Author : MINAL SAEED Category : Romantic Hausa Novels
KECE SILA
(✍️Minal saeed)
(🌹MRS BASH🌹)
https://whatsapp.com/channel/0029VbBl22NAO7RLFvcUlU2g
https://chat.whatsapp.com/FuiNx6HvwgzAheM7xh0Xci?mode=ems_copy_t
://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa
Page1️⃣
Bismillahi Rahmanir Rahim
Cikin salisanin dare wajen misalim ƙarfe 1:30, ya yin da kowane mai rai yake bacci cikin kwanciyar hankali, a daidai lokacin wata azababbiyar bugun ƙofa ta tashemu, a firgice daga daddaɗan baccin da muke yi, abin da ya tsorata ni kowaye ke bugun ƙofar nan to ba na lafiya ba ne, can muka ji muryar wani ya na faɗin za ku buɗe ƙofar nan ko kuma mu buɗe da kanmu, kuma faɗin hakan bai sa sun fasa bugun ƙofar ba.
Nan muka zabura ni da Yaya Sulaiman muka yo falo, muna zagaye domin dai babu maɓoya, ko wata hanya da za mu bi mu gudu, abin da nake faɗi araina, shi Yaya Sulaiman ke faɗi su waye wannan?, tunanin da ya zo ranmu kenan a lokaci ɗaya, a daidai wannan lokacin suka sa mu nasarar ɓalle ƙofar,suka shigo cikin ƙaton falon mai ɗauke da kayan mo re rayuwa.
“Inalilahi waina ilahi raju'un!.”
Abin da muke iya faɗi kenan na zabura na shige cikin. jikinsa “Baby yanzu ya za mu yi kenan?.''
“ ki kwantar da hankalin ki babu abin da zai faru.”
A daidai wannan lokacin suka samu nasarar buɗe ƙofar, tare da iso wa tsakiyar falon, na zabura zan koma bedroom,wani ya finciko ni tare da zabga min mari,sannan ya jefo ni tsakiyar falon.
Saboda tsananin azabar zafin marin, ban san sanda na sa ki fitari a jikina ba, tare da ɓallewar hawaye a fuskata, na kuma ɗora hannayena asaman kaina buɗe baki zan fasa ihu.
Ya zaro bindiga daga aljihun wandonsa ya sa min akai ya ce “Ki na buɗe bakin ki a gurin nan sai na fasa miki kai."
Na mai da bakina na rufe, amma duk da haka hawaye bai bar zuba a idona ba.
Duk abin da ke faruwa akwai ɗaya a gefe, ya na tsaye hannayen sa zube cikin aljihu, sai a yanzu hankalina ya kai kan sa, sannan duk da sun rufe fuskokinmu su hakan bai hana ni gane sa ba, saboda na san shi sosai a zuciyata na ce “Waye wannan kamar Habib?."
Ai ko hasashena na bai faɗi a banza ba, nan ya buɗe fuskar sa, tare da fashewa da wata irin dariya, wacce ta ƙara ruɗa ni na faɗa jikin Yaya Sulaiman.
Yace “A tunanin ki za ki ci amanata ne ki zauna lafiya, ko kuma an faɗa miki ni shashasha ne kamar yadda mahaifin ki yake tunani, dama kin daɗe kina tanbayata mece ce sana’ata, to wannan ita ce sana’ata Ina fatan yanzu kin gane?.”
ya faɗa tare da juya bindiga ya na wasa da ita.
Ya nufi gurin Sulaiman, tare da sa ma sa bindiga a tsakiyar kai, ya ce
“Kai kuma na dawo kan ka,dama na barka ne ka gama cin amarcin, tsayin shekaru shidda da na bar ku ban wai waye ku ba, Ina jiran wannan ranar ne yanzu kuma ranar fansa ta zo."
“ Na yi ma Aisha soyayyar da babu wanda ya yi ma ta a duniyar nan, lokaci ɗaya ka zo karaba ni da ita”, saboda haka ni rayuwarka zan rabaka da ita, sannan zan huce abin da kamin fatan ka gane malam Sulaiman?."
Ina jin haka na rarrafa na riƙe ƙafafun sa, ina ba sa haƙuri akan kar ya yima Yayana komai, Ina cewa “Ko mai kake so zamu yi maka amma, dan Allah kar ka kashe sa,”
Nan suka sake sa kin wata dariya mai cike da rashin tausayi da imani, lokaci ɗaya kuma suka ɗauketa kamar ɗau kewar ruwan sama ya kalle ni ya ce,
“ Haba Aisha aike ba zan miki komai ba, wanda ya raba ni dake shi zan raba da duniyar, sannan na ɗauke ki nakai ki in da babu wanda ya san ki, mu yi rayuwa dake cikin aminci da soyayya,”
Shi ko Sulaiman babu abin da yake faɗi a zuciyarsa sai“ Innalillahi waina ilahi raju'un!.”
Tare da neman ɗaukin Ubangiji mahalicin sammai da kassai, anan ya buɗe bakinsa da ƙyar ya ce
“Aisha ki yi haƙuri, zan bar ki a duniyar nan, mai cike da rashin tausayi da rashin amana, zan bar ki ina mai cike da ƙaunar ki, zan bar ki zan kuma bar miki amanar ƴata Zainab, tare da abin da yake cikin ki, ki kula da su iyakar iyawar ki, ki sa ni ina son ki ina kuma ƙaunar ki."
Nan Habib ya sake sakin dariya tare da faɗin “Sannu romeo sarkin soyayya, ai gara ka yi sallama da ita, domin yan mintuna ne suka rage maka aduniya.”
ina jin haka na faɗa jikin Yaya Sulaiaman, tare da ƙank'me shi ina sakin wani sabon kukan tare da faɗin, “Ba za ka mutu ba Yaya ba za ka mutu ba,Ina tare da kai ba zan bari a kashe ka ba, ka sa ni ina son ka kuma zan kasance a gyefen ka kamar yadda na ma alƙawari”, na faɗi Ina sake shigewa jikin sa.
A nan take Habib ya sa bindiga a ƙirjin Yaya Sulaiaman,tare da faɗin, “Aisha a gabana kike faɗa ma wani kalaman nan, to bari na kashe shi sai na ga yanda za ki y."
Ya faɗi tare da sakar ma Sulaiman harsashin bindiga, tau karar bindiga ta kara ɗe gidan, nan Sulaiman ya sulale babbu nunfashi a jikinsa, jinin jikin sa ya yi tartsatsi har zuwa fuska ta, sauran abokan tafiyarsa su ka saki dariya tare da faɗin, “Sai oga.”,suna sara ma sa da hannu.
Tun faruwar haka na kara sakin kukan tausayi da bakin cikin sanin Habib a rayuwata sanin shi be kare ni da komi ba sai bakinciki da nadama, na tsaya ina kallon Habib sai na kalli gawar Sulaiman, sautin dariyarsu ne ya dawo da ni hayyacina, na k'ara fashewa da wanii ƙarfaffan kuka ina faɗin.
“Yaya Sulaiman ka tashi”, Ina Jijjiga shi, ina faɗin”ka tashi dan Allah, kar ka mutu ka bar ni ka tashi ka tashi na ce ka tashi.”
Habib ya ƙara ɗauke ni da wani marin tare da fadin “za ki min shiru ko kuma kema sai na ɗauke kan ki da bindiga?."
Na ce “Ka kashe ni ka kashe ni,rayuwata ba ta da amfani tunda ka raba ni da farincikina, banda sauran anfani a duniya, ko baka kashe ni ba zan kashe kaina garama ka kashe ni na huta, azzalumi kawai macuci ma ci amana." Na fad'a cikin k'araji da tsananin tsanar shi dake ratsa sansan jikina.
Ya sake gauramin marin da sai da jini ya fito a bakina ya ce
“Kin ci arzikin soyayar da nake miki, da wallahi yau ba za ki kwana a duniyar nan ba, da sai dai ki bi wannan banza in da ya tafi."
Ya faɗi tare da tofa ma gawar Sulaiman yawu, ya kuma fizgo ni ya sab'a a kafaɗar sa, kamar yar tsana suka yi waje su ka bar gawar Yaya Sulaiman a kwance,ina ganin haka na tafi luu na sume, daga nan ban san mai ke faruwa ba.
Ban tashi farkawa ba, sai dai na farka na gan ni kwance a gado, hannu maƙale da ƙarin ruwa, na tsaya na gama ƙare ma ɗakin kallo, nan dai bai yi kama da asibiti ba, kuma nan ba gidana ba ne to ina ne nan?."
Na rufe idona na sake buɗe wa, can na tuna abin da ya faru, na zabura zan tashi zaune, sai a lokacin na ji hannuna ɗaya a riƙe cikin na sa.
Da ƙarfi na fuzge hannuna, domin a lokacin ba wanda na tsana a duniyar nan sa ma da Habib, na tsane sa fiye da yanda na tsani mutuwata, shi ko sai sakin murmushi yake yi, murmushin da ada kafin na san wane ne shi ya za ma abu mafi soyuwa a raina.
Ya ce “Shalelena kin tashi kenan?."
Nan na ji wani baƙinciki ya turniƙe min zuciya, na sa hannu na fuzge ƙarin ruwan dake ɗayan hannuna,tare da shafa fuskata wacce nake jin duk ta yi min tsami, duk halin da nake ciki hawaye bai daina zubar min ba, ya kai hannu zai share min hawaye, na yi saurin kau da fuskata tare da faɗin.
“La’anannen Allah kar ka taɓa ni, in sha Allah yadda karaba ni da masoyina, ba zan taɓa yafe ma ba, kuma.wallahi sai ka yi mutuwar wulakanci.”
Nan ya saki murmushi ya ce.
“komai za ki faɗi ki fadi, ni dai burina ya cika Tun da gani ga ki, a duniyar masoya in da babu mai raba mu ni da ke, dama ke tawace wancan la’anannen ya raba ni da ke, yanzu kuma na amshi abu na”
Gidan Sulaiman da asuba bayan idar da sallah ne, maƙocin Sulaiman ya sanar a masallaci.
“jiya na ji Harbin bindiga a gidan makocina sannan kuma ga shi ban gan shi a masallaci ba.”
Nan mutane suka fara maganganu, wa in da su kaji su ka gasgata shi, nan aka yi gangami aka nufi gidan Sulaiman, suna zuwa suka ga ƙofa a buɗe,nan aka rasa wanda zai fara shiga, maƙocinsa ya ce shi ba ri ya shiga ya gani ko lafiya, ya na shiga ya ga gawar Sulaiman a kwance a ƙasa,da gudu ya juyo ya sa nar da sauran mutanen dake wajen......
“511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa.
Page2️⃣
Suka yi ayari suka shiga ciki, suka ganema idansu “inalilahi waina ilahi raju'un! ."
Banda kalmar ba abin da ke fita a baku nan su, ta ke a gun suka kira ƴansanda da iyayen shi, mahaifinsa na jin hakan ya taho tare da ƙaninsa da kuma Yayyunsa, suka nufi gidan sun iso tare da ƴansanda, nan suka fara bincike a cikin gidan ba su ga komai na sheda ba, bayan ɓalle ƙofar gida da aka yi, iya bincikeken su ba su ga komai ba, domin Habib ba ƙara min mai wayo bane, a duk in da ya yi aiki ba ya barin sheda ko kaɗan.
Ƴansanda suka buƙaci abasu gawar su yi bincike, sannan an nemi Matar gidan an rasa nan hankali ya ƙara tashi ana tunanin shin Ina ta je ko kuma Ina ta yi shin tana raye ne? ko itama an kasheta kamar yadda aka kashe Mijinta?
Nan aka d'auki gawar Sulaiman aka kai asibiti,cikin ikon Allah likitoci na cikin duba Sulaiman, suka ga ya motsa yatsun kafar sa, nan suka fara shige da fice akan shi, har ya farfaɗo daga daguwar suma da ya yi ba mutuwa ba, sannan sun yi nasarar cire harsashin da yake a k'irji shi,sai dai kaɗan ya rage ya taɓa ma sa zuciya.
Aka shiga neman jini da za a’sa ma sa, ana gwada na ƴan uwansa ya yi daidai da na sa, aka ɗiba aka sa ma sa, sai dai har aka kwana aka yini bai farfaɗo ba, amma likita ya tabbatar da cewa lafiya zai tashi, in sha Allahu nan kuma hankula suka koma kan neman Aisha, dan har yau ba wanda ya ƙara ganin ko giccin ta.
Iyayen Aisha sun shiga damuwar rashin sanin halin da ƴarsu take, ya yin da kuma jikar su ke tambayar su “Ina Momyna?.”
Dan ranar da abin ya faru ta jema Kakannin ta week end, dan lokacin ta na da shekara biyar ne.
Kwana Aisha shidda ta fara jin sauƙi, sai dai ta na cikin damuwa, dan a tunanin ta Mijinta ya mutu, a duk lokacin da Habib ya zo yana ma ta surutai, da sunan kalaman soyayya ji take kamar ta daɓa ma sa wuƙa a kahon zuciya ya mutu, ko za ta huta da ganin sa, sai kuma ta ce
" Ni ce ya kamata na mutu ba shi ba, ko dan na bi masoyi na, idan ta tuna maganar Sulaiman kuma sai ta ce zan rayu ko dan yaran ka Sulaiman, zan kula da su zan ba su tarbiyya irin wacce kake so."
Sai ta fashe da kuka, ta ce ya Allah kai min sakayya tsakanina da wannan bawan na ka,ya cutar da ni Allah ka na gani, sai ta sake fashewa da kuka, Habib ya kan yi dariya a duk lokacin da ya same ta tana irin maganganun nan, akwai ranar da ya ce ma ta, “Ni fah na gaji da ganin ki da cikin jikin ki, na ƙosa ki haihu a d'aura mana aure, na gwada miki irin soyayyar da nake miki.”
“Da na aure ka gara na mutu na tsane ka, ina raye ne saboda ina son na ga karshen ka, ni ce zan ga bayan ka in sha Allah,”ban taɓa ga nin in da soyayya ta koma ƙiyayya ba,kar ki manta komai na zama a yanzu son ki ne sanadi.”
Ta tafo ma sa yawu a fuska”Allah ya isa tsakanina da dai, ka ƙara cewa kana sona sai na kashe ka.”kafin ta rufe baki zai ce
"Da nafi kowa farin cikin masoyiyata ta zama ajalina, da na mutu ina farin ciki da hakan.
“Haba Aisha mai ya sa ki ka manta da alkairina a gare ki, mai ya sa kika manta da soyayar mu, ke fa kika ce ba za ki taɓa son sa ba,kin ce ni kike so, sannan yanzu ki juya min baya, ya kike sona yi?, bayan ya riga ni mallakar ki, yan zu kuma kice kin daina so na.”
Ya b'ata fuska cike da jin haushi ya d'ora da cewa.
“Kin san ya na ji lokacin da kike faɗa ma sa kalaman soyayya a gabana, ji na yi kamar na haɗiyi zuciya na mutu saboda bakincikin kalaman ki gare shi, zuciyata kamawa da wuta ta yi, ki dawo hayyacin ki wancan mutumin ba son ki yake ba ni ne masoyin ki na haƙiƙa, ko kin manta har ciwo na kwanta a sanadin son ki, kin manta ina tattare da ciwon zuciya a sanadin son ki?
A sanadin son ki na tsinci kaina a halin da nake ciki yanzu, dan haka duk wanda ya ce zai raba ni da son ki to sai na raba shi da rayuwar sa,zan iya kashe kowa akan ki,dan haka baki isa ki guje ni ba, ko ƙarƙashin ƙasa ki ka shiga sai na biki, na kwakulo ki saboda ke ɗin tawa ce mallaki na ce.”
Babu abin da nake yi sai kuka saboda na tsorata da kalaman shi,na firgita da maganganun shi, babu abin da nake yi sai neman taimako Allah shine kad'ai zai iya cetona daga hannun Habib.
Dan na sha gwada guduwa amma babu hali, dan masu gadi ne sosai a cikin gidan,
“A tunanin ki za ki samu hanyar guduwa ko?, to ki cire hakan a ran ki dan ni dake mutu ka raba, dan haka ki kwantar da hankalin ki shine zai fi miki nutsuwa don babu gurin gudu ko tsira anan.”
Ya tashi ya fice dama abinci ya kawo min.
“Aisha! Aisha!! Aisha!!!”abin da Sulaiman ya farka da shi kenan,
"Doctor Doctor.”Yayansa ya fita ya na ƙwalama likita kira, da sauri likitan ya iso ya zo ya duba shi tare da yin yan gwaje gwaje dan ya tabbatar da samun sauƙin shi, “Alhamdulillah jiki ya yi kyau, yanzu a samu a bashi wani abin ya ci kafin na ma sa alura."
Nan Yayansa ya kama sa ya miƙe ya raka shi toilet, ya wanke baki suka dawo, ya hada ma sa shayi ya ba shi ya sha.
Likita ya shigo ya ma sa alura ya ba shi magani ya sha, kafin ya koma ya kwanta dan ya samu hutu, alokacin iyayen su suka shigo dan Yayan ya faɗa musu a waya, tun farkawarsa, nan su ka zo suna farin ciki da samun sauƙin shi.
“Umma ina Aisha ban ganta ba?,”tambayar da zan maka kenan ni ma
”Umma kuna nufin baku san in da take ba?” Sulaiman tun ranar da abin nan ya faru ba wanda ya ga Aisha kuma ba musan in da take ba.”
“Inalilahi waina ilaihi raju'un!, kar dai ya tafi da ita?."
“Waye ya tafi da ita? Sulaiman magana nake maka waye ya tafi da ita?”
"Umma Habib ne.”waye kuma Habib?”
Tsohon saurayinta Umma dan unguwar su din nan.”
“Innalillahi wa inna ilaihi raju'un!, kar dai kana nufin shi ne ya muku haka?.”
"Umma shi ne dama cewa ya yi zai kashe ni, sannan ya ɗauke ta,Umma abin tashin hankalin ma ga ciki a jikin ta, ban san halin da take ciki ba, ta na raye ko ya kashe ta shi ne babbar damuwata.”ya fad'a ya na share hawaye.
“Dole hukuma su kara ƙaimin wajen binciken nan tunda an samu makama, dama rashin sanin su waye suka yi muku haka, shi ne dalilin da ya sa binciken ya yi sanyi."
Nan mahaifina ya ɗauki waye ya kira d p o d'in da case din ke gurin shi, nan da nan suka iso asibitin, sun yi wa Sulaiman tambayoyi, kuma ya ba su haɗin kai sosai dan duk abin da suka tambaya ya sanar musu.