AKWAI SILA HAUSA NOVELS BY AMANARCOOL.doc

Author :  Amanar Cool Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   3 / 11

6K to 9K   out of 32.7K words

Bata ba shi amsa ba ta sunkuyar da kai ta ci gaba da jan biro tana zana layi ba tare da ma ana ba.

Momy ce ke video call, da yarta da take zaune a can Dubai, cikin damuwa ta ce  Na'ima kina jina Joriyya ta shiga wani hali. Wani mahaukaci ne ya shige mata rai, ni ban ma san wace irin ala?a ce tsakaninsu ba, ni na fara zargin ko dai aljani ne ya fito a suffar mahaukaci, yake son shafarta.

Na'ima ta yi shiru na Wan lokaci cikin jimami ta ce,  Babbar magana, Momy kuna zaman me? Wannan ba abin wasa bane, lamari ne da yakamata a Wauki matakin gaggawa tun da wuri, kafin al'amarin ya wuce tunani. Amma abin da tsoro a ce rana tsaka kawai ta haWu da mahaukaci a ce tana shiga shirginsa kamar ta san shi"

"Wallahi Na'ima na rasa abin yi, da na Wauki abin nata wasa, amma yanzu na fuskanci da gaske akwai matsalar da take bu?atar matakin gaggawa"
Na ima ta yi ajiyar zuciya ta ce "Amma Momy ku faWa min gaskiya wane irin mahaukaci ne haka? Me ya haWa ta da shi? Waye shi? Ya aka ? Yaya ma take jin shi? .

Momy ta jingina da kujera, hannunta Waya na ri?e da wayar, Wayan kuma tana goge zufa duk da sanyin AC dake Wakin, muryarta ta yi ?asa-?asa kamar wadda aka sare wa zuciya ta ce
"Wallahi Na ima tun jiya hankalina bai tsaya ba. Joriyya ta canza, ina jin tsoron kada ta faWa cikin wani abu da ba zan iya fitar da ita ba

"Kin san mai zai faru, zan duba idan da yiwuwar ki bani ita ta dawo nan gurina mu gani"

Momy Wan waro ido ta ce ta ce  Kina nufin ta koma wajanki da zama? .

 Eh Momy idan har ba ku samu mafita ba, ina ga a nesan ta da shi, nesantawa sosai yadda za ta daina ganinsa gaba Waya mu ga abin da hali zai yi  .

"Mummy gaba Waya wannan ba abu ne da za a jira dogon lokaci, ana nazari ko tunanin mafita ba, Joriyya yarinya ce ?arama, babu yadda za a yi a ce rana tsaka ta tsiri ala?a da mutum mahaukaci da ba a san daga inda yake ba, idan ya cutar da ita fa?"
Momy ta katse ta cikin ruWewa,  Na ima ki yi mini shiru! Kar ki kara tsoratar da ni, don tuni tsoro ya ?ara cika zuciyata .

Na ima ta yi ajiyar zuciya.  To Momy ki nutsu. Mu za mu nemo mafita. Ina da ra ayi Waya kuma ina jin shi ne zai iya tsayar da wannan abu .

Momy ta Waga kai duk da ba ta ganinta ta ce  Me ne?

 Ki bar Joriyya ta zo nan wurina. Ki turo min ita Dubai. Ta yi zamanta a nan, sai taci gaba da karatu a nan. A nisanta ta da wannan mutumin kafin lamarin ya yi nisa .

Kalmar ta fito a hankali amma ta huda zuciyar Momy kamar ?usa mai zafi.

Hawaye suka cicciko a idonta.  Na ima ke kina magana kamar sau?i ne a raba uwa da yarinya. Yaya zan hana ta ganin iyayenta? Yaya zan bari ta tashi daga nan ta tafi tsakiyar wata ?asa saboda wani mutum da ba mu san ko waye ba? .

Na ima ta Wan yi murmushi mara annuri.  Momy mafita fa ake nema, kada ki manta ba gurin wasu bare za ta zauna ba a gurina ne. Momy ba fatana nake ba yau idan babu ke a Duniya nice zan zama uwa a gare ta, zamanta zai dawo a gurina .

Momy ta kasa magana.
Wani abu kamar ?wallon dutse ya ma?ale mata a ma?ogwaro.

Na ima ta ci gaba da cewa,  Ki saurare ni Momy wannan yaron da kuke kira mahaukaci ban san waye shi ba, amma wani abu a jikinsa yana jawo hankalin Joriyya fiye da misali. Idan ba ku yanke wannan abin yanzu ba, zai iya kai ta ga wani hali da ya fi wannan nisan .

Momy ta dafe goshinta. Ta tuna yadda Joriyya ta yi kuka har ciwonta ya so tashi, yadda ta mayar wa Zainab magana, yadda idan ta ambaci wannan mahaukacin sai idonta ya cika da wani haske da ba a saba gani ba. Ta runtse idanu, hawaye suka sauka a kumatunta.  Na ima zan yi tunani. Amma zuciyata na tsoro. Yarinya kamar Joriyya an fara Sata ta. Ina jin wani abu zai faru da ita, amma ban san me ba .

Cikin tausayi Na ima ta ce  Momy ki kwantar da hankalinki. Idan Nazir ya dawo zan gaya masa komai, idan kun amince sai mu Wakkota, ba don mu raba ta da ku ba sai don a ceci hankalinta ci gaba da tattaunawa suka yi.

Suna gama magana Momy ta kashe wayar tana mai jin idonta ya Wauki nauyi. Ta jingina da kujera ta saki wani huci mara ?arfin rai, zuciyarta na bugawa a hankali kamar na mace mai jiran hukunci.


Joriyya na zaune a gefen gado ta takure kanta cikin hannaye. Idonta ya kafe gilas Win tagar da ke kallon ?ofar gidan su.
Tun da suka dawo daga makaranta zuciyarta ke faWaWa da wani zafi mara suna, wannan murya, wannan fuska mai datti, wannan idanu da ke rikita mata tunani duk sun mamaye ta, ta yi wani lumshe idanu mai zurfi. Gabanta na faWuwa kamar tana jin shi a wajan.

 Me yasa nake jin shi kamar na san shi? ta furta cikin ?asa-?asa da murya kamar wadda zuciyarta ke ?o?arin tuna abu mai nisa.

Momy na jin ?arar shigowar motar Dady daga waje zuciyarta ta ?ara harzu?a da sabon tashin hankali. Ta san dole ta yi masa bayani. Dole su zauna su yanke hukunci.
Zuciyarta ta yi nauyi, saboda duk hanyar da take gani duk akwai ciwo.

Sai ta dafe ?irjinta ta furta a hankali
 Ya Allah Ka tsare Auta.

Amanarcool
'?
08163516796


https://chat.whatsapp.com/FQae3SgaQbTKcN3EMxobzQ?mode=wwt


=ئ? AKWAI SILA =ئ?


BY AMANARCOOL


YOTA ID/021


*SHIN RAMA CE MATSALARKI? BUSHEWAR JIKI KO KUMA MATSALAR SANYI? TO ALBISHIRINKI, NA ZO MUKU DA INGANTACCIYAR SABAYA DA AKA SARRAFATA DA NATURAL GRAINS, HERBS DA KUMA SPICES, WADDA ZA TA INGANTA LAFIYAR JIKINKU, TA CIKO DA JIKI, SAMAR DA RUWAN NONO GYARAN BREAST, TA KUMA YI MUKU MAGANIN SANYI DA MA SAURAN GYARAN JIKI NA MATA, DUK A KAN KU?I ?ALILAN. SABAYARMU BA MA SANYA ?WAYA A CIKINTA, DA TSIRRAI KAWAI MUKE SAMAR DA ITA. SANNAN AKWAI MAGANIN SANYI GA MASU FAMA DA MATSALAR INFECTION KOMAI DA?EWARSA. AKWAI COMPLETE SET NA GYARAN BREAST, SPECIAL PACKAGE, KU NA IYA TUBTU?A TA KAI TSAYE KU TUNTU?E NI AYSHERCOOL TA LAMBOBIN WAYATA 08081012143*.


PAGE 7-8


Momy ta ?ara gyara zamanta a gefen gado, zuciyarta na bugu da sauri kamar za ta fito daga ?irjinta. Tunanin tura Joriyya ?asar waje ya kasance abu ne da ba ta taSa hango shi ba, balle kuma a irin wannan lokaci, a irin wannan yanayi da yarinyar ta shiga.

Da sallama Dady ya shigo Wakin ya tsaya a bakin ?ofa yana kallonta, fuskarsa Wauke da damuwa, sai dai yana ?o?arin Soye ta saboda jarumtaka irin ta namiji.

Cikin sanyi murya ya ce "Kin yi waya da Na ima ko?".

Ta du?ar da kai ?asa "Eh na yi" ta faWa tare da yi masa sannu da zuwa.

Zama ya yi a gefen gado, yana amsa sannun da zuwan da ta yi masa, kafin ya ce "To me ta ce miki? Shafa lamarin Shalele ya fara bani tsoro, an ya mahaukacin nan mutum ne?".

Momy ta ja numfashi a hankali ta ce, "Haka Na'ima ta faWa, sannan ta ce idan har ba mu samu mafita ba a tura Joriyya can gurinta ta zauna, ta yi karatunta a can, ta samu nisan da zai raba ta da wannan mutumin".

Dady ya lumshe idanu, muryarsa ta sauya, ta yi sanyi ba kamar yadda yake ihu da hargagi akan lamarin ba. "Wato a ce mun kasa magance matsalar ?ar mu har sai mun tura ta wani gari?".

Momy ta ce "Alhaji ka dubi Joriyya yanzu kamar ba ita ce yarinyar da muka raina ba. Tana cikin yanayin da bamu san inda ta dosa ba, bamu san me ye ma?asudin sa ba".

Shiru ya yi ?ijinsa na yi masa zafi.

"Kana ganin jiya yadda ta soma numfashi. Idonta ya rufe, ta soma irin wannan hucin na ciwo, kar ka manta likita ya ce mana damuwarta tana iya tayar mata da wannan ciwon, ciwon da muka kasa gane kansa".

Dady ya saki ajiyar zuciya "To me kike so ayi?"

Ta ce "A tura ta ta yi karatun ta a can har ta gama, nasan a lokacin komai zai fita daga zuciyarta, sannan mun raba ta da wannan mutumin da ba mu san ko waye shi ba cikin ruwan sanyi".

Dady ya yi shiru, ya jin gina da bango, ya daWe jingine da bango zuciyarsa na bugu, kafin ya ce "Zanyi tunani a kai" daga haka ya juya ya bar Wakin.

Bayan sallar isah Joriyya na kwance a falo tana kallon labulaye taga dake motsi a hankali saboda iskar dake kaWawa. Sai dai ba labulen take gani ba inuwa take gani, murya take ji, wata ?aramar dariya tana taso mata kamar ta wani da ta sani amma bata san ko a ina ta san dariyar ba. Abin da ya fi tayar mata da hankali shi ne idanun mutumin nan, ta rufe idonta a zuciyarta take "Me yasa nake jin kamar na taSa ganinsa? Me yasa nake jin ba?in ciki idan na tuna halin da yake ciki?". Shiru ta yi ta kasa samun amsar tambayarta, lokaci Waya ta ji tana son zuwa ta duba wannan mahaukacin "Ko a wane hali yake? Ko ya ci abinci? Wata ?ila ma yunwa yake ji" ji ta yi Dady ya kira ta "Shalele ki zo mana".

Tashi zaune ta yi, ta tsaya tana kallonsu shi da Momy kamar wadda aka yi wa hukunci ba tare da ta san laifinta ba.

Momy ta yi gyaran murya zuciyarta cike da fargaba ta ce "Auta magana za mu yi".

Ta Wan yi murmushi mai "Wace managa Momy?".

Dady ya yi ?asa da murya "Kin san abin da ya faru jiya? Kin ga yadda jikinki ya koma? Ba za mu iya bari ki ci gaba da shiga cikin wannan yanayin ba da ?ananun shekarunki".

Momy ta Wora da faWin "Auta Na ima ce ta bu?a ci mu tura ki can Dubai ki zauna tare da ita. Ki yi karatunki a can tare da ?arta Ummie, idan kika gama karatunki sai ki dawo, ai dai kina son ki yi karatu mai zurfi ko?".

Wani abu ne ya yi tsalle cikin zuciyar Joriyya, idonta ya ?an?an ce, hannuwata suka fara rawa.

"Ni? In tafi? In tafi saboda shi? Don kawai kun ga na damu da shi?".

Momy ta ce "Auta ki fahimce mu"

"Ba zan tafi ba!" Ta faWa cikin hanzari

Dady ya Waga murya. "Ke ba zaki zauna ki saurare mu ba? Wannan abin da kike ji, abin da ya shige miki rai shi muke son nemo miki maganinsa".

Idonta ya cika da hawaye, hawayen Sacin rai da tsoro, kamar wata babba "Dady ku duka baku gane shi bane. Baku gane shi bane!" Ta faWi maganar da murya mai tsuma zuciya. Dady ya kasa daurewa da ?arfi ya ce "To waye shi? Me kike gani wanda ba mu gani? Wace ala?a kike tunanin kina da ita da shi?".

Ta gyaWa kai a hankali, idonta cike da hawaye masu tsananin zafi. Cikin rawar murya ta ce "Na san shi ban san dalili ba, amma na san shi. Idan nayi nesa da shi kamar na rasa wani abu mai muhimmanci nake ji".

Sai hawayenta suka gangaro.


Momy ta rufe baki saboda firgici, Dady ya zaro ido kamar an jefa masa da wuta.

"Shalele kina jin abin da kike faWa? Kina ji kuwa?" Dady ya ce, ba ta tsaya ba ta juya da sauri zuwa sama tana kuka mai ?arfi tana kuka. A Waki ta kwanta tana haki "Me yasa nake jin haka? Me yasa idanuwansa suke biyoni har cikin bacci? Me yasa yake min kama da wani wanda ya....?" Sai kuma ta yi shiru, ta rufe kanta da filo tana dariya mai ciwo hawaye na cigaba da gangaro mata.

Momy ta zauna ta ce "Alhaji wannan abu ya wuce hankali, abubuwan da yarinyar nan ke yi bai kamata ace mai shekaru irin nata na yi ba, gabaWaya ta sauya kamar ba Joriyyata ba". A sanyaye Dady ya ce "Zan san abin da ya kamata muyi, dole ne ta bar ?asar nan".

Jiniyo tunda ya bar gidansu Joriyya zuciyarsa ta koma kamar kwalbar guguwar da ba komai sai hazo, zafi yake ji sosai a cikin ransa, ya kasa zama a gida, ya kasa cin abinci, ya kasa kallon wayarsa. Ya dinga yawo a harabar gida yana jijjiga ?afafunsa kamar zararre. "Ni Jiniyo niWin nan ni da tunda aka haifeta nake sonta, na ba ta dukkan wata kulawata duk da rashin kulawar da take nuna mini ban gaza wajan ?o?arin ganin na faranta mata ba, shi ne yau za ta soma yi mini maganar wani? Wanin ma mahaukaci? Wannan wawan da ba a san ko sunansa ba, balle asalinsa". Ya ju ya tsaya gaban ?ofa yana huci.

Zaune yake a cikin bola kamar kullum, karensa na kwance a gefensa, idanuwansa sun kumbura, yana yawo dasu a hankali kamar yana bin wata murya da shi kaWai yake jinta, magana ya yi kaWan muryarsa ba ta fitowa balle a ji me yake faWa. Sai ya yi murmushin da ya fi kuka taSa zuciya. Ya lumshe idanu yana shafa kan karensa
"Ka gani ko? Duk Duniya bata da armashi sai idanunta, idanunta da suka ce min& " Ya tsaya, yana maimaita kalmomi da ba su fitowa a fili, kamar ba mahaukaci ba.

Da sanyi safiya Joriyya ta fito da rigar bacci tana ri?e da hijabi, idonta sunyi ja saboda kuka da rashin bacci, ta samu Momy da Dady a zaune suna shan tea.

Kafin su yi magana ta fara yi kai tsaye kamar mai ba da umarni "Ina so a kai masa abinci. Ba zan bari yunwa ta kashe shi ba".

Dady ya Waga kai da sauri. "Waye kuma kike magana a kansa da safe ko karyawa ba ki yi ba?" "Dady ku daina yi min kamar bani da hankali. Ku daina".

Momy ta Wan matsa kusa da ita ta ce "Auta ki nutsu mana. Yau ba mu da lokacin wannan batun"

"Ina da lokaci, ku dai ku bar ni kawai na kai masa".

Dady ya daki teburin da hannunsa. "Ba zaki je ba, babu wanda zai sake kaiwa mahaukaci abinci a cikin wannan gida!"

Ta tsaya cak, idonta ya kaWa, zuciyarta ta yi wani irin bugawa. "Zai iya mutuwa idan kuka hana ni kai masa fa, kai wallahi sai na kai masa" tsabar takaici ya sa Dady mi?ewa ya haura sama Momy ta maramasa baya suka bar Joriyya tsaye a gurin kamar wata dusa.

Da gudu ta wuce kitchen ta Wauki flask ta fara zuba abinci tana zubawa da sauri. Jikinta sai rawa yake yi. Ta fito da flaks Win a hannunta ta yi waje, security na zaune suka ga ta nufi get za ta fita.

"Ke Baby Joriyya ina za ki je yanzu? Kuma kin san ba a barin ki fita ke kaWai". ?aya daga cikin su ya yi maganar yana nufarta.

Ta Waga murya cikin huci ta ce "Ku matsa wallahi sai na fita" Ja baya ya yi saboda sun san muguntar fushin ta. Ta kalli direba tana huci.

"Mallam ka Wakko mota mu tafi"

Ya kalle ta yana mamaki, ya tashi jiki ba ?wari ya fito da mota ya buWe mata ta shiga sannan ya kunna motar suka bar gidan. ?arar tashin motar ta jawo hankalin Dady wanda ke Waki.Fitowa ya yi zuwa harabar gidan ya ce "Wace mota ce ta fita yanzu?".

Cikin rawar murya mai gadi ya ce "Ranka daWe Shalele ce ta ce& "

"Ta ce me?" Dady ya katse shi yana zazzaro ido. Cikin ladabi mai gadin ya kuma cewa "Ta ce a fito da mota fita za ta yi, da aka yi ?o?arin hanata sai ta yi fushi tace dole sai ta fita".

Dady ya balbale su da masifa kamar ana zuba masa wuta. "Akan me zaku barta ta fita ba tare da izinina ba? Me ye amfaninku kuma da zaku barta ta fita daga ita sai direba?" Ya yi maganar yana tsare security da ido, ha?uri suka shiga bashi bai tsaya sauraronsu ba ya juya a fusace ya koma ciki.

Jiniyo na tsaye a bakin get Win gidansu yana shirin fita ya ga motar gidansu Joriyya ta wuce, Dim! Ya ji zuciyarsa ta yi
"Me take nema a waje haka da safe? Kuma me yasa aka fito da wannan gudu haka?" Ganin bai da amsa ya sa ba tare da tunani komai ba ya juya cikin sauri ya shiga gida, ya ciro makullin motarsa daga aljihunsa ya shiga ya fi gi motar ya fita kamar iska ya bi bayan su yana jin bugun zuciyarsa kamar ?arar harbi.

Cikin ?an?anin lokaci suka iso bolar da mahaukacin ke zama, gurin ya yi shiru iska mai sanyi tana kaWawa, yana kwance a takure karensa na gefensa. Joriyya ta fito daga mota hannunta ri?e da abinci, yana daga kwance idonsa a rufe kamar an mitsine shi ya buWe idonsa karaf suka sauka a kanta, tashi ya yi a hankali yana kallonta da murmushi mai ciwo. ?arasowa ta yi ta dur?usa a gabansa tana mi?a masa abincin zuciyarta na rawa.

Cikin zafin nama Jiniyo ya fito daga motarsa ya ?araso inda suke da sauri, ya daka mata tsawa cikin muryar da shi kansa bai san yana da ita ba "Dama tunda naji zuciyata ta buga akan ki na san cewar gurin wannan banzan za ki zo, me za ki cinta a gurin wannan Win? Mutum min da ba zai iya banbance fari da ba?i ba, wallahi yau zaki gane kin yi kuskure Joriyya". Yana gama faWar hakan ya fizge abincin ya wurgar da shi gefe.
Abincin ya watse ?asa.

Joriyya ta mi?e da sauri idonta ya canza launi saboda Sacin rai ta ce "Me ya kawo ka nan? Me ya sa ka biyo ni? A kan me za ka zubar masa da abinci?".

Jiniyo ya matsa kusa da ita, jikinsa na rawa saboda kishi da ba?in ciki, ya ce "Ke zan tambaya Joriyya, me yake damunki

3 / 11