Chapter 11 Reading KECE SILA COMPLETE HAUSA NOVELS BY MINAL SAEED.docx Arewa Novels

KECE SILA COMPLETE HAUSA NOVELS BY MINAL SAEED.docx

Author :  MINAL SAEED Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   11 / 12

30K to 33K   out of 34.2K words

asubar fari motar mu ta tashi ba dan nasan inda zan je ba, muna zuwa aka sauke mu a maraban Jos a nan na haɗu da wata baiwar Allah mai saida abinci, na mata bayani halin da nake ciki haƙiƙa ta tausayamin kuma na ji daɗin zama da ita, daren wata ranar Talata aka shigo cikin gidanta aka ma ta yankan rago aka kwashe kuɗaɗenta, da asuba Ina tashi na ganta a wannan hali na ruɗe na rasa ya zanyi, na kurma ihu mutane suka zo, daga ƙrshe ƴan sanda ne suka kamani wai ni suke zargi, na sha tambayi daga ƙarshe dai suka kulle ni.

Dan sanda gurin shine mutum na biyu daya ƙara ɓata in rayuwa, dan cewa ya yi zai taimaka min na fita a gurin, ni kuma banda mafita haka na amince da shi daga ƙarshe dai na fita, saida na gwammace zamana a kulle dan ko ba komai ina samun abinci, tsananin yunwa ta sa na fara mu'amala da maza, dan na samu abinda zanci a haka har Allah ya haɗa ni da ke, a gurin partyn da muka hadu, shima lokacin da wani direba ne muka je ya nemi ya saida ni a gurin wani mutum Allah yasa naji shine na gudu sai kika ganni kika taimaka min.

“Lallai kin fuskanci ƙalubale, amma Allah na tare da ke lokaci ya yi da za ki koma gida gaban iyayen ki, sannan ki koma da ƴan cinki Allah zai dubi maraicinki ki tuba don Allah sahihiyar tuba, dukkanmu ba jahilai bane mun sa ni muke take sa, amma Allah gafurur Raheem ne zai yafe mana, ni dai daga yau na bar karuwanci kema Ina son ki dai na, dan labarin ki ya taɓa min zuciya, ni da Uwata da Ubana a raye son zuciya ne da kuma alhakin marayu, da Mamata ke ɗauka suka Jani cikin wannan halin, amma daga yau na koma ga Allah, Zainab ke ma ina son ki tuba.”

“Shi ke nan Razi in sha Allah nima na tuba kuma zan koma gida gaban iyayena, dan Inna ta bata san duk abun da ke faruwa da ni ba, sai dai ko bayan tafiyata ta samu labari,” suka rungume juna suna kuka ba mai rarrashi saida suka yi suka gaji sannan suka hakura.

Bayan sati buyi

“To Zainab in Allah ya yarda zan kawo miki ziyara har gida, dan Allah kar rabuwa mu a bariki ta sa mu zubar da juna, mu ci gaba da riƙe juna kamar yadda muke a nan,” “in sha Allah Raziƙa kin zama kamar ƴar'uwa ta ta jini haka nake jin ki,” suka rungume juna suna kuka, hehehe “lallai yau ina ganin ikon Allah ni Zeena, amma wallahi duk wanda ya muku wa'azin kuka bar bariki ba masoyin ku bane, dan baku ci ribar bariki ba kuce kun bar ta to me a kayi kenan, mukam bariki yanzu muka sa ƙafa.”

“Dakata Zubairu rayuwar ka da ban tamu da ban,” “Ke ke mai mai ta abun da kika kirani da shi, kamar Zubairu naji kin ce to dan dakata, in za ki kirani da Zeena ta ki kira, in ba zaki kirani da haka ba babu dole, kuma karki sa ke hada ni da jinsin da ba nawaba ehe,” ka dai ji tsoron Allah ni da Zainab shiriya ta zo mana, kuma surutun ka bai isa ya mai damu ruwa ba, dan haka ka kama kanka ka ƙara gaba,” “aikin banza wai ƙunshi a duwawu ni ko kice na tafi ko karki ce ai tafiya zan yi, amma kafin ki tafi dan Allah ki kula Alhaji Isa mai tubin kuɗi ko na ƙarshene daga nan sai kuyi ban kwana.”

“Kawai mai yasa baka gane wane bariki dai na barta, ba Isa ba ko waye zai zo bazan kula sa ba, dan haka ka bamu hanya mu wuce in kai baka da abun yi mu muna da shi,” “ ta baya ta rago ta gaba ta ma lalaci, naga da har wanda bai kaisa ba kina sa na samo miki dan ki samu na cin abinci,” mitss taja wani mummunan tsaki, “Zainab zo mu wuce in ba haka ba wannan ba zai daina ɓata mana lokaci ba,” ta riƙo hannun akwatin ta tana zuwa inda Zubairu yake ta ban gaje kafaɗar sa “a’a kar ki karyani dan na ji ke a matan ma jikin maza gareki,” ya faɗi tare da fita daga ɗakin yana karairaya kamar mace.

“Wa nake gani haka kamar Raziƙa?” cewar Mama, “Mama nice mana ko baki gane ni ba ne,?” “taya zan gane ki na san dai ke ɓaka ce amma dubi yadda kika koma kamar za baya, tukunna ma daga ina ki ke, shekarar ki nawa rabon da ki waiwaye ni, Raziƙa duk sabo da nayi sanadiyar da wancan ɗan iskan yaron ya tafi gidan yari,” yanzu ma sabo da shi na dawo wallahi badan haka ba ke da ganina har abada yana ina,?” “wa” Jamal mana ai kinsan akan sa nake magana dan haka wannan karon dole ya aureni ko yana so ko baya so.”

“Laillai Raziƙa yau she ki ka zama haka ban sa ni ba,” “kinga Umma ni matsa min hanya na wuce, ba dan akwai abun da ya kawo ni ba da tuni na bar mi ki gidan ki, haka kawai daga zuwa na kin tsareni da tambayoyi tun a tsakar gida, haba ai kya bari na huta koh,” “Raziƙa kina cikin hankalin ki kuwa, ko kin manta wace ce a gabanki ne,?” mtss ban manta ba kuma idan kika ce za ki takura min, to wallahi duk wani aiki da kika yi tun shekarun baya zan lalata miki shi, ko an ce miki ban san ke ce kika yi silar mutuwar mamansu Jamal bane.?”

KECE SILA

(✍️Minal saeed)

(🌹MRS BASH🌹)

https://whatsapp.com/channel/0029VbBl22NAO7RLFvcUlU2g

https://chat.whatsapp.com/FuiNx6HvwgzAheM7xh0Xci?mode=ems_copy_t

://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*(J.W.A)*

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚

















(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)

"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa

Page 2️⃣4️⃣

“Innalillahi wa inna ilaihi raju'un!!!, Raziƙa zo nan uban waya faɗa miki wannan maganar,?” hahaha ta yi dariya, “Umma ke nan kina min kallon ƙaramar yarinya ko, to wallahi ki canza tunani, duk wani sirrin ki na sa ni a ciki harda shiga tsakanin Abbansu Jamal da ƴaƴansa da kika yi, hatta da yawon karuwancin da na yi ai bani kika so na yi ba, ko an ce miki ban ji sanda kike shirya zuwa gurin bokanki amso magani bane, da Allah ya sa ba suda alhakin ki, ai ga shi nan ni ce nayi karuwancin ba ita ba, ina taƙaice miki Umma babu abun da ban sa ni ba wanda kike aikatawa da ma wanda ki ka aikata a baya.”

Tafi suka ji daga bayansu, jikinsu na rawa suka waiwaiyo, wa zasu gani Jamal ne tare da ƙannensa, waya riƙe a hannun Abubakar da alamun duk sun gama naɗar duk abun da suka tattauna, “Alhamdulillah in sha Allah ƙarshenki ya zo a cikin gidan nan, sannan silar mutuwar mahaifiyarmu da kika yi ke da Allah, sannan ina mai farin cikin sanar miki, wannan maganganun kamar a gaban Abbanmu kuka yi su, dan haka ki fara tattara kayanki dan barin mana gida, ke kuma Raziƙa kike koma dai mene ne sunan ki, ki zo ki bar mana gidan Uba domin dai ba masaukin karuwai bane.”

“Dan Allah Jamal kuyi haƙuri, duk abun da kake cewa an aikata wallahi ba na da hannu ko kaɗan a ciki, hasali ma tsananin soyayyar da na ke maka ce tasa na dawo daga tafiyar da na yi,” “point of correction, yawon karuwanci dai,” cewar Abubakar, fuuu Jamal ya juya ya yi waje, ke Uwar ƴar bariki afara haɗa Kaya dan gidanmu babu ma saukin masu bin bokaye da kuma ƴan bariki, ba ta sanma mai ya ke cewa ba ta lula cikin dogon tunani.

“Ki shafa wannan man a hannun ki, sannan ki tabbatar kin taɓa ta in dai kika yi aiki dai dai a ranar za ta mutu babu makawa,” hhhh ya kama wata dariya mara fasali, “to boka maganar mijin na ta fa,?” “kar ki damu da wannan, gafalalliya mara rabo tunda kika riga kika sayar da imanin ki, mu kuma za mu cika miki buƙatun ki,” hhhhhh, “tashi tashi ki je azzaluma tashi ki je mara rabo, ta shi ki je sheɗaniya, duniya ki ka zaɓa kuma kin samu zamu baki ita, har sai kin ce bakya so, amma duk daren ɗaɗewa asirin ki zai tonu za ki wulaƙanta,” hhhhh.

Haka ta aiwatar da komai ba tsoron Allah, a daren baiwar Allah nan ta koma ga Allah, hmm “amma Raziƙa kin cuce ni, ina zaman zamana kin zo kin tona min asiri, wallahi kin cuce ni,” “Umma nifa ba wani cutar ki da nayi, dubun ki ce ta cika shi ya sa dama ance rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya ta mai kaya, yanzu ki zo mu tafi kokuma sai ya kawo miki takardar sakin ki,” “Raziƙa yanzu ni kike faɗawa haka,” inaga tsufa ya sa kin fara rikicewa wai ke a tunaninki za ki ƙara kwana da igiyar aure ne akanki?” in ko haka kike tunani kinyi kuskure.

“Assalamualaikum, Lantana maganar da yaran nan suka kunna min na saurara da gaske ke ce, ke ce duk kika aikata wannan mummanan aikin, kika kashe min mata kika rabani da yarana?, ina tambayar ki ki bani amsa, kece kika aikata hakan.?” “Ka yi haƙuri malam wallahi soyayyar ka ce sila, wallahi tun randa muka fara ganinka ni da marigayiya naji Ina sonka, sai dai kai ba ni ce a gaban ka ba ita kake muradi, na so na danne hakan a raina amma har bayan nayi aure na kasa zama da mijina.”

“Shi ya sa na kashe aurena kuma duk zaman da na yi bai dameni, ba sabo da bana da burin da ya wuce kai, amma sai na ga kai baka ta ni ta, matarka kaɗai kake yi, na yi bakin ƙoƙarina dan na cire ka a raina na kasa, haka itama matar taka tana kallon na shekara da shekaru ina zaman gidan mu, amma ta kasa cewa ka aureni, na je gurin boka dan ya fitar da ita sai na aureka amma, sai ya ce babu yadda za'ayi ta fita kuma ba zaka taba aure ba matukar tana numfashi a duniya, ni kuma nace ya yi duk abun da ya dace, shine ya bani turare na shafa a hannuna, ina zuwa nan na taba mata hannu, shine daddare Allah ya yi mata cikawa.”

“Bayan ta rasu naga kana wasa da maganar auren’ sai ya ce na ba sa kwana biyu, dana koma ya ce ba zai iya yi ma komai ba, amma zai yi iya yima Jamal wani abu kuma ta sanadin sa za'a yi auren, shine ya ma sa abun da ya taso da maganar hankalinsa bai kwanta ba saida ya ga anyi auren, bayan auren kuma na ga gaba ɗaya hankalinka baya kaina sai kan ƴaƴanka shi ne naje aka yi abun da aka raba ku, amma dan Allah ka yafe min wallahi son ka ne sila.”

Hmm ya sauke ajiyar zuciya, “ni yan zu babu abun da zan ce miki sai dai na barki da Allah, kije haƙin rai da kika ɗauka ka ɗai ya isheki, dan haka ki tattara kayan ki ki barmin gida na sake ki saki uku, zalincin da kika min ni da ƴaƴana Allah ya min sakayya,”

“Na shiga uku dan Allah ka yi haƙuri, wallahi duk abun da nayi sonka ne sila, kuma kaine sila, da ace tun farko ni ka nuna kana so duk da ban aikata hakan ba, na yi nadamar abun da na yi ka taimaka ka maida ni ɗakin,” “ina tunanin ba ki da hankali kin taba ganin in da aka yi saki uku aka ci gaba da zama,” “eh wallahi ana yin gyara, ka zo muje in da za'a gyara mana aurenmu,” “dakata ni ba jahili bane in ke jahilace, na ba ki awa ɗaya ki barmin gidana in ba haka ba zan sa a fitar min da ke,” ya juya ya fita.

Tana kuka haka ta haɗa kayan ta, ta bar gidan da ƙudurin ko ta halin ƙaƙa sai ta dawo.

Aisha

Ciki ya tsufa anata tu rawa da ƙyar haihuwa yau ko gobe, Yaya Sulaiman na zaune yana kallon ta, tana kaiwa da kawowa tsakanin kichin da falo, lokaci zuwa lokaci sai ya kalle ta ya kwashe da dariya, “Yaya wai dariyar me ka ke yi tun ɗazu,?” “wai ni ke dariyar,?” “a’a ba kai ba ni” na faɗi tare da hararasa, ci gaba da ƙunshe dariyarsa ya yi, waƙa taji yana yi ƙasa ƙasa, da ya ga ta zo wuce wa sai ya yi shuru, sai dai ta kalle sa ta girgiza kai dan ta san da ita ya ke.

Ta wuce kichin sadaf sadaf ta dawo ta bayan sa ta tsaya, karaf waƙar da yake yi ta isa zuwa kunnen ta, “me ciki uhm gani nan tafe” abun da yake ta maimaitawa ke nan, cije baki tayi dan takaicin waƙar nan, ta rasa me za ta yi ta huce takaici kawai sai ta fashe da ƙarfaffan kukan da ya gigita shi, “subhannal Ishat lafiya me ya sa me ki,” banza da shi ta yi ta ci gaba da kukanta, daga ƙarshema zaman dirshan tayi tana kuka, ya rasa in da zai sa kansa sai tambayar ta ya ke yi ta yi shuru ta ƙi daina kukan da ta ke yi.

“A'isha dan Allah me yake damunki, ko wani guri ne ke miki ciwo,?” duk ya firgice, da ƙyar ta buɗe baki tace kai ne, zaro ido ya yi yace “ni kuma to me na miki,? “ “ai duk na ji waƙar da kake yi kuma na san da ni kake,” “yanzu dama akan haka ki ke kuka, to ki yi haƙuri kinji Aishan Sulaiman,” juya ma sa ƙeya tayi, “haba ƴan matana ni ne fa Yayan ki, ki yi haƙuri ba zan sake ba,” da rarrashi da ban baki ya samu ta haƙura, daga ƙarshe dai shi ya ƙarasa girkin da ta ke yi.

KECE SILA

(✍️Minal saeed)

(🌹MRS BASH🌹)

https://whatsapp.com/channel/0029VbBl22NAO7RLFvcUlU2g

https://chat.whatsapp.com/FuiNx6HvwgzAheM7xh0Xci?mode=ems_copy_t

://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*(J.W.A)*

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚

















(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)

"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa

Page 2️⃣5️⃣

Hanifa

“Babyna a wace ƙasa kike son mu je honeymoon ɗin mu?” cewar Yaya Abubakar, Yaya ka zaɓa na bar maka zaɓi,?” “no my sau nawa zan ce a daina cemin Yayan nan, har yanzu ban samu wani suna ba sai dai Yaya, gaskiya daga yau a nema min suna irin na masoya,” “to Yaya wane suna kake so na dinga kiranka da shi,?” “oh God yanzu sunan ma ni zan zaɓar miki,?” ya faɗi cikin alamar tambaya, “eh mana Yayana,” “toh shi ke nan daga yau ko riƙa kirana da my Baby.”

“Baby kuma Yaya?” ta faɗi tare da toshe bakinta tana dariya, ya ce “eh mana ko nayi girma akirani da Baby ne,?” “a’a Yaya amma dai” kuma sai ta yi shuru “amma dai me?” “babu komai Yaya zan dai rinƙa kiran ka da Noor” “wow” na gode babyn Noor,” murmushi ta yi ya ce “bari na tafi Babyn Noor yamma tayi kar Abba ya yi miki faɗa ko,?” “to Yaya au Noor ka gaida min da Ummana,” suka yi ban kwana ya tafi.

A bangaren Jamal da Khadija, wata zazzafar soyayyace ke gudana mai tsayawa a rai, gaba ɗaya Khadija ta gama rikita Jamal, idan

11 / 12