Author : MINAL SAEED Category : Romantic Hausa Novels
dade suna jiran wannan damar da kuma lokacin, dan ƴar wani hamshaƙin Mai Kuɗi suke shirin kamowa, dan yanzu banda fashi har kidnapping din mutane sun fara, sanna duk wanda suka kama, sai an basu ƙudin fansa in ba haka ba su kashe mutum….
Wanna yarinyar da zasu kama sunan ta Hanifa, mahaifinta tsohon minister ne yana da kuɗi sosai, sannan babban ɗan kasuwane, Hanifa itace babbar ƴarsa kuma mace, sai ƙanenta uku duk kansu maza, ta kammala karatun jami’a Ƙasar India inda ta karanci bangaren lafiya, Hanifa yarinya ce mai ji da kai tare da ɗagawa, a haka tafiya ta taɓa hada ta da Ogan su Habib, ya nuna yana son ta ta ƙi amince wa ta kuma wulakanta sa…
Dan haka ya ci burun sai ya ɗaukkota ya lalata mata rayuwa, ya ga da mai taje taƙama, dan haka ya shirya komai kuma ya sawa duk wani motsinta ido, daga na nan gida Nigeria har na ƙasar da take lissafe da lokacin da ta kwashe a in da ta ke, ya kuma san lokacin dawowar ta gida, dan haka a lokacin zai ɗauko ta ta zo tayi rayuwa da shi yaga ƙarshe ƙiywyyar da take ma sa….
Da wannan damar Jamal ya yi amfani ya sanar wa da Kabir, in da suka suke ta na su shirin kafin lokacin ya cika, ana saura awa ɗaya jirgin su Hanifa ya sauka su Kabir suka zo dai dai inda suke da niyar tsayar da motar da ta ɗakko Hanifa suka kafa nasu tarkon, su Habib kuma ana saura minti talatin su ka fito, duk abin da suke yi a idon su Kabir…..
Hanifa….
Tana sakkowa daga jirgi na hango wata tsaleliyar buduruwa fara tass, sanye cikin jar daguwar riga, ta nannaɗe kanta cikin ɓaƙin mayafi siriri, wani ƙaton gilas na gaji sanye a fuskarta, da ya shanye rabin fuskar, na kai idona kan ƙafarta tana sanye da wani dogon takalmi baƙi, dan ƙaramin bakinta yasha man leɓe sai walƙiya yake, a zuciyata nace in banda abin Ogan su Habib, ya rasa wacce zai ce yana so sai wannan hali tar, shima yasan zaren ba kalar yadin bane, cire gilas ɗin fuskarta ta yi tana dube dube gyefe da gyefen ta…….
“Ranki ya daɗe barka da sauka”, “Idi Ina Dadyna ya baizo ɗauka ta ba bayan shi ya ce da kan sa zai tarbeni,?” “Hajiya Ƙarama Alhaji baya nan sun tafi wani taro a Abuja,” “ well muje to.”
Ya ɗauki akwatinta ya sa abayan mota, ita kuma ta shiga, ya rufe ma ta sannan ya shiga ya ja motar, can na hango wani a zaune a jerin masu jiran saukar fasinga, yasa huta pecin cap ta kusa rufe ma sa rabin fuskar sa, ya fito da wayar ya danna wasu lambobi ya kara a kunne, ya ce, “an gulu na hanya sai a fara kula, tana sanye da jajayen Kaya, ta taho da dan shaho, shikuma ya na riƙe da baƙar kafa dan haka sai a kula.”
Hanifa tana shan kiɗa a mota sunyi tafiya ta tsayin minti arba'in, sai taji ƙeee alamun taka birki, da sauri ta ɗago dan taga mai ke faruwa, mutane ta gani sanfa da baƙin fece mark, ɗauke da bindigogi sun zagaye motar, zaro ido tayi tare da faɗin “Inalilahi waina ilaihi raju'un!!.”
KECE SILA”
(✍️Minal saeed)
(🌹MRS BASH🌹)
https://whatsapp.com/channel/0029VbBl22NAO7RLFvcUlU2g
https://chat.whatsapp.com/FuiNx6HvwgzAheM7xh0Xci?mode=ems_copy_t
://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake gina
Page1️⃣7️⃣
“mai ke faruwa ne Idi,?” “Hajiya wallahi ban sa ni ba,” “buɗe ku fito, ka fin mu fasa kanku da bindiga,” Hanifa ta buɗe motar ta fito a dake dan ita haka Allah ya yi ta bata da tsoro ko kaɗan, Idi ko jiki na rawa ya fito, “lafiya malamai zaku tare mana hanya?.”
“Tambaya ki ke yi,” “eh ai dole na tambaye ku dalili, dan sanina babu abin da na muku amma kun taremin hanya,” sai suka buɗe ta tsakiyar su Oga ya biyo, ya ƙara so inda take tsaye, yasa hannu ya shafi gyefen fuskarta, yace “da kyau kyakkyawar tsuntsuwata, ashe har yanzu ba ki canza hali ba.”
Da sauri na buge hanunsa, “malam waye kai da zaka kama taɓa min fuska, kasan wace ce ni,” “ saboda ina son sanin wace ce ke shiyasa na zo gare ki, amma tunda ba ki gane wane ne ni ba yanzu zan mi ki bayani.”
“kin tuna ranar 12/10/2005, kin tuna Airport ɗin Aminu Kano, wani mutum sanye da baƙaƙen kaya, da ya ce mi ki sunansa Jabir, har ya miƙo mi ki ƙoƙon barar soyayyar sa, kin tuna mai ki ka kirani da shi, kin tuna mai ki ka faɗa min, idan ba ki tuna ba zan tu na miki.”
Baya baya ta fara ja, kalaman da ta faɗa ma sa na dawo wa tiryan tiryan cikin kanta, sanye take cikin baƙar doguwar riga Kamar yadda shigar ta ta kasance a koda yau she, kanta sanye da farin mayafi iya kar wuya, fuskarta ɗauke da glas Mai ruwan ƙasa, bakin nan ya sha jan jan baki, tana zaune tana jiran a kira sunanta domin dai lokacin tashin su a jirgi ya kusa har an fara kiran sunayen matafiya….
“Hello young girl,” taji an faɗi da sauri ta ɗago kai, ta gama ƙare ma wanda ke tsaye a kanta kallo, ta ja siririn tsaki ta maida kanta kan wayar ta, domin dai a lokacin ta shiga cikin group din sirrin ƴa mace, tana kallon wata chapter da ake yi akan wata baiwar Allah da ta yi posting akan a bata shawara akan yadda za ta karkato da hankalin mijinta gareta, ana bada shawarwari a group ɗin sosai kuma tana samun nishaɗi.
Da taga wani comment tayi dariya, ta ce kai matan sirri Allah ya sa ka muku da alkairi, “wow kinga yadda dariyar nan ta miki kyau,” ta dan firgita dan har ga Allah ta manta da shi a tsaye, “wai kai malam ina ruwanka da ni ne, ko ka sanni ne zaka zo ka takurawa rayuwata haba.”
“Ƴan mata da alkairi na zo gare ki, wallahi tunda nake ban taɓa son wa ta ɗiya mace ba sai ke,” hahaha tayi dariyar rainin wayau, “ so sofa ka ce amma baka da hankali ko Kaga nama kama da irin sha sha shun Ƴan matan nan ne da kowani sha sha sha zai kula.?”
“To ka koma cikin hankalinka, ni Hanifa ba sa’ar ka bace, ka gane kai baka fi na ɗauke ka a mai min goge goge ba, saboda haka ka kama kanka wawa kawai,” ya buɗe baki zai yi magana, ta tofa ma sa yawu a fuska, ta ja tsaki ta bar sa a gurin a tsaye, shi ko da ƙyar ya taushi zuciyarsa dan alokacin ji ya yi kamar ya bita ya kashe ta, a dai dai nan yaji ana kiran sunansa a lasifika Jabir Jibrin, ya juya ya nufi jirgin da zai bi zuwa garin Kaduna zuciya cike da mugun nufi kan Hanifa…
Daga nan ya fara bincike akanta, har ya samu labarin wace ce ita, ya sa ana bi biyar ma sa lamuranta, har ya san komai nata ya samu labarin shekarar da za ta kammala karatu, aiko har bikin ya ye su ya je duk dan son sanin ranar da wowar ta ya kuma samu abin da ya ke so, dan bai bar ƙasar ba sai da ya san ranar da zata dawo da kuma jirgin ƙarfe nawa zata biyo, hatta da direban da zai je ɗakkota sai da ya sa ni ya kuma sa mai bibiyar sa…
Tana gama tunanin nan ta zaro idonta, “kai kai kai ne,” ta fadi bakin ta na rawa, hahaha ya sa ki dariyar mugunta, “kin yi mamaki ne, ba ki ga komai ba yarinya ba dai ke ba ki da kunya ba, dan haka wuce muje kona fasa kanki a gurin nan kuma na kashe banza.”
“Dan Allah ka yi haƙuri ba zan sake ba,” “taurin kai za ki min kin zaɓi barin duniyar ke nan, dan zaɓi na ba ki ko ki wuce mu tafi ko ma aika ki lahira,” hahaha dariya su ka ji an yi da sauri suka juya dukkan su, mai zasu gani Ƴan sanda ne ke zagaye da su, “wannan zaɓin ba da ita ya dace ba da ku ya dace dan haka you're under arrest, ku miƙa Kan ku ku aje makaman ku ko ku baƙunci lahira yanzun nan.”
Oga ko nace Jabir ya juyo da fuskar ya dan ganin mai yin maganar nan, wa zai gani “ Ka ka Kabir kai ne,” ya faɗi yana nuna sa da hannu, “kwarai Jabir nine kuma kar ka sa ran sanayar dana maka zata sa na ɗagama ƙafa, haka nake aikina basani basabo, ko waye kai ka taka doka sai na taka ka.”
Ganin ba yadda za suyi su tsira yasa dole suka miƙa kansu, suna ji suna gani haka aka wuce da su gidan yari kafin a mi ƙasu kotu, Habib shi baya baƙin cikin ka masu da a ka yi, shi damuwarsa da bai ga Aisha ba, haka nan aka zo mu su tambayi, kowa na fadin da lilinsa da sanadin daya je fa shi cikin halin da yake….
Ita ko Hanifa godiya ta dinga ma su Kabir har ta amsa number sa tace za ra ba na Dadynta, Dady ya shiga tashin hankali da jin abin da ya faru da ƴarsa ɗaya tilo, ya ce suje asibiti a du ba ta, taƙi amincewa dan ta ce ita ba abin da ya sameta, daga karshe ta ba sa number Kabir ta ce ya kira sa ya ma sa godiya dan ba dan shi ba da yanzu bata san a ina ta ke ba…
Oga yace matar babansa ce silar fadawa harkar fashi, Oga kona ce Jabir ya ce tunda suka kammala secondary school, matar babansa ta tsani ganinsa a cikin gidansu, sharrin yau daban na gobe daban, har tayi nasarar masa sharrin fyade, aka kai sa gidan yari ba tare da an ma sa shari'a ba, haka aka dinga gana ma sa azaba wahala tayi wahala, har Allah ya haɗaka da Uban Gidansa Dodo daga nan ya masa hanyar fita tare da sharaɗin zai yi aiki tare da shi……
KECE SILA”
(✍️Minal saeed)
(🌹MRS BASH🌹)
https://whatsapp.com/channel/0029VbBl22NAO7RLFvcUlU2g
https://chat.whatsapp.com/FuiNx6HvwgzAheM7xh0Xci?mode=ems_copy_t
://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake gina
Page1️⃣8️⃣
Bayan wata biyu
Dodo ya fito ya nemi Jabir, tun ina tsoron aikin da yake sa ni har na zo na kware, ban maida kisan kai fyaɗe wa mata komai ba, safarar miyagun kwayoyi da makamai ba komai bane a gurina, mun daɗe tare da Dodo a wa ta rana mun je fashi a banki, jami'an tsaro suka tara mu garin harbe harbe a tsakanin mu, aka kashe Dodo daga nan na maye gurbinsa kunji yadda rayuwata ta kasance, amma ni nan da kuka gani inada shekara sha biyar a duniya, na sauke alqur'ani mai girma, sannan na karanta littafai addini da dama, kawai ruɗin duniya da sharrin matar uba ne ya sa na tsinci kaina a wannan rayuwar da nake….
A ka zo kan Habib ya rushe da kuka, ya ce ba zai yi magana ba sai Aisha tazo, haka Kabir ya taso su Sulaiman daga gidansu, “Habib ga Aisha kace ba zaka yi magana ba sai ta to, mene ne dalilin shigar ka fashi bayan da a mutumin kirki aka san ka?,”.
“Aisha ce sila,” Aisha ta zaro ido ta ce “ni kuma, taya na zama silar shigar ka fashi?.”
“ƙwarai kece sila, kece silar shigata halin da na tsinci kaina, kece silar duk abin da ya faru da ni, kece silar komai a rayuwata, kece sila.”
“kamana bayanin ta yadda ta zama sila,” cewar Sulaiman, “A'isha ce sila domin da banji tana furta maka kalmar so da kunnena ba, daban yi yunƙurin kashe ka ba har aka kai ni gidan yari a silar haka.”
Bayan an kai ni gidan yari kamar yadda alƙali ya ce tare da horo mai tsanani, haƙiƙa a lokacin na yi dana sa ni har na fara cire ta a raina, sai dai wa ta rana bayan mun dawo daga aikin wahalar da ake samu, na dawo ɗakinmu sai aka canza min ɗaki aka kaini ɗaki mai lamba sha tara, a ranar na gwammace kiɗa da karatu, dan na shiga a lokacin babu kowa a ɗakin.
Har na fara tunanin ni kaɗai ne a ɗakin na samu wani gado na kwanta, saboda gajiya da aikin wahala da ke jikina, nan da nan bacci ya ɗauke ni ina cikin bacci sai dai na ji an zuba min duka a gadon bayana, zunbur na miƙe zaune wani basamude na gani tsaye a kaina, “Uban waya baka damar kwanciya a gadona.”
Tsananin azaba ya sa na ka sa motsi, “ba da kai nake ba ne,?” “ni ni ban san godon ka ba ne,” “Uban wa ma ya kawo ka ɗakin nan, sakko ka min bayanin kanka,” ya juya ya zauna a kan wa ta kujera, sumi sumi na taso na zo gurin sa na tsaya, gani na yi ya kalli wasu guda biyu a cikin ƴan ɗakin da suke tsaye, kawai ji nayi an kwashe min ƙafafu na faɗi kasa tim, “wayyo Allah na!” nace saboda azabar zafin da ya ziyarci kwakwalwata….
Kafin na gama rufe bakina na ji duka ta koina na rasa inda zan kare, kuka nake iya ƙarfina amma kamar ba sa ji, sai da suka min dukan tsiya sanna suka zaunar a gabansa, “ga ba ka ga yadda ake zama a ga ban manya, oya fara min bayanin kan ka da ga ina kake, kuma mene ne dalilin zuwan ka gidan nan.?”
Na fara magana “sunana Habib Abubakar ni hafaffen garin kano ne,” daga nan na basu labarina tas, ina rufe bakina wanda na ji suna ma laƙabi da sarki ya ce, “kai yanzu dan Ubanka akan mace kazo gidan maza, lallai kayi asara to yanzu wane mataki zaka ɗauka akanta da mijin nata,” “ni yanzu ba abin da zan kuma yi to yaushe ma na fita a gidan nan balle na ɗauki wani mataki, kawai na barma Allah.”
Hahahaha “yaro man kaza, ai bata isa ba dole ta amsa hukuncin cin amana, za ta ci amanar ka ne ta zauna lafiya, ai bata isa ba, duk da kai ma sha sha sha ne, na dauka wani laifin kayi a ka kawoka ashe a kan mace aka kawoka nan.”
“To ni yanzu mai zan iya yi akai, ban san mai zan yi ba shi ya sa, daga yau daga yanzu ka zama ɗan ƙungiyar mu, saboda haka muna maka maraba da shi go wa ƙungiyar shadow, ka zama member a cikin ta kuma dole ka zauna in kayi musu ba za ka kwana a duniya ba.”
“Inalilahi waina ilaihi raju'un!!, ran ka ya daɗe ban ma mu sa ba wallahi ina son rayuwata,” a taƙaice dai ranar da ƙyar na yi bacci gani nake da na rufe idona kamar zasu kashe ni din ne, sai da na kwashe wata uku a cikinsu sanna na fita a gidan nan, ina fita ko gida ban jeba aka ɗauke ni aka wuce da ni ƙungiyar su.
Ranar da a ka fara kisa a gaba na banyi bacci ba saboda firgici, buni buni zan farka Ina ihu ina ba ni na kashe ka ba, dan ranar hanyar Jigawa mu ka tare, duk wanda bai da kuɗi ko kayan kuɗi tofa sai