Author : MINAL SAEED Category : Romantic Hausa Novels
ginawa
Page2️⃣1️⃣
Hadar
“Yaya Jamal ni fa naga iri, iri kuma tsaya ma na ji kamar da Yaya ka kirani waye Yayan naka,? amma a nan kasan kai ka ɗai ne Jamal ko, to da kai nake waccan ƴar black beauty din, in babu wanda ya rigani kai wallahi ko da kwaima sai ya jira ni, dan sai ya matsa ya bani hanya dan dama ta wace, kai to waya ce ma zanma ƙawata auren dole, abokina mu cire batun wasa wallahi ta tafi da zuciyata, ban mu sa maka ba amma ka fara neman soyayyarta, in har ta amince ni kuma zan tsaya ma sai ka aure ta.”
Ya rungume sa yana murna, “dallah malam sake ni ka manta ni yanzu surukine, naushi ya kai ma sa a ciki ya ce, kar ka ji na kira ka da Yaya kan rainani, wallahi kasan halina zaneka zan yi, ka zaneni ni kuma na hanaka ƙanwata, haba sirikina Kar mu yi haka da kai.”
Jamal dai yace Haidar ya nemi soyayyar Iklima, shi bazai ma ƙanwarsa auren dole ba auren gata zai ma ta, taro ya ta shi lafiya sai murna a ke yi, an basu hutun sati biyu kafin kowa ya zo ya kama aiki.
Raziƙa
“ke ƙawata nifa Ina ga nanda kwana biyu zan tafi gida, dan ni in ba wannan gayen ba ina ga babu ni babu aure har abada, Razi yanzu tafiya za ki yi ki bar ni, idan fa shi ba ya son ki mu muna son ki, mu yi zaman mu kawai ba sai kin koma gida ba dan ni kin gan ni nan ni da gida har abada dan na barsa ke nan, ni fa bama ki fadamin labarin ki ba, ki bar maganar nan dan labarina bai da daɗin ji.”
“Zee ke nan ke dai ki ce ba za ki faɗa min ba ka wai, sai a wuce gurin, dan na lura da duk sanda na tambaye ki labarinki sai kin kauce, a’a ƙawata ba haka ba ne kawai labarin ne bai da daɗin ji amma ki zauna dan Allah zan faɗi miki komai a rayuwata zan ba ki labarin wace ce Zainab.”
Wace ce Zainab ko na ce muku Zee Kamar yadda mukaji ana kiranta.
Ni ƴar a salin garin Katsina ce, ni marainiya ce, Mamana ko kallon farko bata min ba, ta na haihuwata Allah ya amshi rayuwarta, Mahifina Malam Iliya ya shiga damuwa sosai a sanadin haka har ya kamu da ciwon zuciya, ya yi daguwar jinya wacce ta kusa lashe duk abin da ya tara, a wannan lokacin ni kuma ina hannun ƙanwar Mamana tana shayar da ni tare da ɗanta mai wata takwas a duniya, ina da shekara ɗaya dai dai a duniya Mahaifina ya ce ga garin ku nan.
Ƙanwar Mahifiyata tana tsananin so na, domin dai ita Allah bai ba ta haihuwar ɗiya mace ba, dan haka take nuna min soyayyarta a fili, ina da wata sha tara ta yaye ni, Kakani na na gurin Uba suka nemi a basu ni tunda an yaye ni, Inna Hajara ta ce sam ba ta yarda da ta basu ni ba, nan aka fara rigima da ita a kan dole ta bada ni ita kuma ta hana.
Kakata tana zuwa har gidan taci ma ta mutunci, Inna Hajara bata kula ta da tace ita ba zata yi faɗa ko cacar baki, da wacce da haifi kamar ta ba, amma kuma ba su isa su raba ta da Zainab ba dan ita take wa kallon ƴar'uwa, da suka ji haka sai suka can za salo, takakkiya suka yi su uku da kakata da matar ƙanin Babana da ƙanwar Babana, suka zo suka sa Inna gaba da zagi da cin mutunci ita dai tana jin su ba ta kula su ba, da suka ga batada niyar kula su sai suka fita.
Ashe gidan su Inna suka tafi sun sami Hajiya Uwa kakata mahaifiyar su Inna ke nan, assalam alaikum wa alaikasalam, ku ne a gidan sannu ku ku shi go, dakata Uwa mu shiga ina, to ba zama muka zo yi ba kashedi na kawo, akan waccan mayyar ƴar taki Hajara ƙi ce ta bani jikata, daga an bata ƴa ta shayar sai ta kama ta riƙe haka a keyi, to ni dai ban yarda da wannan mulkin mallakar ba, dan haka aba ni jikata ko hukuma ta shiga ciki aiba haka ake yiba.”
Uhm “Ladidi ke nan ke yanzu akan jikar taki, ki ka zo har gidana ki na ci min mutunci, a’a fa Maman Hajara wannan ba maganar cin mutunci a ciki, ƴa dai ta muce kuma mun ce a bamu to a bamu mana, aga in zamu ƙara zuwa wannan kangon da ki ke wa laƙabi da gida, Allah na tuba ni ko sanda Yaya ya auri Zainab, ai ban so ba wallahi ga ƙawata nan ƴar gidan Galadima, da take masifar sonsa amma ya ƙi ya na cewa ƴarki, saida ya aure ta hankalinsa ya kwanta, da ta mutu gurin haihuwa kuma, ba shi ke nan ba amma da yi ke an riga da an asirce ma sa zuciya, sai da ya mutu ya bita sannan hankalin ta ya kwanta, don haka kawai ku bamu tamu ƴar.”
“Shi ke nan ku yi haƙuri in sha Allah zan kawo muku ƴarku har gida, da dai yafi dan za mu iya riƙe ƴarmu, da daddare Hajiya Uwa ta shirya ta tafi gidan Hajara ta je tai ta rarrashinta, ta ce Hajara ƙi yi haƙuri ki basu Zainab, dan kin basu ita ba yana nufin kun rabu ke nan ba, Zainab ƴarki ce ko a lahira, sannan yanzu a duniya ba ta da kamari, amma Umma kwata kwata Zainab din nawa take shekararta biyar fa, kuma kinsan ba za su iya yi mata riƙo da zan mata ba, na sa ni Hajara amma kwanciyar hankalinki nake dubawa, ki daure ki ba su ita Allah na tare da ita, idan sun cutar da ita su da Allah.”
Haka Hajiya Uwa ta lallaɓa Innata ta na kuka Ina kuka ta haɗa min kayana a ganamasgo, Hajiya Uwa ta kama hannuna Ina kuka Ina waiwayen Innata haka muka tafi dan ba yadda zanyi, “assalamualaikum, wa’alaikissalam, shigo, Ladidi ba zama na zo yi ba na kawo muki jikarki ne kamar yadda kika buƙata, ga Zainab nan in kun riƙeta tsakani da Allah ku kuka sa ni, in kun ci amanar marainiya ku da Allah, dan haka na barki lafiya.”
Hajiya Uwa ta ajiye jakata tare da sakin hannuna, ta juya ta tafi ina kallon ta amma ban da halin binta dan gwada bin nata Uwani da daga min tsawa, dole na ja na tsaya ina shashekar kuka, “dallah rufe min baki kafin na miki shegen duka, ai yadda kika shi go gidan nan kin shigo ke nan ko Uwarki ce ta dawo daga kabari ba ki isa ki bita ba,” na sake fashewa da kuka, “Uban waye yake ma mutane kuka?.”
KECE SILA
(✍️Minal saeed)
(🌹MRS BASH🌹)
https://whatsapp.com/channel/0029VbBl22NAO7RLFvcUlU2g
https://chat.whatsapp.com/FuiNx6HvwgzAheM7xh0Xci?mode=ems_copy_t
://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa
Page 2️⃣2️⃣
“Yauwa Nasiru gara da Allah ya shi go min da kai, wannan ƴar iskan yarinyar ce ta tasani gaba da kuka saboda na karɓota da ga hannun Hajara,” “au…., dama ba abun da aka mata take kuka?,” “kai ko ban da abun ka mai za'a mata shagwabace da an riga da an koya mata, ni kuma ba zan ɗauki raini ba dan haka gara tun wuri ki shiga hankalinki, in ba haka ba na sa Nasiru ya ɓallamin ke,” mits ta ƙarasa zancen ta da tsaki.
Tun daga wannan ranar na san ba nida sauran gata a duniya, dan abincima sai da ƴaƴan gwaggo Salamatu, Maman su Nasiru suka ci suka rage aka bani sauran, haka nan na amsa naci na sha ruwa badan na ƙoshi ba sai dan ba mai ƙaramin ko na nema, gurin kwanciya ko ɗakin Mamana aka buɗe min aka jefomin kayana, haka na kwanta babu ko zani a tantagar yar sumunti, daga nan babu wanda yabi ta kaina, cike da tsoro na kwanta ban iya bacci ba tsabar a tsorace nake, sai da asuba bacci barawo ya saceni.
“Ke Zainabu uban waye kike jira ya tashe ki, to maza miƙe ki je ki ɗebomin ruwa a rafi, ki cika min bokitan nan yanzu nan,” “Inna banyi sallah ba,” “to waya hanaki saiki fara ɗebomin ruwana sannan duk abun da zakiyi ki yi, Tasalla matar Liman” haka na amshi bokitin da take mikomin, tun bakwai saura na fara ɗiban ruwan nan, nice ban gama ba sai ƙarfe tara na safe
Ina gamawa ta haɗomin wanke wanke “Inna yunwa na ke ji,” “ko zan baki abinci sai kin gamamin wanke wanke tunda ba ke kika nemomin abincin ba.”
“Inna dan Allah ki bani abinci in naci sai na miki aiki,” tass ta wanke ni da mari “ina magana kina magana ni sa’ar ki ce,” nasa kuka a taƙaice dai sai da nayi wanke wanken nan sannan tabani abinci shima badan na ƙoashiba, ina gama ci na rakuɓe gyafe ɗaya, tun daga ranar dana shi ga gidan nan na fara wahala aiki har wanda yafi ƙarfina, abinci sai ta ga dama take bani na ƙoshi, ranar da na samu sa'a sun je dubiya a sibiti na fita na tafi gidan innata ta min wanka ta bani abincin naci in da na gama cin abinci a nan bacci ya kwashe ni.
Ban farka ba sai ƙarfe biyar na yamma, aiko a gigice na farka ina tashi Inna Hajara na ban ɗaki, na tsaya daga bakin ƙofa nace Inna na tafi gida, ina ji tana gyaran murya na ƙi tsayawa dan ni kaɗai nasan irin azabar da zan sha, a gidan nan yau aiko ina shiga gidan na tadda Nasiru da su Inna Ladidi a tsakar gida, “ai yau saina ku sa karya yarinyar nan a gidan nan, sai ta faɗi daga in da take,” “to ke Inna ki ma yi aduar Allah ya sa ba wani ƙaton ta bi ba dan kwana biyu naga rawar kai take yi, ko dan ta ga ta fara girma ne oho.”
Ina jin haka gabana ya faɗi, dan nasan yau babu mai kwata ta a hannunsa sai Allah, dan dama haushina ya ke ji jiya ya sani gyaran ɗakinsa naƙi yi, sannan naƙi bari mu haɗu da shi, ni kuma abun da ya sa bana son shiga ɗakinsa in yana nan, dana shiga sai shima ya shigo ya dinga tattaɓamin jiki, ranar dana ce ma sa babu kyau malamin islamiyarmu ya ce ba kyau ka dinga yarda wanda ba miji ka ba ya dinga taɓa ka, sai da ya fasa min baki na.
Ba yadda zan yi haka na shiga gidan, aiko ina shiga ya janyo ni ya fara duka, ina ta kuka ina basu haƙuri amma ba wanda ya kalle ni, sai da ya min dukan tsiya Sanan ya bar ni, na ta shi ina dingisawa na tafi ɗakina, saboda jikina ko ina ciwo yake min, na ci kukana na rarrashi kaina, lokacin shekarata sha uku, amma ayyukan gidan nan ga ba ɗaya ni nake yi bana samun hutu ko kadan.
Ranar da ba zan taɓa mantawa ba itace ranar da, dukkan ƴan gidan sunje bikin ɗiyar yayar babana, Nasiru ya shi go ina ganinsa gabana ya faɗi dan yan zu bana son abun da zai din ga hada mu guri ɗaya da shi “ke zo nan ki gyaramin ɗakina,” “Yaya ai na gyara ma tun da safe,” “eh ai na gani bai yi min bane sabo nake son ki sake, ko ba za ki yi ba ne?.”
Haka na tafi gabana na faɗuwa, na shiga ɗakin, a iya ganina babu abun da ke buƙatar gyara a ɗakin nan, dan fes yake kamar ma bai shi go ɗakin ba sai yan zu, sanin ba yadda zanyi na ɗauki tsunman da nake ma sa goge goge da shi, na fara goge in da naga kura ta sauka, burum na ji ƙarar rufe ƙofa, da sauri na wai go Yaya Nasiru naga ni tsaya a bayana daga shi sai gajeran wando, da sauri na rufe idona, “munafukar banza, dallah buɗe idanunki ki kalle ni, miye ba ki sa ni ba ko kuma ni za ki raina wa hankali.”
Ya zo ya ɓanɓanre hanayena dana rufe fuskata, jikina banda rawa ba abun da ya ke yi, ya sa hannu ya shafa gyefen fuskata, da sauri na kauda kaina, “wallahi in ba ki tsaya ba saina ballaki ki san dai babu kowa a gidan nan daga ni sai ke,” “dan Allah Yaya ka bari wallahi babu kyau,” kafin na gama rufe bakina ya karasa haɗa jikinsa da nawa, in taƙaice miki Razi a ranar nan ya min fyaɗe, kuma ya ce idan na faɗi sai ya kashe ni, babu imani a tattare da shi ba tausayi haka ya rasa jikina, bai duba ƙara cin shekaruna ba.
Naci kukana babu meceto na a gurin sa sai da ya ga dama ya barni dan kansa, amma haka da Kakarmu ta dawo tace yawona na banza dana saba naje, ban da ikon buɗe baki na faɗi gaskiya, haka aka sa Nasiru ya yi min dukan tsiya, babu tausayi babu imani, ranar na roƙi Allah ya ɗauki rayuwata na huta, saboda baƙin ciki na kira Uwata da Ubana dan nasan da suna raye da haka bata faru dani ba ranar naga ilar maraici.
Haka na lallaɓa na ja jikina na koma ɗaki, Maryam ƙanwar Nasiru Itace ta faki idonsu ta kawomin magani, da ruwan zafi tace na shiga dan dama tana nunamin alamun tausayi, Mahaifiyarsu ce ke hana ta don wani lokacin har dukan ta take yi saboda ni, ta bani haƙuri tace ta san mai ya faru, dan ta dawo gida ɗaukar mayafinta a Lokacin da yake ɓatamin rayuwa.
KECE SILA
(✍️Minal saeed)
(🌹MRS BASH🌹)
https://whatsapp.com/channel/0029VbBl22NAO7RLFvcUlU2g
https://chat.whatsapp.com/FuiNx6HvwgzAheM7xh0Xci?mode=ems_copy_t
://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa
Page 2️⃣3️⃣
Haka na ci gaba da lallaɓa rayuwata, shi kuma Nasiru ya maida ni kamar matarsa, duk sanda ya ɗebo buƙatarsa a kaina yake sauke ta, tun ina kuka har nazo na haƙura, na fawwalawa Allah komai, kwatsam sai ga ciki ya bayyana a jikina, na shiga tashin hankali mara misaltuwa, suka ce sai na zubar da cikin na ce ba zan zubar ba, duka zagi tsinuwa babu kalar da ban gani ba, amma na ce saina haife sa dan su san ko ɗan waye, laulayi mai zafi nake yi ga rashin gata aiko duk na lalace, haka na fara shan fura ita nake iya sha, a haka
suka yaudare ni suka samin maganin zubar da ciki, ba tare da na sa ni ba na sha furar nan, ban san hawaba ban san saukaba ina Bacci Naji azababben ciwon mara da baya ya turnuƙe ni.
Suna ji ina ihun neman taimako ba wanda ya bi ta kaina balle ya taimaka min, a haka jini ya gocemin tun da sauran ƙarfina, har na rasa ƙarfina ƙarshe na suma a gurin, saida suka ji shurun ta yi yawa suka leƙa dakin, suka ganni a sume daga nan suna ɗauka ta sai asibiti, likitoci sukayi bakin ƙoƙarinsu da ƙyar suka ceto rayuwata ciki kuma ya fita burinsu ya cika, na sha daguwar jinya dan saida aka samin jini, satina biyu a asibiti na ji sauƙi aka sallamoni, ina dawowa suka ƙara lodamin aikin da nake yi, dan koda na ke laulayi bawai na daina bane, ga zagi ga cin mutunci har karuwa suke kirana.
Wahala tayi wahala cikin dare na gudu na bar garinmu, a ranar a tasha na kwana da