Author : MINAL SAEED Category : Romantic Hausa Novels
ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake gina
Page1️⃣1️⃣
Mu ka jero a hanya muna tafe muna hira, ko na ce ya na ba ni labarin ƙuruciyarsa, da irin rashin jin da ya yi, ina ta faman dariya muka iso ƙofar gida muka shiga, Ummana taji daɗin ganin mu tare sai albarka take ta samin, farin ciki ko ya kasa ɓoyuwa a fuskarta, kamar zata goya ni…
Mun gaisa sosai Sulaiman ya mata sallama ya fita, na ɗan zauna ta na ƙara min nasiha, tare da sa albarka da addu’o’i kamar kamar nayi kuka, saboda farin cikin dana gani tare da ita, “tashi ki tafi gida Aisha Allah ya baki masu miki biyayya kamar yadda ki ka mana, to Ummana ameen na gode…
Na fito na tadda Sulaiman a ƙofar gida, sai ya haɗe rai ya turo baki kamar wani ƙaramin yaro, hakan da ya yi sai ya bani dariya sosai, ya ce “shine ki ka yi zamanki a ciki ki bar ni ko?, “kai Yaya Sulaiman to ai gani na fito,” “ba wani nan ni ban yarda ba ni ma sai na rama”, muna tafe muna ni shaɗi ya ci gaba da bani labarin da ya fuskanci yana sa ni farin ciki, cak ya tsaye yana kallon yadda nake dariya…
“Aisha Allah ya dauwamar min ke cikin farin ciki, wallahi a yanzu a duniyar nan Aisha ko rayuwata kika nuna kina so zan baki ita matukar hakan zai sa ka ki cikin farinciki, “Yaya nima ina son ka, kuma dan Allah ka yafe min abubuwan da na maka a baya”, “Alhamdulillah Alhamdulillah, A'isha dan Allah ki maimaita abin da kika faɗi yanzu, nayi murmushi na ce “Yaya Sulaiman ina son ka”...
Abin mamaki sai na ga hawaye na fita a idanunsa, na ce “Yaya ko baka ji daɗin kalamai na bane, “Aisha kukan farin ciki ne, nan na ga ya tafi sujudu shukur, yana ɗagowa ya rungume ni ya shiga faɗamin wasu daɗaɗan kalamai kwantar da hankali, hakan yasa na ji kunya ta kamani na sa hannuna na rufe idanu na bayan ya sakeni, ina murmushi, “ahhh!!, naji ihun Sulaiman da sauri na bude idona….
Mai zan gani Habib ne tsaye da wuka a hanuna jini na binta, na kalli Sulaiman na ga jini na bin hannunsa gashi ya dafe cikinsa, na ɗora hannunna akai na fasa ihu tare da faɗin, “shikenan ka kashe sa, na shiga uku”, “Aisha har za ki tsaya kina furta wa wani kalaman da ni kaɗai na cancance su daga bakin ki, wallahi ba ki isa ki ci amanata ba, Kamar yadda kika ce ke ta wace to bazai canza ba har abada ke ɗin tawa ce”, ya faɗi cikin tsawa…
Jini ya ɗibi Sulaiman ya tafi ƙasa zai faɗi,
da sauri na rikosa muka zube tare, na shiga girgiza sa ina ka tashi Yaya, ban san waya faɗi ma ƴan gidanmu ba sai gasu Umma da Yaya Kabir ya nemo taimakon abin hawa gurin maƙocin mu, nan aka kama Yaya Sulaiman aka sa shi a mota, nima na shiga na ɗora kansa a cinyata ina faɗin tashi Yaya ka tashi !!!.
Muna isa asibiti emergency aka nufa da shi, cikin gaggawa aka ma da ɗinki Allah ya sa sukar bata taba hanjinsa ba, saura kaɗan Allah ya kiyaye, nan Yaya Kabir ya kira su hajiyarsa hankali tashe ta nufi asibitin, da yike Yaya Kabir ɗan sanda ne, nan ya shigar da ƙarar Habib akan ya yi yunƙurin kisan kai, aka ka ma sa an kaisa kotu aka yanke ma sa hukuncin shekara biyar gidan yari da horo mai tsanani tare da tarar dubu ɗari biyu, daga nan ban ƙara jin labarin Habib ko ganin sa ba…..
A asibiti kam babin soyayya muka buɗe ni da Sulaiman, dan shagwabar sa yake yi sosai kamar ƙaramin yaro, ni kuma ina bin sa a yadda yake so, har wani kyau muka ƙara na kwanciyar hankali musamman shi kamar ba shi bane ma jinyaci, ranar da Yayansa yazo dubiya ya na ta tsokanarsa dan har kunya suka bani, dan kamar abokinsa haka yake ta tsokanarsa wai shi ya gama kyau ya yi a asibiti nan anya ba zasu siya mai ɗakin nan ba a kwaso mana kayan mu….
Da irin wannan maganganun da dama, ƙarshe sai fita nayi na bar musu ɗakin saboda kunya, satin mu huɗu Sulaiman ya warke tass kamar ba shi ba, aka sallame mu muna komawa gida bawan Allah nan da ya liƙemin sai da ya tabbatar mun zama abu ɗaya, aiko na ga gata da sa albarka, ni har kunya ma ya dinga bani…
Ya yi jinyata da kansa dan likitane, shiyasa bai wahalar da ni sosai ba, haƙiƙa bansan mene ne soyayaba sai a wanna lokacin kamar kwai haka yake lelena, ni kuma ina zuba shagwabata son raina, ko ya yaga fuskata ta canza ya dinga tambaya ta mene ne mai nake so, Hajiyarsa ma sai ƙara kula dani take kamar ita ta haife ni, a lokacin na yi ƙiba sosai na ƙara haske, har wani sheƙi nake yi….
Bayan wata biyar na kama zazzafan zazzaɓi, Sulaiman ya ɗaukeni mukaje asibitin da yake aiki, da kansa ya duba ni ni dai na ga sai murmushi yake yi, motsi kaɗan zai rungumeni yace mai kike so, ko mai za kici yanzu, za kici ka za ko ka za ne ki ke so, na kan ce ba komai kuma in ina da buƙatar abu, na faɗi kamar jira yake sai ya nemo sa, ashe wai ciki gareni har na tsayin wata uku ban sa ni ba….
Hajiyarsa musamman take dafo min abu ta aiko da shi, ta ce nawa ne ni kaɗai karna ba sa, hakan ya sa na ƙara ganin ƙimarta kuma na ƙara ɗaura ɗamarar zama da ɗanta, na kuma mallaka ma sa zuciyata, ina zuwa antynatal duk lokacin da aka ba ni, anyi sicaining an ce ɗiya mace zan haifa murna gun Sulaiman kamar me, har addu'a ya ke Allah ya sa na haifi mai kama da ni.
Ina ta rainon cikina cikin kulawa da soyayya, bayan wata hudu na tashi da ciwon mara mai tsanani, ban dade ina naƙuda ba da kansa ya amshi haihuwata a gida, na haifi ɗiya mace kyakyawa kamar An tsaga ƙara da Babanta, Yaya Sulaiman yayi murna da haihuwar nan.
KECE SILA
(✍️Minal saeed)
(🌹MRS BASH🌹)
https://whatsapp.com/channel/0029VbBl22NAO7RLFvcUlU2g
https://chat.whatsapp.com/FuiNx6HvwgzAheM7xh0Xci?mode=ems_copy_t
://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake gina
Page 1️⃣2️⃣
Naga gata a wannan karon da kulawa, ƙanwar Ummana ce ta zo ya min zaman bakwai, ranar suna yarinya taci sunan Zainab, akwati guda Hajiyarsa ta mana ni da baby Zainab, uban gayya ko ba a magana duk abin da ya samu ni da baby, kaya ko sai da na ma sa magana akan ya bari haka, sannan ya tsagaita.
Anyi suna lafiya na watse lafiya, taron suna ya yi armashi, dan duk wanda ya zo sunan saida ya tafi da kyautar, jaka mai ɗauke da hoton baby, da kyaututuka a ciki, anyi suna lafiya amma fafur Yaya ya hanamu tafiya wankan gida, Babana yace tunda ya hana a haƙura.
Haka mu kayi Wanka cikin kwanciyar hankali, ranar da mukayi arba'in ƙanwar Mamana ta tafi, tace tayi ƙokari a haka ma, wai Sulaiman bai ma ta kara a gaban ta yake duk abin da ya ga dama, har gida ya maida ta da sha tara ta arziƙi tare da godiya.
Kamar jira yake na yi arba'in sabon babin amarci muka buɗe, da kulawa, Shekarar Zainab biyu na yayeta dan ba inda bata zuwa kuma babu abin da ba ta ci, ban jima da ya ye ta ba na samu wannan cikin na jikina, ina rainon cikina cikin aminci, Habib ya zo ya ɗaukkoni a gida, ya kuma kashe min mijina, yanzu haka rabona da gida wata uku kenan.
“Inalilahi waina ilaihi raju'un!, baiwar Allah kinga jarabawa, gaskiya Habib bai kyauta ba, ya kuma ci amana sannan bai yarda da ƙaddara ba, inda ya yarda da ƙaddara ba zai aikata hakan ba, kiyi haƙuri insha Allah zan maida ki gida da kaina, sai na sa da ki da iyayenki cikin aminci”.
Cewar Jamal, ita ko Hari sai sharar hawaye take yi, Baffa kuma ya yi shuru yana bina da ido, can ya ɓuɗe baki ya ce.
“Sannu yarinya sannu kinji, lallai kin shiga tarkon bawan Allah nan Habibu, bai kyautu ace ya saka miki da haka ba, ya ci ace ya yarda da ƙaddara da kuma ikon Allah, dan duk abin da ka ga Allah bai baka shi ba to ba alkairi ba ne a gareka, kema kinyi kuskuren bijirema iyayen ki duk da Allah bai baki ikon ƙin yi musu biyayya ba amma ba ki kyauta ba”.
Ni dai ba abin da nake sai kuka, dan ba abin da nake gani sai lokacin da Habib ya harbi Sulaiman, “Allah ya isa tsakanina da kai Habib sai Allah ya saka min, sai Allah ya wulaƙanta ka, Allah ya tozarta ka, maci amana azzalumi kawai”.
Na ƙara sa tare da fashewa da kuka, “ki yi haƙuri yar nan, “Baffa ni zan barta a nan na zuwa wani lokaci, saboda na san yanzu boss yana can yana bincike akan inda ta ke, dan yanzu ko kin koma gida akwai matsala, dan ba zai bar ki ba, sannan bana son ya ɗora wani zargi a kaina, dan zuwa yanzu na san ya fara bincike kuma zai iya zuwa har gidan mu dan ya tabbatar Ina gida ko bana nan”.
“To Jamal na gode Allah ya saka maka da alkairi, Allah ya baku mafita kai da ƴanuwan ka, “na gode Anty Aisha kema. Allah ya yi miki mafita insha Allah zan bincika miki gida amma a boye na ji yadda suke kodan hankalinki kwanta”.
“Ni zan tafi zan dinga zagayowa ina ganin yadda ki ke, sannan duk lokacin da zan zo za ki ji labarin ya ƴanuwanki da mahaifiyarki suke, “to Jamal Allah ya tsareka nagode ka gaida gida”.
Jamal ya tafi ya barni a ruga na ci gaba da rayuwa cikin su Hari, tun ban iya cimar su ba yanzu har na iya, haka ina zuwa naga yadda Hari ke ta tsara nonon shanu, Kuma abin na birge ni, suna kula da ni dai dai ƙarfin su, ba abin da na nema na rasa, yanzu cikina na wata bakwai, watan Jamal biyu da tafiya ke nan yanzu, har na fara cire ran zai dawo gareni.
Jamal ko yana zuwa ya tadda kanensa a wani mummanan hali, dan ƙaninsa ya samu a wani hali, Abubakar na kwance baida lafiya sosai, Haruna ne ke fita ya yi buga buga ya nemo musu abin da zasu ci, tare da maganin da zai sha, Iklima kuma gidan wa ta sabuwar Amarya ta ke shiga ta taya ta aiki sannan ta samu abin da zata ci.
Suna ganinsa suka rungume sa, suka sa kukan tausayin kansu dana tuna rayuwar su ta baya, shima duk dariyarsa sai da ya yi kuka, “Haruna ina Abba ya barku a wannan halin”.
“Yaya Abba na nan amma da shi da ba bu kusan ɗaya, dan ba bu abin da ya ke iya yi a gidan nan saida izinin Mama, kwanaki ta sa ya kore mu sai da mai gari ya sa baki, sannan ya ce zai kore su a garin nan in dai Abba ya kore mu, sannan aka bar mu amma ba ruwansa da komai namu”,
KECE SILA
(✍️Minal saeed)
(🌹MRS BASH🌹)
https://whatsapp.com/channel/0029VbBl22NAO7RLFvcUlU2g
https://chat.whatsapp.com/FuiNx6HvwgzAheM7xh0Xci?mode=ems_copy_t
://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake gina
Page 1️⃣3️⃣
“Haruna ka gyara ma sa jikin sa bari na samo mai adaidaita mu tafi asibiti,”
muka je asibiti ana duba sa aka ce yunwa da damuwa ne suka ma sa yawa, aka ba sa gado na biya komai, na dawo gida da yamma Abban mu ya ce mai ya kawoni gidansa, “Abba nan fa gidan Ubana ne ban da in da ya fishi, dan haka ka yi haƙuri na dawo zan kula da ƙannena, tun da wacce aka bar ma amanarmu ba za ta iya ba”.
“Abdul Jamal ni ka ke faɗa wa haka, ni mahaifinka kake wa rashin kunya, “Abba kayi haƙuri amma ba rashin kunya ba ce gaskiya ce na faɗi ma, amma ka yi haƙuri”.
“Dole ya ma abin da yake so tunda mai gari ya ɗaure mu su, shiyasa suke abin da suke so, haka yazo ya kwashi yaran nan ban san ina ya kai su ba, dan ni yanzu tsoro yake bani dan kaɗan ta rage ya dake ni daga na ce ina zai kai su, ya fara zagina”.
“Ke da Mahaifina nake magana bada ke ba, sannan ki shiga hankalin ki kiyi harkarki na yi tawa, kin dai ji mai na ce koh, Jamal yanzu Maman taku kake faɗi ma haka, a'a Abba wannan matar ba Mamana ba ce, ni Mahaifiyata ta rasu, dan haka bana da haɗi da ita”.
“Ka ji ko malam na faɗima wannan yaron ba abin da ya koyo, a gidan yarin da aka kaisa sai rashin kunya da ɗibar albarka, Allah ya sa shi ma bai fara satar ba, dan ance a ɗakin wannan riƙaƙen ɓarawon aka kama sa, ka ga ko abokin ɓarawo ai ɓarawo ne”.
“Ni ba ɓarawo ba ne, dan haka kar ki kuma kirana da ɓarawo,” na juya na ɗibi kayan su Haruna dama shi ya mai do ni gida, sai da Abubakar ya shafe wata biyu a asibiti yana jinya sannan ya samu lafiya, muka dawo gida na ci gaba da kula da ƙannen, duk da haka Anty Aisha na raina ban manta da ita ba…..
Bacirawa,
“Assalamu alaikum, “wa alaikasalam”.
“Bawan Allah gidansu Kabir nake nema, “wane Kabir kenan, “Yayan A'isha, “gidansa kona iyayensa, dan kasan ya yi aure wata biyu da suka wuce ya auri Khairat ƙawar ita Aisha, Allah sarki to ina ne gidan na sa, zo muje na raka ka ga gidan can ba nisa”.
“Yauwa na gode sosai Allah ya biya ka, “ameen ameen”
Ya yi sallama da Kabir ya yi sa'a yana gida yau bai fita aiki ba, bayan ya fito suka gaisa ya ce, “magana ce mai mahimmanci ta kawo ni gurin ka in ba damuwa zamu iya shiga daga ciki, “to bismillah shigo, “na san baka san ko wane ne ni ba, sunana Abdul Jamal ina zaune da iyayena a dorayi”.
Daga nan ya ba shi labarin komai duk abin da ya sa ni, da kuma labarin da Aisha ta ba shi, Alhamdulillah da ma Aisha na raye ni ina jin hakan a jikina, kuma tabbas Habib sai ya girbi abin da ya shuika, yanzu ita A'isha ta na ina, a ina ka barta?“.
“Ta na rugar da suka taimaka mana, dan na dawo gida da niyar na nema ku, sai na taras kanina baida lafiya, abin da ya ja min lokaci kenan amma ban manta da alƙawarin dana ma ta ba, dan tabbas Aisha abin tausayi ce ga ciki a jikinta, amma nasan su Baffa zasu riƙe amana ba zasu cutar da ita ba”.
“Yanzu zuwa yaushe ka ke ganin zamu tafi gurin ita Aisha muje mu dawo da ita”
“Abun da ya kamata yanzu ka fara sanar da mijinta, dan na san shima hankalinsa ba a kwance ya ke ba, Kaga idan shima zai je sai ya shirya mu tafi tare”.
“Eh to kaima ka yi magana a nan, Allah sarki Sulaiman yanzu haka ya na fama da hawan jini, sakamakon abin da ya faru, haka itama Ummanmu, amma na sa yau zasu yi kwanan farin ciki da yardar Allah, matsalarmu ta zo ƙarshe”.
Sun tattauna abubuwa da yawa, kafin Kabir ya ɗauki Sulaiman a motarsa ya kai sa har gida, kuma ya ma sa alkairi, daga nan gidansu ya nufa, ya sanar ma mahaifiyarsu labarin nan mai daɗi, ta yi murna harda hawayen farin ciki, daga can kuma ya yi gidansu Sulaiman…..
Yana faɗima