KECE SILA COMPLETE HAUSA NOVELS BY MINAL SAEED.docx

Author :  MINAL SAEED Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   3 / 12

6K to 9K   out of 34.2K words

ba, an kaimu gidan yari aka samu a wani ɗaki.

Abin mamaki sai na ga suna gaisa wa da Amir, ”ya oga Mir wanan Dan shilan fa tare kuke ne?, ”eh mana ai aboki na ne, ”oga ka ce sabon hannune?, ”bai san komai a harkar ba kawai azabar masu baƙaƙen Kaya ce ta sa ya amsa, kasan su basu da imani”.

Hahaha suka kwashe da dariya, ”oga ka ce mun samu karuwa kawai, ”anya kuwa koda inma bai shigo cikin mu baida mafita, tunda tsoho ya kore sa a gidan sa, shi kuma bai san kowa ba, ”ah oga Mir ai kawai wanna namu ne”.

Suka juya wani yare da ban taɓa jinsa ba, can wani ƙato a cikinsu ya dube ni yace zai iya abinda ake so mana, ”kai dan saurayi mai nene sunan ka?, ”sunana Abdul Jamal, “wow suna mai daɗi, kana son ka fita a gidan nan?, ”eh ina so dan Allah ka taimaka kamin, ”kwantar da hankalin ka, kai ne zaka taimaki kanka da kanka”.

“Ban fahimce ka ba, ”zan maka hanyar da zaka fita, amma da sharaɗi zaka dinga aiki tare da mu, ”kamar wa ne kalar aiki? ”akwai ogan mu da zaima bayani, amma har sai inka fita a gidan nan, ”to ka fara sanar min dan nasan ko wane aiki ne zanyi”.

“Hakane dan samari ka sani ba wani aiki mai wahala bane, raba kaya ne zuwa ga costormers din mu, “wasu kalar kaya ne?,”dallah malam maganar ka tayi yawa”, wani a ci kin su ya faɗi, ”ko ka fita ko kar ka fita damuwar kace ba tamu ba, nan daka ganni a yau nayi ni yar barin gidan nan ba zan kwana ba”.....

“KECE SILA”

(✍️Minal saeed)

(🌹MRS BASH🌹)

https://whatsapp.com/channel/0029VbBl22NAO7RLFvcUlU2g

https://chat.whatsapp.com/FuiNx6HvwgzAheM7xh0Xci?mode=ems_copy_t

://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*(J.W.A)*

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚

















(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)

"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa.

Page4️⃣

“ku bar sa ya yi kwana biyu zai fahimci gata muke ma sa,” su ka kwashe da dariya, sai muka ji ana buga ƙofar ɗakin ”dariyar Uban mai ku ke yi,” aka faɗi bayan an buga ƙofar, maimakon naga sun razana kamar yadda na razana sai naga sun zubama gandrober da ya yi wannan maganar harara, tare da faɗin bar nan kafin na sumar da kai.

Ban san rayuwata ta shiga wahala ba sai da dare yayi, cizon sauro da ƙuɗin cizo ya hanani bacci, suko bayin Allah nan baccin su suke yi hankali kwance, sai munshari mara daɗi suke sa ki, ni ko sai juyi nake yi sannan ga matsatsi a ɗakin, tashin hankali bai same ni ba sai da asuba na ji an watso mana ruwa mai sanyi.

“Ku fito dan Ubanku tun kafin na dawo”, aka buɗe ƙofar ɗakin, gashi ni ne a bakin ƙofa dan haka na fi kowa jiƙewa, haka na fito sharce ruwan fuskanta, nan aka ce muyi sallah bayan mun idar aka tasamu gaba, wani waje aka kai mu, duwatsu aka tara mana akace mu fasa shi, da wasu manyan guduma da ban taɓa ganin su ba, da ƙyar nake ɗagawa, haka muka fara aikin nan.

Mu ne bamu tashi ba sai shaɗayan safe, muka zo bin layin amsar abinci ana bani wani ya ƙwace, na yi ma sa magana ya kama ni ya min duka.

Sai da ya targaɗamin ƙafata, haka na tafi ɗaki ina ɗingisa ƙafa ta, suna gani na suka kwashe da dariya, abin mamaki ban tadda Amir ba, ko na ce tun da muka fita, ban ƙara ganin sa ba, ”da ka amince da sharuɗan mu, da yanzu tare da oga Mir ka fita, dan shi yanzu ya daɗe a gida ya na can ya na hutawa”.

Ni dai ban ce komai ba ba, dan a wannan lokacin wa ta azababbiyar yunwa ce ke damu na, da da hali kuka zan sa ka, ”ko yanzu idan ka amince zuwa gobe kamar wannan lokacin ka na gida,” dogon tunani na tafi shin idan na ci gaba da rayuwa a haka, nan gaba ya zan ka san ce, amma kuma wane kalar aiki ne zanyi musu idan na fita.

Tunanin da na ke yi kenan, ”da alamun wahalar da ka sha na kwana ɗaya baka ɗauki izna ba,” haka na kuma kwana na wayi gari wahalar yau daban ta gobe daban, azaba kala kala ga rashin abinci dan ko wani bai ƙwace ba, ba isa ta ya ke ba, amma su abinci mai rai da lafiya suke ci, in sunga dama su bani in basu ga dama ba ina kallo zasu cinye, a haka na kwashe tsayin wata ɗaya, da dare ya yi na sami wanda na ji suna kira da Gamji, ”Ranka ya daɗe na amince da maganar ka zan yi aikin tare da ku”.

Hhhhhh ya kwashe da wa ta dariya mara ɗaɗin ji ”kar ka damu Aj zu wa gobe za ka fita a gidan nan, ka na fita za ka sa mu wani a waje ya na jiran ka, kar ka damu ka bishi shi ne zai kaika inda za ka fara mana aiki, ya kuma yi ma bayanin kamoi, ”to Oga Allah ya kai mu”ameen.

Kamar yadda ya ce, da safe na ji an zo ana faɗin wanene Abdul Jamal Kasim, na ɗaga hannu, ”ta so ka biyo ni”, na bi bayan sa mu na zuwa aka bani wa ta takarda, aka ce nasa hannu, aka ba ni ka ya na da na zo da su na maida, sannan aka ce na tafi, kamar yan da Oga Gamji ya faɗi, Ina fita na ga wani a mashin ya na jira na, ya ce na zo na hau mu tafi haka na bi bayan sa ba musu.

Nan muka miƙi hanya a mashin ɗin, tun ina gane inda ake bi har na tsinci kai na a wani daji, can na fara hangar wani gida, abin mamaki da muka shigo gidan, ba za ki ce adaji gidan ya ke ba, dan babban gida ne ya ƙunshi komai na more rayuwa.

A ɗarare na ke binsa har muka shiga ci ki, mun wu ce falo na ɗaya da na biyu a na uku muka dakata, sai na za ma dan ƙauye dan tun da nake ban taɓa shiga irin sa ba, dan wani tanƙamemen falo ne mai ɗauke da royal chair, sannan a gyefe ga wa ta kujera kamar ta sarauta.

Idan na ce zan misal ta muku falon zan ɓata lokaci, a taƙaice dai falon nan duk in da ake neman haɗuwa ya kai, na zau na a gyefe na ta kure,can naji ana ana zuba kirari, cikin sauri na ɗago kai na, dan ganin wanene wannan, wa ni ma tashi na ga ni jikinsa duk a murmurɗe a gyefe da gyefensa ga wasu manyan mutane kamar samudawa, ko wanne ɗauke da bindiga, da ganin fuskarsu babu imani ko kaɗan.

Na rikice ɗaya a cikin su ya daka min tsawa “kai baka san sarki bane a gaban ka, da ba za ka miƙo gaisuwar girmama wa ba?, ”a yi haƙuri ran ka ya daɗe, barka da isowa sarki”, na faɗi muryata na rawa, ”mai ne ne sunan ka”, “sunana Abdul Jamal ran ka ya daɗe, “na san baka san dalilin zuwan ka nan ba, saboda haka yanzu zan maka bayani, sannan tunda ka ga maɓoyarmu dole ka kasance ɗaya daga ci kin mu, idan ba haka ba a bakin rayuwar ka”.

Rass na ji gaba na ya yi mummnar faɗuwa, ”ba komai ba ne kayan da zaka dinga raba mana sai, coken, da kananun bindigu idan an kawo, zan haɗaka da ɗaya daga ci kin yarana, Habib da zaku rinƙa aiki tare, ba a cin amana ta, ba a munafunta ta, daga yau suna ka Aj sannan duk sanda aikin dare ya tashi dole ka fita ayi da kai”.

“Sannan akwai wanda zai zo , zai zana ma ka tambarin ƙungiya a tsakiyar bayan ka, ”ka amince da sharuɗan mu ko kuma lahira za ka baƙunta, ”na na na amince”, na faɗi ba ki na na rawa, a raka shi ɗaki mutumin da mu ka zo tare yace na tashi mu tafi.

An yi training ɗina na tsayin wata uku, kafin na fara binsu aiki, kuma ina kai mu su kaya duk in da suka saka ni, kuma aduk lokacin da zasu fita fashi ana fita da ni, duk da ban taɓa kisa ba amma su suna yi, abin da ke sani kuka shine bansan halin da ƴanuwana suke ba, bana kuma da damar zuwa inda su ke, ya faɗi ya na share hawaye.

Hmmm na sauke ajiyar zuciya”haƙiƙa Jamal labarin ka abin tausayi ne, na tausaya maka, kai da ƙannenka, labarin ka nada taɓa zuciya, ”na gode ƴaruwa, sannan mai ne ne dalilin da yasa har Oga Habib ya ɗakko ki ya kawo ki nan gidan?, ”so ne sanadi, ”so kuma?”.

“ƙwarai So ne sanadin da na tsinci kai na a wannan halin, So ne sanadin da ya sa Habib ya raba ni da mijina, So ne sanadin daya sa Habib ya raba ni da iyayena, So ne sanadin daya sa Habib ya raba ni da ƴata Zainab, So ne sanadin daya sa Habib ya mai da abin da ke cikina maraya tun kafin ya shaƙi iskar duniya”.

“Amma wannan wane kalar So ne, da har zai sa ki cikin wannan halin?”, na buɗe baki kenan zan ba shi amsa sai muka ji tsayuwar motoci, alamun sun dawo ke nan, Jamal ya yi maza ya ta shi ya bar gurin, ni kuma na haɗa kai da gwuiwa, kamar yanda na saba,”Ishat ɗina ya ki ka wuni, na ga kamar ba kinyi kewa ta ba, Ishat dake nake fa, ba za ki kula ni ba?”.

KECE SILA”

(✍️Minal saeed)

(🌹MRS BASH🌹)

https://whatsapp.com/channel/0029VbBl22NAO7RLFvcUlU2g

https://chat.whatsapp.com/FuiNx6HvwgzAheM7xh0Xci?mode=ems_copy_t

://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*(J.W.A)*

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚

















(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)

"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa.

Page5️⃣

“Dallah Habib ka rufe min baki, wallahi in dai baka maida ni in da ka ɗakko ni ba, sai na kashe ka kuma kuma na kashe kai na, ”da kin birge ni Aisha, da ace ke ce za ki zama silar bari na duniya zan amince da hakan, ko ba komai masoyiyata ce ta yi a jalina, ”Habib na tsane ka, ”ni ku ma ina son ki Aisha”.

“Sulaiman haƙuri zaka yi ka barma Allah, dogon tunani ba zai yima magani ba, addu'a kawai ita ce magani, kuma ga shi jami'an tsaro kullum cikin bincike su ke, ”Hajiya bincikensu na banza bafa su taɓa zuwa da labari mai ɗadi akan inda matata take ba, hasalima ni ina kyautata zaton Aysha na hannun Habib, su nemo sa wallahi zai fito min da matata”.

“Haba Sulaiman bai kamata ka raina ƙoƙarin su ba, su na bakin ƙoƙarin su, kullum cikin bincike suke har gidansu Habib ɗin sun je, Babansa yace rabon sa da shi shekara biyar ke nan, to ya kake son su yi, yanzu haka ance jinin ka na neman hawa, amma kaƙi kwantar da hankalinka, yanzu idan kaje ka mutu fah, ita Zainab ta zama marainiya ke nan ba uwa ba uba, haba Sulaiman ka miƙa ma Allah al'amuranka”.

Cikina na ta girma dan yanzu ya shiga wata biyar,Habib ya ɗakko likita tana kula da ni,dan yace baya son wani abu ya sameni, saboda shi ke da asara, abinci mai rai da lafiya ake aje min bana komai, da na motsa likitar nan zata ce maine ne, ta na kula da ni kamar kwai, a haka wani aiki ya taso musu ana saura kwana bakwai su tafi dukda sunce babban opretion zasu je dan haka ba zasu fita da yara ba.

Kafin tafiyar su Jamal ya daɗe da jin labarin tafiyar su, dan haka ya nemi zai je ganin gida, dan tunda yazo bai taɓa zuwa ba, dan haka ba musu aka ba shi izinin tafiya, aka bashi kuɗi kimanin dubu ɗari biyar ya yi kuɗin mota da na tsaraba, ya yi godiya ya tafi.

Bayan sati ɗaya”Aisha zan tafi kiyimin adu’ar, na yi dariya amma ta baƙin ciki, “wa zan ma adu’ar kamar wanda zai je neman halal, ai ni babu sauran aduar alkairi a tsakanin mu sai sharri, kuma ko baka nema ba zan maka, dan haka sai ka shirya, ya Allah ka tozar ta wannan bawan naka kamar yadda ya tozar ta aurena, ka hanashi abin da yake so, ka wulakanta shi ka lalata duk wani shiri da yake da shi akan bayin ka, kar ka ba shi abinda yake nema”.

“Aisha iya kar adu’ar da za ki iya yi min kenan?, ni kuma yan zu zan yi mi ki tawa, ya Allah ka san irin son da nake wa wannan baiwar ta ka, Allah ka mallaka min ita, Allah ka bani ita ka mallaka min zuciyar ta, Allah ka na gani a sanadin son ta na zama haka, ”kar ka kara cewa a sanadin so na ka zama haka dama can a haka ka ke”.

Bayan awa uku da tafiyar su ina zaune ni ka ɗai na ji motsi a baya na, da sauri na juya dan na tsorata, amma abin mamaki sai naga Jamal, Jamal ya sa hannu a bakin sa alamun na yi shuru ”shhhh, ta so ki biyo ni, na nuna kaina da hannu ya kaɗa min kai alamar eh, na ta shi na bi bayansa yana gaba ina bayansa.

Haka muka fara tafiya a cikin gidan nan, muna yi muna leɓawa kar a gan mu, dan ma dai mafi yawan su sun fita wasu kuma an tafi aiki da su, har muka iso bakin ƙofar falo na biyu ba wanda ya gan mu, muna shirin buɗe ƙofar muka ji takun tafiya, cak muka tsaya Jamal ya fizgo hannu na muka shige wani ɗan lungu mai duhu, ƙirr karar buɗe ƙofa ta ratsa kunnuwan mu.

Rass gabana ya faɗi, dan ɗuk da Jamal bai min bayani ba, na fahimci taimako na zai yi, na sa hannu bibbiyu na toshe bakina, saboda ganin wanda ya shigo ya nufo inda muka ɓoye, kamar an canza mai hanya kuma ya juya ya nufi ɗaya bangaren da saurin sa, muna ganin haka Jamal ya ja hannuna da sauri muka yi falo na ɗaya, muna zuwa ƙofar falon Jamal ya bani fece mark ya min alamu da hannu akan na sa.

Na saka fece mark din sai ya buɗe ƙofar kaɗan, ya jefa wani abu da ban san ko mainene ba, muna laɓe a bayan labule ya na yi ya na duba agogon hannunsa, mu kwashe wajen minti talatin dan har na fara gajiya da tsayuwar, sai naga ya ƙara buɗe ƙofar ya leƙa a hankali, can kuma sai ya ja hannuna muka fito abin mamaki duk mutanen gurin sun yi bacci.

Nan ya laluba jikin wani sai ga makullin get, ya dauka da sauri ya buɗe ƙofar, ya ce mu tafi ba muda lokaci sosai,muka fito munyi tafiya sosai kafin na ga ya tsaya a wani waje ya na buɗe ciyayi, can sai naga mashin ya kunna ta yasa hular kwano nima ya bani ya ce na sa.

Na saka ya tada mashin din, gudu ya ke tun ina kallon hanya har na gaji da kallon hanya, can na ji ya ja birki ya ce dam it, na dago kaina mai zan gani motoci na hago a gaban mu amma suna da ni sa da mu, ban ƙarasa tunanin da na fara ba akan motocin daga Ina suke, na ji Jamal ya yi wani irin juyi da mashin ɗin muka sake nausawa cikin daji.

Gudu ya ke ashe motocin nan na biye damu a baya, tunda nake ban taɓa ganin tashin hankali irin na ranar ba, dan Jamal tuƙi yake bawai dan ya san ina yake bi ba, can na fara jin ƙarar harbi ban san sanda na ƙanƙame Jamal ba, Jamal ya juya ya jefa musu bom ƙura ta turniƙe su a haka muka samu muka can za hanya.

Muna cikin gudu muka zo bakin wani babban rafi, tare muka juya dan jin ƙarar motocin nan, babu wata mafita da ta wuce mu faɗa rafin nan, “kin iya ruwa?, ”a'a “bamu da wata mafita bayan mu shiga ruwan nan ina son in tseratar da ke, Jamal ka tafi na gode da ƙoƙarin ka a kai na, in suka riske ka a nan zasu iya kasheka”.

“A'a Allah zai taimake mu, mu na sauka

3 / 12