Author : MINAL SAEED Category : Romantic Hausa Novels
da aka kashe shi, sun kashe kusan mutum biyar a gaba na.
Sai dai suka ga ji suka shaƙa min hodar iblis sannan nayi bacci da ba zan ce ga ta yadda ya ɗauke ni ba, ni dai na nasan ban farka ba sai da wani daren ya dawo, shima wata azababbiyar yunwa ce ta tashe ni, kamar sun san na kusa farkawa Ina farkawa Oga da kansa ya ba ni abinci na ci, “kai daga anyi kisa a gaban ka sai ka nemi hana mutane bacci, yanzu dai ya kake jin jikin ka.”
“Lafiya lau kawai dai bana jin ƙarfine a jiki na,” “kar ka damu hakan ba matsala bane rashin sabo ne za ka saba a hankali.” haka suka dage suna koya min dabaru kala kala na ta’adanci, tun in na yi kisa ina kwana banyi bacci ba, sai na sha kayan maye, har na dawo sai dai na damu kaɗan daga baya ma bana jin komai dan na kashe rai, a haka Oga ya din ga Jana jikinsa, har na zama nine na hannun damansa, kuma ya na ji da ni sosai…..
Har shawara ya kan yi da ni wasu lokutan, ya maida ni ɗan gaban go shinsa, da shawararsa na ɗakko A'isha, dan shi cewa ya yi na yi fasiƙanci da ita, ni ne na ga bazan iya aikata hakan ba, shiyasa na kashe mijinta a tunani na ya mutu ashe ya na raye, dan haka duk halin da na tsinci kaina “kece sila.”
KECE SILA”
(✍️Minal saeed)
(🌹MRS BASH🌹)
https://whatsapp.com/channel/0029VbBl22NAO7RLFvcUlU2g
https://chat.whatsapp.com/FuiNx6HvwgzAheM7xh0Xci?mode=ems_copy_t
://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake gina
Page 1️⃣9️⃣
Shi ya sa na ce “kece sila.”
“Inalilahi waina ilaihi raju'un!!.
Habib duk wannan abin da ka ke cewa ni ce sila, banga ta in da na za ma sila ba, na ɗaya ni dai ban tura ka ba, na biyu baka yi shawara da ni ba, Habib son zuciyarka ka bi, son zuciya ne sila, don haka ka koma ga Allah ka nemi gafara ni dai na yafe ma.”
Nan Kabir ya rinƙa yi musu wa’azi da nasiha, duk jikinsu ya yi sanyi harda kukansu suka ce sun amince a miƙa su kotu ta yanke musu hukunci, aka sa ranar kaisu kotu don a yanke musu hukunci kowa ya girbi abin da ya shuka.
2012, kotu
“A yau muke gabatar da ƙarar Jabir, wannan ɗan fashin da ya addabi al’uma tare da yaransa, a kan sunyi yunkurin sace ƴar gidan tsohon minister Hanifa, a hanyarta ta dawo wa daga makaranta.”
Bayan ya gama ya koma ya zauna, alƙali ya dube su ɗaya bayan ɗaya ya ce “kun ji abin da ake tuhumar ku da shi, shin kun amince ko a kwai mai wani ƙorafi ko ƙarin bayani,” suka hada baki gurin faɗin “mun amince ranka ya daɗe amma muna neman kotu mai a adalci ta dubi nadamar da mukayi ta sassauta mana.”
“A bisa duba da yadda masu laifi suka amsa laifinsu, ba tare da sun wahalar da shari'a ba, kamar yadda suka roƙa kotu ta musu sassauci, kotu ta yanke wa Jabir, Habib da sauran yaran su ɗaurin rai da rai, shi kuma Jamal sakamakon bai taɓa kisa ko fyaɗe ba, yana tare da su amma ba ya aikata ta’addacin da suke yi, kotu ta yanke ma sa hukuncin shekara biyar a gidan gyaran hali, ko a biya tara ta naira dubu ɗari biyar.”
“Alhamdulillah,” cewar Yaya Kabir domin dai shi ya yi shige da ficen da Jamal zai biya tara, don Sulaiman ya yi alƙawarin biya ma sa, ko tarar nawa ce in sun samu wanna damar, alƙali ya buga guduma alamun an gama da shari'ar su, a ka zo tafiya da su Jabir ana zuwa daidai in da Aisha take Habib ya cije a gabanta, “A'isha dan Allah ki yafe min wallahi na yi nadama, Sulaiman ban da bakin neman yafiyar ka, amma ka dubi girman Allah ka yafe ko zan samu sassauci a lahira ta.”
“Na yafe ma Allah ya yafe mana baki ɗaya,” “na gode Allah ya saka da alkairi ya baku zaman lafiya kai da Aisha, ya raya muku zuri’ar ku,” “ameen” haka aka tafi da su gidan gyaran hali, shi kuma Jamal a ka biya tarar da aka sa ma sa, suka tafi gida suna murna, bayan kwana sati biyu Kabir ya kammala ma Jamal komai na tafiya makarantar sojoji, ya tafi yana kewar Khadija duk da kafin ya tafi sai da ya sanar ma Kabir da buƙatarsa a kan ta, kuma Kabir ya ce ya je ya yi karatunsa cikin kwanciyar hankali ya ba sa Khadija.
“Assalamualaikum” a ka faɗi bayan y ɗauki wayar da da ke ta neman ɗauki
“Wa alaikasalam, amma ranka ya daɗe ban gane mai magana ba,” “eh baka sanni ba amma ni na san ka, kuma yanzu zan maka bayanin wane ne ni, ni dai sunana Aliyu tsohon dan majalisa, ni ne Mahaifin Hanifa,” “ah ranka ya daɗe barka dai ka yi haƙuri ban gane ka ba,” “kar ka damu nasan da hakan, na kira ka ne na ma godiya a kan abin da ka ma ƴata haƙiƙa na ji daɗin hakan dan na san ba dan kai ba da yanzu ban san wane hali take ba.*
“Haba Alhaji kar ka damu hakan kamar wajibine a gareni, don aikina aikin aluma ne shiyasa na ke ƙoƙarin kare duk wani mutum da yake fuskantar ba razana daga bata gari,” “ma sha Allah haƙiƙa Kasarmu na buƙatarsa irinku, Allah ya taimake ku ya baku sa'a ya tsare mana ku,” “ameen ranka ya daɗe” “idan ba damuwa ina son na haɗu da kai, sai ka sa mana lokaci da gurin haɗuwa,” “Alhaji ka faɗi in da kake so da kuma sanda kake da lokaci sai na zo na sameka ba sai ka zo ba.”
Nan suka gama magana suka sa lokacin haɗuwa da guri, “Haƙiƙa naji daɗin taimakon Hanifa da kayi, lokacin da abin ya faru na so na ganga, sai dai wa ta tafiya ta tasomin zuwa Ƙasar Cairo, sai jiya Allah ya bani ikon dawowa,” “ba damuwa Alhaji,” ina so zumunci mai ƙarfi ya ƙullu a tsakanin mu dan haka ina son na ji tarihinka,” “to Alhaji ba damuwa kamar yadda kaji kuma ka sa ni sunana Kabir,” nan ya bashi labarin rayuwarsa tas da irin gwagwarmayar da ya sha kafin ya kai matsayin da yake kai na dpo.
“Ma sha Allah haƙiƙa na yaba da ƙoƙarinka, amma yanzu shi wancan yaron Jamal da ya yi sanadin kama wa'inna ɓata garin ya na ina,” “Jamal yanzu haka yana makarantar sojoji da ke a garin Kaduna, naga takardun sa sunyi kyau, kuma yadda ya yi zama da ƴan ta'adda na tsayin shekaru, ya san wasu daga cikin lagwansu, shi ya sa nayi tunanin babu abin da ya dace da shi kamar aikin soja,” “lallai ka yi tunani mai kyau, kuma in sha Allah zan shirya mu je dan ina son ganinsa.”
Sun tattauna sosai da zasu rabu Alhaji ya yi ma sa kyauta kuma ya amshi number mahaifinsa, sun hadu da mahaifinsa suka gaisa nan ya ga ashema abonkinsa ne, tare suka kammala makarantar secondary tun daga nan ne kowa ya kama kansa, sunyi farin cikin ganin juna sosai suka tambayi juna ya bayan haduwa, ranar kamar ba su rabu ba haka suka ji.
Nan ya ce yana son su hada ƴaƴan su aure, “to Alhaji ban ƙi ta taka amma ka fara tuntubar ƴar tawa, ni kuma zanma babban ɗanka Mustapha magana akan yaje su daidaita, dama shine yaƙi aure naga alamun kamar tsoron matan yake ji,” “haba abokina ɗana fa ba matsoraci bane, kawai dai lokacine bai yi ba,” “kai dai Alhaji tare ma sa za ka yi kawai,” suka ƙara sa dariya suka tafa.
KECE SILA”
(✍️Minal saeed)
(🌹MRS BASH🌹)
https://whatsapp.com/channel/0029VbBl22NAO7RLFvcUlU2g
https://chat.whatsapp.com/FuiNx6HvwgzAheM7xh0Xci?mode=ems_copy_t
://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake gina
Page2️⃣0️⃣
Jamal ko ana gidan soja ɗan dama ma short sarvice zai yi, shi ya sa yan zu saura wata biyu ya gama, “kai abokina wallahi na kosa mu fita a gidan nan akwai fulawata da nake son na bata ruwa,” “kai Jamal wannan wace mai sa’ar ce haka,” “kai dai bari Nanah Khadija kenan ɗiyar albarka, ita ce ta sace min zuciyata a kallo ɗaya”.
“Allah ya barku tare abokina,” “ameen abokina Ina godiya sosai,” nan suka juyo dama duk maganar nan da suke yi suna gudun safe ne.
A'isha
“Haba Aisha tun safe kike kuka na tambaye ki mene ne, amma kin ƙi sanar min ya kike so inyi da rayuwata,” “Yaya to ni ya zan yi ace yara kwata kwata watan su bakwai, amma wai inada wani cikin, ni ya zanyi da rayuwata da cikin zanji ko da ƴaƴan,” “wow, kina nufin ki ce min wani cikin gare,? In ko hakane ba ƙaramin farin ciki zan yi ba.”
“What? Yaya me ka ce farin ciki fa,?” “ƙwarai my Aisha farin ciki zan yi sosai, ke ba ki san ko duk wata ɗaya za ki dinga haifar min ƴaƴa ina so ba, kin san yadda na ke son a cikamin gida da yara kuwa,?” “ Eh ai dole ka faɗi haka tunda ba kai ke shan wahalar da ake sha ba wajen rainon cikin da haihuwa.”
Ta faɗi tana share hawaye, “ dan Allah ki daina min nasarar hawayenki mai tsada, ƙi faɗa min ya ki ke so ayi,” Yaya a zubar da shi kawai tunda bai yi ƙwarai ba,” “me kika ce? amma ba kya cikin hankalin ki ko, to wallahi kar ki fara cikin nan ko shegene ina son a buna, balle kuma ɗan halal, in ko ki ka yi gangancin da wani abu ya samar min cikina wallahi sai kin yi dana sa ni.”
“Ai dama dole ka faɗi haka kuma sai na zubar da shi sai dai duk abin da zakayi ka yi,” “ ba sai kin tunamin da ba ki so na ba, na san da ha ka amma ki haifar min ɗana ko ƴata, daga nan sai kowa ya kama gaban sa, “ban fahimci kowa ya kama gaban sa ba,” “ina nufin na haƙura da neman soyayyarki dan na ga alamun ba zan taɓa samun haka daga gare ki ba.”
Da ga nan ya ɗauki fushi da ita, baya dawowa gida da wuri sai tsakiyar dare abun da ba halinsa ba, nayi nayi na shawo kansa na kasa, duk yadda na so mu yi magana ya fahimce ni ya ƙi, wata ranar Monday tun safe da ya fita bai dawo ba sai ƙarfe ɗaya na dare, yana shigowa ya tadda ni a falo zaune ina jiran sa, ya dan yi jim yana kallona sai kuma ya ɗauke kai ya wuce ɗakinsa.
Na rasa ya zanyi nabi bayansa, ina Shi ga ya na shi ga banɗaki, na samu bakin gado na zauna na fara rera kuka, dan nasan yanzu ban da hanyar shawo kansa bayan ta na tasa shi gaba ina kuka, yana fitowa ya tadda ni a haka sai shashekar kuka nake yi.
“kai inalilahi wa ina ilaihi raju'un!!, haba Aisha ya kike so na yi da rayuwata ne, fisibillahi mai na miki za ki zo ki tasani gaba kina kuka,” ni dai ban ce ma sa komai ba kukana na ci gaba da yi, ya zagayo ya zauna kusa da ni ya ce “yanzu me kike son na miki dan Allah ki daina kukan nan kinsan bana son kuka koh?.”
“Yaya ai kai ne na baka haƙuri ka ƙi haƙura, na ce na fasa zubar da cikin amma ka ƙi saurarata, duk sanda nazo dan muyi magana sai ka nuna baka da lokacina, bama gara na mutu kowa ya huta ba,” ya sa hannu ya toshe min bakina, “haba Aisha ki mutu ki barni da wa, dan Allah ki daina maganar mutuwar nan bana so.”
Daga nan ya shiga rarrashina, daga rarrashi muka sauya hanya, ni dai ganin haka nayi waje da sauri na.
Jamal
A yau shu Jamal suka kammala karatunsu, inda ya fito da stars biyu, ma sha Allah su Kabir nagani da Autar Umma, can na hango Iklima sai washe baki take, Yaya Jamal dinta ya zama soja, “wow,” Naji wata ta furta a lokacin da zazzakar muryar Jamal ta kareɗe gurin, San da yake jawabin godiya ga Allah da ya ga wannan ranar lafiya, “dan Allah Razi ji wancan gayen.”
Na juya dan ganin wa aka kira da Razi, tsaf na tsaya ina ƙare mata kallo, wata koɗaɗiyar budurwa nagani, da alamun dai farin nan na kantine ba na ta bane, ta katsemin kallon da nake ma ta sanda na ji ta ce, “ke Zee wa na ke gani kamar Yaya Jamal,” “kar dai kin san shi,?” “ sa ni na sosai ma ƴaron mijin Mamana ne wanda na ke baki labarinsa.”
“Kar dai ki ce min wanda aka kai gidan yari,?” “shi fa amma abin tambayar a nan, ni dai na san sanda na bar gida yana gidan yari, to ya aikai ya fito har ya zama soja banda labari, kinsan ta dalilin abun da Mama ta ma sa ya sa na bar gida, da na san ya dawo ai da tuni na waiwayi gida, amma yanzun ma ban makaraba.”
“Gaskiya kwata ina bayanki wannan lu'ulu'un kar ki bari ya wuce ki, dan dai kina cikine ai da ni na shiga,” “kar ma ki fara, ki shi ga ina?, dama ai macijiya ce ha kya ramin kanki,” “cool your mind mana ƙawas ai wannan ramin yafi ƙarfina, dan haka bama zan fara shi ga ba,” “ya dai fi miki.”
Ajiyar zuciya Iklima ta sauke jin tattaunawa abokan biyu, ta ce “in sha Allah Yayana yafi ƙarfin ki, tun ba ki kai haka lalacewa ba, balle yanzu da duk wanda ya ganki yaga ƴar bariki,” “Ikin Yaya ke dawa kike magana ke kaɗai,” “a’a fa ba komai,” “ok zomuje su ƴaƴa ne ke neman mu zamuyi hotuna, wai kinsan ban taɓa sanin Yaya na da zuciya haka ba, saida wata yarinya taje wai suyi hoto, kuma harda riƙe ma sa hannu aiko yana juyowa ya mareta,” “ita ma waya aike ta ba ta san Yaya ya tsani wata mace ta taɓa saba.”
Suna ƴar hirar su suka ƙarasa, a kayi hotuna sosai, ana cikin hotuna saiga abokin Yaya Haidar, yana zuwa gurin ya kafe ni da ido, “Iki kin san wancan abokin Yayan tunda ya zo nan ya kasa sauke idonsa a kan ki,” aiko ina ɗaga idona muka haɗa ido, na zabga ma sa harara tare da murguɗa bakina, murmushi naga ya yi “wow” na ce a zuciyata, dan ba ƙaramin burgeni ya yi ba, girarsa ɗaya ya ɗagamin alamar yane, da sauri na sunkuyar da kaina ƙasa.
KECE SILA
(✍️Minal saeed)
(🌹MRS BASH🌹)
https://whatsapp.com/channel/0029VbBl22NAO7RLFvcUlU2g
https://chat.whatsapp.com/FuiNx6HvwgzAheM7xh0Xci?mode=ems_copy_t
://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake