Author : MINAL SAEED Category : Romantic Hausa Novels
a mashin ɗin suna ƙara sowa, da gudu ya ja hannuna mu ka faɗa cikin ruwan nan, ”damm it, Habib ya faɗi “lallai wannan ko waye sai na hallaka shi da hannuna, na sha wahalar jira na shekaru sai yanzu da ya rage min ɗan taƙi kaɗan na mallake ta zai raba ni da ita”.
KECE SILA
(✍️Minal saeed)
(🌹MRS BASH🌹)
https://whatsapp.com/channel/0029VbBl22NAO7RLFvcUlU2g
https://chat.whatsapp.com/FuiNx6HvwgzAheM7xh0Xci?mode=ems_copy_t
://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake gina
Page6️⃣
Ya durƙusa ya fasa wani ihu da sai da dajin ya amsa, muna ci kin ruwa Jamal na riƙe da ni da hannu ɗaya, mun shafe sa ma da awa uku, kafin Allah ya sa mu ka iso bakin gaɓar ruwan nan, mun isa a galabaice, ga ciki a jikina hakan yasa muna fita a ruwan na sume, ban ƙara sa nin waye a kaina ba, ni dai na farka naji ana faɗin Alhamdulillah ta farka.
Dishi dishi na fara gani, kafin na buɗe idona duka, “sannu” na ji wata murya daga gyefen damana, na kai hannuna na shafi cikina na ji yana nan, na yunƙura da ƙyar na tashi, zaune wata baiwar Allah ta taimaka ta jinginar da ni jikin bango.
“shannu” ta faɗi cikin muryar da sai yanzu na lura ashe fulani ne, ”ke Hari kawo ma shi madara ya sha, ”to Baffa,” ta kawo min madarar shanu mai zafi, ai ko na sha sosai, ”shannu” ta ƙara faɗi ba yan na miƙa ma ta ƙwayar da ta bani madarar shanu a ciki.
“Hari dafa ma shi ruwa mai zafi ya yi wanka” ta tashi ta fita bayan mintuna sai gata ta shigo, ta shi muje ka samu ka yi wankan,” ta kama ni na miƙe ta raka ni na, je nayi wanka, kuma na ji ƙwari a jikina, na dawo ɗakin ta bani riga da zani na atampa na sa.
Sai ga Jamal da Baffa sun shigo a tare, “sannu Anty Aysha, ”yauwa Jamal, na gode sosai da ka cece ni daga hannu mugun nan, ”ba komai Anty na hakan kamar haƙin ki ne a kaina, dan na san cutar wace tasa ya kawo ki nan da sunan soyayya, ”bawan Allah dama ba matar ki ba she wannan?”.
“Eh Baffa, taimakon ta nayi dan ni kaina ban san wacece ita ba, amma a halin da na ganta ta na buƙatar taimako, shi ya sa na yi kasada da rayuwata na taimake ta, ko Allah zai dubi hakan ya yafe min zunubai na”.
“Amma Anty zan so sanin wacece ke, kuma mene ne ya haɗaki da boss, ”haka ne Jamal yanzu zan sanar mu ku,” Hari ta shi go a dai dai wannan lokacin.
Wacece Aysha.
Wata ranar alhamis mun dawo da
ga hadda, da misalin ƙarfe huɗu na yamma, “Khairat ni fa ba zanbi ta hanyar nan ba sai dai mu zagaya, “wallahi Aisha ga hanya mai sauƙi, ba zanbi ta wancan hanyar mai shegen nisa ba, ”dan Allah ki zo mu zagaya, dan wallahi yanzu na san su nanan, sun yi zaman majalisarsu ta ƙaddara, ”ke wai ina ruwan ki dasu ne, ga liƙaf a fuskarki ga safa a ƙafarki, to ina abinda ya dame ki dasu, ”hmm Khairat baki san kallon da ake min a cikin jikina nake jin sa ba”.
“Haba Khairat ɗin Aysha ni da ke fa bata ɓaci, ”ai sai ki wuce muje mutum kamar maye in ya fara naci kamar kuturu, ”ko ke fa ƴar uwa rabin jiki, Allah ya barmu tare, ”ni dai muje ai kin iya daɗin baki”.
Mu ka tafi muna hirar duniya dan wallahi na tsani bi ta hanyar nan, duk da tafi sauƙi da kuma sauri, amma saboda majalisar da ke hanyar na tsani binta, dan ana yin sallar la'asar kamar ana kiran maza, za ki samu sama da mutane goma a gurin,
Ni ce ta huɗu a ɗakin mu,ina da yayyi uku Yaya Mustapha shi ne babba, da Yaya Ibraheem, sai Yaya Kabir, sai ni sai autar mu khadija, mu ba masu hali ba ne, mu na dai da rufin asiri, na kammala secondary ɗi ta, a yan zu ina zaman jiran sakamako ne, dalilin dayasa namai da hankalina ke nan akan haddar da nake yi.
A ba cirawa mu ke la yin Lawal mai ke ke,layin talakawa ne so sai masu neman na rufin asiri, Alhamdulillah ummamu ta na karamar sana'a a cikin gida ta kunun aya da zoɓo, kuma ta na samun kasuwa saboda umma akwai tsafta, ku san a gurin ta na ga ji tsafta, ƙawata ɗaya ce kaf layin saboda tun muna ƙanana, umma ta hana mu ta ra tarkacen ƙawaye, dan ace war ta wai su ke ɓata ma wasu ƴaƴan tarbiyya.
Ƙawata ɗaya ce Khairat, ita ma maƙota mu ke da su, sannan ku san halin mu ɗaya da ita,na kasance ma ta shiyar buduruwa,mai cikakken diri da duk wan da ya ganni sai ya yi shawar da ma shine a haka, ni ba fara ba ce kuma ba baƙa ba ce, fatar jikina ta kasance mai ɗaukar hankali, inada dara daran idanu, da gashin ido za ra za ra, ga kuma gashin gira da har kusan haɗe wa da juna su ka yi, a ƙasan hancin na na ɗauke da dan ƙaramin baki mai ɗuke da siraran laɓɓa, yayin da a saman leɓe na na sama akwai wani dan baƙin di gon abu wanda yake ƙaramin kyau.
KECE SILA
(✍️Minal saeed)
(🌹MRS BASH🌹)
https://whatsapp.com/channel/0029VbBl22NAO7RLFvcUlU2g
https://chat.whatsapp.com/FuiNx6HvwgzAheM7xh0Xci?mode=ems_copy_t
://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake gina
Page7️⃣
Haƙora na farare ne tass, a taƙaice dai duk inda ake buƙatar cikakkiyar mace na kai, tunda na kai shekara sha huɗu, na fahimci irin kallon da mutane ke bina da shi, na wajabtawa kaina sa hijabi da liƙaf da safa, tun Khairat na min tsiya har ita ma shigar ta fara birge ta tafara…
Habib
Habib shine yaro biyu a gidan su, na ta so matashi ne mai ne man na kaina, a da gani nake masu zama a majalisa basu da aikin yi ne, har sai wata rana dana zo gurin a bokina, a wannan majalisar, dai dai lokacin da su Aisha ke wucewa, tun Ina shekara sha takwas A'isha ke burge ni, ban san son ta nake ba sai wata rana dana ganta ta dawo daga makaranta.
A lokacin sai na maida majalisar nan kamar gidan mu, kullum da munyi sallar la'asar nake zuwa na zauna, bana tashi har sai na ga wucewar ta, ana haka ban saniba ko ta fahimci ina zuwa gurin domin ta ne, sai ta dai na bi ta hanyar kodayaushe sai jifa jifa, duk ranar da ban ganta ba ina kwana cikin damuwane da ƙuncin zuciya.
Tun ina jurewa har na sare, a yanzu haka na shirya tunkarar ta da maganar, dan na fahimci ita ce rayuwa ta, sai dai kash yau tsayin sati ɗaya ke nan ban ganta ba, haƙiƙa hankali na ya ta shi, dan yanzu na kwashe shekara biyar ina zaman majalisa, na fara tunanin ko batada lafiya ne, kwatsam shawara ta zomin na shirya na tafi gidan su Khairat..
“Assalam alaikum, a'a Yaya Habib yau kai ne a gidan na mu, ”malama Khairat ni ne ya ki ke, ”lafiya lau Yaya, ”na ji daɗin hakan, Khairat taimako nake nema a gurin ki, ”to Yaya Allah ya bani Ikon taimaka ma, ”akan ƙawar ki ce Aisha, haƙiƙa Aisha tun ta na ƙaramar ta nake son ta, na dauka ba so bane sai a shekarun nan na fahimci hakan”.
*yanzu taimakon da za kiyi min shine ta ya zan samu damar magana da Aisha, ko kuma ki bani lambar wayar ki sai na kira ki bayan kin sanar mata, ”to ina ga kamar hakan zai fi mana sauƙi Allah ya zaɓa muku alkairi, ”ameen na gode ƙawar mu”.
“Assalamu alaikum, Umma ina yini, ”lafiya lau Khairat ya ki ke ya Umman ki, ”lafiya lau tace tana gaida ki, ”ina amsawa, ”Umma Aisha na nan?, ”eh ta na ci ki, ”to Umma, “A'isha A'isha A'isha!!, ”maine ne za ki kama ƙwala min kira tun a waje, ”dallah malama tashi ki zauna, gurin ki na zo”.
“To Allah ya sa lafiya ba laifi na yi ba, ”laifi babbama kuwa, ”na shiga uku mai aka ce na yi, ta faɗi idonta na tara ƙwallah, ”hmm Aisha abin ba ɗaɗin faɗi, ”dan girman Allah Khairat ki faɗi min kafin zuciyata ta buga”.
“Aisha ta ni kai na da na ji sai da jini na ya kusa hawa, ”kin ji ko dan Allah ki faɗi min, ”sata fa aka ce kin yi, ”sata na shiga uku yaushe a ina?, ”ke dai bari Aisha, ai ko ta sa min kuka wi wi, na kwashe da dariya na ce, ”amma wallahi kin shiga uku ke da ga faɗin abu ba bincike har kin amince, harda kuka Allah ya kyauta wa wannan zuciyar ta ki,” na ƙa ra sa da Dariya!!…
Ai ko Aisha tayo kai na da niyar duka, na kwasa da gudu na yi waje ina dariya, Umma ta kalle mu ta girgiza za kai ta ce ”Allah ya shirye ku, zan ga ranar da zaku girma, ace yara shekara sha bakwai, amma har yau baku dai na wasan berori ba”.
Nan mukai ta zagaye tana son ta dake ni, ni kuma na ƙi ba ta dama, sai da mu ka ga ji ta ja gyefe ta na mai da nunfashi ni ma haka, ta na kumburi sai da mu ka da wo natsuwar mu sannan na ba ta haƙuri, ”yanzu dai ki ba ni hankalin ki, maganar gaskiya za mu yi ba wasa ba, ”ina jin ki”.
“kin san Habib?, ”wani Habib ku ma?, ”na gidan su Jamila Umar, ”oh na gane sa yanzu, ”yauwa toh shi ne ya aiko ni gurin ki, ya ce na faɗa mi ki wallahi ya daɗe ya na son ki, ya rasa hanyar faɗi mi ki ne, amma yanzu dai ya bani lambar sa bari na kira sa ki ji da kunnenki”.
Na kira wayar sa ai ko bugu ɗaya, ya yanke kiran ya biyo ba ya, na amsa wayar bayan mun gaisa, na ce ma sa toh ga Aishan, na miƙa mata wayar..
“Assalamu alaikum”
“wa alaikisalam amincin Allah da rahamarsa su tabbata a gare ki, ya ke ma’abociyar murmushi da kyewun fuska”.
“Ina yini, ”lafiya lau sarauniyar mata ta duniya, ma’abociyar kwarjini da kyewun halaye”.
“Duk da na san an sanar mi ki da ƙuduri na akan ki, amma bari na ƙara faɗi miki da bakina, haƙiƙa Nana Aisha na daɗe ina son ki dan tun ki na yar ƙaramar ki nake son ki, amma ban tabbatar da hakan ba sai da na daina ganin ki na kwana biyu, yanzu dai ba wannan ba dan Allah ki taimaka ki karbi ƙoƙon bara ta a gare ki”.
“Kar ki juyar da buƙata ta, dan in har hakan ta faru zan shiga wani mummunan yana yi, ”hmm, “A'isha tu na kin yi shuru, dan Allah ki yi min magana mana”.
Lokacin rasa mai zance ma sa, sai daga baya na buɗe baki na ce, ”to shike nan Yaya Habib na amince, ”Alhamdulillah Aisha na gode mi ki sosai, da amsar soyayyata da ki ka yi, ataice dai a ranar Habib bai barni ba sai da ya tabbatar da ya kafa soyayyar sa a zuciyata.
KECE SILA
(✍️Minal saeed)
(🌹MRS BASH🌹)
https://whatsapp.com/channel/0029VbBl22NAO7RLFvcUlU2g
https://chat.whatsapp.com/FuiNx6HvwgzAheM7xh0Xci?mode=ems_copy_t
://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake gina
Sadaukar wa’, ga manyan gobe return Allah ya albarkaci rayuwar al’umar da ke cikin sa, haƙiƙa kaunar ku a gareni mai girma ce, na gode Allah ya bar zumunci ya ƙara soyayya a tsakanin mu, Allah yajiƙan Anty Bilkisu Ahmad ya kai haske ka bari ta, munyi rashi Allah ka bamu haƙuri.
Page8️⃣
Da ga nan sabo da shaƙuwa mai tsanani su ka shiga tsakanin mu, ku san koda yaushe mu na tare in dai ba na tafi makaranta ba, to muna tare a waya, ko kuma ya zo gidanmu mu na hira.
Munsha yiwa juna alƙawarin rayuwa tare komai tsanani, ba wanda bai san mu tare ba, wa su har sun can za min suna da Aisha Habib, mun kwashe tsayin shekaru uku mu na tare da Habib, hatta da yan gidan mu da gidan su sun san da soyayyar mu.
Duk abun da nake so Habib na min bakin ƙoƙarin sa, duk ranar ban gan sa ba kuma ba muyi waya ba, yini na ke cikin damuwa har sai na gan shi ko munyi waya walwala ta ke dawo wa, haƙiƙa soyayyar da muke wa juna har mamaki take ba mutane.
Kwatsam Yaya Sulaiman ya yi kutse a tsakanin mu, ya shigo rayuwata da ƙarfin sa, tun bana kulasa Ina wulakanta sa har na gaji nake tsayawa da shi, ranar da Habib ya same mu a tsaye duk da ba wata hirar arziƙi ba ce tsaka ni na da Sulaiman, dan wata rana har ya yi surutusa ya gama ba na tanka mai, sai dai na bisa da tsaki, ranar Habib da zazzabi ya kwana ni kuma na kwana ina kuka.
Habib ya yi fushi da ni mai tsanani, wanda na shawahala kafin na shawo kansa ya hakura, Sulaiman ya zo ranar na manta da tarbiyar gidan mu, na rufe ido naci ma sa mutunci, duk dan ya rabu da ni amma ina kamar na ƙara zuga sa...
Har kuka na ma sa akan dan Allah ya fita a rayuwata, kuma na yi da na sanin bikin da na je muka haɗu da shi, ”assalm alaikum, an ce wai Aisha ta zo in ji Sulaiman, ”je ka ce bata nan” na ce, maganar da na yi dana sanin faɗin ta dan duk ita ce mafarin komai.
“Ke Aisha mai na ji kin ce, ”Baba ban ce komai ba, ”ungo na ki na ce, za ki tashi ki fita gun mai kiran ki ko sai na zo,” na tashi na sa hijab na fita ina ƙunƙuni, ban jima da fita ba sai ga Babanmu ya fito da kan sa, Sulaima na ganin sa ya duƙa har da sa guiwowin sa a ƙasa, duk da fararen kaya ne a jikin sa ya gaida Baba.
Baba ya amsa cike da farin ciki, ya ce “in ka samu lokaci ina son ganin ka,” rass gabana ya faɗi, mai baba zai faɗi ma sa da ya ce ya na son ganinsa, ”to Baba ai ko yanzu ma zaka iya gani na, ”to to Alhamdulillah, bismillah shigo da ga ciki”.
Ji nayi kamar na bisu cikin ɗakin Baba dan na ji mai zasu tattauna, ina zaune a tsakar gida Sulaiman ya fito daga ɗakin Baba muna haɗa ido ya sakar min murmushi tare da kashe min ido ɗaya, zaro ma sa ido na yi, sai ya ɗago min ya tsun biyu yana kaɗa min su ya yi waje…
Da dare Baba ya kirani yake sanar min ya bama Sulaiman ni, daga yau karna kuma kula Habib dan ba aurena zai yiba, tunda in aurena zaiyi yanzu shekara nawa muna tare, da an ma sa maganar turo manya sai ya ce a ƙara ma sa lokaci, tunda ga wanda ya shirya da shi za'ayi..
“Inalilahi waina ilaihi raju'un?, wallahi Baba bana son Sulaiman, ni Habib nake so kuma shi zan aura, ”Aisha kina da hankali kike faɗawa Mahaifinki haka, ko kin fara shaye shaye ne?, “ni Umma Habib nake so dan ba wanda zan iya zama da shi sai Habib”.
“Ke ina magana shine kike ƙara maimaita abun da ki ka ce koh, ”to wallahi zan ɓata miki rai, ”rabu da ita karki ƙara ce mata komai,