AKWAI SILA HAUSA NOVELS BY AMANARCOOL.doc

Author :  Amanar Cool Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   9 / 11

24K to 27K   out of 32.7K words

tashi har abun ya fara Waga mana hankali. Sai ta ri?a ce mana wai shi ba mahaukaci bane, ta san shi, mantawa aka yi da shi, sannan kuma tana yawan Waga hankalinta akan shi, dalilin haka ya sa muke zargin ba mutum bane aljani ne yake zuwar mata a suffar mutane".

Malam Nura ya girgiza kai ya ce "Gaskiya ba aljani bane, tabbas mutum ne, kawai dai akwai wani al'amari mai girma tsakanin wannan bawan Allah da Joriyya, amma na kasa fahimtar komai, kuma ina son ku kwantar da hankalinku, ku sani lafiyar ?arku ?alau, sai dai akwai wani abu da yake fizgarta zuwa gare shi".

Joriyya ta kyaSe fuska tana ?o?arin yin kuka ta ce "Yawwa Malam gaya musu dai ba aljani ba ne mutum ne kamar kowa, kuma ba mahaukaci ba ne mantawa aka yi da shi".

"Ka ji ko Malam, kaga irin wannan surutun ne bana son tana yi" Dady ya faWa yana nuna Joriyya. Malam Nura ya ce "Yi ha?uri Alhaji in sha Allah za ta daina, idan na koma gida zanyi mata wani rubutu sai ka aiko a karSa mata" Dady ya jinjina kai yana yi masa godiya, sannan ya yi masa alkhairi, bai so karSa ya tilasta masa ya karSa dole. Suka fito harabar gidan Dady ya sa a mayar da shi gida. Sannan ya kama hannun Joriyya suka koma ciki, suna shiga falon ta zame hannunta daga na Dady ta dafe ?irjinta, Dady ya ce "Shalele lafiya dai?".

"Dady"

"Na'am Shalelena"

"Mu je mu duba shi, bashi da lafiya, Dady yunwa yake ji bai ci abinci ba!".

"Yi mini shiru babu in da za muje, kuma kika sake zancensa sai na kai gurin Na'ima in nisanta ki da ?asar nan kowa ma ya huta" yana gama faWar haka ya wuce da sauri ya bar ta a gurin. Yana ?o?arin haurawa sama ne ya ji ?arar faWuwar abu, juyowar da zai yi yaga Joriyya zube a ?asa numfashinta na fita da sauri.


Amanarcool
08163516796



=ئ? AKWAI SILA =ئ?


BY AMANARCOOL


YOTA ID/021


*SHIN RAMA CE MATSALARKI? BUSHEWAR JIKI KO KUMA MATSALAR SANYI? TO ALBISHIRINKI, NA ZO MUKU DA INGANTACCIYAR SABAYA DA AKA SARRAFATA DA NATURAL GRAINS, HERBS DA KUMA SPICES, WADDA ZA TA INGANTA LAFIYAR JIKINKU, TA CIKO DA JIKI, SAMAR DA RUWAN NONO GYARAN BREAST, TA KUMA YI MUKU MAGANIN SANYI DA MA SAURAN GYARAN JIKI NA MATA, DUK A KAN KU?I ?ALILAN. SABAYARMU BA MA SANYA ?WAYA A CIKINTA, DA TSIRRAI KAWAI MUKE SAMAR DA ITA. SANNAN AKWAI MAGANIN SANYI GA MASU FAMA DA MATSALAR INFECTION KOMAI DA?EWARSA. AKWAI COMPLETE SET NA GYARAN BREAST, SPECIAL PACKAGE, KU NA IYA TUBTU?A TA KAI TSAYE KU TUNTU?E NI AYSHERCOOL TA LAMBOBIN WAYATA 08081012143*.


PAGE 23-24


Dady ya tsaya cak ganin Joriyya kwance a ?asa tana shure-shure. Da gudu ya ?araso kusa da ita yana Waga kanta ya Wora a cinyarsa. "Shalele Shalele ki buWe idonki ki kalle ni" Ya faWa cikin rawar murya. Momy ta fito da sauri tana faWin "Subhanallah meya same ta kuma?" .

"FaWuwa ne ta yi daga cewar ba za ta je gurin wancan yaron ba".

Momy ta buWe baki za ta kira sunanta, suka ga Joriyya ta girgiza jikinta da ?arfi, ta buWe idanunta dake cike da hawaye, ta mi?ar da hannunta sama kamar tana neman taimako "Dady.... Don Allah mu je mu duba shi, mu kai masa abinci" ta faWa muryarta a sanyaye idonta na sake rufewa.

Daga Dady har Momy shiru suka yi, suna kallonta, zuciyoyinsu cike da ?unci. Momy ta ce "Alhaji wai me Malam ya ce ne akan wannan matsalar?" "Ba abin da ke damunta, kuma ya tabbatar mini da cewar yaron nan mutum". Dady ya ba ta amsa.

"To amma Alhaji me ya sa take yin waWannan abubuwan akansa?" Kafin Dady ya yi magana Joriyya ta sake buWe idanunta, hawaye na zubowa a gefen fuskarta. Ta kama rigar Dady da ?arfi "Don Allah Dady mu je yanzu, idan bamu je ba zai iya mutuwa" Ta faWa tare da fashewa da wani irin kuka mai taSa zuciya. Dady ya kasa magana. Abin da Malam Nura ya faWa masa ne yake dawo masa Waya bayan Waya "Akwai wani abu da yake fizgarta zuwa gare shi". Shiru ya yi yana nazarin me yake fizgar Shalele zuwa ga wannan yaron da bashi da saiti a ?wa?walwarsa.

?ara ri?e rigar Dady ta yi tana kuka, Momy ta ce "Alhaji me ya kamata muyi? Wannan kukan da take yi ina tsoron kar ciwonta ya tashi".

"Stop crying Shalele, na ji zan sa a je a duba shi, kuma za a kai masa abinci, ki yi shiru..." kafin ya ?arasa ta katse shi da cewar "A'a Dady tare dani nake son a je in duba hannunsa idan ya warke".


"Ya salam!" Dady ya faWa yana dafe kansa, sannan ya ce "Na ji tashi ki shirya mu je, shikenan hakan ya yi miki?" Ya yi maganar yana kallon Joriyya, mi?ewa ta yi tsaye da sauri tana murmushi ta ce "Eh Dady, bari na canza kaya" tana gama faWar haka ta nufi Wakinta da gudu. Dady ya dubi Momy ya ce "Shafa ina ga dole ne Joriyya ta bar ?asar nan, saboda banga alamar za ta daina nuna damuwarta akan wannan yaron ba, ba zan yarda da girmana da mutuncina a garin nan ba a ri?a ganina a gurin wani ?as?astaccen talaka ba, talakan ma mahaukaci". Momy ta ce "Alhaji nima na goyi da bayan ta bar ?asar ko hankalin mu zai kwanta daga mu har ita". Ba a Wauki dogon lokaci ba Joriyya ta fito cikin ?ananun kaya riga da wando, ta ce "Momy zuba masa abin a flaks mu kai masa" da sauri Dady ya ce "A'a bari idan mu je can sai a siya masa" fita suka yi zuwa harabar gidan Dady ya sa aka fito da Waya daga cikin motocinsa, suka shiga tare da rakiyar security biyu direba ya ja suka bar gidan.

Jiniyo ne kwance a Wakin Salim, juya wa ya yi a hankali yana murmushi, abin da ya faru daren jiya na dawo masa daki-daki irin yadda mahaukacin ya ri?a kakari yana son yin ihu babu hali. Da yadda ya daina motsi, lumshe idonsa ya yi na Wan lokaci kafin ya buWe su ya ce "Shegen kaya ai yanzu mun koya masa hankali". Ya mi?e zaune ya dubi Salim da Yasir "Gayu Allah jiya wawan can fa ya daku ba ?arya" ya ?arasa maganar yana dariyar mugunta.
Salim ma dariyar yake yi ya ce "Ya daku dan uwarsa, har yanzu ina tuna yadda yake shure-shure, ya ji dukan manya, yanzu ai zai san bakin rijiya ba gurin wasan makaho ba ne". Yasir ya Sarka uwar dariya suna tafa hannu da Salim.Ya ce "?ila ma ya mutu". Jiniyo ya yi dariya cike da sha?iyanci "Ai bai mutu ba, zafin duka ne ya ji, irinsu ba sa mutuwa da wuri, azaba ce ta yi masa yawa ya suma". Dariya suka kwashe da ita, dariya irin ta samari masu cike da sha?iyanci, babu alamar nadamar abin da suka aikata a tare da su.

Yana kwance a cikin bolar rana na dukansa, karensa na zaune a gefensa sai zuga yake yi yana fitar da harshe waje, zafin ciwo da azabar da yake ji ba za su misaltu ba, idonsa Waya ya ?ara kumbura sosai, cikin ?arfin hali da jarumta ya samu da ?yar ya tashi zaune, kallon hannunsa yake yi, daga jiya zuwa yau hannun ya ?ara canza kamanni, fatar gurin ta fara Wayewa, ga wata uwar tsokar da ta zazzago tana na rawa kamar an yanko ta da wu?a, yana jin zafin ciwo sosai, zuciyarsa ba ?aramin Waci take yi masa ba. Wani abu mai kamar tsinin wuta yake jin yana ratsa hannunsa zuwa ?irjinsa. Ya runtse idanu yana jan dogon numfashi mai azaba. BuWe Wayan idonsa ya yi hasken rana ya doki ?wayar idon, da sauri ya rufe idon, gurin ya yi shiru baka jin motsin komai sai na iskar da take kaWawa, ya Waura hannunsa mara ciwon a kan ?irjinsa kamar yana tantama ko zuciyar da ke bugawa a ciki tasa ce, ko kuma wata irin halitta ce da ta tsaya masa a ciki. A hankali kamar wanda ya manta yadda ake magana, ya furta kalmomin da ba shi kaWai yake fahimtar su. Ji ya yi kamar ana kiransa daga nesa, kamar wata ?aramar murya na yi masa amsa kuwa a ?asan zuciyarsa, bai san me yasa ba. Bai san me yake nema ba. Bai san wa yake nema ba. Amma yana jin sautin wannan kiran da ya kasa fahimtar daga ina ne? Ya sunkuyar da kansa, yana lumshe idonsa, yana jin kamar wani abu yana ja masa rai zuwa wani guri, guri da bai san shi ba amma yana jin shi daga cikin jini da tsokarsa, kamar ya haWu da wani Sangare nasa da ya daWe da Sacewa. Jama'a na wuce suna kallonsa babu wanda ya yi tunanin ya tsaya, balle ya yi yun?urin taimaka masa akan halin da yake ciki.

Motar ta tsaya nesa da gurin bolar nan kaWan. Dady na jin kamar zai yi bindiga saboda takaici, kamar shi ace yana zuwa wannan ?as?antaccen gurin, bolar cike take da tarkace, warin ?azanta na tashi yana zunkuWar zuciya, motar na tsayi Joriyya ta buWe ?ofa ta fito a firgice. Fitowa Dady ya yi, ya tsaya yana kallon bolar yana yamutsa fuska, zuciyarsa na tashi, yana jin wani zafi a ?irjinsa, bai taSa tunanin ?arsa za ta ja shi zuwa irin wannan guri ba.

Kafin ya anka tuni Joriyya ta ?arasa in da yake, da sauri security suka bi bayanta. Dady ya taka a hankali ya ?arasa gurin, yana zuwa ya ce "Shalele ki yi a hankali mana, idan ya ji miki ciwo fa".

Cikin kuka Joriyya ta ce "Dady dubi yadda hannunsa ya koma, don Allah Dady a sai ya masa magani, shi ma fa mutum ne kamar kowa". Sai a lokacin mahaukacin ya Wago da idonsa, ya kalli Joriyya, sannan ya mayar da kallonsa ga Dady. A mugun firgitace ta mi?e tsaye tana ja da baya ta ce "Dady kalli fuskarsa, me ya same shi haka ne? Dubi jikinsa, idonsa Waya baya buWewa Dady". Ta ?arasa maganar jikinta na tsuma tsabar kaWuwa da ta yi. Shi kansa Dady sai da ya ji tsoron ganin fuskar mahaukacin, lokacin Waya ya fahimci cewar doka ne aka yi masa ba na wasa ba. Ganin yadda Joriyya ke gunjin kuka tana tambayarsa me ya same shi? Ya ce "Shalele dukansa ne aka yi, kuma duka ba na wasa ba".

Cak ta tsaya, ta daina kukan da ta yi, ta kalli Dady sannan ta mai da duban ta ga gare shi, cikin sar?ewar murya ta ce "Dady duka kuma? Waye zai dake shi haka? Me ya yi masa? Wanda ko magana baya iyayi?".

Dady ya nisa ya ce "Shalele kin san fa mahaukaci ne bashi da hankali, wata?ila ya yi yun?urin cutar dani wani ne ya sa aka yi masa wannan dukan, shi ya sa nake ?o?arin ankarar dake hatsarin dake tattare da wannan mahaukacin amma kin ?i ki fahimta, yanzu dai ai kinga irinta, ya je zai cutar da wani ya jawowa kansa duka".

Cikin ihu ta ce "Dady wallahi ba haukaci ba ne, mantawa ne aka yi da shi, wannan zaluntar sa ne aka yi. Dady don Allah ka sa a kama wanda ya dake shi a rama masa, ji yadda idonsa ya yi" . "Shalele ki yi shiru da wannan kukan da kike yi, taya zan sa a kama wanda ya yi masa wannan dukan bayan ban san ko waye ba. Duk yadda aka yi wanda ya dake shi Win nan ya yi yun?urin cutar da shi ne ya sa ya kare kansa". Tsalle ta yi ta fara ihu a gurin, hankalin jama'a ya fara dawowa kansu, ba?in ciki ne ya ?ara turni?e zuciyar Dady. Cike da ?unar rai ya daka mata tsawa "Shalele ki rufe mini baki kafin na Sarar dake a gurin nan". "Dady don Allah..." "Ba za ki yi mini shiru ba ne!" Ya sake daka mata tsawa, idonsa sun kaWa sunyi jajur. Ya dubi Wayan security Win ya bashi umarni da ya siyo masa abinci, babu Sata lokaci ya karSo masa abincin ya kawo tare da ruwa ya ajiye a gaban mahaukacin. Dady ya ja hannun Joriyya da ?arfi ya tura mota, tana ihun kuka, security suka shiga motar direba ya ja motar da ?arfi suka bar gurin. Tsohon nan da yana tsaye a gefe ya yi dariya tare da jinjina kai ya wuce.

Har suka ?arasa gida kuka take yi, Momy ta fito daga kitchen taga sun shigo gidan Joriyya na rusa uban kuka, ta ce "Alhaji me kuma ya faru ne?".

Ran Dady ya gama Saci, tun a hanya ya yanke shawar dole ne gobe ya bar ?asar nan da ita.


"Alhaji magana nake yi ka yi mini shiru"

Dady ya sha?i iska ya fitar da ?arfi ya ce
"Na gaji da wannan abin, yau tura ta kai bango, ba zan bari Shalele ta ci gaba da tozarta ni a gaban jama'a ba, dole ne ta bar ?asar nan". Ya juya ya kalli Joriyya
"Ki shirya gobe jirginmu zai tashi zuwa Dubai, za kai can gurin Na'ima ki zauna ko da na tsawon wata biyu ne, wata?ila rashin ganinku a gari Waya zai sa zuciyarki ta samu nutsuwa hankalinki ya kwanta, kuma na gama magana kada in ji kin ce ?ala". Dim! ?irjinta ya buga da ?arfi ta ce

"Daddy Dubai? Ni Win?".

"Ke Win!" Ya ce cikin tsawa "Ba zan barki ki lalata rayuwarki ba, ba zan bari ki sake kusantar wancan yaron ba, ba za ki zubar mini da mutunci ba. Dubi yadda kika tara mini jama'a yau, kowa ne banza ya tsaya sai kallon mu yake yi". Lumshe ido ta yi, zuciyarta na tsananta bugawa, kalmar raba ta da ?asarta ta dake ta sosai. RaSa su ta yi ta haye sama tana jin zafi sosai a ranta.

Tun da motarsu ta bar gurin ya yi shiru yana bin hanyar da motar tabi da kallo, numfashinsa na fita a hankali, yana jin Waci a zuciyarsa. Idonsa na yi masa zafi sosai, yunwar da ya ji ta addabe sa ne kamar hanjin jikinsa za su fito ya sa ya jawo ledar abincin da ?yar ya fara ci, bakinsa ne ya soma karkarwa cikin wata irin murya ya ce "Kar ki tafi& " Sai kuma ya ji zuciyarsa na buWewa, wani abu daya rasa gane ko meye na shigarsa da ?arfi. Lokaci Waya tunaninsa ya sake hargitsewa.



Littafen akwai sila na kuWi ne, saura pages biyu free page ya ?are, ga mai bu?atar cigaba zai biya 500 kacal ta wannan account Win 1019533255 Nafisa Muhammad UBA, sai a tura mini shaidar biya. Ka da ku bari a yi tafiyar nan ba da ku ba.

Amanarcool
08163516796



=ئ? AKWAI SILA =ئ?


BY AMANARCOOL


YOTA/021

*SHIN RAMA CE MATSALARKI? BUSHEWAR JIKI KO KUMA MATSALAR SANYI? TO ALBISHIRINKI, NA ZO MUKU DA INGANTACCIYAR SABAYA DA AKA SARRAFATA DA NATURAL GRAINS, HERBS DA KUMA SPICES, WADDA ZA TA INGANTA LAFIYAR JIKINKU, TA CIKO DA JIKI, SAMAR DA RUWAN NONO GYARAN BREAST, TA KUMA YI MUKU MAGANIN SANYI DA MA SAURAN GYARAN JIKI NA MATA, DUK A KAN KU?I ?ALILAN. SABAYARMU BA MA SANYA ?WAYA A CIKINTA, DA TSIRRAI KAWAI MUKE SAMAR DA ITA. SANNAN AKWAI MAGANIN SANYI GA MASU FAMA DA MATSALAR INFECTION KOMAI DA?EWARSA. AKWAI COMPLETE SET NA GYARAN BREAST, SPECIAL PACKAGE, KU NA IYA TUBTU?A TA KAI TSAYE KU TUNTU?E NI AYSHERCOOL TA LAMBOBIN WAYATA 08081012143*.


PAGE 25-26


Bayan shigar Joriyya Wakinta, shiryawa Dady ya yi ya wuce gurin aikinsa ransa a jagule, gidan ya yi shiru. Momy ta zauna tana sa?e-sa?e a zuciyarta. Lamarin nan ya wuce duk yadda suke tunani, a hankali ta Wauki wayarta ta kira Zainab, bayan sun gaisa ta ce "Zainab abin da ba so dai shi ne zai faru".

Zainab ta ce "Subhanallah Momy me ya faru kuma?".

Nisawa ta yi, sannan ta ce "Auta dai dole za ta bar ?asar nan, abin da take yi ya yawa. Yau har ta tunzura mahaifinku babu shiri ya ce gobe zai bar ?asar nan da ita. Zainab zuciyar Auta ta ?e?ashe akan yaron nan, tana yin abubuwan da ba mu taSa tunanin ba".

Zainab ta yi shiru na Wan lokaci, sannan ta ce "Tafiya kuma Momy? Da dai an ?ara ha?uri a gani, duk da Joriyya ba ta iya saka abu a rai ba, amma ni ba na son ta yi nesa damu".

Momy ta share hawayen da suka zubo mata, tana kokawa da zuciyarta, kar kukun da take ri?e wa ya kufce mata, ta ce "Zainab kin san halin Dadyn ku magana Waya yake yi, tunda ya zartar da wannan hukuncin babu wanda zai hana shi, ni kaina ban so tafiyar nan ba, wallahi Zainab yau ba zan iya bacci ba. Autata rashinta a gida nan zai Sata min rai sosai".

"Ki yi ha?uri Momy, na sani, in sha Allah wannan tafiyar za ta kawo ?arshen wannan damuwar, muci gaba da yi mata addu'a. Ina da tabbacin Anty Na'ima za ta ba ta duk wata kulawar da ta dace".


Momy ta jinjina kai kamar tana ganin ta, ta ce "Shikenan Allah ya shiga lamarin Auta ya yaye mata komai" Zainab ta amsa da amin tana ?ara bawa Momy ha?uri tare da kwantar mata da hankali, daga ?arshe suka yi sallama.

Daddy na zaune tare da abokansa Alhaji Fahad, da Alhaji Hamza a ofishin sa suna tattaunawa akan abin da ya shafi kasuwansu. Sai dai babu annuri a fuskar Dady saboda abin da ya faru kafin ya baro gida, sun lura da yanayinsa Alhaji Hamza ya ce "Sulaiman lafiya kuwa naga yanayin ka ya canza kalmar akwai abin da ke damunka?". Dady ya nisa tare da furzar da iska mai zafi ya ce "Ina tunanin rabuwar da zanyi da Shalele ne, in Allah ya nufa gobe zamu yi tafiya da ita, zan kai ta can Dubai gurin Na'ima ta zauna na Wan wani lokaci".

Ya ce "Dubai kuma? Akan me za ka kai ta can ta zauna?" Dady bai Soye musu komai ba ya faWa musu abin da ke faruwa. Alhaji Fahad ya ce "Dan?ari, wata sabuwa in ji ?an caca, to lallai gara ka

9 / 11