Author : MINAL SAEED Category : Romantic Hausa Novels
Sulaiman halin da ake ciki, ya rikece yace lallai a tashi a tafi ruga yau, da rarrashi da ban baki Sulaiman ya haƙura sai gobe a shirya a tafi, Yaya Kabir ya sanar da Jamal komai ya ce ba damuwa, “Ikilima, Ikilima ba bu in da za ki fita sai kin yi min aikin gidan nan, kin san ai Raziƙa ba zama take yi ba balle kice ita ce zata yi”....
“Ke”, “na’am Yaya zo kiyi tafiyar ki inda za ki, ke ba baiwarta bace daga yau kin daina aikin wahala a gidan nan”.
KECE SILA
(✍️Minal saeed)
(🌹MRS BASH🌹)
https://whatsapp.com/channel/0029VbBl22NAO7RLFvcUlU2g
https://chat.whatsapp.com/FuiNx6HvwgzAheM7xh0Xci?mode=ems_copy_t
://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake gina
Page1️⃣4️⃣
“Jamal to wa kake so ya ma ta aikin in bata yi ba?, “babu aikin da zata ƙara yi a cikin gidan nan da ga yau, saboda ko ta yi ba gani kike ba, a da kin bautar da mu, kin cutar da rayuwarmu amma yanzu ba ki isa ba, dan haka babu mai ƙara sa Ikilima aiki, kina da ƴa ki sa ta ta yi ko ki yi da kanki”......
“Yaya na tafi, “ki bari sai yamma ki dawo gida dan zan fita ne”, “to Yaya Allah ya tsare ya dawo da kai lafiya”, “ameen ƙanwata”.
Mama tsayawa tayi tana kallon su, daga ƙarshe ta girgiza kai tace, “dani kuke magana, yara uwarku ma da na ga za ta bani matsala gaba daya duniyar na sa ta bari, balle ku kananun ƙwarai dan haka yanzu za'a fara buga wasan, mallakar danawa Ubanku bata yi tasiri ba, tunda wannan munafukin mai garin ta shiga cikin abin da bai shafe sa ba”.....
Duk a zuciyarta take wannan maganar, “assalamualaikum”.
“Wa alaikasalam”.
“Yauwa Jamal yau bayan an fito sallar azahar zamu tafi”.
“To Oga Kabir sai kunzo nima a shirye nake”,
Ruga
“Sannu ƴar nan Allah ya sauke ki lafiya, gashi ba bu asibiti nan kusa balle a kai ki dole sai an shiga birni, amshi rubutun nan ki bata ta sha muga abin da Allah zai yi”.
“To Baffa,” ta miƙa ma ta ruwan rubutun a ƙoƙo, ya fita yana mai addu’ar Allah ya sauke ta lafiya, “ki daure ki sha rubutun Nan,” ta fadi tare da miƙa mata ƙoƙon rubutun, A'isha ta share zubar da ke goshinta, ta amshi rubutun jikinta na rawa ta kai bakinta tana sha, a zuciyarta addu’a take yi Allah ya sauke ta lafiya, dan tunda take bata taba shan wahala irin ta yau ba, naƙuda tun daren jiya amma har yanzu da ake neman sha biyu rana bata haihu ba……
Cikin ikon Allah tana shan rubutun nan ta sa ki ƙara, saboda wata sabuwar azaba data ziyarci ƙwaƙwalwarta, bayan mintuna biyar ta haifi ɗanta namiji, shanu shanu ƴar nan, bata gama maida numfashi ba wa ta sabuwar naƙudar ta tashi, wannan Karon bata ɗauki lokaci mai tsayi ba, kukan jariri ya karaɗe ɗakin, Hari ta sa ki wa ta guda data karaɗe gidan ba ki ɗaya…
Hari ta gyara mai jego da ƴaƴanta suna lafiya, Hari ta dafa mata ruwan wanka ta shiga tayi wanka, ita kuma ta gyara yara suka fito tsaf da su, dama Baffa na suyi kayan jarirai idan ya fita cikin gari, dan haka basu sha wahalar neman kayan yara ba…..
“Umma zamu tafi masallaci daga can zamu tafi inda Aisha take”, “toh Kabir Allah ya kaiku lafiya ya dawo da ku lafiya, yasa Aisha tana cikin ƙoshin lafiya”.....
“Ameen Umma na in sha Allah yau da ƴarki zan dawo gida,” “to Kabir Allah ya tabbatar mana da alkairi,” nan suka tafi bayan sun fito daga masallaci, saida suka yi tafiyar awa uku sanna suka shiga cikin rugar, tir yan tir yan Jamal ya yi musu kwatance gidan Baffa….
Bayan sun isa ya yi sallahma, anyi sa'a Baffa na nan ya fito, yana ga nin sa fuskarsa ta cika da fara’a, “ah ah Jamalu kai ne a gidan namu, “eh Baffa nine”, ya durƙusa ya gai da shi, “Baffa amana ta na zo amsa”...
“Jamalu amanar ka na nan lafiya lau saima karuwa da aka samu, dazu da rana Allah ya sauketa lafiya”.
“Baffa kana nufin A'isha ta ce ta haihu?, “Jamalu Shi kuma wannan waye?, “Baffa wannan da ka ke ga ni shi ne mijin Aisha, ɗayan kuma Yayanta ne”......
“Ma sha Allahu Ai duk ƴan gida ne ku shigo daga ciki,” suka ranka ya suka shi ga, tunda suka shiga ba abinda Sulaiman ya ke yi, sai zare idon in da zai ga Aisha ta fito, Baffa na lura da shi sai dai ya yi murmushi, suka gaisa nan Jamal ya ƙara gabatar da su Sulaiman a gurin Baffa…
Ya ce yana zuwa su ɗan jirasa, ya fita ya bar su a cikin bukkar da suke, duk da daga ciki ba zaka ce bukka ɓace sai in ka fito waje, sai ga Baffa ya shigo A'isha ta biyo bayansa, hanunta riƙe da jariri, Sulaiman ya miƙe kamar an tsumgule sa ya rungume A'isha, sai kukan farin ciki sukeyi…..
Su Baffa dai sai fita suka yi suka bar musu ɗakin, sai bayan sun natsu sun dawo cikin hayyacinsu, aka zauna ana maida yadda a kayi, Sulaiman ya ɗauki jariri yana kallo, can saiga hari ta shigo hannunta ɗauke da ɗayan babyn, zunbur ta miƙe “A'isha shima wannan nawane?”.....
“kwarai da gaske Yaya kyautar da Allah ya mana kenan, “Sannu Aisha Allah ya miki albarka, “ameen Yaya, amma Yaya dama Habib bai samu nasarar kasheka ba kamar yadda ya yi niya”...
“Allah bai ba shi nasara ba ina raye, kuma insha Allah tunda kin bayyana, sai an nemo shi shima duk in da ya shiga, A'isha bani labarin bayan rabuwa”...
Duk wanna zancen suna yin sa ne bayan su kebe da daddare, dan ba yadda za'ayi su koma gida dare ya yi musu kwana ya kama su, nan Aisha ta basa labarin tun farkawar da ta yi ta tsinci kanta a gidan nan, har irin yadda sabo ya shiga tsakanita da Jamal, da kuma ta yadda suka samu nasarar guduwa, har yadda ta farka ta tsince kanta a ruga gurin su Baffa da irin taimakon da suka ma ta….
KECE SILA
(✍️Minal saeed)
(🌹MRS BASH🌹)
https://whatsapp.com/channel/0029VbBl22NAO7RLFvcUlU2g
https://chat.whatsapp.com/FuiNx6HvwgzAheM7xh0Xci?mode=ems_copy_t
://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake gina
Page1️⃣5️⃣
In banda kuka babu abin da Sulaiman ke yi, ya rungumeta sai kuka sukeyi, Aisha wallahi wallahi sai Habib ya biya bashin abin da ya aikata, sai ya yi dan sanin abin da ya aikata miki, da ni ya taɓa ba zan ma sa komai ba, amma tunda ya taɓa ki sai ya biya bashi, Habib gani nan gare ka”……
Kwana suka yi suna hira, gari ya waye suka yi karin kumallo suka shirya, “Baffa ya kamata ku bimu kuga inda muke, dan zumunci tsakanin mu ya riga ya ƙullu”.
Bayan sun shirya Aisha ta yi sallama, da mutanen da suke gaisa wa suka tafi, suna isa gida da gudu Aisha ta fita tana kiran Ummanta, “Ummana! Ummana!!” da sauri Umma ta fito har zaninta na neman faɗuwa.
“Aisha ashe da rabon na kuma ganin ki, ashe Allah bai yanke ganawar mu ba,” da sauri Aisha ta faɗa jikin Umma “Ummana!” ta faɗi cikin kuka, “Umma Habib ya cu ce ni shine ya rabani daku na tsayin watanni, Umma bazan taɓa yafe ma sa ba.”
“ki yi haƙuri A'isha in Allah ya yarda ƙarshen Habib ya zo, tun da Allah ya dawo mana da ke lafiya, Yayanki zai tada, maganar ai dama a office ɗin su take.”
Kwata kwata Umma bata ga su Baffa ba sai da kabir ya ce ma ta, “Umman A'isha tare da baƙi muke,” sai a lokacin ta gansu, Kuma suka shiga cikin falo, sun gaggaisa Kabir ya ma ta bayanin su waye, nan Umma ta hau godiya ta shiga hidima da su.
Basu jima ba sai ga su Abba sun shigo, shida su Yaya Ibraheem, suka gaisa da su Baffa Abbana ya yi musu godiya, Umma na ko ta rasa in da zata sa kanta, da ƴan biyu ta ɗauki wannan ta aje wancan, lokaci bayan lokaci ta ce Alhamdulillah sannu Aisha kinji sannu.
Gari ya waye su Baffa suka ce zasu tafi, Abbana da su Yaya suka haɗa musu sha tara ta arziki, Yaya Kabir ya mai da su har gida, suna ta godiya suma su Umma suna ta godiya.
Yaya Sulaiman ko daga masallaci dalar asuba, gidanmu ya taho ya zo da shi muka yi karin kumallo ana ta shan hira, sai wajen ƙarfe goma na safe sannan ya tuna wai hajiyarsa ta ce in zai taho zata biyo shi su zo tare.
Ya riƙe baki da hannu, “Yaya lafiya kuwa?, “A'isha wallahi na manta Hajiya ta ce za ta biyo ni in zan zo,” na kwashe da dariya na ce, “ to ai sai ka tashi kaje ta taho da ita,” hararata ya yi “ki ci gaba da min dariya zan kama ki ne.”
“To ni kuma mai na yi maka Yaya, “ba ma ki san mai kika yi ba,” “eh mana ka faɗi min,” “kawo kunnenki” na miƙa kunnena, ya samu ya cije ni a kunnen, nan na saki kukan shagwaba, ai ya ruɗe yana rarrashina, Ina botsarewa, muna ta shiririta sai Jin sallamar hajiya mukayi a bakin ƙofa.
Zabura Yaya ya yi ya kuma rasa inda zai ɓoye, dana fahimci nufina sai na ce Hajiyata ki shigo mana, cak ya tsaya a in da ya ke, da hannu ya min alamun zai kama ni, na ma sa gwalo.
Hajiya ta shigo na durƙusa har kasa na gasheta, sai jin Zainab na yi tace “Momyna ina kika je kika barni?, “oh Zee ƙanne na je na samo miki , lah momy na suna ina?”.
Tana ganin su sai murna da farin ciki, “Momyna zan dinga goya su?, “eh mana Zee ai kece mai rainonsu, yehhh tayi waje da gudu “in je na ce ma Umma Momyna ta siyomin Yara guda biyu”.
Dariya mukayi daga ni har Hajiya, “Alhamdulillah yau dai na huta da tambayar ina Momyna, dan aikinta kenan kullum yaushe Momy zata dawo, mai taje siyo min?, kai ai na sha tambayoyi da rigimarta.”
Nan muka sha hira nida Hajiya ta ɗauki jikokinta, Hasan da Usaini duk da ban san ko akwai sunan da Abban su zai sa musu ba, tun da bamu yi magana akan sunan ba to wake ta sunan yara ana ta farin ciki.
Yara sunci sunan Maihaifina da Maihaifisa wato, Usman da Ahmad muna kiransu da Hammad da Hamid, wannan karon a gida na zauna, sai da na yi arba'in sannan na koma gidana, Sulaiman ya gwadamin soyayya mai tsayawa rai, gata nake samu nida ƴaƴana Zainab ko Hajiya ta rike tace wannan ta tace ba tamu ba.
Soyayya muke gudanarwa cike da natsuwa da kwanciyar hankali, Yaya Suleman da Yaya Kabir suna can suna bincike, da hada hujjoji saboda su kama Habib, dan sunce wannan karon in ya shiga ya shiga kenan, ba zai fito ba, Jamal ya ƙi komawa gurin su Habib dan yace ya bar cikinsu kenan har abada.
“KECE SILA”
(✍️Minal saeed)
(🌹MRS BASH🌹)
https://whatsapp.com/channel/0029VbBl22NAO7RLFvcUlU2g
https://chat.whatsapp.com/FuiNx6HvwgzAheM7xh0Xci?mode=ems_copy_t
://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake gina
Page 1️⃣6️⃣
Habib har yanzu bai haƙura da binciken inda Aisha take ba, alokacin da aka ɗauke har gidansu Jamal saida ya zo, in da Allah ya taimake sa suna asibiti da ƙanensa, ya kuma sa an bincika an tabbatar da yana asibiti yana jinyar ƙaninsa, hakan ya hana zargin sa ya bi ta kan Sulaiman….
Amma fa masu gadin gidan da sauran da aka bari, sun sha azaba a gurin sa dan yace a cikin su ne wani ya ɗauke ta, sai dai duk iya azabar da ya musu bai gane komai ba haka ya haƙura badan ya so ba, amma fa bawai ya haƙura da Asiha bane dan ya ce dole ta zauna da shi…..
Habib har layin su Aisha ya sa yan (c i d) amma babu Aisha babu labarinta, dan haka ya haƙura da zama a layinsu, amma ya sa ana bibiyar ma sa Sulaiman da duk wani motsinsa, shima dai ta bangarensa babu wani labari, haka ya daina bibiyar su amma duk da haka yana neman Aisha, kuma ya ci alwashin in dai ya gan ta sai ya hukunta ta kuma sai ta faɗi ma sa waye ya gudu da ita sannan wace alƙace a tsakanin su…
Habib na can yana shirya yadda zai samu Aisha, bai san ana nan ana shirin yadda zaa ka ma sa ba, bincike suke yi so sai kuma da haɗin gwuiwar Jamal, a haka suka shirya Jamal zai koma cikinsu dan ya rinƙa sanar musu da motsin su, “Jamal duk wata hanya da zamubi dan ganin mun kama Habib, amma taƙi yuwuwa saboda haka dole za ka yi haƙuri ka koma cikinsu, da mu rinƙa sanin motsinsu a haka ne zamu samu damar kama sa.”
“Toh shi kenan Yaya Kabir zan koma cikin satin nan, amma ina tunanin ƙannena musamman ma Iklima da ta ke mace, ka dai ga yadda gidan namu yake,” “kar ka damu zan ma Umma magana Iklima sai ta koma gidan da zama, sai su zauna tare da Auta Khadija, su ma mazan zan ɗauke su na kaisu makaranta dan su ci gaba da karatu.”
“Na gode Yaya Allah ya saka da alkairi ya biya ka,” “ameen Jamal ai ba za mu iya biyan ka abin da ka mana ba, kaima aikin nan na kammala zaka koma makarantar sojoji tunda takardun ka na nan kuma sunyi kyau.”
Nan suka shirya ranar da Jamal zai koma, ana saura kwana uku ya tafi ya rako Iklima gidan su A'isha, Khadija Auta sai murna ta ke yi ta samu ƙawa, tunda Jamal ya ɗora idonsa kan Khadija, ya kasa sauke wa dan a lokacin soyayyarta mai zafi ce ta shige sa, ya daure bai ce komai ba a haka suka yi sallama da Iklima, ana gobe zai tafi suka raka ƙanensa makaranta A B U zariya, basu kwana ba suka juyo Kano……
A daren Jamal da su Kabir suka gana shirya yadda zai rinƙa kawo musu duk abin da suke buƙata, gari na waye wa Jamal ya ɗauki hanya dama ya sanar musu da dawo war sa ta waya, dan haka bai wahalab a dai dai ƙarshen gari ya sauka bai jima ba saiga ɗaya daga cikinsu ya zo da mashin da ɗaukar sa bayan sun gaisa ya hau suka yanki daji suka fara tafiya…..
Suna isa ya kai gaisuwa gurin Oga, daga nan ya bi sauran suka gaisa ana ta murna da dawowarsa, a wannan Karon jakar ya saki jiki so sai ana komai da shi, haka duk inda fita ta kama yana bin su aje tare da shi, sannan bai fasa abin da ya kawo sa ba wato leƙen asiri…..
Ana haka sai ga wani gagarumin aiki ya taso musu, haƙiƙa sun