Author : MINAL SAEED Category : Romantic Hausa Novels
ke kuma tashi ki tafi, na gama magana ba ki da miji bayan Sulaiman, in dai nine na haifeki, na ɗora hannu akai na fashe da kuka ina faɗin “na shiga uku na lalace za’a raba ni da masoyina, ”tashi ki fita Aisha kafin ki kaini bango”.
Sumi sumi na tashi na tafi ɗaki na, ranar kwana nayi ina kuka, da safe naƙi fitowa na taya Umma aiki nayi zamana a ɗaki, na ci gaba da aikin kuka na, Umma ko yi tayi kamar bata san ina gidan ba, har zuwa sha biyun rana ban fito ba ga yunwa ga baƙin ciki, dan na yiwa abinci yaji.
A zuciyata babu abinda nake yi bayan tsinewa Sulaiman, dan duk abinda ya faru shine sila, da bai shiga rayuwata ba da hakan bata faru ba, ”salam alaikum, ke Aisha lafiya nake ta sallama tun ɗazu amma ba ki amsa min ba, A'isha Aisha!!!.
Firgigit na farka daga tunanin da nake, ina ganin Khairat ƙawar amana na faɗa jikinta, ”Khairat zasu rabani da shi zasu kashemin rayuwa, su Baba basa son farin cikina, na shiga uku yanzu ya zan yi da rayuwata”....
“ke Aisha mai ke faruwa ne ki sanar min, bawai ki tsaya kina sanbatu ba, ”su Umma ne wai sun ba Sulaiman aure na, ”ke Aisha wane Sulaiman ɗin?, ”wanda muka hadu da shi a bikin khadija, nayi danasanin zuwa bakin nan ashe ƙaddara ta ce ke kirana…
“Yanzu mai nene abin yi Aisha?”.
“Ni ban saniba Khairat, kinga yanzu tun ɗazu Habib ke kirana na kasa ɗaukar kiran da ya ke min, ”ki ɗauka ki ma sa bayani kar yaji a wani waje, ”hmm ina ga rayuwata ta zo karshe, dan bazan iya rayuwa babu Habib ba”.
Habib bai daina kira na ba har saida na ɗauki kiran wayar sa, sannan hankalinsa ya kwanta, “hello!!, A'isha lafiya kuwa ina ta kiran ki kin ƙi daga wayar, kin san tashin hankalin dana shiga kuwa, Aisha please ki yi min magana mana, ni dai ba abinda nake sai shashekar kuka….
“Haba Aisha ki buɗe baki ki yimin magana mana, dan Allah ki fadamin abinda ke damun ki, har ya sa ki ke zubar da hawayen ki mai tsada, dan Allah ki faɗi min damuwar ki da alamun kin daɗe kina kukan nan”.
“Yaya in ka samu lokaci kazo zamuyi magana anjima, ”ni ko yanzu ma inada lokaci ki bani minti goma gani nan”.
KECE SILA
(✍️Minal saeed)
(🌹MRS BASH🌹)
https://whatsapp.com/channel/0029VbBl22NAO7RLFvcUlU2g
https://chat.whatsapp.com/FuiNx6HvwgzAheM7xh0Xci?mode=ems_copy_t
://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake gina
Page 9️⃣
Kamar yadda ya faɗi minti goman ma bata cika ba sai ga shi ya zo, na fita ina ganinsa na ƙara sa kuka, tsabar kuka bansan lokacin dana faɗa jikinsa ba, ya maida hannu ya rungume ni yana rarrashina, ga ba dayan mu mun manta a ina muke, ni tashin hankalin rabuwa da shi ya sa ni nayi hakan, shi kuma ganin irin kukan da nake yi.
Da ƙyar Habib ya mallaki hankalinsa ya cire ni a jikinsa yaci ga ba da rarrashina, ”Aisha in ba so kike zuciyata ta buga ba ki buɗe baki ki faɗi min mai ke faruwa, ”Yaya zasu raba mu, ”ban gane mai kike nufi ba, nan na buɗe bakina na ma sa bayanin komai duk abin da ke faruwa.
“Inalilahi waina ilaihi raju'un!, Aisha yanzu maine ne abin yi, ”ban sa ni ba Yaya tun jiya bana cikin natsuwa ta, ina cikin tashin hankali mara misaltuwa, zuciyata daf take da bugawa”.
Ya shiga share zufa ya dafe kansa sai ambaton Allah ya ke yi, muna cikin wannan yanayin sai ga Baba ya dawo daga kasuwa, Habib ya gaishe shi ya amsa, ”ke Aisha shi ga ciki, haka na juya ina waiwayar Habib shima ni YA ke kallo har na shige.
“Habib har ga Allah na so ka da Aisha, amma ganin ba aure ya kawo ka ba, shiyasa na fitar ma ta da mijin da zata aura, ”Baba wallahi auren Aisha zanyi akwai abin da na ke jira ne, ”to ni dai aurar da ƴata zan yi dan haka sai kaje ka ci gaba da jira”.
“Baba dan Allah karka min haka, wallahi ina son Aisha, hasalima ita ce rayuwata, ”assha Habibu abin baiyi zafi haka ba, ni dai na faɗi ma nama Aisha miji dan haka daga yau karna kuma ganinka ƙofar gidana, kaga tafiya ta”.
Nan Habib ya durgushe a ƙasa, ya daɗe a gurin kafin ya tashi da ƙyar ya wuce gida, yana zuwa gida zazzafan zazzaɓi da ciwon kai ya rufe shi, da ga nan ya fita hayyacinsa, ranga ranga akayi asibiti da shi, ana zuwa likitoci suka duƙufa kansa, da ƙyar aka samo nunfashi sa, a takaice dai Habib ya kamu da ciwon zuciya.
Sai da ya kwashe tsayin wata uku yana jinya kafin ya samu lafiya, amma dukda haka Aisha na ransa, kwatsam na dawo daga makaranta muka ci karo dashi a hanya, muka tsaya muna kallon kallo, ”Aisha kin manta da ni?”.
”Yaya Habib ban manta da kai ba, hasalima kullum cikin tunanin ka nake, bansan ina zan gan ka ba, gashi su Umma sun ƙwacemin waya”.
Na faɗi cikin kuka, ”kiyi haƙuri A'isha nima Mahaifin ki ne ya hanani zuwa inda kike, amma har yanzu ina son ki, ”nima ina son ka Yaya, kana asibiti na saci jiki naje duba ka ranar saida Baba ya kusa kashe ni da duka”.
“Yaya wallahi banason wanda zasu aura min, ni kai nake so, ”Aisha son ki a jinina yake ba zan taɓa rabuwa da shi ba, da shi zan ci gaba da rayuwa a duniyar nan, na sa hannu na share hawayen da ke bin kumatuna, a wannan lokacin sai da muka ƙara farfaɗo da soyayyar mu, Habib ya bani ƙaramar wayar sa muka ci gaba da waya da shi a boye.
Biki saura wata biyu, na wanke ƙafata na tafi gidansu Habib nasamu mamansa, akan dan Allah su je suba Babana haƙuri, kar ya aurmin wanda bana so ni Habib nake so, Mamansa ta bani haƙuri haka na dawo gida jiki a sanyaye, tsakani na da Umma sai dai fatan shiriya, Khairat kam har ta gaji da bani shawarwari ta zuba min ido,
Bayan sati biyu na ƙara balle wa da borin nifa bana son Sulaiman, Babana ƙafa da ƙafa yaje gidansu Habib, ya samu iyayensa akan su ja ma sa kunne, yana hure min kunne, shi ya ke ƙara zugani ranar ko anga tashin hankali a gurina da gurin Habib, dan daga ni har shi a asibiti muka kwana, shi Habib ciwon sa ne ya tashi na zuciya, ni kuma jinina ne ya hau, Baba yace ko mutuwa zanyi sai dai na mutu amma sai na auri Sulaiman.
Tsakanina da Sulaiman sai cin mutunci, zagi ko ba irin wanda bana ma sa, amma sai dai ya yi murmushi yace wata rana ko ance nayi bazanyiba, saina bi shi da tsaki na wuce na bar shi a gurin.
Wayar da Habib ya bani ba wanda ya san da ita a gidan, duk wa ta magana ta nan mukeyi tun da an hanani fita, ranar da na samu dama na fita da daddare bayan sallar isha’i na je har ɗakin Habib abun da ban taɓa yi ba kenan, na je na same shi cikin damuwa, na dafa kafaɗar sa da sauri ya ɗago kai yana ganin nice ya saki murmushi, nima na mayar ma sa na ce, “Yayana mai ke damun ka, “kece silar damuwata.
“Kayi haƙuri Yayana insha Allah zan kasance farin ciki a gare ka, akwai abun da ya kawo ni gurin ka Yaya, “wane abu ne wanan?, “Yaya me zai hana mu gudu muje muyi auren mu tun da Babana ya hanani abin da na ke so, kuma ni bazan iya rayuwa da wani namiji ba bayan kai ba”.
“A'a bai kamata mu gudu ba, mu dai tsaya akan maganar mu ta ke ba za ki auri Sulaiman ba, “na yi duk iya kar ƙoƙarina Yaya har zagin Sulaiman nake yi, duk dan ya zuciya yace ya fasa amma yaƙi, Babana ya ce in dai ba shi bane ya ce ya fasa to sai na aure sa, “na sa ni Ishat amma ki ƙara nemo mana wa ta mafitar bayan wannan, nayi shuru cikin dogon tunani wace mafita ce ta dace da mu a yanzu biki saura sati biyu.
“Nasamo mafita, “wace kalar mafita ce kika samo mana?, “Yaya zaka iya komai saboda soyayyar da kake min?, “ki daina tantama akan hakan zanyi komai saboda ke, na tashi na je na kulle ƙofar ɗakin da muke ciki, shi dai Habib kallona yake yi bai ce komai ba.
Na dawo kusa da shi kamar zan shige jikin sa, “Yaya a yanzu bamu da mafitar da ta rage mana bayan na baka kaina, ya zaro ido “mai kike nufi Aisha?, “ina nufin tunda ba zasu fasa aura min Sulaiman ba, ni kuma nayi alkawari bazan kai masa budurci na ba, dan ba shi na yiwa tanadin kaina ba”.
“Aisha ko dawo cikin hankalinki mana, “a hankali na nake Yaya Habib, “kiyi haƙuri A'isha amma ba zan iya aikata abun da kike so ba, amma ina so ki yimin alƙawari komai daren dadewa ba za ki daina so na ba, sannan za ki dawo gare ni, kimin alƙawarin za ki ka she aurenki ki dawo na aureki, ni kuma zan jiraki”.
KECE SILA
(✍️Minal saeed)
(🌹MRS BASH🌹)
https://whatsapp.com/channel/0029VbBl22NAO7RLFvcUlU2g
https://chat.whatsapp.com/FuiNx6HvwgzAheM7xh0Xci?mode=ems_copy_t
://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake gina
Page1️⃣0️⃣
Na faɗa jikinsa na sa Kuka ya nata rarrashina da ƙyar nayi shiru, ni ce ban bar ɗakinsa ba sai goma na dare, ban san lokaci ya tafi haka ba, a daren dana koma gida sai da Yaya Kabir ya min duka, amma ko a jikina, da dare muka ɗora da waya, a daren nan sai da muka yiwa juna alƙawura da yawa wa’inda ba zasu faɗu ba.
A cikin alƙawarin dana ma sa harda bazan taɓa son Sulaiman ba, kuma bazan taɓa ba shi kaina ba, ya yi min alƙawarin bazai taɓa aure ba zai jira ni duk daren daɗewa ni zai aura ba wa ta ba.
Ana gobe za'a ɗauramin aure ranar kwana muka yi babu bacci, ni da Habib karshe ma shine ya ɓige da rarrashina, dan kuka nake ma sa sosai, akan yaƙi bari na cimma burina, yanzu ba shi bane Mijin da zan aura, sannan na basa kaina yaƙi amincewa.
Ranar Juma'a aka ɗaura mana aure ni da Sulaiman, haka na yini ina kuka, dama ban gayyaci kowa a ƙawaye na ba, daga ni sai Khairat sai kuma wasu ƴan ajinmu guda uku da suka zo, suma Khairat ce ta gayyato su, ana yin sallar isha'i aka zo tafiya da ni, kuka na sa ina ba inda zani, Yaya Kabir ya shigo har gida ya kama hannuna ya kai ni mota.
Haka aka kai ni gidan maƙiyina Sulaiman, mutane sai yaba kyan gidan suke yi, ni ko a zuciyata nace kyan banza, ni da an barni da masoyina, Habib ko a kangone ya aje ni zan zauna, haka nan dai su leƙa nan su leƙa can Ina jinsu suka gama suka tafi, abin takaici har da Khairat, ba wanda aka bar min.
Ina zaune a bakin godo har ƙarfe tara na dare, muna waya da Habib ina ƙara kwantar ma sa da hankali, akan ni ta shi ce ba mai raba mu, zan dawo garesa duk daren daɗewa, a wannan daren na ma sa alƙawarin ba abin da zai shiga tsakanina da Sulaiman, kamar yadda na tafi haka zan dawo ma sa.
Ina kuka mu kayi sallama da shi na kashe wayar ba jimawa, sai ga Sulamain ya shigo, “Aishatu ki taso zaku gaisa da abokaina, na watsa ma sa wani mugun kallo, “zaka iya ɗauka ta ka fitar dani idan kai ka ajiye ni anan din, “haba gimbiya sarautar mata Kema kin san hakan ba zai yuwu ba”,
“To ka je ka ce ba zan fito ba idan kuma cikinsu akwai wanda,” ya isa zai iya zuwa ya fitar da ni, na ƙarasa maganata da jan tsaki, haba A'isha dan Allah karki yimin haka, ko mene ne ki barsa tsakanin mu karki sa abokaina a ciki.
Sai kuma kayi, dan ni na gama magana, ba bu in da zani, to shikenan na ji, ya juya ya fita, nan abokan suka fara ma sa tsiya akan daga shiga ciki yaje ya yi zamansa, suda har sun tashi zasu wuce sun ɗauka ya shiga kenan sai da safe, yace musu a'a tare da basu haƙurin amarya ba ta da lafiya ba zata samu fitowa ba, nan suka musu adu'ar zaman lafiya tare da ma ta fatan samun lafiya suka tafi.
Nan ya dawo ya shigo min da kaza da drinks, na ce ba zan ci ba, ya rinƙa lallabani da su roko har sai da na ci, bai nemi komai a gareni ba koda ya nema ba samu zai yi ba, ya ce min saida safe na tashi na shirya na kwanta, na yi banza da shi ya kalleni ya girgiza kai ya fice, haka muka shafe tsayin sati biyu, ko gaishe shi ba na yi sai dai shiya gaidani, kuma na amsa ko a jikina.
A taƙaice dai ba bu irin wulaƙancin da bana ma Sulaiman, amma sai ya nuna bai damu ba, mahaifiyarsa na so na sosai haka ƙannensa da ƴanuwansa suna nuna min ƙauna, hakan ya sa bana iya wulaƙanta Sulaiman a gaban su, bawai dan ba zan iya ba kawai dan inajin kunyar su, ina waya da Habib har yanzu bawai na fasa ba ne.
Watan mu uku a haka ranar da daddare Sulaiman ya shigo ɗakina, yaji Ina waya da Habib a ranar ya amshe wayata, Kuma daga ranar ya fara kwana a ɗakina, ba bu irin baƙaƙen maganganun da bana faɗa ma sa , amma ya yi kamar bai jiba hasalima daga ranar ya fara shishigemin, dan ada banda gaisuwa ba bu abinda ke shiga tsakanin mu.
Sai ya tsiri idan ina falo shima ya zauna, idan ina ɗaki shima ya na ciki, duk inda na sa ƙafa in dai ya na gidan to yana biye da ni, abin na kona min rai ba yadda zan yi ne kawai, haka ya ci gaba da shishigemin, a yanzu yana cin albarkaci mahaifiyarsa ne har nake raga ma sa.
Ganin haka yasa sai ya dinga debo ƙannensa ya kawo su gidan, mu wuni tare da su shima kuma sai ya zaune ayi ta hira da shi, a hankali a hankali Sulaiman ya far shiga zuciyata, saboda komai zan ma sa baya fushi da ni, sai dai ya yi dariya wani lokacin kuma ya ce Allah ya shirya min ke Aisha, na kan ce ameen in da gaske kake.
Duk ƙarshen sati zai ɗebemu muje siyayya ya kashe min kuɗi sosai, duk abinda yaga ya birge sa sai yace wannan zai ma Aisha ta kyau, tun bana kula zancen sa har na zo ina murmushi aduk sanda ya faɗi haka, zuciya da son mai kyautata ma ta a haka na fara son Sulaiman ba tare da na sa ni ba…..
Soyayyar sa ya ci gaba da cusamin a zuciyata, ba tare da na sani ba, lokacin da zan farka sonsa ya min illah, har na fara mantawa da Habib, a rin yawon da muke fita da yamma wata rana mun fita sai motar Sulaiman ta samu matsala, ta bayan layin mu muka biyo, sai ya ce tun da munzo kawai mu karasa gidanmu ya gaida su Umma…
KECE SILA
(✍️Minal saeed)
(🌹MRS BASH🌹)
https://whatsapp.com/channel/0029VbBl22NAO7RLFvcUlU2g
https://chat.whatsapp.com/FuiNx6HvwgzAheM7xh0Xci?mode=ems_copy_t
://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu