AKWAI SILA HAUSA NOVELS BY AMANARCOOL.doc

Author :  Amanar Cool Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   6 / 11

15K to 18K   out of 32.7K words

fiye da tunani jama'a.

Matarsa Waya Hajiya Maryam, mace ce mai kunya, nutsuwa, da tarbiyya, wadda ke da mutunci a idon jama'a da dama. A duk faWin birnin Kano, idan ka ambaci familyn Alhaji Kabiru, to ka ambaci iyali ne da babu wanda ya san ?arshen arzikin su. Sai dai duk da wannan yalwar arziki akwai wani abu da ba daidai ba a gidan, abin da tarin dukiyarsu bai isa ya warware musu shi ba. A falon gidan wanda yake ?yalli, fitillun falon na fitar da wani kalan haske mai Waukar hankali. Hajiya Maryam na zaune ri?e da wayarta ta tsura mata ido da alama abu ne mai muhimmanci take kallo a wayar, ta sauke numfashi a hankali "Ya Allah" ta faWa cikin sanyi murya.

Alhaji Kabiru ya shigo cikin falon fuskarsa cike da damuwa, zuciyarsa cunkushe da wani irin tunani mai girma, idan ka duba shi ba za ka iya gane cewar akwai wani abu dake damunsa ba. A waje mutane na yi masa kallon mutum mai cikakkiyar natsuwa, sai dai a cikin zuciyarsa akwai rauni Waya da ya gagara warkewa.


"Hajiya lafiya dai?" Ya tambaye ta yana ?o?arin karSar wayar hannunta, da sauri ta yi baya da wayar saboda ba ta son ya ga abin da take kallo a wayar, ta ce "Alhaji wai wannan karon wane gari za'a je yin taimakon kamar yadda aka saba?"


Ya nisa sannan ya ce "Wannan karon ina son tura wasu daga cikin yarana su je asibitin mahaukata dake garin Abuja da ma sauran wasu asibitocin, idan akwai wa?anda zasu iya warkewa daga matsalar dake damun ?wa?walwarsu, da marasa lafiyar da ke bu?atar taimako duk zan Wauki nauyin kula da komai har Allah ya basu lafiya daga nan idan ta kama a fita dasu waje ne duk zan yi" Hajiya Maryam ta ce "Ma sha Allah, Allah ya taimaka ya yi jagora, na ji daWin wannan abin, Allah ya ?ara tsare mini kai Alhajina". Ya amsa da Amin tare da rumgumota jikinsa yana shafa ta "Alhaji a falo muke fa, ka da Nihal ta tarar damu a haka, kasan wayo ne da ita" . Dariya ya yi yana la?ace mata hanci kafin ya mi?ar da ita tsaye ya ja ta zuwa bedroom Winsa.


*****

Dady tunda ya je ofis zaune ya kasa aikin komai, tunani da damuwar halin da Joriyya ke ciki sun hana shi suku ni a zuciyarsa, noking Win ?ofa ya ji, sai da ya Wauki lokaci kafin ya ba da izinin a shigo, Waya daga cikin ma'aikatan sa ne, "Sir sa?o ne aka ce in ba ka" ya faWa tare da mi?a masa wata ?aramar takarda, har ya juya zai fita Dady ya ce "Waya baka sa?on ka kawo mini?" "Sir ban san shi ba" da hannu Dady ya yi masa alama da ya tafi. A jiye takardar ya yi ba tare da ya duba ta ba, ya ciro wayarsa yana dubawa bayan ya gama duba wayar ne, ya Wakko takardar ya buWa, idonsa ya sauka a kan rubutun dake ciki, wata irin zabura ya yi da ?arfi ya mi?e tsaye, jikinsa ya soma rawa, ya ?walalo idanu waje yana sake kallon rubutun. Duk da sanyin Ac dake cikin ofishin bai hana zufa ya fara fira fita daga cikinsa ba, komawa ya yi ya zauna daSas, yana sauke numfashi, tare da lumshe idanunsa. A hankali ya furta "Ya Allah, waye wannan Win? Me yake nufi da wannan takardar?" . Ji ya yi ba zai iya zama a ofis Win ba ya mi?e da sauri bai tsaya duba komai a ofis Win ba ya Wauki wayarsa ya fita, ma'aikata sai gaishe shi suke yi, bai kula su ba, tun daga nesa security suka ganshi ya fito kamar baya cikin nutsuwarsa, kafin ya ?araso suka buWe masa mota ya shiga, cikin ba da umarni ya ce "Ku yi sauri ina son in ganni a gida yanzu". Ta motar suka yi kamar wal?iya suka bar kamfanin.


Kwance yake a takure cikin kangon, da ?yar yake fitar da numfashi saboda raWaWi da azabar da yake ji, sai juyi yake yana yun?urin tashi ya kasa saboda ciwo da hannun ke yi masa. Hawaye masu zafi na bin gefen fuskarsa, ya ?ara Waga hannun kaWan ya Wan juya sai ya ga karensa baya gurin. Joyawar da zai yi sai ya ga mutum tsaye a gurin. ?uri ya yi da ido yana kallon Jiniyo da idanunsa suka yi ja, fuskar nan tasa babu alamar imani balle tausayi, kallo Waya za ka yi masa kasan tsantasar mugunta da rashin imani ne kwance a kan fuskarsa "Ka ga abin da ka jawo mini ko? A kan ake ?o?arin nisanta ni da Joriyya, yadda ka hana mini jin daWi kai ma ba za ka ji daWin ba, sannan kai da Joriyya har abada". Ya ?arasa maganar cike da ihu da hargagi, cikin rashin imani ya sa ?afarsa ya take masa yatsun ?afa, wata ?arar azaba ya saki yana so ya tashi zaune ya kasa, "Ai wallahi baka ga komai ba, ba kai mahaukaci ba ne yanzu zan koya maka hankali. Ka ga yadda hannunka ya fara yi ki? Zan tabbatar baka mance wannan ciwon ba har abada"

Mahaukacin ?o?arin tashi yake yi ya kasa, cike da raunin murya ya ce
"Ka bar ni"

Jiniyo ya yi dariya mai cike da mugunta.
"Kai ba ni da niyyar barinka, ai tunda ka bari Joriyya ta fifita ka a kaina ba zan taSa barinka ba". Tsayawa ya yi yana kallon hannunsa da ya kumbura sosai, cikin rashin tausayi ya sa ?afarsa ya taka hannun iya ?arfinsa. Mahaukacin ya sake wata irin ?ara, ?arar da ta karaWe gurin, daga nan kuma ya yi shiru saboda numfashinsa da ya Wauke, Jiniyo ya kuma kai masa harbi ga ciki sannan ya bar gurin cike da rashin imani, yana isa bakin ?ofar fita ya yi turus yana ?walalo idanu waje, jikunsa ne ya Wauki rawa, lokaci Waya tsoro da firgici suka bayyana, ja da baya ya fara yi yana girgiza kansa cike da kaWuwa.


Amanarcool
08163516796



=ئ?AKWAI SILA=ئ?


BY AMANARCOOL


YOTA ID/021


*SHIN RAMA CE MATSALARKI? BUSHEWAR JIKI KO KUMA MATSALAR SANYI? TO ALBISHIRINKI, NA ZO MUKU DA INGANTACCIYAR SABAYA DA AKA SARRAFATA DA NATURAL GRAINS, HERBS DA KUMA SPICES, WADDA ZA TA INGANTA LAFIYAR JIKINKU, TA CIKO DA JIKI, SAMAR DA RUWAN NONO GYARAN BREAST, TA KUMA YI MUKU MAGANIN SANYI DA MA SAURAN GYARAN JIKI NA MATA, DUK A KAN KU?I ?ALILAN. SABAYARMU BA MA SANYA ?WAYA A CIKINTA, DA TSIRRAI KAWAI MUKE SAMAR DA ITA. SANNAN AKWAI MAGANIN SANYI GA MASU FAMA DA MATSALAR INFECTION KOMAI DA?EWARSA. AKWAI COMPLETE SET NA GYARAN BREAST, SPECIAL PACKAGE, KU NA IYA TUBTU?A TA KAI TSAYE KU TUNTU?E NI AYSHERCOOL TA LAMBOBIN WAYATA 08081012143*.


PAGE 15-16


Sake buWe idanunsa ya yi, jikinsa na Sari, fitsari na ?o?arin zubo masa, ko a mafarki bai taSa ganin wannan tashin hankalin ba balle kuma a zahiri, mutum biyu ne tsaye a bakin ?ofar kangon kamar an dasa su, idanunsu a buWe suna kallonsa ko ?iftawa ba su yi, fuskarsu kamar an shafa mata karmatako, ko ina a jikinsu raunuka ne. ?ayan ri?e da sar?a a hannunsa, Wayan kuma yana Wauke da wani ?aton tabo a goshinsa. Cikin ruWa ni Jiniyo ya buWe baki zai yi magana sai muryarsa ta ?i fita, numfashinsa ya Wauke. ?ayan ya Waga hannu ya nuna Jiniyo da yatsa, nan take numfashinsa ya dawo, ya mi?e tsaye da sauri, gani ya yi idanunsu na fitar da wuta haWe da wata ?ara da ya rasa sanin daga ina take fitowa, nan ya ji kamar wani abu ya lauye ?afafunsa, kasa tsayuwa ya yi ya faWi ?asa. Lokacin da ya sake Waga kansa da zumar kallon su, ya ga gurin ya koma shiru, kamar babu abin da ya faru, da sauri ya mi?e tsaye, ya juya ya ga har yanzu mahaukacin na nan a kwance ba ya motsi. Jikinsa na rawa. A guje ya fice daga gurin, zuciyarsa na bugu da ?arfi, tsoro da ruWani na ?ara shigar sa.

Su Dady na ?arasa wa guda kafin security su buWe masa ?ofa har ya fito, fuskarsa Wauke da tashin hankali, idanuwansa sun sauya kala. Kamar wanda aka jefo ya shiga falon gidan. Momy na zaune ganin yadda ya shigo Win ta mi?e da sauri "Alhaji lafiya? Me ya faru?" Ta yi tambayar tana tsare shi da ido.

Bai ba ta amsa ba ya haura sama kai tsaye, zuciyarsa na tsananta bugawa, Wakin Joriya ya shiga tana kwance saman gadonta. "Shalele" ya kira sunanta a hankali.

Tashi zaune ta yi tana kallonsa ta ce "Dady".

Ya zauna a gefen gadon yana kallonta kamar zai ce wani abu, sai kuma ya yi shiru, ya san ko da ya yi mata maganar ba za ta fuskanci kalmomin ba, da kuma inda suka dosa ba, lumshe ido ya yi, yana tuna takardar da aka bashi, kalmomin da ke ciki na yi masa yawo a zuciya.

"Shalele ki faWa mini gaskiya" ya yi maganar ?asa-?asa "Idan kika ga wancan mahaukacin me kike ji?".

Joriyya ta kalle shi "Dady wallahi ban sani ba, amma dai ina jin tausayinsa, Dady a ko zamu je mu sake dubawa ko hannunsa ya warke?".

Dady ya lumshe ido wannan ne abin da ya fi tsorata shi akan lamarin ?ar tasa, abin da take yi ya wuce tausayi. "Ya Allah" ya furta a hankali sannan ya dubi Joriyya ya ce "Koma ki kwanta"

"Dady ba za muje mu duba shi ba?"

"Zamu je amma ba yanzu ba" daga haka ya bar Wakin, a bakin ?ofa ya ce karo da Momy, raSa ta ya yi ya nufi Wakinsa, Momy ta le?a Wakin Joriyya ta ganta a zaune ta Wakko wayarta tana dannawa, ba ta ce mata ?ala ba ta juya ta nufi Wakin Dady.
A zaune ta tarar da shi ya du?ar da kansa ?asa, zama ta yi kusa da shi ta dafa kafaWarsa ta ce "Alhaji lafiya? Me yake damunka ne?".

Cike da sanyin jiki ya Wago da kansa yana kallon ta, "Babu komai bana jin daWi ne, gashi yau na yi aiki na gaji".

Shiru Momy ta yi tana kallon sa, ba dan ta gamsu da babu komai ba Win "To ka samu ka yi wanka ko za ka ji daWin jikin ka mana" ta faWa tana ?ara tsare shi da ido. Mi?ewa ya yi a hankali ya cire kayan jikinsa ya shiga toilet saboda baya son ta yi tunanin wani abu. Ganin ya shiga toilet Win ya sa Momy tashi ta fita domin ta haWa masa abinci.

A ruWe Jiniyo isa gida, kamar guguwa haka ya wuce Mama da Abbansa dake zaune a falon gidan, wanda dawowarsa kenan daga tafiyar da ya yi, bai ma lura da Abban nasa dake zanune ba, Wakinsa ya je yana shiga ya saka wa ?ofar key, ya haye gadonsa, ya rufe kansa da bargo ban da rawar sanyi ba abin da yake yi.


"Ba ka tsira ba" ya ji an faWa da murya mai firgitarwa, buWe ido ya yi a firgici ya tashi zaune, gumi na tsatstsafo masa a goshinsa. Ya duba gefensa, babu kowa, ri?e kansa ya yi yana girgiza wa. "Me yake shirin faruwa da ni ne? Wai waye wannan mahaukacin? Daga ina ya fito? Lallai ta tabbata ba mutum ba ne, in ma mutum ne tabbas akwai wani zafi da yake yi, ko wani abu da ba daidai ba a tare da shi, ya zama wajibi na ?ara nisanta Joriyya da shi". ya ?arasa maganar yana sake kwanciya ya ?udundune a bargon, zuciyarsa na ?ara gaya masa abin da ya gani ba wasa ba ne. Duk da wannan hali na firgici da yake ciki, bai fasa jin tsanar mahaukacin ba da kuma sake shan alwashi akansa.

Iyayen Jiniyo ganin yadda Wan nasu ya wuce ba tare da ya kalli inda suke ba suka san cewar ba lafiya ba, ko da Mama ta biyo bayansa ta ji ko lafiya? Ta tarar daya rufe ?ofar ta buga ?ofar tare da yi masa magana ta ji shiru, jin an fara kiran sallar magariba ya sa ta juya ta bar gurin.


Bayan sallan isha su Momy na zaune a falo tare da Joriyya, game take yi a wayarta tana murmushi, Momy ta kalle ta cike da jin daWin ganin yau ta sake jiki tana walwala ba kamar kullum ba, ta ce "Auta ko ke fa, hakan yafi ai, ki ri?a sakin jikin ki, kina wasa da dariya kamar yadda kika saba, ki cire damuwar komai da tunanin komai a ranki" .

Hankalin Joriyya na kan game Win da take yi ta ce "To Momy na daina, daga yanzu ba zan sake ba" . DaWi ne ya cika zuciyar Momy ta kalle Dady da hankalinsa baya kansu, yana can Duniyar tunani ta ce "Alhaji kana jin abin da Auta ke faWa?" Sai a lokacin ya mayar da hankalinsa kansu ya ce "Me ta ce?"


"Au baka ji abin da ta faWa ba? Alhaji kamar akwai abin da ke damunka, tunda ka dawo daga gurin aiki na lura da yanayin ka ya canza, don Allah idan akwai abin da ke damun ka ka gaya mini?".


Kafin Dady ya yi magana suka ji Joriyya ta ce "Dady wai nima yaushe za a yi mini aure in haifi yara? Anty Na'ima tana da ?arta Ummie, Anty Zainab tana da Fahat, nima ina son in haihu a ri?a ce mini Momy da Dady kamar yadda nake kiran ku" ta ?arasa maganar tana dariya tare da ajiye wayarta ta sake duban iyayen nata ta kuma cewa "Momy wai yanzu shima wancan mutumin haifarsa aka yi ne ko kuma daga sama ya faWo? Bashi da iyaye ne? Naga kullum shi kaWai yake zama a cikin datti, Allah Sarki Dady gobe zamu je mu sake duba shi ko? Hannunsa na yi masa ciwo sosai, Dady shin wai...."

"Auta ki yi shiru haka nan" Momy ta katsita, kafin ta ce "Ba yanzu kika gama ce mini kin daina zance sa ba? Auta ki raba kanki da zancen yaron nan idan ba haka ba Dubai zamu tura ki can gurin Na'ima kowa ma ya huta".

"Momy ba zanje ba"


"To ka da na sake jin kin yi maganarsa, idan ba haka ba Dadyn ki zai kai ki gurinta".

"Dady da gaske za ka iya kai ni can ku daina ganina?" ta yi maganar tana tsare Dady da ido.


"Eh mana Shalele idan baki son zuwa to ki daina nuna damuwar nan da kike yi akan wanda baki san daga ina yake ba, ba a san asalinsa ba, kuma gashi yana fama da matsalar ?wa?walwa".

"Dady shi ma fa mutum ne, kenan in ba a san asalinsa ba daga sama ya faWo ko?".


Dariyar takaici ce ta suSuce musu gabaWaya, suka kasa ba ta amsa, a wannan daren haka Joriyya ta shiga zuba musu shirme kamar ba ita ba, wani abin ya basu dariya wani kuma haushi suke ji.
Sai da dare ya yi sosai sannan Momy ta raka ta Wakinta ta kwanta, suma suka wuce nasu Wakin.


Haushin karensa ne ya farfaWo da shi daga suman da ya yi, a hankali ya buWe idonsa sai dai duhun dare ya sa baya iya ganin komai, cikinsa na ?ugi alamar yunwa yake jiki sosai, ga azabar da hannunsa ke yi masa wanda a yanzu ko motsa shi baya iya yi, ya yi iya yinsa ya tashi zaune ya kasa, gefen cikinsa na yi masa ciwo. A haka ya ?ara komawa ya kwanta tare da rufe idonsa hawaye masu raWaWi na zubo masa. Karensa sai kuka yake yana zagaye shi. A haka bacci ya kuma Waukar sa, washe gari, cike da ?arfin hali da jarumta ya samu da ?yar ya tashi zaune, ya jingina bayansa da jikin ruSaSSen tsohon ginin dake cikin kangon, zuciyarsa ba ?aramin Waci take yi masa ba. Wata irin suka yake jin tana ratsa hannunsa zuwa ?irjinsa. Ya runtse idanu yana jan dogon numfashi mai azaba. BuWe idanuwansa ya yi hasken rana ya doki ?wayar idonsa da sauri ya rufe su, gurin ya yi shiru baka jin motsin komai sai na iskar da take kaWawa, ya Waura hannunsa mara ciwon a kan ?irjinsa kamar yana tantama ko zuciyar da ke bugawa a ciki tasa ce, ko kuma wata irin halitta ce da ta tsaya masa a ciki. A hankali kamar wanda ya manta yadda ake magana, ya furta kalmomin da shikaWai yasan abin da yake faWa. Ji ya yi kamar ana kiransa daga nesa, kiran da ya kasa fahimtar daga ina ne? Ya jingina kansa da bango, idanu a lumshe, yana jin kamar ana jansa zuwa wani guri, guri da bai san shi ba. Karensa ne ya shigo masa da ledar abinci ya ajiye a gabansa, da sauri ya Wauki ledar abincin da hannunsa mai lafiyar ya fara ci yana zaro ido waje. Bayan ya cinye abincin duka, ya samu da ?yar ya mi?e tsaye ya fita daga cikin kangon a hankali yake tafiya har ya isa cikin bolar da yake zama ya zauna. Yana kallon jama'ar dake wuce.

*****

"Yaya gaskiya ya kamata ka ?ara aure, ka dubi irin arzikin da Allah ya azzurta familyn mu da shi. Sannan a cikin familyn ma kafi kowa arziki mai yawan gaske, amma a ce ka zauna da mace Waya? Yaya ka dubi sauran ?an uwa da basu kai ba, daga mai mata biyu sai mai uku. Haba ai ko dan ka samu yaran da za su iya tallafa maka a nan gaba ka ?ara aure, tunda ita wannan ba haihuwar take yi ba, tunda ta haifi Nihal shekara goma kenan ba ta sake yin ko da Sari ba ne balle a saka ran sake samun wani rabon daga gare ta". Shiru ya yi yana kallon ta sai da ta gama faWar abin da ke ranta kafin ya gyara zamansa ya ce

"Kina ji ko Mariya? Ni Alhaji Kabiru Umar mai nera, bani da ra'ayin zama da mata biyu, matata ta ishe ni, komai nake so shi take yi mini, ba ta rage ni da komai ba, sannan maganar yara da kike magana idan da rai da rabo zamu iya koma samun wasu yaran, idan ma bamu samu ba Alhamdulillah Nihal ta ishe ni, babu wata mace da zan iya tsayawa da ita balle har in

6 / 11