KECE SILA COMPLETE HAUSA NOVELS BY MINAL SAEED.docx

Author :  MINAL SAEED Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   2 / 12

3K to 6K   out of 34.2K words

/>
A nan suka gano cewa ai tsohon case ɗin suma gurin su yake, dan wannan karon shi ne kashi na biyu da Habib ya gwada kashe Sulaiman, lallai Sulaiman na da tsayin kwana a duniya dan wancen karon da wuƙa ya so kashe shi shine sanaɗin da ya tafi gidan yari har na tsayin wani lokaci, shine ya dawo ya ƙara kawo ma sa hari, lallai wannan case ɗin babban ne.

Haka na ci gaba da rayuwa a hannun shi, har na zo na saki jikina, amma duk da haka ban fasa neman sa’ar guduwa ba, na ci gaba da zama da su tun ba na sakewa a cikin su, har na saba da su, mukan zauna mu yi hira da su,a cikin su akwai wani wanda na lura da shi,lokuta da dama ya kan zauna ya yi zurfi ci kin tunani,har ya kan share hawaye jefi jefi.

Ranar wata laraba sun fita aiki a cewar su, suka barmu mu biyar, ni da wannan saurayin, sai kuma wata buduruwa sai Maza biyu, ya na zaune ya na aikin tunanin na shi da ya saba, har hawaye na ta zuba a idon shi, sai na matsa kusa da shi, duk da nasan ya girme min sannan a tsarina,bana shiga abin da bai shafe ni ba, amma haka nan na ji ina son sanin damuwar shi.

“Ɗan uwa, kai ko mai ya sa kusan kullum sai ka yi kuka ne,ni na dauke ka a matsayin Yayana, haƙiƙa duk lokacin da na ganka a wannan halin ina shiga halin damuwa ni ma,da farko dai zan so na san wane ne kai,?kuma mai nene dalilin da yasa ka tsinci kanka a cikin su Habib?, dan na ga duk lokacin da za su fita kai kuma baka bin su.”

Sai ya kuma fashe wa da kuka, na din ga rarrashin shi har ya yi shuru,”haƙiƙa tunda nake ba wanda ya taɓa tambayata, dalilin kasancewa ta a cikin su sai ke,kuma yanzu zan sanar miki, ko dan na sauke nauyin da yake zuciyata.

“Suna na Abdul Jamal, na taso a hannun iyayena duka biyu, na taso cikin gata ni da ƙannena su uku, Mahaifiyarmu mu huɗu ta haifa, duk da mu talakawa ne amma iyayenmu na ba kin ƙoƙarin su wajen sauke nauyin da ya rataya a kansu, ni ne ɗansu na farko sai kanina Abubakar, sai mai bi masa Haruna, sai autar mu Iklima.

Iyayen mu talakawane kamar yadda na sanar ma ki, Babanmu sana'ar gini yake yi, hakan ya sa mahaifiyarmu take ƙulla kayan miya a cikin gida ta na siyar wa, a haka su ke rufa ma kan su asiri,tare da sauke duk wani nauyinmu ni da ƙannena, na kammala makarantar secondary ya yin da Abubakar yake aji ɗaya a babbar secondary sai Haruna yake aji uku a secondary, Auta ta na agaji Shidda a primary.”ya ci gaba da ba ni labarin shi.

"Mahaifiyarmu ta kamu da rashin lafiya mai tsanani,hankulanmu sun tashi sosai, muna ta faɗi tashi akan yadda za ta samu lafiya, amma ciwon bana tashi ba ne. ya share hawaye ya ci gaba,

"A kwai wata ƙawarta da take taimaka mata wajen kula da mu, ganin irin kulawar da muke samu, yasa Umman mu ta cewa, mahaifina ya auri ƙawarta bayan mutuwarta, dan ciwon ta bana tashin ba ne.

Hankalin mu ya tashi sosai, muna ta kuka muna faɗin

" A'a “Umma za ki tashi da yardar Allah, ba ta wayi gari a wannan ranar ba, mai kira ya kira kuma ta amsa,mun yi kukan rashin Mahaifiyarmu, dan mun yi rashi daga mu har Mahaifinmu,haka ƙawarta kullum ta na hanyar gidanmu tana rarrashinmu.

Har aka yi adu’ar arba'in din k'awar Mahaifiyarmu, bata dai na yi mana hidima ba, wata ɗaya biyu shiru Babanmu bai ƙara ta da maganar da Mahaifiyarmu ta yi akan ya auri ƙawarta ba, ni kuma a matsayi ne na babba ganin hakan, ya sa na je gidan kakaninmu nasanar musu, suka kira sa suka ƙara tunatar da shi.

Aka ta da maganar biki aka sa sati biyu, an d'aura musu aure a wata Juma'a a Masallaci,da farko Mahaifinmu ba ya wani kulata, amma ganin irin kulawar da take bamu,yasa shi ma ya fara kulata, baiwar Allah nan da muke wa laƙabi da Mama, watanta Shida agidan nan,ta fara fito mana da ainihin halayen ta.

Babanmu zai fita ya nemo abinci, amma sai ta hana mu, mun sha kwana da yunwa, ga shi Haruna ya na da ciwon ulcer, idan ta hanamu abinci bayan ta shiga ɗaki sai na je na ɗebo na ba su su ci, ban damu da na. ci ba, ga shi ni kaina ba wani aiki nake yi ba, garejin gyaran mashin na fara zuwa shi ma ni nasa kaina.

Sai ta fara min sharri wai ina ma ta sata, ranar sai da Babanmu ya min duka, a lokacin da Mahaifiyarmu ke raye ko faɗa ba ya mana, amma yau shi ne ya min dukan da ban taɓa ganin an yi ma wani kalar saba, na yi kuka haka ma ƙannena sun yi kuka, lokacin sai da muka yi kukan maraici Umman mu.

Lalai Mama bata riƙe alƙwari ba,dukan da tasa aka min bai hana idan ta hanamu abinci,na ƙara ɗebowa ƙannena su ci ba,watarana na d'ebo musu abincin ta zo ta same ni cikin fad'a take cewa.

"Abdul Jamal Ubanka ya ce ka taɓa min tukunya? “Mama gani na yi ga abinci kin hanamu rabon da ki bamu abinci tun jiya, ga shi Haruna na da ulcer ina gudun ta tashi dan wahala yake sha....”Ta tari numfashina

"Ya mutu mana ina ruwana, duk ranar da na ƙara yin abinci ka ɗibar min abinci sai ka ga abin da zai biyo ba ya.......



KECE SILA”

(✍️Minal saeed)

(🌹MRS BASH🌹)

https://whatsapp.com/channel/0029VbBl22NAO7RLFvcUlU2g

https://chat.whatsapp.com/FuiNx6HvwgzAheM7xh0Xci?mode=ems_copy_t

://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*(J.W.A)*

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚

















(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)

"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa.



Page3️⃣

“Mama kar ki manta cewar mu amana ne a gurin ki,”amanar banza amanar wofi, I dan kayi wa sa kai ma sai ka barmin gidan nan dan naga alamun kai zaka bani matsala, ”ni da gidan Ubana ba wanda ya isa ya kore ni, wallahi kinci arzikin Mahaifiyarmu, da ba ki riƙa mana abin da ki ke yi ba,”ni ka ke faɗi ma haka?, ”an faɗi ki yi abin da za ki yi”.

“Eh lallai Jamal ka kawo ƙarfi, amma ba laifin ka ba ne, zan ɗauki mataki akan hakan, ”mtss” na ja tsaki na wuce, tun daga wannan ranar ta ƙara tsananin ta a gare mu, makirci kala kala, tun Mahaifina mu na duka na ni ƙaɗai, yanzu dukkan mu ya ke duka.

Ranar da bazan taɓa manta wa ba, ita ce ranar da ta zama silar ƙaddarata, silar halin dana ke ci ki, wacce aduk lokacin da na tuna na ke kuka, ranar da Mahaifina ya kore ni a gidan sa, ranar da hatta da Mahaifiyata sai da ya zage ta, ranar da aka rabani da kannena.

Ya cigaba da kuka, ni ma duk da bansan mai ya faru ba sai da na taya sa kukan, ya share hawaye ya cigaba, wata ranar talata da yamma sai ga yarinyar Mama da da bari a gidan tsohon mijinta, tashi go da kaya niƙi-niƙi, ni dai ko kallo bata ishe ni ba, saboda na santa ba ta da kunya ko kaɗan, da dare na ji Mama na ma Abban mu bayani, wai Raziƙa ta dawo nan da zama, saboda can matar Baban ta tasa ta gaba da zalunci.

Ɗakuna uku ne a gidan mu, ɗaya ni da kanne na maza, ɗaya Kuma Iklima ce aciki, Abban mu ya ce ba damuwa ai sai ta zauna ita da Iklima, haka aka yi ta ko ma ɗakin Ikilima, sai dai fafur ta hana Iklima kwana a katifa, haka ta haƙura ta na kwanciya a ƙasa, ga shi ita ce wankinta ruwan wankanta, a taƙaice dai duk wa ta wahala Iklima ke yi a cikin gidan nan.

Hatta da makaranta Mama ta hana ta zuwa, muna gani ba yadda zamu yi sai dai mu bata haƙuri, tayi kukanta mu rarrashe ta, haka aka kwashe tsayin wata uku a gidan, ba wani cigaba sai dai baya, ”Jamal ni fa Wallahi son ka na ke yi, ”Ke Raziƙa ni sa’an wa san ki ne, kin ga tunda ki ka zo gidan nan ina kulaki ne?, dan haka ki shiga hankalin ki”.

Mafarin ƙaddarata ke nan, yarinyar nan ta nace min kullum ina kyararta amma bata ji, bata gani a kai na, ni kuma na tsane ta ita da Uwarta,ranar Ina zaune Mamanta ta shigo, “Kai Jamal ka fita hanyar ƴata, idan ba haka ba wallahi sai na ɓata ma rai, ”ke za ki jawa ƴar ki kunne, ta fita harka ta, ai na faɗi ma ta bana son ta, kuma ko mata sun ƙare ba abin da zan yi da ƴar maci amana”.

Tass da ɗauke ni da mari, na tsaya ina kallon ta ”ko za ka rama ne?, ”ba zan rama ba amma akwai ranar ƙin dillanci, ”ƙaramin mara kunya kawai, ai na zaci rashin kunyar taka ta fi haka, ”ai ban gaje ta ba ne shiyasa,” na bata amsa tare da juyawa na fita a gidan baki ɗaya.

Lokuta da dama har mamaki nake yi, akan rayuwar da mu ke yi yanzu, kwata kwata bamu da gata, Allah ne ke son mu badan haka ba da mun daɗe da mutuwa, duk da wani lokacin ina mana aduar mutuwa, dan sai naga kamar za tafi zama hutu a gare mu, sannan gaba daya dangi da ƴanuwa kamar sun manta da mu, mu kuma kamar an hana mu zuwa inda suke.

Ina zaune ne a ɗakina Raziƙa ta shigo, “ke fitar min a ɗaki, ”ina ɗakin yake a nan, wannan kangon ne ɗaki, ta yi dariya da ace zaka so ni, dana fitar da kai da ƙanenka da ga halin da kuke ci ki, ”ke ba ki isa ki min abin da Allah bai yi min ba, kuma ki faɗiwa azzalumar uwar ki, ni Jamal kafin Allah ne, bata isa ta min abin da Allah bai yi min ba”.

“Kar ka sa ke zagar min Uwa, ”an zage ta kiyi abin da za kiyi, ”ni ba wannan ba dan Allah ko ba zaka yi soyayya da ni ba, ka bani lokacin ka wallahi na daɗe ina son na ka sance da kai,” Tass na gaura ma ta mari, ”a tunanin ki kowa ma fasiƙi ne kalar ki?, to ni ɗan sunna ne ba dan zina ba, dan haka ki je ki nemi fasiƙi irin ki”.

“Ni ka mara, dan nazo na taimaka ma?, ke jaka fita ki bani guri banza yar bariki kawai karuwa, hmm tayi murmushin mugunta ”yanzu zan nuna maka halin ƴan bariki, zaka ga halin karuwai yanzun nan, ta ɗora hannu a kai ta fasa ihun da ya ratsa gidan ta ko ina, sai da na toshe kunne na.

Sanan ta yaga wuyan ɗan ƙaramin hijabin da ke jikinta, ta yi jifa da ɗankwalin ta, na tsaya kawai ina kallon ta, sai ga Mahaifiyarta ta shigo,”lafiya Raziƙa ki ke ihu, ta sa kuka “Mama Jamal ne, ”Jamal kuma mai ya yi mi ki?, ta sa hannun ta janyo ta tana dudduba ta can ta sa ki salati, ”Jamal kar dai iskan cin naka ya zo kan ƴata”.

Wani mugun kallo na bita da shi daga ita har ƴar ta ta, ”Mama dan yace ya na so na na ƙi, shi ne ya ce sai ya lalata min rayuwa yaga ya zan yi, sannan akai na zai ɗauki fansar abin da ki ke ma sa shi da ƙannensa”.

“Inalilahi waina ilaihi raju'un!, Jamal dama haka kake, to wallahi bari malam ya zo, ko ya ɗauki mataki kona bar ma sa gidansa, dan bazan yar da a lalata ma ƴata rayuwa a banza ba, haka kawai ƙato da kai ka nemi haikewa yarinya ƙarama”.

Takaici da baƙin ci ki su suka hana ni magana, da ƙyar na buɗe baki na ce ”wallahi kiji tsoron Allah Mama akwai ranar ƙin dillanci, bai kamata ace dan ƙasa ta rufe idon Mahaifiyar mu ki ci amanar ta ba, ki tuna sai da ta ba ki amanar mu, ki ka ce kin amsa ashe ganin idon ta ne yasa kika ce kin amsa, idan ita bata kallon ki Allah na kallon ki, kuma shi ne zai mana hisabi”.

“Dallah rufe min baki akwai wanda ya kai ka cin amana ne, ace har kanada kwarin guiwar haikewa ƴata, ashe zaka iya neman Ikilima, ”auzubillahi, kar ki ƙara haɗa ni da wannan ƙazamar ƴar ta ki, haka kar ki ƙara haɗa ta da ƴaruwa ta, dan ita tsaftatatciya ce ba ƙazama ba”.

“Ni ka ke zagi Jamal,”ni ban zage ki ba, kuma idan ma zagin na ki na yi ai kin can-can ta ne, dan ke da tsinuwa ki ka dace ba zagi ba, ”Mahafinka zai dawo yau sai ya zaɓa ko ni ko kai”.

Karfe 8 na dare muna zaune a ɗakin mu, na ji kira daga mahaifina, haka na tashi na fita, na je na tsugunna, “Baba ga ni, ”Talatu ga shi na kira sa, ”malam so na ke yau ka zaɓa ko ni ko Jamal, saboda ba zan zauna da gardi kamar sa ba, yana neman lalata min ƴa,”ban fahimce ki ba, ki yi min maganar ta yadda zan fahimta”.

“Ga shi nan a ga bansa bazan ma sa ƙage ko sharri ba, ɗazu ya matse Raziƙa a ɗakinsa zai yi lalata da ita, da ma maƙota na faɗamin halinsa, ban yarda ba sai da ya nemi ƴata a gabana, to a gabana mana tunda ina cikin gidan ko nauyin idona bai ji ba”.

Ta faɗi ta na share hawaye, ”yi haƙuri Talatu, kai Jamal dama mutumin banza ne kai, ƴaƴan mutane kake bi kana ɓatawa, to ni dai ban yafe maka ba, dan ban taɓa ɓata ƴar kowa ba, ka jamin zagi a banza, Uwar ka ta tafi ta barni da kai, ta haifa min bala'i ban yafe muku ba”, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, ”ka tattara naka ya naka ka bar min gida, da ga yau ko ƙofar gidana ka ƙara bi ban yafe ba”.

Da na buɗe baki da niyar yin magana sai ya kawo min duka, haka ya koroni har ƙofar gida yana zagi na, ina kuka ƙannena na kuka, haka ya tasani gaba har na bar unguwar, ban san ina zani ba na ɗauki hanyar gidan su abokina Amir, na je Ina kuka na faɗi ma sa damuwata, na ce ni yanzu ban san ina zan dosa ba.

“Jamal ke nan in dai gurin kwana ne kar ka damu, ai kai ɗan halak ne, ka taimaka mana lokacin baya, dan haka ka zauna a nan har lokacin da Baban ka zai huce, sannan dan abinci da kayan sawa zan maka komai, kar ka damu ai ka wahala yanzu lokacin hutune a gare ka”.

Haka na ci gaba da zama a ɗakin Amir, ba tare da nasan sana'ar sa ba, ”Amir wai kai wace sana'a ka ke yi, kullum baka zama da dare sai da rana ka sha baccin ka a gida, ”share kawai zan sanar ma amma ba yan zuba”, kusan duk sanda zan ma sa tambayar maicece sana'ar sa haka ya ke ce min.

Ranar dana shiga halin dana ke ci ki, da misalin ɗaya na dare, ina kwance kawai na ji bugun ƙofa, a tunani na Amir ne ya dawo, ashe ƙaddarata ce ke buga min ƙofa, ban tambaya ba na tashi na buɗe kofa, mai zan gani ƴansanda ne ɗauke da bindigu a hanunsu, sai Amir a gyefe sanye da ankwa a hannun.

Na wartsake saka makon jin wani azababben mari daya ratsa fatar Kuma tuna, ”wuce ci ki mu je” haka na juya ɗan sanda ɗaya ya ɗora min bindiga a ƙeya, su ka tunkuɗa Amir cikin ɗakin “dan ubanka ɗakko sauran makamai da kayan da ke ɗakin nan kafin mu aika ka lahira”

Na kasa ƙwaƙwaran motsi, numfashi ma da ƙyar na ke yi, abin mamaki nan Amir ya buɗe wata ƙofa a bayan labule da duk zama na ban san da ita ba, ƴan sanda suka shiga suka fara fito da makamai kala kala bindigu,harda bom a cikin wani akwatin ƙarfe,sai kuma wani ɗan ƙaramin akwati dake ɗauke da hodar iblis.

Da ga nan suka tasa ƙyeyar mu sai police station, ban san hawa ba ban san sauka ba, suka sa ni a gaba da duka da azaba kala kala, kan tare da Amir muke wannan kasuwanci, naƙi na amsa wahala tasa ni na amsa, a lokacin da suka sa min wata hular lantarki akai, tare da jona min wasu wayoyin a sassan jiki na daban daban.

Na amsa laifin da ban san ina tare da mai aika tasa ba, su ka kaimu kotu aka yanke mana hukuncin shekara takwas tare da horo mai tsanani, abin mamaki Amir ko a jikinsa kamar ba mune a halin nan

2 / 12