba ta fito ba.

*****

Tun jiya da Jiniyo ya kulle kansa a Waki bai fito ba sai yanzu, iyayensa sunyi bugun ?ofar bai fito ba, har sun fara tsorata idan ba wani abu ne ya same sa ba, falo ya fito ya tarar da babu kowa, kai tsaye ya wuce Wakin Mama.


Amanarcool
08163516796


=ئ? AKWAI SILA =ئ?


BY AMANARCOOL


YOTA ID/021


*SHIN RAMA CE MATSALARKI? BUSHEWAR JIKI KO KUMA MATSALAR SANYI? TO ALBISHIRINKI, NA ZO MUKU DA INGANTACCIYAR SABAYA DA AKA SARRAFATA DA NATURAL GRAINS, HERBS DA KUMA SPICES, WADDA ZA TA INGANTA LAFIYAR JIKINKU, TA CIKO DA JIKI, SAMAR DA RUWAN NONO GYARAN BREAST, TA KUMA YI MUKU MAGANIN SANYI DA MA SAURAN GYARAN JIKI NA MATA, DUK A KAN KU?I ?ALILAN. SABAYARMU BA MA SANYA ?WAYA A CIKINTA, DA TSIRRAI KAWAI MUKE SAMAR DA ITA. SANNAN AKWAI MAGANIN SANYI GA MASU FAMA DA MATSALAR INFECTION KOMAI DA?EWARSA. AKWAI COMPLETE SET NA GYARAN BREAST, SPECIAL PACKAGE, KU NA IYA TUBTU?A TA KAI TSAYE KU TUNTU?E NI AYSHERCOOL TA LAMBOBIN WAYATA 08081012143*.


PAGE 17-18


Ya isa ?ofar Wakin Mama, har zai yi noking sai ya fasa "Me zan ce mata idan na shiga? Taya zan yi mata bayanin abin da na gani jiya?" Ya tambayi kansa, juya wa ya yi ya koma falo ya zauna, dafe kansa da ya yi, yana jin zuciyarsa na yi masa zafi, ?o?arin kawar da abin da ya faru jiya yake yi, sai dai tunanin ya ?i barin zuciyarsa.

Mama ta fito falon, ganin Jiniyo zaune a gurin ya sa ta ?araso da sauri ta ce "Jiniyo lafiya kuwa? Me yake damunka ne tun jiya ka kulle kanka a Waki? Ni da mahaifinka har mun fara tsorata".

?ago kai ya yi ya kalle ta, ya ce "Mama kin taSa ganin hallitar mutum gashi dai siffar mutum ce amma zuciyarki ta kasa yarda da cewar mutum Win ne?".

Kallon sa ta yi da mamaki ta ce "Kamar ya? Ban fahimci hausarka ba?". Shiru ya yi ya kasa ce mata komai, don bai san ta yadda zai yi mata bayani ba.

"Jiniyo kodai mafarki ka yi ne?".

Ya girgiza kai "Ba mafarki ba ne Mama".

"To me yake damunka? Ka yi mini bayani mana". Ya ce "Babu komai Mama kaina ne ke ciwo"

Kallonsa ta yi da kyau, tasan akwai abin da yake damunsa ba ciwon kai ba ne, ta ce "To yanzu ka tashi ka je ka watsa ruwa, ka zo ka ci abinci kafin Abbanka ya dawo, bai daWe da fita ba wani uzuri ne ya fitar da shi. Bai musa mata ba ya mi?e ya nufi Wakinsa, Mama ta bishi da kallo tana girgiza kai.

Tun jiya Dady ya kasa samun nutsuwa, du?e yake a Wakinsa hannunsa ri?e da wata tsohuwar takarda da ya Wauko a ?asan drawer, rubutun dake ciki ya fara disashewa, kallon takardar yake, kalmomin dake ciki suna suna ?unar masa zuciya. A hankali ya ce "Ba zan bari tarihi ya maimaita kansa ba, ko da hakan yana nufin zan zama azzalumi a idon ?ata". Mayar da takardar ya yi inda ya Wakko ta, ya koma saman gadonsa ya zauna.

Momy ta shigo Wakin tun daga bakin ?ofa take kallosa, ?arasowa ta yi ta zauna "Alhaji me yake damunka ne? Ina lura da kai tun jiya walwalar ka ta ragu, kamar akwai abin da ke damunka".

Murmushi ya yi ya ce "Babu komai Hajiya, abubuwa ne suka yi mini yawa, ina Shalele ta tashi ne? Ina fatan dai ta wuce school?". "Alhaji kenan, mu bar zancen tunda baka son in sani. Auta tunda safe ta tashi, yau sai 11 za ta je school". Dady ya gyaWa kai ya ce "Bari na shirya ina son fita da wuri ne, yau ina da ba?i".

Ta ce "To shikenan" tashi ya yi ya fara shiri, Momy sai kallosa take yi, tasan akwai abin da ke damunsa amma ya ce mata babu komai, to kodai lamarin Auta ne ke damunsa haka? Haka dai ta shiga sa?e-sa?e a ranta daga ?arshe tashi ta yi ta fita zuwa na ta Wakin.

Tana shiga Wakinta a kwance ta tarar da Joriyya, ta ce "Auta yau kuma ke ce a Wakin nawa? Hira kika zo yi mini ne? Naga kin kwana biyu baki shigo kin kwanta irin haka ba".

Dariya ta yi ta ce "Eh Momy hira zan yi miki".

"To shikenan ina sauraren ki".

"Momy idan mutum bashi da iyaye, bashi da Momy kenan shi ya haifi kansa ko?"

"To za ki fara ko?" Momy ta ce tana kallon ta

Joriyya ta kuma cewa "Momy to shi wai ina iyayensa suke ne? Nifa ji nake kamar na san shi" kafin Momy ta yi magana Dady ya shigo Wakin cikin shirinsa.

Ta ce "Yawwa Dady zo ka ji" isa ya yi ya zanuna, ta ce "Dady idan zuciyar mutum nada kyau ana gani? Sannan ana yi mata kwalliya ko? Kuma ana shafa mata mai?".

Dady ya nisa yana murmushi ya ce "Shalele idan mutum nada kyakyawar zuciya ana sani, amma taya za a shafa wa zuciya mai?" .

Tsaki Momy ta yi ta ce "Idan ka biye mata sai ta Sata maka lokaci da wannan shirmen nata.

"Dady in sha Allah sai na yi karatu mai yawa, kasan wani abu Dady wallahi ba mahaukaci ba ne, kawai an manta da shi ne". "Shalele ki daina yin surutan nan mana, ki yi shiru".

"To na yi shirun, amma Dady kaga yadda hannunsa ya yi? Me aka yi masa? Don Allah a siya masa magani, sannan mu tambaye shi ina ne gidan su".

Cikin fusata Momy ta ce "Wai ke bakin ki baya yin shiru ne? Alhaji ka tashi ka yi tafiyarka idan ka biye mata makara za ka yi". Joriyya ta ce "Ni dai tambaya ce kawai na yi, amma sai na yi karatu na zama likita in warkar da shi, ko in zama malama in koya masa karatu da yin magana, ko kuma in zama Momynsa in ri?a bashi abinci kullum".

Tashi Dady ya yi, tare da yi wa Momy sallama ya fita. Joriyya ta ci gaba da zuba wa Momy surutu kamar wata suda, idan ta saki wata maganar sai Momy ta razana, ita har tana murna daga jiya zuwa yau ?arta ta fara samun nutsuwa ta rage damuwar nan, amma ta lura abin na nan a ranta har yanzu.

*****

"Madam ya dai na jiki shiru tunda kika shigo baki sake fitowa ba?"

"Alhaji baku guri na yi ka gana da ?ar uwarka, ka ga ban san abin da yake tafe da ita ba".

Tsura mata ido ya yi yana kallon ta, ta ce "Abbin Nihal wannan kallon fa?".

"Na so da ?aunarki ne ?ammatana" ya yi maganar yana jan kumatunta.

Dariya ta yi ta ce "?ammata kuma? A'a sai dai uwar ?ammata".

Ya ce "In ji wa? Ni Alhaji Kabiru Umar mai nera har yanzu kamar ?ammata kike a gurina, gaki nan shar dake, komai naki a kintse, kullum zam-zam nake jinki kamar..." Da sauri ta rufe masa baki tana faWin "Haba dai ka yi shiru, mu fa ba yara ba ne yanzu da zaka saki baki kafara Sarin zance, tunda nake da Nihal ai na wuce zama ?ammata" ta ?arasa maganar da tana dariya.

"Waya faWa miki mu ba yara ba ne? Ai ni a yadda nake jina nafi wani sabon angon more wa" ya faWa yana rugumota jikinsa. Dariya take yi sosai, tasan halin mijin nata idan abin ya motsa masa komawa yake yi kamar wani yaro, ba ta yi aune ba taga ya kashe wutar Wakin tare da rufe su da bargo.

******

Jiniyo wanka ya yi, ya shirya jikinsa tsaf ya sake fitowa falo, nan ya tarar da Abbansa zaune, tun daga nesa ya ?urawa Jiniyo ado kamar yana karantar abin da ke zuciyarsa. "Jiniyo" ya kira sunan sa "Tun jiya kake kulle a Waki lafiya dai? Baka san na dawo ba ne?".

Murmushin ya ?e ya yi ya ce "Abba ba na jin daWi ne, shi ya sa na manta cewar jiya za ka dawo". Mama ta ce "?arya yake yi akwai abin da yake Soye wa" .

Abba ya ce "Idan ma akwai abin da zai damuwar yarona nasan akan ?ar yayarki ba ce, da ina da ikon da zan cire masa son yarinyar nan da na yi".

"Haba Abban Jiniyo ?ar uwarsa ce fa, taya za ka hana shi ya so ta?" .

"Yi mini shiru Munira, tun da aka haifi yarinyar nan yake nuna mata so da kulawa, amma da ta buWa ido ta fara wayo babu wanda take hantara kamar shi, ina kiyaye da ita ko gidan nan ta zo da Mamanta ba ta kula shi, akan me zan so yarona ya fara shiga damuwa akan yarinyar da ba ta san yanayi ba?".

Tsam Jiniyo mi?e ya fita daga falon gabaWaya, ya ja motarsa ya bar gidan.

Mama ta ce "Abban Jiniyo bai kamata kana wannan maganar ba, Joriyya fa kamar ?a take a gurink..." "Bana son jin komai daga bakin ki, ai ba za ki bari a yi magana ba" . Ya katse ta yana gama faWar hakan tashi ya yi ya ba ta guri.


Dady ne tare da ba?in sa suna tattaunawa akan harkar kasuwanci su da tsare-tsaren shigo da kaya daga waje, Waya daga cikin su ya ce "Alhaji wannan sabuwar yarjejeniyar da muka ?ulla da su za ta amfane mu sosai". Dady ya gyara zamansa ya ce "Ina so komai ya tafi bisa tsari, ba zan yarda da asara ba, mun sha darasi a baya, yanzu ba zan lamunci a sake maimaita abin da aka yi mana a baya ba".

"In sha Allah babu wata matsala da za ta kuma faruwa a yanzu, da mun san akwai matsala ba za mu koma gayyato ka cikin tafiyar ba" Dady ya yi na'am da maganar sosai, suka ?arasa tattaunawar sannan suka yi masa sallama tare da barin ofis Win. Suna fita suka kalli juna suka yi murmushin da suka Wai suka san ma'anarsa.


Joriyya na zaune a class tare da ?awarta Safina, Malam Musa na yi musu darasi amma ba ta fasa surutun da take yi ba, kallon sa take tana dariya ?asa-?asa ganin yadda yake yi musu bayani kamar baya jin daWin jikinsa, cikin ?asa da murya ta ce "Safina kin ga Musa yau kamar wanda aka hana shi shayin safe, sai layi yake yana lumshe ido kamar yadda Indiyawa ke yi a film".

Safina ta girgiza kai ta ce "Ke dai ba za ki daina surutu ba? Joriyya ka da ki jawo muna duka fa".

"Surutu fa yanzu na fara, Safina kin san bashi da lafiya hannunsa ke ciwo" . Joriyya ta ce tana lumshe ido

Safina za ta yi magana kenan suka ga Malam Musa na kallon su dole ta yi shiru.

Da aka tashi daga school Win, direba ya zo Waukar Joriyya, kai tsaye gida ya nufa, babu za to ya ji Joriyya ta ce masa

"Tsaya ba wannan hanyar zamu bi ba, ka wuce ta can baya nake son mu bi".

Ya ce "Amma Shalele ga hanyar..."

"Don Allah kabi inda na bu?ata, zan Wan tsaya ne wani guri" ta katseshi

Direban bai sake magana ba, ya juya akalar motar zuwa inda ta bu?ata, tun daga nesa ta hango shi zaune a cikin bolar, rana na dukansa. karensa na gefensa, hannunsa ya ?ara kumbura, fuskarsa ta yi duhu, idanunsa sun zurma sosai, bakinsa ya bushe, sai hamma yake yi alamar yunwa yake ji, tasa direba ya tsaya daidai bakin bolar. A firgice ta fito daga cikin motar tana faWin "Subhanallah". Ta matsa kusa da shi hawaye har sun fara zuba a fuskarta ta ce "Me ya ?ara kumburar maka da hannu haka? Me yasa ba wanda yake taimaka maka ne? Yanzu dama haka kake fama da hannun? Da gani ma yunwa kake ji?".

Mahaukacin ya Wago da kai a wahale, ya kalle ta da idanunsa da suka yi zurfi, bai ce komai ba. Hawaye suka ?ara zubu mata, ta rufe fuskarta da tafin hannunta tana kuka. "Ba haka ya kamata rayuwar mutum ta kasance ba" ta faWa cikin muryar kuka.

Direban ya tsaya daga nesa yana kallon ta, zuciyarsa cike da fargaba.


Amanarcool
08163516796


=ئ? AKWAI SILA =ئ?


BY AMANARCOOL


YOTA ID/021

*SHIN RAMA CE MATSALARKI? BUSHEWAR JIKI KO KUMA MATSALAR SANYI? TO ALBISHIRINKI, NA ZO MUKU DA INGANTACCIYAR SABAYA DA AKA SARRAFATA DA NATURAL GRAINS, HERBS DA KUMA SPICES, WADDA ZA TA INGANTA LAFIYAR JIKINKU, TA CIKO DA JIKI, SAMAR DA RUWAN NONO GYARAN BREAST, TA KUMA YI MUKU MAGANIN SANYI DA MA SAURAN GYARAN JIKI NA MATA, DUK A KAN KU?I ?ALILAN. SABAYARMU BA MA SANYA ?WAYA A CIKINTA, DA TSIRRAI KAWAI MUKE SAMAR DA ITA. SANNAN AKWAI MAGANIN SANYI GA MASU FAMA DA MATSALAR INFECTION KOMAI DA?EWARSA. AKWAI COMPLETE SET NA GYARAN BREAST, SPECIAL PACKAGE, KU NA IYA TUBTU?A TA KAI TSAYE KU TUNTU?E NI AYSHERCOOL TA LAMBOBIN WAYATA 08081012143*.


PAGE 19-20


Tana dur?ushe a gabansa, ba tare da tunanin komai ba, ta buWe jakar makarantar ta ta Wauko kwalbar ruwa da biskit ta mi?a masa hannunta na rawa ta ce "KarSi ka ci don Allah".

Ya kalli ruwan a hankali ya karSa ya sha kaWan ya ajiye, da ?yar yake iya motsa hannunsa, Joriyya ta buWe masa biskit Win ta mi?a masa ya amsa.

Direba ya matso kusa yana cewa "Shalele mu tafi, wallahi ina cikin matsala idan aka gan ki a nan fa".

Cike da tsiwa ta juya tana kallonsa ta ce "Bazan tafi ba, taya zan tafi na bar shi a haka? Ka jira ya gama ci sai mu tafi".

KarSar biskit Win ta yi ta fara karya masa shi ?ananu tana bashi, amsa ya yi yana ci a hankali, idanunsa na kallon ta ko ?iftawa baya yi.

"Baka da suna ne?" ta tambaya murya a sanyaye

Shiru ya yi mata, ta kuma cewa "Ko ka manta da sunan naka ne?".

Ya girgiza kai kaWan, ya buWe baki kamar zai yi magana sai ya fasa, yana jin yadda hannunsa ke yi masa raWaWi, ya Waga shi sama yana huci. Joriyya ta kalle hannun hawaye na ci gaba da zubo mata ta ce "Wannan hannu ciwo yake maka sosai ko? Zan sa Dady ya kai ka asibiti".

Da jin kalmar asibiti ya janye hannunsa da sauri, tsoro ya bayyana a fuskarsa, ya fara girgiza kai yana ja da baya.

"Baka son asibiti ne? To ba za a je da kai ba, za a siyo maka magani kasha ka ji dama". Ta faWa tana matsowa kusa da shi.Kallon ta yake yi sosai, idanuwansa sun yi ja, hawaye sun taru a ciki, bakinsa ya fara motsi a hankali "Ki tafi..." Bai ?arasa ba ya yi shiru.

Ta tsaya cak, zuciyarta na bugu da sauri ta ce "Kana magana da ni ne?"

Direba ya dafe kansa ya ce "Wannan yarinya ?ar bala'i ce, ko tsoron ya sha?eta ba ta yi".

Wata tsohuwa ta zo wucewa ta tsaya tana kallonsu, ta ce "Ke yarinya kin san ko waye shi kuwa?".

Joriyya ta Wago ido cike da hawaye ta ce "Ba na san shi ba, sai dai bai kamata ya kasance haka ba, dubi hannunsa babu wanda ya taimaka masa, kuma jama'a na kiran sa da mahaukaci".

Tsohuwar ta girgiza kai ta ce "Shi ba mahaukaci ba ne, abin da ya same shi ne ya fi hauka muni".

"Me ya same shi?" Joriyya ta tambaya da sauri

Tsohuwar ta yi murmushi ta ce "Yariya tashi ki wuce gida kin ji".

Kafin Joriyya ta sake yin wata maganar direba ya ce "Shalele wallahi lokaci yana tafiya, ki taso muje ka da ki saka ni a matsala".

Ta kalli mahaukacin ta ce "Ka yi ha?uri zan dawo, za a baka maganin wannan ciwon".

A hankali yake tu?in zuciyarsa a cunkushe. Idanunsa sai shawagi suke yi a titi, motar da ya gani a gefen titi kusa da bola ya sa zuciyarsa ta buga da ?arfi.

Ya rage gudu yana kallon motar sosai "Joriyya?" ya furta a ransa, taka birki ya yi, ya fito daga motarsa ya tsaya can nesa, ji ya yi zuciyarsa na harbawa da sauri, idanunsa suka sauka a kan Joriyya dake dur?ushe a gabansa tana kuka, mutumin da kowa ke gudu, wanda Duniya take kira da mahaukaci, shi ne yarinyar da yake yi wa kallon uwar ?a?ansa take yin wannan abin a gabansa? Take ransa ya ?ara Saci ya ce "Haba Joriyya, me kike nema a gurinsa ne? Me yasa kike kusantar shi haka?" ya tambayi kansa cikin Sacin rai. "Ba zan bari wannan abin ya ci gaba da faruwa ba". Yana kallo Joriyya ta mi?e ta shiga mota direba ya ja suka bar gurin.

Shiga tashi motar ya yi, zuciyarsa cike da ba?in ciki ya rufa musu baya.

Suna isa gida ta fito da sauri ta shiga ciki zuciyarta cike da damuwar halin da ta baro shi a ciki, tana shiga falo ba ta ma lura da Momy ba ta fara ?o?arin hawa saman bene. "Auta" Momy ta kira ta "Ina kuka tsaya tun Wazu? Me ya faru kika dawo cikin wannan yanayin?". "Momy shi ne fa" kafin Momy ta

7 / 11