AKWAI SILA HAUSA NOVELS BY AMANARCOOL.doc

Author :  Amanar Cool Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   2 / 11

3K to 6K   out of 32.7K words

gira ta ce  Joriyya wannan wannan wace irin rigimar ce kike ?o?arin jawo mana? Bayan abin da ya yi wa Dadynki jiya? .

Ranta ya soma Saci, ta fara tattare leSe, numfashinta na ?aruwa, ta ce  In kun ce ba zamu je ba to zan yi kuka. Zan yi kuka sosai Momy, kuma kun san idan na yi kuka ciwon ?irjina yana tashi, kuma bana so in yi kuka Da sauri Momy ta kalli Dady ta ce  Alhaji ka ga abin da nake faWa kuwa? Yanzu tana fara kukan nan amai yake zuwar mata, numfashinta ya rikice. Ka tafi kawai, don Allah ka barta ta samu natsuwa. Dady ya yi shiru. Wani abu cikin zuciyarsa ya yi masa nauyi, ya ce  To shikenan zamu je Win . Joriyya ta yi tsalle cikin farin ciki, ta manta duk fushin da ta yi Wazu. Ta nufe sama cikin sauri. Momy ta kalli mijinta tana girgiza kai,  Ga abin da nake gudu nan ya fara bayyana, wannan yarinya tana son sa mu a cikin walagigi saboda wani mahaukacin da ba mu ma san asalinsa ba .

Jiniyo yana ta faman buga ball Win hannunsa, idonsa a kan ?ofar gidansu Joriyya da ya ga get Win gidan a buWe, da yake unguwa Waya suke, shima mahaifinsa mai kuWi ne amma ba kamar gidansu Joriyya ba. Jiniyo yana ?o?arin zama cikin tarbiyya da nutsuwa, amma soyayyar Joriyya ta yi wa zuciyarsa kulle.

Ya hango su Joriyya na fitowa da flask a hannunta da sauri tana bin bayan Dadynta, an buWe musu mota sun shiga direba ya ja suka bar gidan. Ya yi murmushi mai cike da soyayya.  Allah ya bani ikon samun ki Joriyya ya mallaka mini ke ya furta a hankali

Wajan da suka zo jiya mai ?ura, datti, da zafin bola nan suka ?araso. Mutanen gari suna wucewa suna ?o?arin kaucewa matsugunin mahaukacin. Yau yana zaune luf ciki yana Wora tsakuwa saman tsakuwa.

Dady ya tsaya daga nesa yana kallon yanayin gurin kamar wanda aka tilasta masa shiga kasuwar ?an daba.  Ga shi can ya ce da Wacin rai.  Ki tsaya baya, kada ya kusance ki Joriyya tuni ta taka gaba da ?afafunta tana tafiya a hankali kamar wata mai tsoron karya abu.

Mahaukacin ya Waga kai da sauri kamar mai jin motsin ruwa a cikin rijiya. Idanuwansa jajaye, gumi na gangarowa daga goshinsa. Da ya hango flask a hannun Joriyya ya tsaya cak, idonsa ya lumshe, Dady na dakatar da ita, ita kuma sai ?ara kusantarsa take, ta ?arasa gurinsa ta tsugunna, a hankali ta buWe flask ta zuba miyar a cikin leda mai kauri ta mi?a masa. Dady ya ?araso gurin da sauri yana zaro ido.

Wannan karon bai yi ihu ba, ya mi?a hannunsa ya karSi abincin a nutsuwa, yana kallonsu kamar jaririn da aka ba hanci ya fara sha.

Idanun mutane suka fara bibiyar su, suna mamakin Alhaji Sulaiman a tsaye cikin bola saboda mahaukaci.

Wani dattijo dake zaune a can gefen titi ya ce  Wannan fa sabon abu ne, Alhaji Sulaiman wanda ko talaka ba ya saurare, yau ya tsaya ga mahaukaci? Wasu suka tsaya suna kallonsu da mamaki, wasu suka yi dariya, wasu murmushin mamaki da ganin ikon Allah suke yi.

Dady ya so nuna rashin amincewa da zaman Joriyya a gurin, amma sai ta kama hannunsa ta ce da siririyar murya  Mu bari ya gama Dady ta yi maganar cikin murya mai karya zuciya, hakan ya saka shi yin shiru. Mahaukacin ya zauna da abincin ya fara ci a hankali kamar wanda yake jin tsoron abincin ya Sace kafin ya Wan WanWana shi. Ya Wauki lokaci yana ci, yana kallon Joriyya lokaci zuwa lokaci, kamar yana tantance wani abu cikin zuciyarsa.

Yana gama cin abincin ya mi?a musu flaks Win ya yi ?asa da kai kamar yana mi?a godiya da harshen da ba shi da kalma. Jama a suna kallo. Joriyya ta Wauki flask Win suka juya. Dady bai yi magana ba har suka shiga mota, sai lokacin ya ce da ita cikin taushin da bai saba da shi ba  Shalele ki bar wannan abu. Ba gurin da ya dace da ke ba ne .

Ta lumshe ido ta ce  Shi ma fa mutum ne Dady Sai zuciyar Dady ta yi wani irin kakkarwa, bai san dalili ba.


Motarsu na tsayawa a harabar gida Joriyya ta nufi ciki da flask Win zuciyarta cike da wata irin natsuwar da ta kasa bayyana. Dady ya rufe ?ofar mota da ?arfi, alamar ransa a Sace yake, ya kasa Soye damuwarsa.

Momy na tsaye a tsakiyar falo tana jiran dawowarsu, tana ganinsu ta mi?e tana Wan zaro ido ta ce  Kun kai masa? Da har zan tura yaranka su bi bayanku .

Dady ya ture hularsa gefe ya zauna  Mun kai ya faWa a gajiye  sai dai ni wannan abin ya fara fitowa daga da'irar da za a iya sabawa da shi . Ta kalle shi da damuwa.  Alhaji ya ake ciki ne? Yarinyar nan ta fara nuna halin da ban taSa gani ba. Zan sanar da ?an uwanta, wannan ba ?aramin abu bane .

 Gara ki sanar da su yafi Dady ya furta yana lumshe idanu, ciwon ?afarsa na sake motsawa. Ana haka sai ga Anty Zainab ta kira, ?ar Momy wadda ke aure nan cikin Abuja Wayar kuma babbar ?arsu tana can ?asar waje take da zama tare da mijinta.
Momy ta Waga wayar tana faWin  Yanzu nake shirin kiranki Zainab ta gaishe da Momy tare da tambayar Dady sannan ta ce  Momy ina rigimammiyarki? Kwana biyu ba ta zo mini ba .

Momy ta ce  Tana nan, yanzu wata sabuwar rigima ce ta Wakko, abin nata sai gaba yake yi, narasa ya zanyi, wannan yarinya da nake ganin abin da take yi a matsayin shirme, yau ga shi ta fara wani abu da ban yarda da shi ba .

 Wane abu kuma Momy? Aunty Zainab ta tambaya.

Tsaki ta yi ta ce  Jiya ne ta fita da Dadyn ku ta ga wani mahaukaci, shikenan Auta ta saka masa rigimar sai ya siya masa abinci, garin kai masa abincin ya yi ?o?arin illata Dadyn ku Win, yau ma ta a za rigimar sai an kuma kai masa abinci, har take cewa idan ba a je ba za ta yi kuka, ?irjinta zai yi mata ciwo, ciwon ta zai tashi, tausayinsa take ji .

Aunty Zainab ta lumshe ido  Wallahi akwai matsala. Wannan ba tausayi ba ne kawai, kamar dai akwai wani abin, anya Momy ?ar nan taki lafiyarta ?alau? . Momy ta ce  Shi ya sa na ce zan kira ku domin Joriyya tana bu?atar a kula da ita sosai. Kar fa mu yi sakaci .

Zainab ta ce  Bari Momy wannan maganar ba ta waya ba ce in sha Allah zan zo gida sai musan abin yi, wannan ai zubar da mutunci ne suka yi sallama Zainab sai mita take yi. Momy sukaci gaba da tattauna matsalar, Joriyya ko haka ta yini a Waki da tunanin wannan mutumin, komai take sai ya faWo mata a rai.

Washegari kasancewar Monday ce ya sa da wuri Joriyya ta shirya aka kai ta school, Joriyya ba ta kula kowa a makarantar sai mutum Waya da kusan halinsu ya zo Waya wato Safina, tunda ta je take bawa Safina labarin mahaukacin nan har sai da Safina ta fara jin haushinta, yanzu ma zancensa take yi mata  Safina wallahi abincin jiya ya yi masa daWi. Kin ga yadda yake cin abinci cikin nutsuwa kuwa? Yafi wani mai hankali iya cin abin fa .

Safina ta runtse ido  Don Allah ki saurara mini haka Joriyya, na ji zancen ya fi a ?irga, tun safe kike yin abu Waya, ki barni na huta mana, ko so kike ki cika mini kunnuwa ne? Ki daina ka da a jiki a ce yara damu muna zance maza .

 A a wallahi ki bari in gama faWa Joriyya ta ce tana motsa hannuwanta da annashuwa.  Kin ga yadda yake yi wa idonsa kamar mutum mai jin bacci? Safina ni fa nake ji kamar yana jin...

 Joriyya Malam Musa ya daka mata tsawa.  A mai da hankali ga karatu

Sai ta yi shiru, amma zuciyarta na ci gaba da tunani, tsawon zaman da ta yi a makaranta ba ta yi komai ba face tunanin shi har aka tashi, ko da ta fito daga class an zo Waukarta.

Tana shiga gida ko kayan jikinta ba ta cire ba ta kira mai aikin gidan.  Lami kina ji? Ki shirya wani semo na gobe. Gobe ma zamu kai masa .

Lami ta ce  Auta kin ga dai wannan abin& 

 Ki yi abin da nace Joriyya ta katse ta tana haurawa sama.

Yau tun daga ma'aikatan gidan har su Momy kowa ya fahimce cewar Joriyya rigima take ji sosai, yanzu ma fitowa ta yi harabar gidan ta tsaya tana kallon kowa. Can ta ce  Kai Baba Sale daga yanzu idan zan fita kar ka sake tsaya mini a hanya. Na isa na fita na je duk inda nake son zuwa .

Baba Sale ya ?urawa Joriyya ido kamar zai yi kuka.  Auta ni aikin nan fa& 

 Ka bar wannan maganar ta katse shi, sannan ta kuma ga mai wankin motoci ta ce  Kada ka taSa flask Wina dake cikin motar nan saboda yana da muhimmanci . Haka tabi ma'aikatan gidan Waya bayan Waya kowa da abin da za ta ce masa.

Tunda ya ci abincin jiya, zuciyarsa ta fara motsi da wani sabon abu da bai iya tunawa da shi ba, tun Wazu yake dubin hanyar da motarsu Joriyya ke bi. Idan yaro ya zo wucewa sai ya watsa mishi tsakuwa ya kau da kai. Wasu yara suka fara tunzura shi  Mahaukaci, mahaukaci mai kwana a bola . Sai dai ya juya ya kalle su amma ba zai bi su ba. Zuciyarsa ta fara yin wani abu mai kama da tunawa. Ya tsurawa karensa ido, karen da kullum yake kwana kusa da shi. A yau ma karen ya kwanta yana lumshe ido, mahaukacin ya sunkuya ya shafa kansa, ya tsaya cak. Lumshe ido ya yi, numfashinsa ya tsaya na Wan lokacin. Wani ?amshi ya ratsa shi.
?amshin miyar taushe wadda ta yi masa kama da wata miyar da ya taSa ci kafin rayuwa ta juya masa baya. Bai tuna lokacin ba, bai tuno wace rayuwa ba ce, amma zuciyarsa ta yi wani irin lugude kamar ana buWe ?ofa daga ciki.



By Amanarcool
'?
08163516796


=ئ? AKWAI SILA =ئ?


BY AMANARCOOL


YOTA ID/O21


*SHIN RAMA CE MATSALARKI? BUSHEWAR JIKI KO KUMA MATSALAR SANYI? TO ALBISHIRINKI, NA ZO MUKU DA INGANTACCIYAR SABAYA DA AKA SARRAFATA DA NATURAL GRAINS, HERBS DA KUMA SPICES, WADDA ZA TA INGANTA LAFIYAR JIKINKU, TA CIKO DA JIKI, SAMAR DA RUWAN NONO GYARAN BREAST, TA KUMA YI MUKU MAGANIN SANYI DA MA SAURAN GYARAN JIKI NA MATA, DUK A KAN KU?I ?ALILAN. SABAYARMU BA MA SANYA ?WAYA A CIKINTA, DA TSIRRAI KAWAI MUKE SAMAR DA ITA. SANNAN AKWAI MAGANIN SANYI GA MASU FAMA DA MATSALAR INFECTION KOMAI DA?EWARSA. AKWAI COMPLETE SET NA GYARAN BREAST, SPECIAL PACKAGE, KU NA IYA TUBTU?A TA KAI TSAYE KU TUNTU?E NI AYSHERCOOL TA LAMBOBIN WAYATA 08081012143*.


PAGE 5-6


Ya sake lumshe idanunsa, ?amshin miyar taushe na ratsa masa hanci kamar ?amshin wani wuri da ya taSa rayuwa a ciki. Numfashinsa ya Wan tsaya, ya doke shi da wani irin firgicin da bai fahimta ba. Hannunsa ya Wora a ?irji, zuciyarsa na lugude kamar ana buWe ?ofa daga duhun da ya daWe a kulle.

Sai ga wasu hotuna kamar inuwa, sautin dariya, ?amshin girki, murya mai taushi, duk suna ?o?arin fitowa, amma suna Sacewa kafin ya kama su. Ya buWe idanu da sauri, jijiyoyin kansa na matsewa kamar ana jawo su. Karensa ya matsa daf da shi, yana lumshe ido kamar shima ya fahimci wani abu ya faru.

Zuciyar Joriyya ta fara tayar da wata guguwa ta daban, ta fara Wagawa kowa hankali. A falo ta tsaya tana huci kamar wadda aka ci amanarta.

Momy ta ce  Auta ki zo nan

Joriyya ta ce  Momy ku dai ku bar ni ku bar ni kawai! .

Dady ya sauko daga sama a hankali kukan takaici yana barazanar ?wace masa  Shalele ya kira ta da murya mai nauyi  Ni fa ba zan yarda ki Sata mana suna saboda wani mahaukacin da ba mu ma san asalinsa ba, kina ?aramar yarinya dake da ?ananun shekarunki za ki Waga mana hankali! .

Ta juya masa baya ta ce  Dady ba ku gane shi bane! Shi mutum ne kamar kowa!

Wannan kalma ce ta huda ransa. Zuciyarsa ta tashi duka. Ya Waga murya fiye da yau da kullum.  Ni ki ke faWawa haka? Ni? Ni na raine ki ne da wannan dabi'ar? Na koya miki ?aunar kowa ne? Abin da na sani shi ne ban koya miki mugunta ba, wannan abin da kike yi ?as?anci ne na fi ?arfin wannan zancen da kike jawowa! .

Joriyya ta tsaya cak. Muryarta ta soma rawa.  Kai ka ce ?as?anci? Don ina jin tausayin mutum? Don ina son& don ina son&  Numfashinta ya fara birkicewa. Idonta ya cika da hawaye, hannunta ya fara rawa, Momy ta ruga da sauri  Auta ki yi shiru, ki daina amma hawayen sun zubo. Ciwon ya motsa a ?irjinta wanda duk gidan ke tsoro, numfashinta ya Wauke na Wan lokaci.

Dady ya ruWe.  Ke Hajiya ri?e ta, bari na Wakko ruwa! Sai ta zauna a ?asa tana haki kamar za ta faWi, da ?yar suka samu abin ya lafa mata, gashi dare ya fara yi idan ba'a yi sa'a ba sai ciwon ya hanawa kowa bacci a gidan.

Washegari.

Joriyya ba ta je school ba saboda yanayin jikinta, misalin ?arfe goma sha Waya na safe Anty Zainab ta iso gidan cikin hargagi kamar wadda aka kira ta don kashe gobara, Dady na ?o?arin fita suka gaisa, ganin Zainab ta zo ya sa shi komawa ya zauna, zama ta yi bayan sun gaisa ne ta ce

 Dady, Momy tun jiya da kika gaya mini maganar nan hankalina ya tashi, wannan ba abin wasa ba ne. Yarinyar nan tana da neman magana, wannan ai zubewar mutunci ne . Ta yi maganar tana kiran

 Joriyya zo nan Joriyya


Fitowa ta yi ta zauna ba walwala.

Anty Zainab ta ce  Joriyya dubi yadda kika fara fita hayyacin ki saboda wani mahaukaci da ko sutura ma bai iya sakawa ba, wane irin rashin hankalin ne da ke? Wannan wane irin abu ne kika Waukar wa kanki? .

Joriyya ta mi?e da sauri kamar an hura ta, ta ce  Ki daina zolayarsa, ki daina faWin mummunan abu akansa bana so, bana son ana yi masa haka! .

Anty Zainab ta yi dariya mai ciwo ta ce  Shi fa mahaukaci ne Joriyya, mahau....

Bata gama ba Joriyya ta katse ta da murya mai kaifi  Ki yi shiru, ba zan bar ki ki zage shi ba, ni fa ban taSa jin kunya ba kamar yanzu da kuke faWar hakan, ku duka ba ku gane shi bane wai?" Ta yi maganar jikinta na tsuma tamkar za ta fita hayyacinta.

Falon ya yi shiru. Idanun Momy sun cika da hawaye. Anty Zainab ta ce  Ke Joriyya, ni kike mayar wa magana haka? Mu gane shi a ina? Waye shi Win? Ni anya Joriyya ba iskokai ne suka shige ki ba kuwa? Ko dai ba mutum ba ne mahaukacin? .

Zuru ta yi musu da manyan idanunta, tare da rasa abin da za ta gaya musu, domin su fahimce ta. Fuu ta bar musu falon gaba Waya, su duka suka bita da ido har ta haura sama, Dady ya maida kallonsa ga Anty Zainab ya ce  Kin ga dai yadda muke fama da ita, gabaWaya ta rikice, ita ba abin a yi mata magana ba wannan ciwon nata ya tashi, da haryanzu shi ma ba a san kansa ba, sai lalube kawai da ake yi a dubu. Anty Zainab ta ce  Lallai Dady wannan abin babba ne dole a san matakin da ya kamata a Wauka, kafin abubuwa su rikice fiye da haka, Momy kin gaya wa Anty Na'ima ne? . Girgiza kai Momy ta yi ta kasa magana saboda ta fara tsorata da lamarin yarinyarta ta, Dady ya mi?e ya yi musu sallama ya fita, ranar a gida Zainab ta yini su na tattauna lamarin Joriyya, sai bayan la'asar ta bar gidan.

Da yamma Jiniyo ya zo gidan da nufin ganin Joriyya kamar yadda ya saba yi da ?aunar da ta wuce misali, yau saboda halin da Momy ke ciki ya sa ba ta tsaya sunyi hira da shi ba, Joriyya na jin maganar Jiniyo ta fito da sauri, ba don shi ba sai don tana son yi masa zancen mutumin nan, babu sallama ba komai ta ce

 Jiniyo tana tsaye hannaye a ?ugu,  akwai wani mahaukacin wanda nasa muka kai masa abinci jiya ni da Dady, ka ga yadda yake cin abinci? Ka ga yadda idanunsa suka yi?

Da farko Jiniyo ya yi dariya da tunanin soyayya ce kawai. Sai ya gane ba soyayyarsa take faWa ba, sautin wani mutum daban take faWa.

Nan take ?irjinsa ya buga da ?arfi, zuciyarsa ta yi masa nauyi mai girman gaske, ya ce  Ke kina jin zancen da kike yi? Kin manta kina da ni? .

Cikin ko in kula ta ce  Ka yi ha?uri Jiniyo ban da lokacin hakan yanzu .

Wannan kalmar ba ?aramin Sata ransa ta yi ba, ya juya cikin fushi ya bar gidan, zuciyarsa na tafasa da kishin wanda bai san ma asalinsa ba.

Yau ma kamar kullum Joriyya ta je makaranta, sai dai gabaWaya yanzu ba ta mai da hankalinta wajan karatu, idan aka zo tambaya game da karatun da aka yi musu sai ta yi shiru tana tunani kamar wadda ta yi nisa da Duniya.

Malam Musa ya ce  Joriyya me ke damunki?

2 / 11