AKWAI SILA HAUSA NOVELS BY AMANARCOOL.doc

Author :  Amanar Cool Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   5 / 11

12K to 15K   out of 32.7K words

karya masa ?afa ba? Tsaki ya yi yana jin tsanar mahaukacin mai tsanani a zuciyarsa.

Joriyya na zaune a kan gadonta, tana jin zuciyarta kamar an Wora mata wani abu mai nauyi, a duk lokacin da ta rufe idanunta sai ta hango yadda mahaukacin ya faWi, da lokacin da ya mi?a mata hannu, da ajiyar zuciyar da ya sauke. A hankali ta ce "Ya zan tafi? Ya zan bar shi haka? Ya zan tafi ba tare da na san ko zai ci abinci ba?". Kuka ne ya kuma ?wace mata, kwanciya ta yi ta ci gaba da kukan.

Tunda Jiniyo ya bar gurin, yake zaune ri?e da hannunsa da ya fara kumbura, wasu ?ananun jijiyoyi sun fito, fatar hannun ta yi ja sosai. Ya kalli hannun kamar ba nasa ba, ya tsaya yana rawar sanyi da raWaWin da ya ke yanka masa tun daga yatsunsa har zuwa kafaWarsa.

?o?arin tashi yake amma gwiwoyinsa sun kasa Waukar nauyinsa, sake buWe idonsa ya yi kamar wanda ya ga wani abun tsoro. A hankali yake motsa hannun yana ?o?arin danne raWaWin da yake ji, wata ?ara ce ta suSuce masa. Ya kalli ?ofar kangon, yana jiran ko zai ga wadda kullum ke zuwar masa da abinci ko murmushi. Sai dai ya ga wayam babu komai sai iskar da ke shigowa tana shigar masa hancinsa tare da tunatar da shi cewa yau shi kaWai yake cikin Duniyar da bata da suna. Karensa na tsaye sai zagaye shi yake yi yana fitar da harshe.


Momy na falo ta ji shirun Joriyya ya yi yawa tunda ta shiga Waki ba ta fito ba, tashi ta yi ta shiga Wakin, kwance ta tarar da ita numfashinta na fita sama-sama, da sauri ta ?arasa inda take "Auta lafiya? Ina fatan dai ba jikin ba ne?". Cikin fizgar numfashi ta ce "Momy ?irjina, zuciyata, zan mut..." Ba ta ?arasa ba jikinta ya fara girgiza idanunta suka birkice nan take jini ya fara zuba ta kunnenta da hancinta, fashewa da kuka Momy ta yi, ta fara jijjigata "Auta Auta ciwon ne ya tashi? Don Allah kar ki mutu Auta, kin ga abin da muke yi miki gudu ko? Shi ya sa ba ma son kina shiga damuwa". Momy ta rikice sosai ganin wannan karon hadda jini ke fita a jikin ?ar ta ta. Wani irin yun?uri Joriyya ta yi, ta ja numfashi mai haWe da gurnani daga haka ta yi Wif. Ihu Momy ta yi ta sauka daga kan gadon ta yi waje da sauri, Wakinta ta je ta Wauki wayarta cikin ruWani ta fara kiran Dady, sai dai wayar ba ta shiga, nan ta ?ara shiga ruWa ni ta koma Wakin Joriyya da sauri, tana shiga Wakin, turus ta yi ta ?ame a bakin ?ofa tana kallon abin mamaki da al'ajabi. Joriyya ta gani zaune kamar babu abin da ya faru da ita, ta yi shiru tana kallon gefe.

Cikin sar?ewar murya ta ce "Auta"


?ago da kai ta yi ta kalli Momy ba ta ce ?ala ba "Auta babu abin da ke damunki ne?" Momy ta yi maganar tana zama kusa da Joriyyar.


"Momy"

"Na'am Auta"

"Ka da ku kai ni gurin Anty Na'ima ba na so, idan kuka kai ni can mutuwa zanyi".


"To Auta ki kwantar da hankalinki in sha Allah ba za ki je ba, amma da sharaWi Waya, sai in za ki daina shiga harkar wancan mahaukacin?". Shiru ta yi ba ta amsa ba, daga ?arshe ta yi kwanciyarta, ganin haka ya sa Momy tashi ta bar Wakin don ta san ba kulata za ta kuma yi ba.


Wasa-wasa mahaukacin nan ya kasa iya tashi. Hannunsa ya kumburi sosai har ya fara sauya launi. Ya matse yatsunsa, yana jin wani irin raWaWi mai zafi, ya cusa hannun a ?irjinsa yana neman sau?i da sassauci akan zafin ciwon yake ji. Ya jingina da bango yana fitar da numfashi mai zafi kamar mai ciwon daji.

A hankali ya fara furta wasu kalaman da shikaWai ya san me yake faWa, ya lumshe idanuwa yana jin zuciyarsa na yi masa nauyi fiye da kowane lokaci, hanjin cikinsa sai ?ugi suke yi alamar babu komai a cikin nasa. Sake buWe ido ya yi ya kalli ?ofar kangon ya sake rufe idonsa, yana son tashi ya je bolar da yake zama amma babu hali. A haka ya koma kada kai ya kwanta cikin mawuyacin hali.


Yau lamarin Joriyya ya ?ara tsorata Momy, ya ba ta mamaki matu?a, ta fara gasgata cewar akwai abin da basu gane ba akan Auta, yarinyar da idan ciwon nan ya tasar mata da ?yar yake lafawa, sai gashi yau ya kwanta cikin ?an?anin lokaci, sannan ya zo da wani sabon salo. Ko da Dady ya dawo ta gaya masa abin da ya faru shima ya tsorata matu?a. Cikin dare suka je Wakin Joriyya a kwance suka same ta tana kuka, jikinta ya yi sanyi, idonta a kumbure. Momy ta zauna a gefen gadon ta dafa kanta ta ce "Autata ki yi ha?uri ki kwantar da hankalinki, ai na ce miki ba za ki je ko ina ba kina nan tare da mu, dama munyi hakan ne don nema miki mafita amma tunda baki so Shikenan, sai dai idan baki daina wannan damuwar ba, da shiga harkar mutumen can, dole ne ki bar ?asar nan".

Joriyya ta gyaWa mata kai, hawaye na zuba a idonta kamar ruwa, ta ce "Momy shi fa? Wane hali zai kasance a ciki? Wa zai kula da shi? Shi baya da kowa? Babu mai sonsa ne?".

Momy ta runtse ido ta ce
"Allah zai kula da shi. Kin yi abin da duk wata zuciya mai tausayi za ta yi. Amma yanzu ki kwantar da hankalinki. In sha Allah komai zai tafi daidai, zamu sa a ri?a kula da shi a bashi abinci ba tare da kin je gurinsa ba". Shiru ta yi ba ta kuma magana ba, ta zubawa Dady ido tana kallonsa.

"Dady"

"Na'am Shalele"

"Mu je yanzu mu kai masa abinci yunwa yake ji". Dim! ?irjin Dady ya yi, ya runtse kafin ya ce "Shalele kwanta ki yi bacci da safe sai mu je". Daga haka ya buWe ?ofa ya bar Wakin.

Momy tasa hannu tana rufe bakinta jin kuka na ?o?arin ?wace mata, ta mi?e a hankali ta koma bakin ?ofa, tsayawa ta yi cak, ta juya ta kalli Joriyya "Allah ya tsareki Autata" ta furta cikin rauni.

?akin Dady ta wuce da sallama cikin murya mai raunu ta tsaya a bakin ?ofa

Amsawa ya yi ya ce "Shigo"

Shiga ta yi yana zaune a gefen gado hannunsa ri?e da kansa, tun da ya dawo daga ofis baya cikin nutsuwarsa, abubuwa da yawa na damunsa, ga matsalar Joriyya, ga wani abu mai girma da yake Soye a cikin ransa wanda baya fatan fitowarsa.

Momy ta sauke ajiyar zuciya.
"Alhaji Joriyya ba ta cikin hayyacinta fa, wannan lamarin ya dame ta sosai".

Dady ya lumshe ido, ya Wauki lokaci kafin ya buWe su. "Na sani Shafa, amma dole ne mu yi wannan tafiyar matu?ar naga abin yana neman fin ?arfinmu, wane irin al'amari ne haka? Lokaci Waya yarinya ta rikice akan mutumin da kowa ke gudu".

"Alhaji kamar akwai abin da ke damunka bayan wannan?"
"Ina ma akwai, bari mu gama da wannan matsalar tukuna, shi ne abin da ya fi muhimmanci a yanzu".Ta yi shiru tana kallonsa, yanayin sa ya nuna cewar akwai wani abu mai girma da yake tsoro fiye da komai. A haka shiru ya shiga tsakanin su, haka suka kwanta ko wanne zuciyarsa a cunkushe.

Washegari kafin kowa ya fito Joriyya ta fita harabar gidan cikin sauri, idanunta a kumbura, ta kusanci get Win gidan security biyu suka taso da hanzari Wayan ya ce

"Baby Joriyya ina zuwa haka?"

"Fita zanyi" ta bashi amsa

"Ba za ki fita ba, ki yi ha?uri umarni ne daga oga".

Ta tsaya gabansu tana rawar sanyi da kuka "Ku matsa ku matsa na wuce!" Ta Waga musu muryarta cikin tsiwa da hargagi "Ba za ku takura mini ba, zan je duk inda nake so, ku matsa mini!" Mamaki ne ya cika su, ?aramar yarinya da ita amma muryarta ta cika da hargowa da tsanani kamar wata babba.

"Haba Shalele don Allah ki koma ciki& "

"Ku ?yale ni" ta katse su tana fashewa da kuka, ta fara ture su da ?aramin jikinta, ta hau ihun da ya karaWe ko'ina, "Kada ku hana ni, don Allah ku bar ni na gan shi, ba daWewa zan yi ba yanzu zan dawo".

Hankalin security ya tashi sosai. Da sauri Wayan security ya nufi cikin gidan a bakin ?ofa ya ce karo da Dady ya fito da sauri jin ihun Joriyya, ?arasawa ya yi yana faWin

"Me ke faruwa ne?"

Ganin Joriyya ya yi a tsaye idonta cike da ?walla tana neman Waukewar numfashi "Shalele" ya kira ta cikin murya mai rauni "Me yasa ki ka fito yanzu? Ina zaki je ne?".

Da sauri ta ?arasa gareshi, ta kama rigarsa tana kuka kamar za ta suma.
"Dady don Allah zan je in duba shi, zai mutu da yunwa idan ban je ba!".

Dady ya furzar da iska mai zafi, ya lumshe ido "Shalele na ce ba za ki je gurin wancan mutumin ba, ki manta da shi!"

"In manta da shi? Dady ya zan manta da shi?" Ta rushe da kuka tana girgiza kai. "Dady shi baya da kowa, ni ce kawai nake zuwa gurinsa ina taimaka masa" Momy da ta fito a guje ta tsaya zuciyarta na yi mata zafi, tana jin kalmomin ?arta na ?ona mata rai, hana mata fita Dady ya yi ya jata zuwa ciki ya zaunar da ita a Wakinsa cikin damuwa da rashin sanin abin yi.

Yana zaune a kangon nan kamar jiya.
?ura ta lulluSe shi, hannunsa ya ?ara kumbura har fatar ta fara tsagewa a gefe, karensa na zagaye da shi yana yi masa kuka da wata irin murya da ba a saba ji ba.Ya Waga hannun yana kallonsa kamar an canza masa shi. Hawaye ya gangaro gefen idonsa, ya jingina kansa a kan dutse yana jin zafin ciwon na ratsa shi. Da ?yar ya iya mi?ewa tsaye ya fito ya zauna a cikin bolar da ya saba zama, mutane na wucewa suna kallonsa, sun ga halin da yake ciki amma ba wanda ya tsaya, ba wanda ya yi tunanin me ya samu wannan mahaukacin a hannu? Ba wanda ya damu da ciwon sa. Wasu yara ma jefa masa tsakuwa suka fara yi suna ihu da dariya, wani ?aton dutse da aka jefo masa ne a hannun ya sa shi sakin ?ara yana Soye hannun nasa a baya. Karensa ne ya zo da sauri bakinsa ri?e da leda ba?a, ya ajiye a gaban mahaukacin, da ?yar ya sa hannunsa mai lafiya ya buWa ledar wani abinci ne da ya fara lalacewa, cikin rawar jiki ya fara tura wa cikinsa abinci, yana gama ci ya leda a gefensa da kingin ruwa a ciki ya Wauka ya shanye, nan take cikinsa ya ?ulle ya fara mur?usu a gurin.


Joriyya na zaune a falo ta yi shiru kamar wadda ta amince da duka umarnin da aka gindaya mata, sai dai shirun na rigima ne, sulalewa ta yi kamar iska ta fita daga falon ta Soye cikin fulawowi, sai da ta fake idon security, mai gadi ya shiga banWaki tabi ta ?aramar ?ofa ta bar gidan. Ta fara gudu saman titi kamar za ta tashi sama. Jikinta sai rawa yake yi, duk nisan tafiyar nan Joriya ba ta ganta ba cikin ?an?anin lokaci kamar wal?iya ta isa bakin bolar, jin motsi ya sa shi Wagowa. Joriyya ya gani tsaye tana kuka tana magana "Na zo, na zo, gani na zo, me ya sa meka a hannu?" ta dur?usa gabansa ta kama hannunsa, ta ji da zafi kamar wuta, ta yi ajiyar zuciya mai tsami, cikin kuka ta ce "Yi ha?uri yi ha?uri, me ya sa meka a hannu? Garin yaya ka ji ciwo haka?" ta faWa hawaye na bin fuskarta.

Ya saki wani irin kuka na manya, ba irin na hauka ba, kuka ne mai cike da ?unci yaron da ya rasa komai, kafin ta yi magana ta ga motocin gidansu sun tsaya a bakin titin. Dady ne shi da security Winsa, Dady ya fito cikin hargowa, ya nufi gurin zuciyarsa cike da jin haushi da ba?in ciki.

"Shalele!"

Mi?ewa ta yi ta fara kuka "Dady ka bar ni da shi don Allah ka bar ni ka duba hannunsa!"

Mahaukacin ya ja baya yana kuka yana Waga hannunsa da ya kumbura sosai. Dady ya kama Joriyya ya cireta da ?arfi daga gurin "Shalele ki tsaya, ta ya ya ki ka fito daga cikin gidan nan?" Ta ri?e rigarsa tana kuka tana girgiza kai. "Dady kada ka tafi da ni don Allah kada ku raba ni da shi!"

Amanarcool
'?
08163516796



=ئ? AKWAI SILA =ئ?


BY AMANARCOOL


YOTA ID/021


*SHIN RAMA CE MATSALARKI? BUSHEWAR JIKI KO KUMA MATSALAR SANYI? TO ALBISHIRINKI, NA ZO MUKU DA INGANTACCIYAR SABAYA DA AKA SARRAFATA DA NATURAL GRAINS, HERBS DA KUMA SPICES, WADDA ZA TA INGANTA LAFIYAR JIKINKU, TA CIKO DA JIKI, SAMAR DA RUWAN NONO GYARAN BREAST, TA KUMA YI MUKU MAGANIN SANYI DA MA SAURAN GYARAN JIKI NA MATA, DUK A KAN KU?I ?ALILAN. SABAYARMU BA MA SANYA ?WAYA A CIKINTA, DA TSIRRAI KAWAI MUKE SAMAR DA ITA. SANNAN AKWAI MAGANIN SANYI GA MASU FAMA DA MATSALAR INFECTION KOMAI DA?EWARSA. AKWAI COMPLETE SET NA GYARAN BREAST, SPECIAL PACKAGE, KU NA IYA TUBTU?A TA KAI TSAYE KU TUNTU?E NI AYSHERCOOL TA LAMBOBIN WAYATA 08081012143*.


PAGE 13-14


"Dady kada ka tafi da ni don Allah, kada ku raba ni da shi!" Ta yi maganar cikin gunjin kuka kamar wadda ake ?o?arin raba ta da rayuwarta "Dady dubi hannunsa, duba ka gani bai ci abinci ba, Dady a siya masa abinci ya ci kafin mu tafi".

Dady ya sauke numfashi mai zafi, zuciyarsa na yi masa zafi kamar an yi masa duka a ?irji. Ya rasa kalmomin da zai yi amfani da su, gani yake kamar zai fashe idan ya ?ara kallon yadda yarinyarsa ke ri?e shi take yi masa kuka mai tsanani saboda mahaukaci.

"Shalele ki tsaya, ki nutsu zan sa a kawo masa abinci yanzu, ki daina yin kukan nan kin san ba lafiya ce dake ba" ta girgiza kai kamar za ta karya wuyanta "Dady ka duba hannunsa, zai mutu, ni ce kaWai nake zuwa wajensa, ba shi da kowa sai ni" kukan da take yi ya tsananta, ya cika gurin da sautin da ya yi kama da wani abu mai tarwatse zukata. Jama'a suka fara tsaya wa da mamaki, suna kallon ikon Allah, wani dattijo dake gefe ya yi murmushi yana jinjina kansa ya ce "Farawa ce, yanzu ma kuka fara ganin irin wannan abin, saura Wayan".

Mahaukacin yana kallon su cike da tsoro. Ya ja baya yana ?ara ri?e hannunsa, idonsa jajir tamkar mai neman mafita ta ?arshe. Yana kuka, irin kukan da mutum ke yi idan ya ga zai rasa wani abu na ?arshe da ya rage masa a Duniya, security biyu suka ?araso da sauri suka kama Joriyya a hankali ganin halin da take ciki. "Shalele ki yi ha?uri don Allah ki kwantar da hankali& "

"Ku ?yale ni ku ?yale ni!" Ta fara ture su, sai dai ?arfinsu ya rinjaye nata. Dady ya fizgeta daga hannun mahaukacin da ?arfi. Wata irin ?ara ta yi "Dady don Allah kada ku bar shi haka, ku duba hannunsa, ka duba yadda yake kuka, ku bashi abinci ya ci!" Da hannu ya yi wa yaransa alama da su karSo masa abinci, da azama ya tsallaka titi ya isa gurin matar nan mai siyar da abinci ya karSo da ruwa ya kawo masa. Dady ya ce "Kin gani an kawo masa abincin? To zo mu je gida" ya faWa yana janta zuwa mota, shiga suka yi aka ja motar da ?arfi suka bar wajan. Joriyya ta jingina kanta da gilas Win motar tana kuka mai sosa rai. "Dady ya isa, ka tsaya, ka dawo Dady ba haka ake yi ba, ka dawo mu taimaka masa". Babu wanda ya kuma kulata a motar, Dady na jin zuciyarsa na yi masa zafi da Waci, har suka ?arasa gida kuka take yi, Dady ya fito da ita ya ri?e hannunta zuwa ciki, Momy na zaune a falo hankalinta a tashe. Dady ya shigo ri?e da Joriyya a hannunsa, zaunar da ita ya yi kusa da Momy sai shashekar kuka take yi, "Hajiya ki kula da ita sosai, ka da ki bari ko harabar gida ta kuma fita, ni zan wuce gurin aiki".

"In sha Allah zan kula Alhaji, Allah ya kiyaye a dawo lafiya" fita Dady ya yi, Momy ta mayar da hankalinta ga Joriyya ta ce "Auta, ina so ki nutsu, ki gane cewar bai kamata kina bibiyar wannan mutumin ba, ba girmanki ba ne, hakan da kike yi kina zubar mana da mutunc..." ba ta ?arasa ba Joriyya ta tashi da sauri ta haye sama tana ?un?uni.

Zauna yake bayan tafiyarsu ya zuba wa hannunsa ido, da ?yar yake jan numfashinsa, idonsa sun ?ara yin ja saboda azabar ciwo, karensa sai kuka yake yi yana zagaye shi, ya Waga kansa ya kai hannunsa zai shafa kan karen ya kasa, saboda ciwon da yake ji. Karen ya matso ya kwanta a gefensa, shiru ya yi kamar mai tunanin wani abu, yara sai tsokanarsa suke yi, babu wanda ya kula a cikinsu. Abincin da aka siyo masa yana ajiye bai taSa shi, du?ar da kai ?asa ya yi, yana jin yadda hannunsa ke ci gaba da yi masa zogi da azaba. A hankali ya yun?ura da ?yar ya nufi cikin kangon da yake zama, kwanciya ya yi a ciki yana fitar da numfashin a wahale.


****

Houses no 18 GRA Kano.

Katafaren gidane mai tsanani kyau da tsari irin na zamani, harabarsa na da faWi sosai a ?alla zai iya daukar motoci sama da goma. Kallo Waya za ka yi wa gidan ka gane cewar mai gidan ba ?aramin mutum ba ne. Alhaji Kabiru Umar mai nera, Waya daga cikin manyan attajiran da Kano ta sani kuma take alfahari da shi saboda taimakonsa ga al'umma. Mutum ne wanda kalmarsa ke da ?ima, duk inda sunansa ya shiga ana ja da baya saboda girmansa da kuWinsa. Kasuwancinsa ya bazu daga cikin Najeriya zuwa ?asashen waje, yana da masana'antu, gidajen haya, kamfanoni, da kadarori

5 / 11