AKWAI SILA HAUSA NOVELS BY AMANARCOOL.doc

Author :  Amanar Cool Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   8 / 11

21K to 24K   out of 32.7K words

yi magana Jiniyo ya shigo falon fuskarsa a murtu?e, idanuwansa sunyi jajur.

"Jiniyo?" Momy ta furta da mamaki "Lafiya ka shigo haka kamar wanda aka je fo?". Bai ba ta amsa ba, kai tsaye ya nufi Joriyya da ta tsaya cak a tsakiyar falon "Me kika je yi gurinsa?" ya tambaye ta cikin fushi. Joriyya ta kalle shi ta ce "Shi wa?" "Karki raina mini hankali Joriyya! Na ganki da idona, na ganki gurin mahaukaci nan, kina dur?ushe a cikin bola kamar wata mara galihu".

Momy ta ce "Subhanallah! Jiniyo me kake nufi? Ba dai gurin wannan mahaukacin ka ganta ba" . "Can na ganta Momy, baki ga a yadda na ganta ba. Momy Joriyya na son zubar da mutuncin gidan nan". Joriyya ta Waga kai tana kallonsa idanunta cike da hawaye, cike da rawar murya ta ce "Ba mahaukaci ba ne, ka da ka sake kiransa da wannan sunan!". "Me kika ce?" Ya tambaya cikin fushi da zafin kishin da yake jin yana nu?ur?usar sa a zuciya.

"Na ce ba mahaukaci ba ne, mutum ne kamar kowa, kawai an manta da shi ne" ta faWa da ?arfi, ?ara har zu?a ya yi ya ce "Ke Joriyya ki shiga taitayin ki, wannan mahaukaci ne, kin san irin hatsarin da kike jefa kanki a ciki kuwa? Bana son damuwar nan da kike yi akan sa, wannan ai hauka ne". Ya ?arasa maganar cikin hargagi

"Idan tausayin sa ne da nake ji ya zama hauka, na ji Win ni mahaukaciya ce" Joriyya ta maida masa da martani.

Mutuwar tsaye Momy ta yi, ganin abin na shirin zama rigima a tsakaninsu ya sa ta ce "Ya isa haka, ku daina wannan rikicin ba na so. Auta wuce ki bani guri kafin in saSa miki". "To Momy zan wuce" ta dubi Jiniyo ta ce "Ka da ka sake shiga harka ta, kuma ka daina kiransa da mahaukaci, idan aka bibiya ya ma fika hankali". Jiniyo ya girgiza kai cikin takaici ya ce "Na yi tunanin kina da hankali ashe ba haka ba ne, yau kin karya mini zuciya Joriyya".

"A'a bayanka na karya ba zuciya ba, ina naga zuciyar taka da zan karyata? Bana son sharri kuma ka daina shiga harka ta". Tana gama faWar haka ta haye sama da sauri.

Cike da ba?in ciki Jiniyo ya juya ya fita ransa a matu?ar Sace, yana ?ara jin ?iyayyar mahaukacin nan mai tsanani a zuciyarsa, take ya sha alwashin sai ya kuma Waukar hukunci mai tsanina a kansa, sai dai komai zai faru ya faru.


Momy ta zauna a falon idanunta sun canza launi "Wannan wace irin masifa ce? Yarinya gabaWaya ta rikice, anya ba malami zamu samu ya yi mata addu'a akan wannan lamari ba?" Tana tsaka da tunani ta ji ana kiran wayarta ko da ta duba Na'ima ce, Wauka ta yi jiki a sanyaye

"Hello Momyna"

"Na'am Na'ima ya kuke?".

"Alhamdulillah Momy ya gida? Ya Dady da kuma rigimamiyar ku?".

"Kowa yana nan lafiya, Auta yanzu ta dawo daga school, ina Ummie ne tana lafiya?".

Na'ima ta ce "Ummie yanzu ta fita da Dadyn ta. Momy ina fatan dai Auta ta daina rigimar da take yi Win?". Momy ta nisa ta ce "Tsakanin jiya da yau kafin ta je school ta yi sau?i duk da abin na ranta, amma daga fitar ta makaranta kinga yanzu ta dawo a rikice, ashe da aka tashe su daga school sai da ta biya gurinsa kafin ta dawo gida, baki ga rigimar da suka gama yi da Jiniyo ba da ya ganta a gurin. Na'ima al'amarin nan ya fara isa ta, na fara tunanin ko malamai za mu sa suyi mata addu'a. Yanzu fa hadda faWin take yi wai ha mahaukaci ba ne, an manta da shi ne, ban san me take nufi da wannan maganar ba. Yaro kamar ba mutum ba gabaWaya yarinya ta rikice akansa, kuma fa sai kin ganshi ba wani babba ba ne, matashi ne kamar Jiniyo".

Na'ima ta ce "To Momy ya aka yi ta je gurin sa? Ba tare take da direba ba?".

"Na'ima sai ka ce baki san halin Auta ba, tare take da direba kin san dai halin tsiwarta idan ta tashi, ina tunanin tursasa masa ta yi, dole ba yadda ya iya ya je Win".


"Duk da haka Momy bai kamata suna biye mata ba, tunda sun san ba ku son hakan da take yi, sannan Momy na ce idan kunga da matsala ta dawo gurina da zama mana, ina ga idan aka nisanta ta da shi ai za ta ha?ura".

"Ina ga hakan za a yi, duk da ta ce ba za ta je gurinki ba, amma dai yanzu bari Alhaji ya dawo na ji yadda zamu yi da shi, a fara saka malamai su yi mata addu'a tukuna mu ga abin da hali yayi, idan ba ta daina ba dole za ta bar ?asar nan".

Na'ima ta ce "To shikenan Momy, duk yadda ake ciki ki sanar dani, ai ba dole sai ta yarda ba" ci gaba da tattauna matsalar suka yi daga ?arshe suka yi ajiye wayar.


Joriyya na shiga Waki ta zauna idanuwanta cike da hawaye, zuciyarta na bugawa da sauri, ta yi shiru tana tunanin yadda taga hannunsa ya ?ara kumbura "Dole ne nasa Dady ya siya maka magani, ba na son ganin wannan ciwon a hannunka" ta ?arasa maganar tana matsar ?wallah.

Da yamma sosai Dady ya dawo gida, bayan ya yi wanka ya ci abinci. Momy ta ce "Alhaji Auta fa ta koma gurin mahaukacin nan yau". "Kamar ya? Ban gane ba? Ba yau school ta je ba? Taya aka yi har ta fita ta je gurin sa?" Ya yi maganar yana tsare Momy da ido.

"Alhaji daga school Win ta wuce gurinsa, bayan an tashe su".

"What! Taya aka yi ta je can Win? Ina direba ne ko ba aje Waukar ta ba ne?"

"Tare fa da direba take, tare suka je gurin" Momy ta faWa tana kallonsa. Cikin tsanin fushi Dady ya mi?e tsaye zai fita, da sauri Momy ta ce ''Alhaji ina za ka je ne?" .

"Zan je in ji dalilin daya sa zai kai mini yarinya gurin wannan banzan" . Momy ta ce "Haba Alhaji kafa san halin Auta, ni yanzu ba zanga laifinsa ba, ina da ya?inin takura masa ta yi, ka yi ha?uri ka da je yanzu, idan ma magana za ka yi masa ka bari sai gobe. Alhaji lamarin nan ya fara Waure mini da kai, yau dalilin zuwanta gurin nan sai da na shiga tsakaninta da Jiniyo, baka ga rashin kunyar da ta yi masa daga ya yi mata maganar ta daina zuwa inda yake, ka yi ha?uri koma ka zauna ina da shawara".

Komawa ya yi ya zauna yana jin zuciyarsa na yi masa zafi sosai "Duk da haka Shafa bai kamata ya biye wa Shalele ba" ka yi ha?uri Alhaji, yanzu dai ina da shawara, ni a ganina mu saka malamai su fara yi mata addu'a, saboda ina tunanin kamar yaron nan ba mutum ba ne, yarinya gabaWaya ta rikice". Shiru ya yi yana nazarin maganarta kafin ya ce "Kin kawo shawara, zan yi wa Malam Nura magana ya ri?a zuwa yana yi mata addu'a ko Allah zai sa a dace".

Kafin Momy ta yi magana, kamar daga sama suka ji Joriyya ta ce "Dady nima aljanu ne dani irin na Anty Teema ta makarantarmu? Ru?iyya za a fara yi mini? Dady bari na kwanta na fara birgima irin yadda Anty Teema ke yi sai a kira Malam ya yi mini ru?iyya".

Amanarcool
0816351679



=ئ? AKWAI SILA =ئ?


BY AMANARCOOL


YOTA ID/021


SHIN RAMA CE MATSALARKI? BUSHEWAR JIKI KO KUMA MATSALAR SANYI? TO ALBISHIRINKI, NA ZO MUKU DA INGANTACCIYAR SABAYA DA AKA SARRAFATA DA NATURAL GRAINS, HERBS DA KUMA SPICES, WADDA ZA TA INGANTA LAFIYAR JIKINKU, TA CIKO DA JIKI, SAMAR DA RUWAN NONO GYARAN BREAST, TA KUMA YI MUKU MAGANIN SANYI DA MA SAURAN GYARAN JIKI NA MATA, DUK A KAN KU?I ?ALILAN. SABAYARMU BA MA SANYA ?WAYA A CIKINTA, DA TSIRRAI KAWAI MUKE SAMAR DA ITA. SANNAN AKWAI MAGANIN SANYI GA MASU FAMA DA MATSALAR INFECTION KOMAI DA?EWARSA. AKWAI COMPLETE SET NA GYARAN BREAST, SPECIAL PACKAGE, KU NA IYA TUBTU?A TA KAI TSAYE KU TUNTU?E NI AYSHERCOOL TA LAMBOBIN WAYATA 08081012143.


PAGE 21-22


Baki buWe Momy ke bin Dady da kallon, Dady kuma na kallon Joriyya dake ?o?arin kwanciya a ?asa. "Shalele" ya faWa da ?arfi, fasa kwanciyar ta yi, ta Wago da kanta ta kalle shi ta ce "Na'am Dady".
"Me kike ?o?arin yi ne?"

"Dady birgima zanyi irin yadda Anty Teema ke yi idan..."

"Shalele!" Ya daka mata tsawa "Ke daina wannan wasan ba na so, ka da na sake ganin kin kwatanta yin irin haka".

Shiru ta yi ta Sata fuska kafin ta ce "To Dady addu'ar me za'a yi mini? Ko don in daina jin tausayin mutane ne? Dady kasan wani abu? Jin zafi nake idan na ga mutum yana wahala".

Sai a lokacin Momy ta yi magana "Auta wai ke bakinki ba zai taSa yin shiru ba ne?". Joriyya ba ta ce ?ala ba, ta bar falon ta haura sama, tana shiga Waki ta kulle ?ofa, zama ta yi a gefen gadonta, hawaye na taruwa a idonta "Me ya sa mutane ba sa ganin abin da nake gani ne? Bana son ganin mutum a cikin damuwa". Ta faWa tana du?ar da kanta tsakanin ciniyoyinta.

Bayan tafiyar Joriyya Momy ta kalle Dady ta ce "Oh ni Shafa'atu ina ganin abin da yafi ?arfina, ji mini wata lukutar masifa da take ?o?arin gayyato ma kanta. Alhaji bori fa take wasan yi". Dady kasa magana ya yi yana jin yadda gabansa ke faWuwa, wani irin tsoro da fargaba na ?ara shigarsa, ya mi?e a hankali ya nufi Wakinsa zuciyarsa cike da tunani iri-iri.

Jiniyo ne kwance a Wakin abokinsa, idonsa a rufe, wani tu?u?in ba?in ciki yake jin yana taso masa tun daga tafin ?afarsa zuwa cikin ?irjinsa, zuciyarsa na yi masa zafi mara misaltuwa, buWe idonsa ya yi yana furzar da isaka mai zafi, ya kalle abokansa Salim da Yasir ya ce "Gayu wallahi ni ne zanyi ajalin wancan wawan mahaukacin, wai har ni Jory za ta kalla ta ce wancan banzan yafi ni hankali? Ni? Ni Jiniyo? Impossible, sai na ?ara koya masa hankali, idan ma da sauran hankali a tattare da shi sai na yi sanadiyar da zai rasa shi gabaWayaa. Zanyi masa abin da zai ?ara zama silar Sarkewar haukarsa!" Ya ?arasa maganar cikin ?unar rai.

Salim ya ce "Jiniyo this is sad and frustrating for us, taya za'a yi mahaukaci ya ri?a baka matsala irin haka? This is embarrassing for us".

Cike da jin haushi Yasir ya ce "I'm not happy about that, tabbas wannan abin kunya ne a gare mu, dole ne mu Wauki matakin da ya dace akan wannan lamarin, kamar mu za a zo wa da wannan rainin hankali?".

Jiniyo ya dube su da idanunsa da suka canza launi ya ce "Me ya kamata muyi masa wanda zai sa jikinsa ya gaya masa?". Salim ya yi wuff ya ce "Kamata ya yi an jima da isha mu same shi muyi masa Wan banzan dukan da sai ya kasa tashi, mu canza masa kamanni ta yadda idan ta gan shi ba za ta yi marmarin sake ganinsa ba".

Yasir ya ce "Good job Salim, that s a suggestion this is how we should handle him." Cike da gamsuwa suka yi na'am da wannan shawarar.

Bayan sallar isha da ?yar ya tashi daga cikin bolar ya koma kangon nan ya kwanta yana fitar da numfashin da ?yar saboda azabar da yake ji a hannunsa. Karensa ya fita, nesa da gurin suka yi parking Win motarsu, a hankali suka ?arasu gurin cikin sanWa, yana kwance sai gani ya yi an haske shi da fitar wayar dake hannunsu. Ya sa hannunsa mai lafiya yana kare fuskarsa. Jiniyo ya ?arasa inda yake suna ci gaba da haske masa fuska da fitilar waya, du?awa ya yi ya cusa masa wani abu mai raWaWi a cikin bakinsa, ya sa salatif ya li?e masa baki. Shure-shure ya fara yi yana jin raWaWi da azaba na ratsa masa baki kamar ana yanka shi da reza. Cike da rashin imani Salim ya du?a yana Wauke sa da mari tare da matse hannunsa mai ciwon. Zabura ya yi ya fara ?o?arin tashi zaune, cikin ?ita da mugunta Jiniyo ya mayar da shi kwance yana ?ara matse hannun daya kumbura yana wal?iya. Mimmi?ewa ya fara yi yana kakari, Jiniyo ya ce "Ai baka ga komai ba tukuna, sai na yi ajalinka" Ya faWa yana mi?ewa tsaye, babu imani balle tausayi suka fara dukan shi da sandunan da suka zo da su, duk inda suka samu a jikinsa duka suke yi. Wani bugu da Jiniyo ya yi masa a ido sai da ya mi?e zaune da ?arfi, da ?afa Yasir ya mayar da shi kwance. Sai da suka tabbatar da sunyi masa duka ba na wasa ba, kafin suka ?yale shi, Jiniyo ya fito da sabuwar reza a cikin aljihunsa, ya dam?i hannunsa mai ciwon ya yi masa yanka uku manya, sannan ya mi?e. Nan take numfashinsa ya Wauke gabaWaya, ganin ya daina numfashi ya sa suka fice gurin da gudu, motarsu suka shiga tare da janta da ?arfi. Jiniyo ya lumshe idonsa yana jin zafin zuciyarsa na raguwa.

Bayan kamar minti goma da tafiyarsu Karensa ya dawo bakinsa Wauke da ledar abinci, gabansa ya zo ya ajiye ledar, sai dai duk da duhun da ya mamaye gurin ya lura da rashin motsin sa, zagaye shi ya fara yi yana kuka. Sai dai shiru bai motsa ba, da ya gaji da kukan ya zo kusa da shi ya kwanta.

Hasken ranar da ya fara fitowa ne ya dake kumburariyar fuskarsa, a hankali ya fara motsa jikinsa da yake a kumbure, hannunsa mai ciwo ya ?ara kumbura ga busashen jinin da ya bushe ya ?ara mannewa da fatar gurin, idonsa Waya ya kumbura sosai. Ciwon da ke ratsa jikinsa ba zai iya bayyana shi da baki ba, ajiyar zuciya yake saukewa kaWan, idanunsa suka fara buWewa a hankali. Ji ya yi kamar ?wayar idonsa Waya za fito tsabar azabar daya ji a gurin, ?o?arin motsa bakinsa yake son yi ya kasa saboda salatif Win dake manne a gurin, cikin azaba ya saka hannunsa mai lafiyar wanda shima ciwo yake masa a yanzu sakamakon dukan da a ka yi masa, cire salatif Win ya yi daga bakinsa yana zubar da yawo, abin da suka tura masa a baki tuni ya narke masa a ciki. Iska ya furzar mai zafi yana nishi da ?yar, cikin ?arfin hali da jarumta ya tashi zaune yana jingina jikinsa da ruSaSSen ginin dake gurin. Kallon hannunsa ya yi yaga yadda hannun ya ?ara hawa, ga yanka a cikinsa, ya runtse idonsa hawaye masu zafi na zuba a gefen fuskarsa. Dubawa ya yi baiga karensa ba, ya mi?e da ?yar yana tangaWi, fuskarsa a kumbure ya fita waje yana jan ?afarsa dake yi masa ciwo sosai, bakin bolar nan ya je ya zauna ya tsurawa hanyar da motar su Joriyya ke biyo wa.

Misalin ?arfe tara Dady ya je har gida ya samu Malam Nura. A ?ofar gida ya same shi zaune yana karatun da ya saba a nutse, cikin tsafta da kamala. Dady ya fito daga motar shi ya nufe shi. Malam Nura ya saki fuska ganin Dady, da sallama ya isa gurin, Malam Nura ya amsa yana mi?a masa hannu suka yi musabaha suna gaisawa cikin mutunci, Dady ya zauna akan tabarmar dake shimfiWe a gurin.

Malam Nura ya ce "Alhaji yau kai ne da kanka a ?ofar gidana?".

Dady ya dubi shi cikin yanayi na damuwa ya ce "Na zo ne akan batun yarinyata ne, kwana biyu bamu gane ma kanta, shi ne muke tunanin ko akwai matsalar shafuwar aljanu a tare da ita, akwai wani mahaukaci da tunda ta fara ganinsa gabaWaya ta rikice, da farko mun Wauka tausayinsa ne take ji, daga baya sai muka ga abin ya fara wuce gona da iri. Shi ne nake son ka taimaka mana da addu'a. Saboda ina zargin mahaukacin nan kamar ba mutum bane aljani ne, kullum bata da batu sai na shi, gabaWaya ta bi ta susuce akan shi".

Malam Nura ya jinjina kai ya ce "Babu damuwa in sha Allah zamu yi abin da ya kamata, gidan zan je ko kuma nan za ka zo da ita?".

Dady ya ce "Idan babu damuwa ina son mu je yanzu, idan kuma kana da wani uzuri ne sai mu bari zuwa anjima da yamma sai na aiko a Wauke ka"

Malam Nura ya ce "A'a muje yanzu, anjima da yamma akwai in da zani". Dady ya yi murna sosai da hakan, Malam Nura ya naWe tabarma ya kai cikin gida sannan ya fito, mota suka shiga direba ya ja motar suka wuce. A rantsatstsen falon saukar ba?in Dady aka sauke Malam Nura, nan aka kawo masa lemu da ruwa. Dady ya wuce ciki, bai Wauki lokaci ba ya dawo falon hannunsa ri?e dana Joriyya. Da sallama ya shigo, Malam ya Wan bi ta da kallo yana nazartarta. Risinawa ta yi cikin sanyin murya ta gaida Malam, ya amsa mata cikin sakin fuska, Dady ya dubi shi cikin yanayin damuwa ya ce

"Gata nan Malam, lokaci Waya muka kasa gane ma kanta, gabaWaya ta birkice, don Allah a Wan duba mana ita ko da wata matsalar" Malam Nura ya jinjina kai sannan ya fara yi mata karatu tare da karanta addu'oi. Ya Wauki dogon lokaci yana karatun, ita dai Joriyya kanta a ?asa tana sauraren ikon Allah, zuwa can Malam Nura ya kalle ta na Wan lokaci kafin ya girgiza kai ya dubi Dady ya ce "Alhaji yarinyar nan bata da komai, babu wani shafar aljanu da yake damunta, wata?ila ta sakawa ranta tsananin tausayin shi ne shi ya sa take yin haka, sai dai akwai al'amari mai girma a tare da wannan ?ar taka wanda na kasa fahimtar ko mene ne, amma in sha Allah nan kusa ko mene ne zai fara bayyana".

Dady ya girgiza kai cike da damuwa yana dafe kai ya ce "To yanzu babu wani taimakon da za ka iya bamu ne? Saboda tana yawan ambaton shi, tana yawan magana akan shi, tun hakalinmu baya

8 / 11